Sashe 12
Ali Dan Tsoho Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
.... Shin jama'ah wai su waye iyayan Mubina? ina ne asalin su?, *ABDULRAHIM KABEER ALGÈRIE* cika ken balarabe ne na asali. *KABEER NABEEL* balaraban Algèrie ne, Allah ya masu tarin dukiya me yawa, Kabeer Nabeel mutune shi wayayye ɗan son aji dadi, kuma shi ɗaya Allah yaba iyayansa, dan haka ya sami tarbiyya me kyau yayi karatu sosai, bayan ya kammala karatunsa ne ya kama aiki Allah ya haɗa shi da Jawahir, sukayi aure cikin so da kaunar juna, bayan auransu da sati biyu suka shiga yawo ƙasa daban-daban, wanda daga karshe suka yada zango a Niger a babban birnin Naimey, suka sauka a grand hotel, tsawon sati ɗaya suna cin duniyar su yawo babu inda basa zuwa Kabeer yaji duk duniya babu ƙasar da yake sha'awar zama kamar niger a yanzu... Nan akwai wani bazabarme me suna maiga da suka saba ma'aikacin hotel ɗin ne, yake faɗa masa buƙatarsa ta yana so ya dawo niger da zama se dai yana tsoron iyayansa bazu yarda ba... Maiga ya kwatanta masa ya koma ya bisu a sannu har su amince harakar mahaifa ba'a wasa da ita. To daga nan yabar maganar bai sake neman shawara ba har suka koma ƙasarsu. inda kafin su tafi ya amshi number maiga. Tinda Kabeer suka dawo yake ma mahaifinsa wayo da kwatanta masa su koma ƙasar niger mana da zama, rayuwar akwai dadi. Irin tsawar da fushin da Nabeel ya nuna ƙarara akan Kabeer da ƙyamar abinda ya faɗa, yasa Kabeer koda wasa be sake maganar ba ya barta ya rungumi aikinsa da matarsa suna soyewarsu... Cikin ikon har ta sami ciki, murna ba'a cewa kome wajan Kabeer da iyayansa da itama nata dangin. Har cikin ya girma ranar haihuwa tazo Allah ya sauki Jawahir lafiya ta haifo yaranta kyawawa mace da namiji, murna a dangi da iyayan yaran ɓata lokacin faɗi ne... Ranar suna ta zagayo yaran sukaci sunah Namijin Abdulrahim macan kakarta ta uba Sabeela. Haka yaran suka taso cikin gata da kulawa dangi kowa na sonsu, suna shekara biyu Allah yama Nabeel rasuwa mutuwar ta girgiza Kabeer ba kadan ba, yayi kuka har ya gaji ya barwa Allah yaci gaba da kula da matarsa da yaransa da mahaifiyarsa... Bayan cikon shekarar Nabeel ne Sabeela mahaifiyar Kabeer take faɗa masa ita garin ya fice mata aranta! kamar ta koma tunis da zama... Kabeer najin haka ya bijiro mata da manufarsa ba yauba yana sha'awar komawa niger, nan tayi na'am da maganar. Ba a ɗauki lkc ba Kabeer ya kira maiga yana faɗa masa kome nan ya masa gaisuwa da tambayar sa garin da yake so a niger? Kabeer yace nan Naimey yake so zai zo ya sayi fili a maka masa gini irin nasu na larabawa... Ba ako jima ba Kabeer ya kwashi dukiya yaje niger inda suka fara fafutika neman guri me kyau nan ko a yantala ya samu filin da ya masa aka kafta masa maƙareran gida. Cikin wata uku aka gama kome ya damƙama maiga amanar kome koma ya riƙe amana har aka gama aka zuba kayan duniya tare da saukar AQura'ani mai girma. Suka tattara suka dawo ƙasar niger tare da dukiyar su wata kumana can ƴan uwa suna juyawa masu, suko suna rayuwarsu me dadi tare da yaransu biyu. Haka suka kasance a niger Kabeer ya gina babbar asibiti domin temakon al'ummah duk da tana asibitin kudi amma akwai