← Book details Ali Dan Tsoho Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 55 OF 124

Sashe 55

Ali Dan Tsoho Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sageer yaje ya hado duk irin alluran da yasan baza su mata illa ba ya hada cikin drip ya É—aura mata. Umpah yace"Bari naje gida na dawo Nusaiba ki kula da ita sosai Allah ya bamu hakuri mu duka kawai." ya faÉ—a yana ficewa. Sageer yace "Mom zan kai Umpah gida sai naje na dawo mu kwana anan É—in." Mamu kai ta É—aga masa bata iya magana ba... Sageer yabi bayan Umpah É—in. Gaba ya buÉ—e masa ya shiga ya rufe, ya zagaya ya zauna mazaunin direba yaja motar suka tafi.

Har suka iso kofar gidan Umpah ba wanda yama wani magana, kowa yana cikin tashin hankali. Umpah ya buÉ—e ya fita, yace"Sageer Allah yayi albarka." Sageer yace" ba kome dady anjima nima ina komawa kafin drip É—in da na samata ya kare." ya faÉ—a yana tshin motar yabar gurin. Allah kadai yasan halin da Sageer yake ciki. Umpah kai tsaye gidan Abbu ya nufa.

Su Abbu na zaune parlo bayan sun gama lunch, suna hira da Safiyya, se mita take masa har ina ya tura Kamal? Ummah tace"Wlh bamu saniba fa in da ya shiga , a gaskiya ina buƙatar ɗana yazo na masa aure..." Abbu yace"Hum Fatima kenan Allah dai ya tsare mana shi duk in da yake ya shiryar dashi..." sallamar Garba ce ta katse masu mgn. Abbu yace"Garba lfy dai ko?" Garba yace"Yallaɓai makwafcin ka ke sallama." Abbu yace"Wanne kenan? Ce gani nan fitowa." ya faɗa yana miƙewa. Garba yace"To yallaɓai." ya faɗa yana juyawa.

Abbu ya fito domin yaga waye, yana fitowa yaga Umpah ne. Da sauri ya isa bakin get, É—in yaba Umpah hannu sukayi musabaha, Abbu yace"Haba Abdulrahim ka tsaya daga kofar get bismillah muje ciki to..." ya faÉ—a yana jan hannunsa. Umpah yaja shi nesa da kofar get, yace"Abubakar wata kaddara ce ta sake hawan mu abun babu dadi, Mubina ciki ne da ita tsawon sati 6 cif, tin ranar gini ranar zane, daman rabon hakan ne yasa yaron ya rufta mata." ya faÉ—a yana jinjina kai.

Abbu tunda Umpah ya anbaci ciki yayi mutuwar tsaye! yaji kansa na juyawa, hankalinsa yayi mugun tashi, daket ya samu damar furta,
"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un!! Allah me iko oh Ni Abubakar Sadiku ina zan shiga da rayuwata, Kamal ya gama tozartani, ya kunyatani a idanun duniya, ya zanyi da raina?" ya faɗa yana sakin kuka mai tsuma zuciya. Umpah ya riƙeshi yace"Haba don Allah kayi hkr wlh duk abinda Allah ya tsara babu wanda ya isa ya dakatar da hakan, bawa baya tsallake kaddara sa wajan ubangijinsa, dan Allah kabar kuka ka nemi yaronka ka saka shi a jikinki ka kawai mu rungumi kaddara shi yafi. Insha Allahu cikin satinan zan haɗamata duk takardunta daman tanada posport sai kawai muje London ta zauna gun ƙanwata taci gaba da karatunta har Allah ya sauke ta lfy se ta kammala karatun ta acan, yaron nan yace zai aureta haka ma, yana sonta idan tana can zata fi saukin manta kome ta nutsu tayi karatun ta ta rungumi abinda zata haifa." Abbu ya rungume Umpah yana bashi hakuri da kuma masa godiya kan irin yanda yake da tawakali da rungimar kaddara.

Abbu yace"Banida bakin maka godiya amman dan Allah kayi hkr bazan hana a É—auketa daga garin ba , ko nine hakan zanyi, amman muna son muma mu kula da ita sosai har Allah ya sauketa lafiya, muna kaunar abinda zata haifa, dan haka a fara shiri dani za'a kaita London É—in, amman me zai hana bayan ta haihu mu haÉ—asu aure da Kamal É—in, dan nasan duk inda yake zuwa lkcn zai waiwayi gida?" Umpah yace"Wlh ba wai naki bane amman yaron nan bazan masa butuci ba, bayan hka shi ranta ke so, kawai mubar maganar aure tsakanin su nafi so zumuncin mu ya dore." Abbu yace"Hakane ba kome Allah ya bamu ikon cinye wannan mummunar jarabawa É—in." Umpah yace" Amin zan shiga gida." Abbu ya rako shi har waje bakin get. Nan yake sheda masa suna hospital, nan Abbu ya koma gida domin shedama Ummah.

