← Book details Ali Dan Tsoho Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 124

Sashe 50

Ali Dan Tsoho Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Misalin kafe ɗaya na rana Ummah zaune cikin parlo, ta rabka tagumi tana fitar da kwalla, ita ɗaya Samha na makaranta. Wayarta ta ɗauki ringing, da sauri ta ɗauka tayi picking ganin number ƙasar waje ba suna yasa jikinta yayi sanyi, ta manna a kunnenta tace"Assalamu alaikum." Shiru ba ayi mgn ba. Tace"dawa nake mgn ne? Ko ba'ayi mgn ba bane?" shiru ba'a ce kome ba. Tsaki taja ta tsinke kiran,tana cewa"Wasu basu san a halin da mutum yake ba sai a dame shi..." Sallamar goggo Rumana ce da Ibrahim ya katse mata faɗan. Ta amsa tana cewa"Goggi sannu da zuwa." Goggo ta zauna tana cewa"Ke ɗaya kina mgn Fatima kisa ma zuciyarki hkr ba kune kika fitar dashi ba daga garin? To damuwar me zakuyi ai yanzu hankalin ku ya kwanta." ta faɗa tana matsar kwalla. Ibrahim yace"Allah yasa duk inda yake yana lfy cikin kwanciyar hankali..." Ummah tace "Amin" da gaggawa. Wayar goggo ta ɗauki ruri ta ɗauka tana cewa"Nifa bana son shegantakar banza, wata zungureriyar number zata kirani nayi ta cewa Alo ba'a mgn." ta faɗa tana picking ɗin call ɗin tana karawa kunnenta, tace"Kai wai wasu ƴan ashatane ne? Naga number ba ta Niger bace?" Ummah tace"Goggo nima an kirani yau yakai kwana goma, amman ba'a mgn ko masu gidan layi ne dai kuma naga akwai+." wani sansanyan Murmushi akayi aka tsinke kiran. Goggo ta dage se cewa take"Alo kunajina bana son shegantaka kunji ko, yau tsawon sati ana min shegantakar nan..." Ibrahim yace"Nima fa an kirani shekaran jiya amman ni number Saudiya ce, muga nakun." ya faɗa yana amsar wayar goggo ya duba yace"Lah ai number Saudiya ce goggo, Aunty Ummah muga taki" ya faɗa yana amsar wayar Ummah ya duba yaga itama ya ciro wayarsa ya haɗa duka number iri ɗayace"Yace wai ko dai Kamalu ne yake saudiya wlh number iri ɗaya ce." Ummah tace"Kamal zaije Saudiya bamu sani ba, bari na kira naji." ta faɗa tana kiran number amman har an kashe wayar. Ummah tace" an kashe wayar baki ɗaya" ta faɗa tana matsalar kwalla. Goggo tace"Wlh yamun daidai Allah yasa shine ma kun huta yaro yayi kuskure amman kunki sauraransa bare kuji garin ma ƙaƙa ya aikata abu..." Ibrahim yace"Goggo me ya aikata ne? Goggo tayi saurin cewa "Kai ɗana ne na cikina bazan ɓuye maka ba, amman ya zama daga kanka ba wanda zai kuma ji idan ka faɗama wani ban yafe maka ba." nan ta bashi lbrn kome. Ibrahim yace"Kai ina wlh karayane akwai dai wata a ƙasa haba me yasa ba'a faɗamin ba? tabbas akwia ƙulliya amman wlh se na bibiyi number nan, idan na tabbatar shine sai nabin ciki ko su uban waye wlh ba yabon kai ba ban taba jin inda zuri'ar mu suna irin wannan aikin ba bare Kamal nutsatsan yaro, duk da uwa ce muke ɗaya da Abbu ni na ɗauka har uban ma ɗaya ne bana jin hafsat da Sumaiyya kamar yadda nake jin Muhuseen da Saffiya da Abubakar a raina , wlh se inda karfina ya kare..." Goggo tace"Tabbas haka ne Allah ya maku albarka." Ummah tace"Ameen tana kwalla. Haka suka ci gaba da hira suka kwantar ma da Ummah hankali, se da Samha tazo bayan sunyi sallah Azuhur, sunci abunci suka tafi gida.

