← Book details Ali Dan Tsoho Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 124

Sashe 36

Ali Dan Tsoho Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Mubina tana shigowa cikin gidan, Haladu ya fara cewa"Ah Hajjaju hijab kuwa yayi kyau."Baba megadi yace"Haladu baka rabo da tsokana ko?" idi me bama plowers ruwa yace"Ai ya santa sarai ba raga masa zatayi ba..."Mubina bata juyo ba tace"Baba megadi baba idi ku barshi wlh yaci bashi zan kamashi."ta faÉ—a tana shigewa can ciki. Dariya suka yi, Haladu yace"uhumm kyaji dashi an fita da wando an dawo da hijabi yanzu haka Kamalu ne zai korota ya temaka ya suturtata yarinya se kace haihuwar jinnu..." dariya dai suka yi basu tanka masa ba ya kari mitarsa.
Parlour ta fado kamar an nasota tayi wurgi da jakar tana kiran"Mamu kina ina Mamuuuuuuu nah..." ta faɗa tana diddira ƙafa. Mamu ta kaɗo da gudu daga kitchen tana hadama Ablah shayi. Mamu tace "Mubina lfy ya nagan ki da hijabi?" Mubina ta afka jikin Mamu tana zumburo baki tace"yo wannan gurgun bane yayi ta marina ya samin hijab ya koroni gida Allah sai na faɗama umpah, Ablah kina ina zo kiji abinda akamin Mamu kalli fuskata..."Mamu ta rufe mata maki tace"don Allah yarinyar kirki karki faɗa yi shiru abinki muje na dafa maki indomie da kwai kici kayan ki , ga shayi nan me dadi ina dafawa." ta faɗa tana shafa fuskar Mubina tayi jajur alamar taci mari. Mubina ta shige jikin Mamu tana diddira ƙafa tace"to Mamu goyani ni wlh se kin giyani ko na faɗa masu" Mamu tace "Ok hau muje ai ba yauni gareki ba."ta faɗa tana sunkuyawa, Mubina tako ɗare bayan Mamu tana ɓangala dariya Mamu ta miƙe da ita babu wani nauyi atare da Mubina amman duk da haka Mamu se da tace"Woshhh baby."Amrah ce ta sauko tana riƙe baki, Ablah tana fitowa ta tsinkayo Mamu ta goya Mubina tana kyalkyata dariya, taji daɗi sosai tace"Yauwa Nusy ko ke fa yarinya karama agida ba'a kula da ita a gida." Kabeer yana sanyo kansa parlon yay tozali da Mamu ta goya Mubina, yace"Kai Mamu salon ta kashe mana ke katuwar budurwa zaki goya haka?" Amrah ta karasa ta kama hannun Kabeer ta masa mgn ƙasa-ƙasa, ya bushe da dariya yace"Au haka abin yake?" Ablah tace"Amrah munahirci ne zai kasheki ƴar banzar yarinya , yanzu wannan baƙin ciki kike yi ko?" Amrah ta murguda mata baki taja hannun kabeer suna bin su Mamu. Mamu a kitchen ta ajiye Mubina, laure na masu dariya, Mubina na manne jikin Mamu, Kabeer dariya yayi sosai ya wuce part ɗinsa dama ɗaukar wata laptop yazo. A haka Mubina na manne da Mamu har ta haɗa shayin ta bata ta kaima Ablah, ita ko ta haɗa mata indomie da kwai ta soya mata.
Jikin Ablah take a zaune tana cin indomien tana haɗawa da shayi tana zuba santi tace"Mamu ki koyamin irin wannan suyar idan nayi aure na ma oga ko ba haka Ablah nah?" ta faɗa tana ɗagama Amrah gira. Mamu tace"ke dai ci abinki ba wani surutu ba..." Basma ce ta shigo da sallama. Mubina ta miƙe ta taro ta tana dariya. Basma ta zaro idanu tace"Ni inacan ina larura ashe ke ko a jikinki?" Ablah tace"Me ya faru ne.? Mamu ta ƙif tama Basma idanu. Basma ta kara so ta gaishe su tace"Ablah daman na zata bata iso ba daga makaranta dan direban mu ya riga nata zuwa." Ablah tace "Ai Haladu ya cika shiririta sakare ne." Amrah tayi dariya ta miƙe. Mubina tace"zo kici indomie tayi dadi" ta faɗi tana zubama Basma shayi ta beƙa mata. Nan suka baje suna ci suna hira Basma na mamakin taurin rai irin na Mubina... Umpah ne ya shigo da sallama. Mubina ta miƙe ta tarbo shi da gudu ta ruƙumƙumeshi tana dariya. Umpah ya rikota yace"Baby ya naga fuskarki tayi ja lafiya?" zatayi magana Mamu tayi saurin cewa"yo ba dole ba goyo fa tasa na mata tana gurza fuskarta bayana." umpah yace"Ah lallai yau baby tasha bayan uwarta." ya faɗa yana janyo hannunta suka zauna yana gaishe da Ablah, tana murmushi ta amsa tana masa sannu da zuwa. Basma tace"umpah ina yini." umpsh yace"Basma ya gida dasu isma'il mun hadu dazu gun meeting." Mubina ta miƙe tana cewa"umpah bari na zuba maka shayi yayi dadi umpah kaji kuwa indomie da kwai da Mamu ta soya min wai dadi , wlh yau ko dan naji yunwa ne se naji tafi ta kullum." Amrah tace "umpah ni inata sannu anyi banza dani" hannu umpah ya bata ta ko kama ta zauna kusansa. Yace"to shikenan ko?" murmushi tayi. Mubina taba umpah shayin tace"Basma tashi muje sama muyi hira." Basma ta miƙe suka haye sama. Ai fa Mubina se da ta faɗama Basma kome... Basma tace"Tab yanzu da sai ki zauna a matsayin makauniya ki kawoma karatunki cikas?" Mubina tayi fari da ido tace"Ai Sageer yace bayan auran Aunty zai tayani na rama. Basma ta bushe da dariya dan tasan wayo Sageer yay mata. Mubina tace"uban waye kike ma dariyar ne?" Basma tace"irin yadda zamu rama ne nake hasasowa yana fitsarin wuya..." Mubina ta bushe da dariya tana riƙe ciki... Haka suka kasan ce se bayan magarib Mubina ta raka Basma gida Haladu ya kaisu a mota.

