← Book details Ali Dan Tsoho Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 87 OF 124

Sashe 87

Ali Dan Tsoho Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Bayan su Ummah sunyi sallar magarib, su Hafsat suna zaune a parlo, Ummah sauko tana riƙe da haɓa, tace.
"Ikon Allah Goggo ashe yaron nan yana london? Yanzu nan ina gama sallah ya ƙirani wai na masa Addu'a yaje wani aiki, shida yace yana Germany. " Samha tayi caraf tace"Ummah bani number na ƙirasa kai yaya Kamal ya manta dani."ta faɗi a shagwaɓe tana rungume Ummah. Ummah tace"Jeki wayar na ciki ɗauki."Da gudu Samha ta nufi sama. Goggo tace"Hummm ba naƙira mahaifinsa ba na faɗa masa ya ɗauki abin dariya, wai wasa yake min, shiko Kamal fa da gaske yake, yace zai sace tafa ya gudu saudiya a ɗaura masu aure." Hafsat tace"To don Allah meye a cikine, ai ni tare muke kome..." Sumaiyya zatayi mgn Abbu ya shigo da sallama. Goggo tace"Wai ina kuka tsaya ina ibrahim ɗin? Shin ko ƙarya yake mana ne?" Abbu yace.
Goggo kuyi haƙuri mun tsayar daku tin yamma, wlh muna cikin hidimomine, kuzo muje gidan Abdulrahim, zakuga abin mamaki." Goggo tace"To muje."Ummah tace"Allah yasa lafiya, ko vedion da ibrahim yasa aka dauko ne?" Abbu yace.
"Kumuje dai ana jiranmu, ina Samha?" sai gata tace"Gani Abbu" Yace "Muje har ke."Su Hafsat ne gaba² suka dumguma gidan Umpah.
Can kuwa parlon baƙin na gidan Umpah su Ablah ne da Mamu sai Kabeer da Amrah da Sageer Ibrahim da Umpah da Zabairu, isma'il da Lubah sai Basma. Dan Umpah yay ƙira Sageer da Isma'il ɗin yace suzo tin kan su shiga masallaci. Su Abbu ne suka shigo da sallama. Nan aka gagaisa da jama'a Mamu dai kallon ikon Allah take tana raba idanu, da makin wai vedion ɗin ne nasu Mubina da Kamal zasu nuna? Umpah yayi gyara murya yace"Ba kome yasa nace mu haɗu anan ba sai dan kuga abin al'ajabi" ya faɗi yana kallon ibrahim yace"Ibrahim bismillah jona masu a jikin Tv kowa ya gani." ibrahim ya miƙe ya haɗa kome ya jona ajikin Tv. Kowa hankalinsa ya maida wajan kallon abinda su Mounkaila suke faɗi akan abinda sukama Kamal da Mubina da murnar barinsa gari arzikin su ya bunƙasa. Kowa ya firgita ya tsorata a gurin, hankalinsu yayi mugun tashi. Ummah ta fashe da kuka ita da Samha. Ummah tace"Allah ya isa ban yafe maku ba duniya da lahari wallahi najima in mamkin wannan lamari ɗan yau ne kawai da baka shedarsa..." Mamu ta fashe da kuka Tana cewa"Allah ya tsine maku ya wulaƙantaku kamar yanda kuka wulaƙantamu." Ablah Ma kukan take tace"Allah ka saka wannan bayin Allahn acikin bala'in da yafi wanda muka shiga..." Lubah dasu Hafsat suka shaiga basu baki suyi haƙuri. Goggo Rumana kasa kukan ma tayi tayi tagumi tana kallon ikon Allah, d mamkin Dan Adam wanda yafi ibilis da sheɗan iya sheɗanci. Sageer zufa ma ce take keto masa dan sai yanzu yake tunanin me ya saka ya kasa gano abinda Kamal zai iya da wanda bazai iyaba.!! Umpah yace.
"Don Allah kuyi haƙuri to bari kuji abind aya faru dasu a yau idan labarin baizo gareku ba, ƴan matan kuwa munsa a masu azaba mafi muni da horo mai tsanani har sai sunyi nadama ta gaske..." Nan Umpah ya basu labarin kome game da halin da suka shiga a yau. Babu wanda ya tausaya masu ko ɗaya a cikin jama'ar wajan. Umpah yaba ibrahim wayarsa ya jona da Tv suka kalli abinda Mubina ɗin ta turo masu abinda Kamal yake faɗa tana daukarsa tana dariya, da voice note ɗin da tayi ma Umpah ɗin. Kowa yasha mamakin wannan lamarin. Sageer yace"Umpah na hakura a aura masu juna kawai wallahi suna son juna yanzu haka Kamal baya min magana saboda yasan nine zan auri Mubina..." Hafsat ma ta dora kan bayanin da ta sani akan Kamal da irin son da yakema Mubina kuma duk abinda zaiyi ita yakema shawara. Goggo tace"Ke Hafsat yaushe kika koyi zurfin ciki haka?" cewa, Ablah tace"Kwarai kuwa kam yanzu na amince ashe yaro ƙwaya suka dura masa a shayi ba da saninsa yayi ba."Amrah kallon su kawai take tana hawaye. Mamu tace"Ah Sageer aure dakai ba fashi fa." Umpah yace.
" insha Allahu kuwa." "Ina Zuwa" Umpah

