← Book details Ali Dan Tsoho Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 124

Sashe 52

Ali Dan Tsoho Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*Pls ki bani amsa meke damun ki? Tabbas bakida lfy, nasan zakiyi mamaki ni waye ni mutum ne kamar ki me son ya faranta miki har karshen rayuwarki, yana son yaga kinyi farin ciki yasa ki manta damuwar ki ta baya har abadan, ni sunana Deen Kurmane bana mgn amman ina ji idan an mani, nayi kuskure ne arayuwata cikin rashin sani, shine kowa ya tsaneni baya sona, dan nayi wani laifi bisa kuskure amman an kasa fahimtata.... Ina son na zama abokin ki abokin shawaraki kafin auranki da Sageer bana son ki ɓuye min kome dake damunki a rayuwa, kuma kar kiyi kokonto samana Mubee ki rinƙa kirana ko na kira ki kina mani hiri ni niko ina maki msg dan ina ji amman bana mgn se murmushi kawai, Ina so ki zama me tawakali da yafiya ki amshi kaddara da hannu biyu duk lkcn da Allah y jarabe ki, bisa wani mummunan abu ko akasin hakan, zan so ki yafema duk wanda ya cutar dake ko yana dane ko baya sane, yanada kyau yafiya Baby Mubee, Baby Mubee pls yanzu faɗamin me ke damunki? Idan baki faɗamin ba to shikenan zan kasance cikin bakin ciki, da kuma rashin walwala ne na har abadan bana fushi dake, neman hanyar faranta miki nake, amman ina son ki faɗamin me ya sameki wlh naji a jikina bakida lfy, Babyn Sageer faɗamin ko nayi kuka, gani Kurma bana mgn kuma banida ƙawa wacce zata tausaya min ta lallasheni na faɗa mata damuwata ko ta faɗamin damuwarta na bata shawara.😰😥*

Horn ɗin da Haladu yay ne bakin get ya hana Mubina kiran sa, bayan ta gama karanta sakon tayi saurin tura masa sako kamar haka, ```Allah sarki ɗan Kurma wlh naji tausayin ka ya mamayeni, me kama mutane suka tsaneka kaida baka mgn ma?😭 wlh ina tausayin maras baki,amman me yasa kace na yafema duk wanda ya zalumceni...? Tab wani abun baya yafuwa ɗan kurma,yanzu na shigo gidane amman zan kiraka se na faɗama ina da lfy ko banida ita dan yanzu ma dauriya ce nake😥kuma za na tambayeka,inda ka sanmu nida mijin da zan aura... Ɗan Kurma karka damu zamu rinƙa hira wlh naji mugun tausayin😭 ka gashi kana wata ƙasa bare na rinƙa dafama abunci nasayama duk abinda kake so kuma nasa a dena jin haushin ka... Tinda bakada baki, kuma Namaka hira me dadi bye se na kira zuwa anjima, yanzu yunwa nakeji😭 ``` Haka ta tura masa sakon. Dede lkcn Haladu yay parking cikin tafkekiyar rumfar ajiye motocin. Mubina ta saka wayar a jaka ta buɗe motar ta fito.

Haladu yace"Allah huta gajiya Hajjaju."Mubina ta yamutsa fuska, ta zubar da yawunɓda ya cika mata baki, batayi mgn ba ta nufi cikin gida. Haladu ya mufi gun Baba megadi yana dariya, Baba megadi yace"Wai anya Haladu ba son ƴar masu gida kake ba kuwa?"
Haladu zaiyi mgn yaga Mairo tana kallonsa ta leko daga ɗan kewayansu dan tana laɓe. Haladu kansa ya ɗauke ya zauna saman bencin baba megadi suna hira, Mairo ta koma ciki tana cizon baki.

Da sallama ta shigo parlon ba kowa se Ablah, Ablah ta amsa da harshen larabci tace"Oyoyo Mubinat sannu ya jikin naki?" Mibina jifa tayi da jakar ta isa gun Ablah ta zauna ta kwanto jikinta ta cusa kanta kirjinta tana sauke numfashi.

Ablah ta taɓa jikin nata tace"Baby tashi maza kisha magani jikin ki akwai zafi sannu."Mubina ta shige jikin Ablah tana lumshe idanu can ƙasan makoshi tace"Ablah ina Mamu nah ta shiga? Da Aunty Amrah nah?" Ablah tace"Sun fita su uku sunje can gidan su Nusaiba ɗin." Mubina ta miƙewa zaune tace"Shine suka ki jira na? Hum ba kome , Ablah wlh yau ina son cin taliya fara da man Ja da yaji." ta faɗa tana haɗe miyau tana miƙewa. Ablah ta miƙe ta kama hannunta suka nufi kitchen. Laure na tsaka da aiki suka shigo, Ablah tace"Laure ki dafa ma Baby taliya fara ki daka yaji kisoya manja yanzu fa muke so."Laure tace "an gama Ablah." Ablah tace"Yauwa Laure." Mubina dai batayi mgn ba kallon su take, bakinta na tara yawu sbd yanda taji son abin sosai a ranta. Ablah ta kama hannunta suka fito. Mubina tace"Ablah bari nayi wanka wlh zafi nake ji sosai na saka karamar riga na fito." tana faɗar haka ta ɗauki jakarta ta haye sama tana jin wani ɗan jiri jiri, ta dai daure ta haye saman. Tana shiga ta ajiye jakarta sama bed ta tuɓe kayan jikinta ta nufi bathroom.

Ta jima sosai tana wanka da shower, kafin ta É—aura towel ta fito, ta shirya a gaggauce ta saka riga iya guiwarta milk coulor me kyau, gashin kanta na É—igar da ruwa haka ta É—aure shi da ribbon ba tare da ta busar dashi ba haka ta fito.