Su Mubina ana tashi suka tafi gida, basu tsaya shiririta ba. Sageer se da suka tafi gida shima ya wuce hospital.
Abbu na zaune cikin Office da misalin karfe hudu da rabi na yamma, wayar sa ta ɗauki ringing, ya ɗauka ganin number Saudiya yasa ya ɗaga yana murmushi yace"Ah Alhaji Jafara yau an tuni dani ko?" ya faɗa karawa kunnensa, yayi sallama yace"Ran Jafaru ya daɗe yau zamuncin ya motsa ko? To barka da yamma ya Madina da iyali number ka sauya kenan? ranar na kiraka da waccan number bata shiga ba?" ya faɗa yana murmushi. Shiru ba'ayi mgn ba, Abbu yace"Hello Jafar baka jina ne?"dif aka tsinke kiran. Abbu yayi murmushi ya girgiza kai yace"ko Netrowk ne." ya faɗa yana ajiye wayar yayi tagumi yana tunanin ɗansa Kamal, bai san yaron zai iya nisa dashi ba dan gatse ne yace zai masa baki ayau idan bai bar maradi har ya waiwaye sa bayan yarinyar ta samu nutsuwa tayi aure. A hankali ya furta"Kamal ashe biyayarka takai haka sbd na sami nutsuwa kabar mahaifarka nan da damagaram yaci ka kira muji lafiyar ka..." ya faɗa yana miƙewa ya ɗauki makullin mota ya fito, companyn kowa na sabgar gaban sa, se gaishe suke yana amsawa ya shiga mota ya fita. Kamfani dai har yanzu bunƙasa yake babu abinda ya sauya kamar yanda su Mounkalila suke so. Iyamu da Leeza haka suka yini cikin jin hushin Bashir, suna neman hanyar da zasu kunyata shi tako ci alwashin ramuwa... Hum.....😆

Misalin karfe 8:00 pm Sageer ne zaune a parlon baƙi gidan su Mubina inda suke hira su, yana amsa waya. Mamu ce riƙe da hannun Mubina cikin parlo tana mata mgn. Amrah da Ablah na masu dariya, Sabeela tace"Oh gobe zanyi missing ɗin baby banso hutun mu ya kare ba..." Umpah yace"Ko zaku tara ne da babyn?" Mubina ta fara diddira ƙafa ta zumburo baki gaba tana son fizge hannunta daga rikon da Mamu ta mata, dan ƙamshin ta take so taje ta shaƙo ta wani riƙeta, tana sanye cikin doguwar riga ta shadda blue da hijab ɗan ƙarami blue shima tayi kyau sosai masha Allah. Mamu tace"Baby rabu dasu yanzu ina miki mgn shine nima yau halin kike min ba mgn sai kumbure kumbure?" Mubina ta shige jikin Mamu tana sauke tagwayen ajiyar zuciya taki mgn. Umpah yace"Auta kije mana yana jiranki pls." ta ɗaga kai ta janye jikinta daga Mamu ta fara tafiya a nutse ta fice daga parlon. Amrah tace"Kai baby dama ya bare yanzu baiwar Allah..."Ablah tace"Nifa Amrah bana son tashin magana." Umpah yace"Ayi hkr muje yanzu muyi lunch." Sabeela tace"Oh Ablah" Azeeam da Aleem suka ce"Kakarmu zamuyi missing ɗinki ko dai muje tare dake ne...?" Ablah tace" Babu mai kaini ƙasar anrna wlh tallahi kunji na rantse, kujini da yara da wata fitina." Majeed da yake gefe shida Kabeer banda dariya ƙasa-ƙasa babu abinda suke dan Ablah ba karamin dariya take basu ba, ita bata ganin kowa sai Mubina. Aleem da Azeema dariya kawai suke yaran akwai wayo. Kan dining suka nufa domin cika tumbin su.

Mubina da Sallama ta shigo parlon. Sageer ya ajiye cup glass É—in hannunsa wanda yake kurba fruit ya amsa, sallamar. Yace

"Welcome my wife."