sauki sosai, haka jama ke tururuwar zuwa. Akwana a tashi har su Abdulrahim suka girma sun sami tarbiyya me kyau da karatun book da na mahammadiya, tin daga haihuwarsu Allah bai sake ba Kabeer haihuwa ba, cuɗanya da suke da hausa da zabarmawa yasa suka iya hausa sosai hakama duk ma'aikatan gidansu daga bahaushe se zarma. Sabeela tana gama secondary school ɗinta aka mata aure ta auri wani buzu babban ɗan jarida me suna Saleem sabo a gidanta ta shiga jami'a, yayin da Abdulrahim ya maida hankalin sa kan karatunsa medicine, saboda yay aiki ana hospital ɗinsa me suna *Clinique Annur hospital*. Akwana a tashi babu wuya har ya gama ya fara aikin sa tare da mahaifinsa, watarana an kawo wani maras lafiya abin tausayi gasu talakawa likis, cikin ikon Allah Abdulrahim ne akan aiki shi ya masu kome kyauta sun bashi tausayi barin budurwar yanda take kuka tamkar mahaifinta ya rasu. Nan take yarinyar ta burge Abdulrahim duk da bayada ra'ayin auran bahausa. Dattijon kwanan sa uku ya warke ras zuwa lokacin Nusaiba ta shaƙu da Abdulrahim, duk tasan ba lallai ta sami balarabe ba. Nan yake tambayarta wane unguwa suke? ta faɗa masa su ba ƴan gari bane ƴan maradi ne, labarin irin temakon da ake a likitan yasa suka seda kadarasu suka zo ita da babanta da mamarta da yayanta... Kamar wasa kafin ake sallamar su suka kulla soyayya saboda Nusaiba kyakyawace son kowa kin wanda ya rasa fara doguwa me diri kawai de tallauci ne da ya masu cikas babu wadatar abunci me kyau da sutura shi ke boye kyanta. Seda suka kwashe shekara guda suna soyayya ya wanke ƴan gidansu tass, yasa aka masu ginin zamani duk karshan wata se yaje maradi daga Naimey har yaji sha'awar zama maradi fiye da Naimey ɗin. Koda Abdulrahim ya gwadama iyayansa pic ɗin Nusaiba sunyi na'am da ita basu nuna kyama ba cewar se balaraba ƴar uwasa saboda tana da kome na mace da ake buƙata a tare da ita, dan haka basu yi ƙasa a guiwa ba wajan nemarwa ɗansu auran Nusaiba sukayi tattaki har garin maradi. Babu ɓata lokaci aka saka ranar aure, lokaci yazo akayi biki na kece reni, wanda har yanzu babu na biyun sa da aka taɓa yi a garin maradin... A ka ɗauko amarya aka kawota gidanta dake Naimey gida tamkar aljanar duniya, dangin Nusaiba fa sai buɗe hanci ake a garin maradi babu ta biyun jininsu ta auri balarabe. Soyayya me tsaf ake zubawa tsakanin Nusaiba da Abdulrahim tamkar zasuci junansu. Nusaiba tana bin surukanta sau da ƙafa da kakar mijinta rayuwarsu abin sha'awa nan da nan suka koya mata larabci. Shekara su ɗaya da aure ta haifo yaronta santalele kyakyawa aka saka masa suna Kabeer wanda hakan yama Kabeer kakansu dadi matuƙa, lele kam ya shashi gashi daman kamar su ɗaya da Kabeer ɗin. Seda Kabeer ya shekara biyar cif aka haifi Amrah zankaɗeɗiya kyakyawa da ita a ranar kuma Sabeela mahaifiyar Kabeer ta cika mutuwar ta girgizasu sosai sun jima kafin suke mantawa Lkcn Sabeela da mijinta ta yaransu biyu mace da namiji suka koma london da zama saboda BBC na buƙatar irin Saleem sabo . Amrah tana da shekara biyu aka sami cikin Mubina wanda Mamu taci wahalar laulayi kamar bazata rayu ba, har kuka take a cire mata cikin sbd bata iya ci bata iya sha se amai, umpah yace