Tana zuwa ta isko Laure ta kawo mata taliyar a plate, Ablah na riƙe da plate ɗin se kace zai gudu. Mubina ta zauna tana murmushi tace"Ablah har ta gama min ashe?" ta faɗa tana amsa ta zura hannu ta yamutsa yajin dake gefe ta kai bakinta ta fara ci. Ablah tace"Baby yajin yayi yawa fa." Mubina bata saurari Ablah ba se da taci tayi dam. Tana share zufa goshinta tana tanɗe hannu. Ablah tace"Wai Baby zako kuyi dambe da yaji nan anji ma."Mubina ta miƙe tana tanɗe hannu ta nufi kitchen ta wanko hannunta, ta ɗauko bottle water me sanyi ta fito, tana sha ta kwanta tayi matashi da cinyar Ablah, batayi mgn ba ta lumshe idanunta. Ko 4 minutse bata cika ba se bacci. Ablah tana shafa mata kanta wanda ke jiƙe da ruwa, tana mata hira bata san ko tana bacci ba...

Ummah zaune a parlo ita da Safiyya suna hira, dan Hafast da Sumaiyya sun tafi gidajansu sunyi ta jiran Abbu bai shigo ba... Su Abbu ne suka shigo da Ibrahim da sallama. Ummah ta amsa tana cewa"Yau megida kace ni zan baka ruwan alwalla."ta faÉ—a tana murmushi. Abbu yace"Safiyya se na bulaleki, kika cema Ibrahim da goggo kar a faÉ—a min se na ganki ko?" ya faÉ—a yana mata harara wasa. Ya isa ya É—auki Suhailat kamar yar yaye yana mata wasa. Ibrahim yace,

" Ummah ai kuwa dai ke zaki ban ruwan alwalla, ya gida ina Samha ne?" ya faɗa yana kallon Safiya yana dariya. Ummah tace"Tana gidan goggo..." Abbu ya ajiye Suhailat yace "Ibrahim muje kaji ana kiran magarib."Ibrahim yace" Ai ko muje to daman tambayar ta zan yi bari mana idan mun gama sallah na biya gidan Hafsat , dan bata kasa sanin wani abu." ya faɗa yana kallon Abbu. Abbu yayi gaba, Ummah tace"Wai mgnr ce?" Ibrahim yace"Eh ina so gobe na fara binki ce insha Allahu, na tafi." ya faɗa yana bin Abbu dan sunyi alwalla a waje. Ummah da Safiyya suka miƙe domin zuwa yin sallah.

*Saudi Arabia* cikin garin Makkah, Misalin karfe tara dai-dai na dare agogon Saudiya, wanda a lkcn karfe 7:00 pm agogon Nigeria da Niger, kuma adede lkcn ake kiran sallah magarib a Niger, wanda su kuma can sun gama sallah isha'i. Zaune yake saman wasu dirka-dirkan kujeru masu masifar laushi da kyau, a wani ƙayataccan parlo, wanda ya gaji da haduwa palon kade zaka kalla kasan lallai ƙasar larabawa yake, duk da babu abunda suma basu malkaba a ƙasar su, wani babban santre table ne gaban sa na glass, wanda yake shaƙe da kayan marmari iri-iri sanye yake da Jallabiya fara tas har ƙasa da hirami a kansa wani irin kyau Kamal yayi na ban mamaki, cikar girmansa da zatinsa da kuma kwarjininsa na nan, ya tara ƙasumba, yayi wani irin kyau, banda kamshi babu abinda ke tashi a jikinsa, dama parlon baki ɗaya, carbi ne riƙe a hannunsa yana ja, waya hannunsa, yana dannawa alamu ya nuna kamar yana dan cikin damuwa, dailing ɗin wata number yay ya miƙe tsaye, ya kara wayar kunnensa, ya nufi hanyar bedroom cikin wani irin taku na isassun maza tare da izzar da ta zame masa jinin jikinsa...

*Wannan littafi na kudi ne ki biya kiyi karatu cikin salama, da kuma kwanciyar hankali, duk me so zaku tuntuɓeni ta wannan lambobin*
*👉🏻+22792589446/ +22796515805*
[03/08, 9:00 pm] +234 703 561 1565: *KAMAL NE*

*Book 1*

*Bismillahir Rahamanir Raheem*

3️⃣0️⃣

Yana shiga cikin wani haÉ—adÉ—an bedroom, ya zauna bakin wani makeken gado ya zare wayar daga kunnensa, ya zuba mata tsumammun idanunsa.

Sake dailing ɗin number yay Sunan Babyn Sageer ke yawo saman screen ɗin wayar, ganin ba'a dauka ba ya tsinke kiran yay dailing ɗin number, Sageer, lkcn yana cikin masallaci wayar tana cikin gida. Kamal ganin ba wanda ya dauka cikin su biyu yasa ya ja tsaki yayi wurgi da wayar saman bed, ya dauki ɗayar wayar ya kira wata number, bugo ɗaya aka dauka da sallama, cikin zazzaƙar murya shi yace.

"Momy ina yini fatan kowa lfy?" murmushi ta saki tace"Lfy lau my son ka saki ranka ka ajiye hankalin ka, karka saka damuwa a ranka, pls my son kaji, kuma kome zai zo da sauki insha Allahu ni yanzu mgn ta gaskiya ina so ka faÉ—amin meye dalilin da yasa Abbu ya kore ka daga gida? wlh na maka alkawali kamar yanda nama babu wanda zai san inda kake har sai ka so hakan.... Tinda ni na yarda da kai nasan bazaka aikata abin Allah wadai ba...?"
Chapter 52 · 0% Book details