Mubina ta karasa ta zauna ɗan nesa dashi tace"My One ina yini"Sageer yace"Lau tinda na ganki yanzu Babyna ykk?" ɗan karamin bakinta ta zumburo gaba tace "Ni ba dole nayi fushi ba ina kiran ka ɗazu da yamma baka san me zan faɗa maba kaƙi ɗauka ni fushi nake yanzu ma Mamu ta matsamin da bazan fito."

ta karasa mgnr a shagwaɓe. Sageer yace"Sorry my wife wlh ina cikin aiki ne fa." Mubina ta ɗan yi murmushi ta ɗauƙi cup ɗin ta kara zuba masa sansanyan fruit ɗin inibi ta kai bakinsa tana murmushi dan taga ya shiga damuwa. Amsa yayi yana kurɓa yana mai farin ciki. Wayrsa ta katse masa amsa ya janye bakinsa yana haɗiye wanda ya kurba ya ɗauki wayar wacce take kan table, yayi picking yakai kunnensa, Mubina tace"My one kamar number waje ma?" ta faɗa tana kai cup ɗin bakinta tana kurba. Sageer yay sallama yace"da wa nake magana wai me yasa idan an kirani ba'a mgn pls wanene? ko wacece...?"Saukar ajiyar zuciya mai karfi Sageer yaji a dodon kunnensa." Mubina ta shagwaɓe murya tace"To my one kabar ɗauka kawai wlh ni de idan ma wata shegiyace zanyi maganinta Allah sai kaban number naji wacece."

Sageer yace"Anshi Baby yi magana muji"Mubina ta amsa ta kara a kunnenta, cikin zazzaƙar muryata tace"Hello wacece ne wlh ki daina kiran min miji ko na sauya maki kama uwar jaraba kawai..."Wani sansanyar murmushi aka watso mata ta cikin wayar tare da huro mata isakar baki haɗe da ajiyar zuciya sai wani sansanyan kiss ya biyo baya, dif aka kashe kiran. Mubina da ta gama shiga wani irin mugun yanayi tinda taji murmushin da huro iskar ɓakin, haɗe da kiss gashin jikinta ya fara mimmiƙewa ta lumshe shanyayyun idanunta, tana turo baki gaba. Sageer yace"My wife meye ne, ana maki mgn ne?" firgigit Mubina tayi tace"Ni ba wanda yamin mgn Allah sai na kira number , murmushi kawai akamin fa, wlh kasan ko wacece dan ku cimin fuska ne." ta faɗa tana sakar masa kukan sangarta. Sageer ya rikice ya shiga lallashinta yana bata baki da rantsuwa bai sabina mace ko namiji. Daket ya samu ta sauko ya ɗauki wayarta ya saka mata number yace ta kira suji. Nan ta kira a kashe. Haka dai ta saki jikinta suna hira sai tara da wani abu ya tafi ta rakashi har mota. Ko da ta shiga gida bata sake bi takan number ba abunci kawai taci sai bacci....

*************** ********* ***************
*Bayan kwana 12*
Su Mubina sosai suka maida hankali kan karatunsu, soyayya ita da Sageer abu sai gaba yake, se dai tin ranar da taji murmushin nan da kiss ɗin da aka mata ya tsaye mata arai! tasha gwada kiran number bata shiga, har Sageer take tambaya yace tin ranar ba a kuma kiran saba, dole ta watsar, sai ƙamshin nan abin ya zame mata masifa dan yanzu sai ta rungume rigar take iya bacci. Bangaran Basma da Kabeer an ɗinke tsaf an fara zuba love na ban mamaki, haka Amrah da Lameer ta amcin masa. Lbrn Kamal kuwa har yau ba lbr, Abbu da Ummah suna kai kukansu wajan Allah, ya baiyana masu yaronsu, ibrahim Ko ya dage na bincike ko zai samu wani dan dalilin da zai gano gaskiay. Sageer ko jiya ya zauna yayi kukan rashin Kamal se ana kiransa da number saudiya idan ya ɗaga ba a mgn, kullum su Ummah haka ake masu har Umpah ba da yayi mgn ake kashewa.
Chapter 50 · 0% Book details