ya faɗa yana miƙe yana latsa waya, ya kara a kunnensa. Zabairu yace"Abdulrahim don Allah kada a raba yaran nan fa tinda Sageer yace ya haƙura." Umpah ya waigo yace"Bana magana biyu Sageer kara kawai yayi." ya faɗa yana ficewa a parlon. Kamar 10 minutes ya dawo ya ƙirayi Zabairu, da Sageer da Abbu da Isma'il, suka fice sun jima waje tare da wasu baƙi kafin su dawo ayi Addu'a Umpah ya goge vedion ɗin baki ɗaya, taron ya watsa nan Umpah ya jadadda ɗaurin auran Sageer da Mubina gobe bayan sallar juma'ah. Haka suka watse dayawa sunso a ɗaura da Kamal tinda suna son juna, Sageer kansa ya dangana ne jin nauyin Umapah da yace ya amshi Mubina kamar farko babu fashi. Sageer jikinsa yayi sanyi ga Mahaifinsa da ya masa nasiya akan ya amshi auran tinda dai yarinyar ba wani aibu bane gareta, ga mahaifinta nada nagarta. Tunda ke shi sam Abban Sageer baisan dawan garinba kawai dai Umpah ya nemi gobe suzo da tawagarsu da goronsu na ɗaurin auran a babban masallacin sawabah za'a ɗaura... To fa haka kowa ya kama gabansa Mamu kuwa ta barma Allah kome suka saki jikinsu har can dare ko bayan lunch sun jima suna hira, sunyi ta kiran Mubina wayarta a kashe take. Ummah kuwa taso aba yaran junansu amman ba yanda ta iya ta haƙura. Nan wajan bacci tace da Abbu yayi azamar ɗaurawa Kamal aure shima. Nan yace "ai dama mana kamar ya auri Umaimah ya ƙare."

A can london Kuwa bayan Makel yazo, Kamal yasa ya kuma kaishi gidansu Mubina, suna kofar gate a cikin mota wai ko saga wulgin Majeed ma su masa wayo ya fito masu da Mubina, dan Kamal hankalinsa a tashe yake jin tace tana zazzaɓi ga wayarta akashe. Mubina kuwa tinda tayi bacci bata ko farka ba bacci kawai take, har maganin ya ratsata zazzaɓin ya sauka. Ummi kuwa bayan Nabeel da matarsa sun tafi da suka zo, su Azeema da Aleem sunyi bacci dakyar ta iya kaisu ɗaki ta shimfiɗe ta nufi gun mijinta. Bayan sun raba dare ta kintsa kanta ta fito ta nufi ɗakinta taga ko Mubina ta farka, ko da tazo wayar Mubina ta ɗauke ta duba taga akashe, ganin akashe yasa ta buɗe drower ɗin gadon ta nasata ta kwanta ta taɓa jikin nata babu zafi sosai sai kaɗan, rungumeta tayi ta kwanta tana cewa" Rigimammiya kawai."Mubina ko ƙara shegewa jikin ummi tayi tana turo ɗan ƙaramin bakinta, baccinta take cikin nutsuwa.

Kamal sai da suka raba dare, a kofar gidansu Mubina, tin fitar su Nabeel megadi ya rufe gidan saboda Majeed ya kwanta yana ciwon kai. Haka Kamal da Makel suka raba dare suka tafi, ran Kamal duk a ɓace. Abinci daren da bai ciba kenan, daman baici na rana ba, haka yayi wanka ya ɗauro alwalla ya fara kaima Allah kukansa..... Har asuba sai da yayi sallah ya kwanta ramuwar barci.

Washegari Ta kama Juma'ah Mubina koda ta tashi batajin daɗin ranta, haka ta daure tayi shirin zuwa makaranta, ummi ta hana kuka tayita yi har zazzaɓi da ciwon kai suka lulluɓeta, ga ta duba wayarta bata ganiba haka taji tana son ƙiran Kamal. Jin zazzaɓi ya rufeta sosai ya tashi hankalin ummi ta ƙira Majeed yazo suka nufi hospital, suna zuwa aka mata Allura aka daura mata drip saboda taƙi cin kome, a haka bacci ya ɗauketa, sai lokacin Ummi ta sami nutsuwa...

a Niger Kuwa bayan sallar juma'ah A Babban masallacin *Sawabah* Na Juma'ah Dake cikin garin maradi dubun Al'ummah ne zaune zasu sheda É—aurin aure, yayin da Umpah yake sanye da tsadaddiyar shadda ganilah fara sul, se Sageer da tawagarsa Shadda tasha kashi a wajan, sai Abbu da nasa gaiyar da yama Umpah, gefe ga Zabairu Kai da sauran jama'a manya manya ga sarki nan. Ga alwalin amarya ga Alwalin Ango Nan aka fara shirye shiryan sheda É—aurin auran da ya tara manya manya mutane cikin masallacin mai martaba sarkin maradi da kansa Yace"To bismillah malamai Waliyin amarya da Na Ango ku matso...." Sageer sai Washe baki yake nan mahaifinsa da wani dattijo mai dattako suka matsa gun malaman...... Wow Allah yasa a É—aura a sa'a.

*Real Ladingo Timnit Welday ce💃🏻*

*Wannan littafi na kudi ne ki biya kiyi karatu cikin salama, da kuma kwanciyar hankali, duk me so zaku tuntuɓeni ta wannan lambobin*
*👉🏻+22792589446/ +22796515805**KAMAL NE*

*Book 2*

*Bismillahir Rahamanir Raheem*

1️⃣7️⃣&1️⃣8️⃣
Chapter 87 · 0% Book details