sam bai san zancan ba dan yana son cikin sosai tayi hkr dan Allah. Haka dai aka samu har yayi wata tara amma sam babu haihuwa idan ya dubata yaga da saura ana haka seda Amrah ta ahekara uku aka haifi Mubina, kenan seda ta shekara a cikin Mamu aka haifeta, wanda kyawunta ya kere na kowa a gidan gata katuwa aka haifota fara sul kallo ɗaya zaka mata kasan balarabar asali ce ga farin jinin jama'a tin ranar da aka haifeta amma se shegen kuka dan bata bar kuka ba se da akayi arba'in basa baccin kirki, amma cikin ikon Allah ana arba'in ta fasa kukan, se tsotsar nonon tsiya da son hannu dan ba'a ajiyeta, bata kwanciya se ahannun mutum ko baya, haka Ablah take fama da Mamu Kabeer yayi ta dariya da Amrah. Tin daga kanta har yau Mamu bata samu haihuwa ba, suka rungume yaran su uku suna basu tarbiyya haɗe nema masu ilim na addini da boko. Umpah da Ablah da Kabeer sun ɗauki son duniya sun ɗorama Mubina, se sangarta da shagwaɓa, dan se abinda take so ake a gidan, Mubina itace ta dasama Abdulrahim umpah Nusaiba Mamu tin tana ƴar shekara uku idan kana son masifa da bala'i kace mata shekarara, to Allah zai rabaku da ita. Se dai fa akwaita ilimi sosai daga na book har na Qura'ani mai girma ɗin. Umpah ya zubama ƴaƴansa makudan kudi domin ne ma masu ilim, Kabeer farine kyakyawa me fara'a da son jama'a yana son kanninsa sosai tafiyarsa *Balgique* karatu ne ya raba su se ta waya. Tin a primary school Mubuna ita ce ke cin ta farko, har zuwa secondary school babu wacce ta shiga gabanta, ga farin jini duk masifarta dan lkcn tana primary kullum sai ta jibgi ƴaƴan mutane da cizo akunne, to har secondary ɗin ma bata daina fada da cizo ba, gata ƴar siririya in ta manne maka a jikin ka se an ɓanɓareta daket, kamar wahainiya take, ga ɗaukar magana tsokana kamar masifa, dan kafin Amrah take shiga university Mubina ke tsaye kanta ko kallon banza baka isa kama Amrah ka kwana lfy ba, seda ta shiga Jami'ar Abdou monmuni university nan Naimey suka rabu. Kuma lokacin ne Kabeer ya rasu mutuwar ta girgiza umpah AmrahdA iyalinsa, dan Mubina se da tai jinya sosai kafin take warwarewa daket. Ablah ma kamar tayi hauka miji ya tafi ya barta, anyi shekara kafin suke komawa normal, dan sunsan dai dole duk mai rai se ya ɗanɗani zafin mutuwa. Amrah matsagaiciya ce ita ba doguwa ba ita ba gajera ba me diri tana da ƴar ƙiba kadan, tana da dogon gashi sosai fuskarta doguwa me ɗauke da dogon hanci da faffadan lips da matsagaitan idanu, ba laifi kyakyawace. son kowa se dai Mubina ta kereta a kome gashi kawai Amrah tafi Mubina da jiki, amma suna kama sosai. Mubina doguwace kyakyawa fara sul ƴar siririya mai ɗauke da doguwar fuska me dan faɗi, me ɗauke da dogon hanci da dara-daran idanuwa lumsassu bakinta ɗan ƙarami kalar pink hakoranta sirisiri farare sul me ɗauke ƴar wushirya, tanada dimple a gefen damarta wanda ko magana take yana loɓawa, se kirjinta me cike da albarkatun fulani tantsam-tantsam jajur a tsaye suke kyam, kansu irin masu tsinine sosai duk da kasancewarta siririya tanada mazauna ƴan matasa gata ƙirar coca cola akwai hips, tana da gashi amma ba sosai ba ya sauka de har kafadarta yana da samtsi sosai ba baki bane yasa