← Book details Ali Dan Tsoho Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 124

Sashe 45

Ali Dan Tsoho Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Abbu da ummah suna mata sannu kallonsu kawai Mubina take tana hawaye. Umpah ya miƙe ya shimfiɗa masu dadduma, Mamu ta zaunar da ita, Umpah ya hado tea me kauri ya zauna ƙasa ya rungumo Mubina ya bata taki sha tana kuka, daket Ablah tasa baki ta shanye, cikin ikon Allah Ablah ta hado mata farfesun kayan cikin dasu Mamu suka kawo suna mata wayo da dubara taci kadan tana rungume jikin Umpah. Sunji dadi sosai matsalar su rashin tafiya da batayi. Bayan sun samu taci Umpah zaunar da ita sosai ta kalli alƙibla yace tayi sallah, ya faɗa mata tun jiya suke nan. Sallah Asubah kawai ta iya bata rama sauran najiba, jikinta ya ɗauki rawa gab-gab tana rawar sanyi. Umpah ya kirawo Dr Khadija, nan ta ɗubata ta tambaya"Ina maganin an bata"?Ablah tace"Aa ga shi" Khadija ta amsa ta ballo, Mamu ta ɗauko ruwa nan taba Mubina maganin sai rawar sanyi take, allurai ta haɗa ta mata ta sake ɗaura mata drip ta fice. Ba jimawa se bacci tana sauke ajiyar zuciya tama zabura...

Umpah tagumi yayi Mamu na sharɓar hawaye. Ablah tace "Ai kam muna cikin masifa Mubina Allah ya baki lfy Amin." Umpah ya ɗago yace "Abubakar dan Allah kuje ku sami koda tea kusha ku huta zuwa yamma sai ku dawo pls."Abbu bai musaba ya miƙe Ummah tace da Mamu"Allah ya kara sauƙi sai mun dawo." Mamu ta amsa da "Yo Fatima." Abbu yama su Ablah sallama Umpah ya miƙe ya raka su har mota, sai da suka tafi ya juyo ciki. Ablah tace"Abdul ka maida kanka sakarai haka kawai a zalumcemu ka hana ayi magana sbd Allah?" Ya kwanta kusa da Mubina yana riƙe da hannunta jikin nata da zafi har yanzu. Yace"Ablah ai mun gama magana dan Allah abar zancan" shiru sukayi kowa ya kwanta domin ramuwar bacci kafin Mubina ta tashi... Kabeer kasan cewar ajiya abin ya faru da yamma bayan ya shigo ya fita tafiyar gaggawa ta same su zuwa Naimey meeting a jirgi baya da labarin kome, sai yanzu suka diro garin yana fita daga Airport gida ya nufa a texi. Yana shigowa parlon ya gansu wani iri sunyi jigun Amrah tayi tagumi sunyi jugum. Sallama yayi ya, Amrah ta miƙe da gudu ta faɗa jikinsa ta fashe da kuka. A rikice Kabeer yace"Subahanallahi lfy kuwa Amrah?" Majeed zaiyi mgn Sabbela ta kwaɓeshi tace"Kabeer sannu da zuwa je kayi wanka ka nutsu zanma bayani."ta faɗa tana janye Amrah daga jikinsa. Kabeer yace "Allah yasa lfy ina su Mamu da umpah da Auta baby?" ummi Sabeela tace"Eh je ka fito dai." jikin kabeer a sake ya shige ciki gaban sa na faduwa. Ummi Sabeela tace"Amrah gaskiya ki daina irin haka yaya mutum daga zuwasa bazaki bari ko ruwa yasha ba ki masa mugun lbr , kiyi hkr kalli duk abin yaya Abdul akan Mubina amman ya fauwalama Allah..."Haka tayi ta mata nasiya har jikinta yayi sanyi. Kabeer bayan yayi wanka ya shirya ya fito nan ummi Sabeela ta masa bayani a nutse da duk bayanin da Umpah yayi. Kabeer ya shiga mummunan tashin hankali a rikice ya fita sai da Majeed yabi bayan sa nan suka shiga mota sai hospital. Suna zuwa suka iske su Umpah na bacci, Kabeer ya saka Mubina gaba yana kuka gashi babu damar yayi karan Kamal ko tozarta shi idanun duniya duba da abinda Umpah ya faɗa, kuma hakane tabbas ƙanwarsa zai tozarta. Haka suka zauna suna jiran tashin su...