Misalin karfe goma na dare iyamu da Leeza suna zaune leeza tace"amman ina ga kamar wannan ba mafita bace ko ya kika gani?' iyamu tace"wlh itace zamu bi na rama dan wannan hanyar itace mafita zai fi jin kunya har ma ya tsani kansa da kansa bayan haka na ruguza farin cikin sa kuma anyi biyu babu🙅🏻‍♀️ ni ban samu ba ita bata samu ba ,🙅🏻‍♀️kuma sunan sa ya ɓaci duk bazan ɗsu video ba bana son gani..." dariya suka saka suna tafa hannu, leeza tace bari kiji yanda abin zai faru kafin su ankare" ta kama kunnen iyamu ta mata raɗa. Ihun dadi ta saki tace "na fa yarda ai in dai zaka ɗauki fansa cire kishi a ranka kawata." dariya sukayi suka yi suka tafa hannun nan suka shiga yadda zasu yi abin ta ruwan sanyi ba tare da an ankare ba...

Yau saboda tsabar bacci da Kamal yake ji ko zama parlo baiba tinda ya ci abuncin dare, wanka yayi ya kwanta sbd wani irin baƙon yanayi da yake ji a jikinsa wayoyin sa ya kashe ya kwanta. Ko da ummah ta shigo domin taji lfy yake kuwa? Ta isko ya naɗe cikin lallausan bargo yana sharara bacci. gyara masa kansa tayi saman pillow ta rage gudun Ac ta kashe wutar ɗakin ta fice. Mubina ma da wuri tayi bacci suna tsaka da hira da Sageer wayar ta suɓuce mata ta fadi saman bed, jin saukar numfashinta yasa Sageer kashe wayar. Amrah ce ta jima tana jiran kiran Kamal dan bayan isha ya kirata yana tafe kuma taji shiru, kiransa tayi taji a kashe, itama a haka har bacci ya ɗauketa...

*************** ******* ***************

Bayan kwana biyar
Tinda abin nan ya faru, Mubina ta ɗauke kanta daga duk wani abu da ya shafi Kamal, ko makaranta bata yarda ta kalleshi idan ba ya kama dole ba yana masu lecture ba to ba yanda ta iya idan ya kama dole se magana ta haɗa su, ko tambaryata a kan wani abun dole take bashi amsa dan karatun ya kawota... ko wayar Amrah da take sata ta kira shi zaman Amrah ta daina, sabgar gabanta kawai take. Shiko Kamal sosai yanzu yake son mgn da ita ba kamar baya ba ko yay ta kallonta yana sakin murmushi shi kadai, dan rigimarta ta fasa bashi haushi, yau tsawon kwana uku baya fashin zuwa zance, kawai dan ya rinƙa ganinta da dare yadda take ninniƙewa jikin Mamu, dan da yaje se ya shiga ya gaishe da yan gidan. Sageer kuwa sosai yake ba Mubina kulawa ganin tana ji dashi sosai kuma babu namijin da yake gabanta se shi. Yau ake kawo kayan Amrah tin safe gidan su Kamal yake cike da ƴan uwa da abokan arziki anata shiga ganin kaya, anata sanya albarka dan Kamal ya kashe maƙudan kudi ba kadan ba, babu irin kayan da bai sakawa Amrah na yayi ba, karfe 4:30 pm za'a kai kayan, gidansu Amrah, Kamal baki har kunne yaji dadin yadda ake yabon kayan. Su Samha kuwa anata famar ɗinka kayan anko na kece raini. Gidansu Amrah tin safe cike yake da ƴan uwa Mamu da Sabeela abokiyar haihuwar Umpah da yaranta sunzo daga London gida ya hargitse da murna, Mubina kuwa ana makaranta daga can tace gun tella zata wuce bazata dawo ba har yanzu ko anko ɗaya bai ɗinka mata ba! Anko kuwa har kalla hudu ne less material shadda atamfa, ga wani uban narkeƙen less biyu da umpah ya kawo mata, duka sunagun Mezamani telan mata...
Chapter 36 · 0% Book details