Sageer yana fita daga hospital direct gidan su ya nufa da Kamal. Suna shiga parlo da sallama su Nini na zaune a parlo ta amsa sallama tace"Wai Kamalu ango yaushe rabon mu dakai anyi sati fa?" Sakina ta karasa da gudu tana cewa "Oyoyo yaya kamal i miss u" ta faɗa tana kama hannunsa. A mugun zabure ya warce hannunsa yaja da baya da sauki yana girgiza kai. Nini tace"Au ƙanwar taka sai kace mai wutar lantarki a jikinta dai." ta faɗa tana dariya. Tace "Sakina kuma ake gudu yau?" sakina ta shagwaɓe fuska ta sake nufar Kamal tana cewa "Barshi Nini dan kar na koma gidan sane idan anyi auran shine zai wani fizge hannunsa..." Ai Kamal yana ganin Sakina zata sake kamashi yayi baya a guje. Sageer yay zafi nama ya kamoshi. Yana cewa "Kai wlh ka fiye ragwanta wai Nini kinsan meye? Kawai fa yanzu ne a makaranta yaje garin yanka mangwaro ya wulɓe hannu shine jini yaƙi tsayawa na ɗauko shi na masa wannan maganin na gargajiya, gun shine Sakina ta taɓa gurin." Nini da Sakina sukayi dariya Nini tace "ɗana ba rago bane muga gurin zo nama Addu'a..." Sageer yace"A'a zan saka masa magani, bari mu shiga ciki." sai lkcn Kamal yace"Nini ina yini ya gida ina su Abba?" Nini tace jeka dai a dubaka kazo mu gaisa ɗin keko Sakin ai kinyi barna ashe gun ciwo kika taɓa." Sageer ɓangaransa suka shiga.

Suna shiga ya haɗa masa ruwan wanka yasa ya shiga yayi wanka, ya ɗauko masa shadda blue mai shegen kyau da tsada ya fesa turare. Yana fitowa ɗaure da towel ko jikinsa bai goge ba yana shirin maida kayansa Sageer ya hana shi ya saka wannan. Ya kama hannunsa suka nufi kan dining ya hada masa tea da soyayyan dankalin turawa da kwai. Da farko kiyawa yayi saida Sageer ya masa wayo zai faɗawa Nini kome sai tazo ta lallaɓa shi, dole yaci ba dan dadi ba. Saida ya gama Sageer ma ya sha tea kadai suka koma ciki yay wanka ya shirya suka fito sukama Nini sallama, suka tafi Sakina na miti Kamal yau yaki kulata...

Sageer can gidan goggo yakai Kamal lkcn har ya fara jin bacci, dan Sageer ya saka masa maganin bacci a tea dan ya samu yayi bacci ko nutsuwarsa ta dawo. Bedroom suka shiga Sageer na zaune Kamal na kwance, sai da bacci ya ɗauke shi ya fito yama goggo sallama ya tafi makaranta. Goggo kuwa ta shirya ta tafi hospital duba Mubina. Lokacin da taje su Abbu basa nan su Umpah sai tiƙar bacci suke se su kabeer shida Majeed suka gaisa ta zauna jugum tana kallon su cike da tausayi.

Su Abbu suna zuwa gida Samha da zakiyya suka saka su gaba da kuka ina Kamal ko an kamashi ne? Nan Abbu ya faÉ—a masu kome, suka ce zasu ganin Mubina Abbu ya hana dan baya so Umpah yaga kamar wasu sun sani duk da yasan a gaban su akayi kome, ya gargaÉ—e su ko hafsat kar su faÉ—ama da sauran Æ´an uwa... Dole suka hkr. Wanka Abbu yayi ya kwanta domin ramuwar bacci duk da baccin baya idanunsa. Ummah kusan sa ta kwanta ta rungumeshi tana kuka. Daket ya samu ya rarrasheta tayi shiru nan bacci ya kwashe su rungume da juna...

Basma tana makaranta shiru bataga Mubina tazo ba har aka fito break, duk hankalinta a tashe gashi ta kira wayar a kashe, dan Kamal ya kashe wayar yay har wayar shi duka har yanzu wayar na motar shi. Basma ana tashe, kai tsaye gidan su Mubina ta nufa. Tana zuwa ta isko su ummi Sabeela da Amrah saman kujeru suna bacci, Amrah ta tasa a hankali tace"Aunty Amrah ina Mubina lfy yau bataje makaranta ba kuma wayarta a kashe?" Amrah ta buÉ—e idanu me cike da bacci tana murzawa, tace"Ayyah ai sunyi Æ´ar tafiya ne ita da umpah da Mamu maybe babu Netrowk ne inda suke É—in." Basma tace "Wai hankalaina ya kwanta yo jiya ba'a gantaba har bayan magarib yau naji shiru to bara na wuce gida nasan ana samun Netrowk zata kirani, anty na wuce gida ummi bacci ake? yaya Kabeer bai iso bako?" Amrah ta saki fuska tana murmushi tace"Yazo ya fita ne." Nan ta raka Basma har mota suna fita ta kira Kabeer waya ta ma kasheÉ—in kar fa ya kuskura ya faÉ—ama Basma kome ko ta tambaye shi yace sunyi tafiya. Ya amsa da to...

*************** ******* ***************
Chapter 45 · 0% Book details