Umpah yana shiga gida lkcn Kabeer yazo, bai ɓoye masu kome ba. Nan kuwa Ablah ta fara kuka ita da Amrah suna tsinewa Kamal albarka. Daket Umpah ya samu suka hkr Umpah yasa Amrah ta hadoma Mubuna kayan sawa kala biyu, suka shirya suka koma hospital.

Abbu yana faɗama Ummah tasha kuka tana mai jin tamkar Samha ce hakan ta faru da ita. Nan take suka shirya suma suka nufi Hospital har Safiyya dan sun gama gaya mata kome, taci kuka kamar ranta zai fita, takuma ce akwai ƴar ƙasa cikin wannan lamari, idan yana sane ya mata fyade bazai dawo ya faɗama su ba...

Mamu kuwa tinda Umpah ya tafi ta kwanta ta rungume Mubina tana kuka, har ta gaji, tayi shiru, haka Sageer ya iskota lkcn Mubina zazzaɓin ya ɗan sauka, haka ya zauna jigum.

A haka su Umpah suka dawo Ablah da Amrah suka kafa masu kuka, daket Sageer ya basu baki suka hkr. Su Abbu ma da suka zo sun jima sosai suna dai ta basu hkr suna me tausayin yarinyar. Kabeer ji yake da yana da dama zai iya kashe Kamal ma kowa ya huta, dan ya ɓata masu zuri'a. Sai shabiyu na dare su Abbu da Kabeer da Amrah da Ablah suka nufi gida, daket Umaph ya lallaɓa Ablah ɗin suka tafi, dan yasan idan tana nan Mubina ta tashi to idasa rikitata za tayi.

Sageer yana zaune saida drip biyu ta kare yaji babu zazzaɓin jikinta. Umpah ya mtsa msa yaje gida ya kwanta. Dole Sageer ya masu sallama wajan 1 pm ya tafi gida yace da yayi sallah Asubah zai dawo.

Mubina se karfe uku na dare ta farka. A hankali take motsi, ta fara buÉ—e runanun idanunta wanda suka mata mugun nauyi, ga zafi da suke mata, ta buÉ—e su tar tana kallon cikin É—akin, ta kalli Mamu a gefenta ta rungumeta ta kalli Umpah ma a gefenta yana bacci wato sun sakata tsaka.

A hankali tace"Mamu yunwa nake ji ina agwaluma na É—in?Mamu ki tashi ki bani." firgigit Mamu tayi ta farka tana kallon Mubina, tace"Baby sannu me kike so?" Mubina ta shige jikin Mamu tace"Mamu agwaluma nake so da taliya me yaji da manja yunwa nake ji." ta faÉ—a tana fitar da kwalla.

Mamu tace "Ok bari yanzu na kira a dafa maki se Umpah yaje ya ɗauko maki" ta faɗa tana janyo wayar Mubina dake manƙale a chaji nan gefen gado, ta kunnata. Nan take ta kira Amrah tajima tana ringing kafin a ɗauka ɗin. Cikin bacci Amrah tace"Mamu lfy dai ko?" Mamu tace"Lfy lau, maza ki sauka ki dafa mata taliya fara naga akwai soyayen manja da yaji a dake ki zuba yanzu Umpah zaizo ki bashi ki haɗa da agwalumarta a kawo." Amrah tace"Tom Mamu naga karfe ukku na dare ne fa?" Mamu tace"Eh kiyi maza don Allah shiyasa na saki kar ashiga hakkin Laure." Amrah ta miƙe da sauri tace" Ok yanzu zan dafa mata kuwa." Mamu ta tsinke kiran, tana kallon Mubina ta kafeta da idanu tana yamutsa fuska. Mamu tace"Baby Maza miƙe kije ki zuba ruwa a jikin ki kiji sanyi kafin taliyar ta dafu ko?" Mubina ta ɗaga kanta, cikin sanyin murya tace"Mamu to me yake samuna ne?" Mamu ta kamata ta temaka mata ta sauka tace"Oya je ki watsa ruwa ki fito zaki iya ko na kama ki?" Mubina ta Zumburo ɗan ƙaramin bakinta gaba tace "Zan iya mana." ta faɗa tana bubbuga bayan Umpah. Idanunsa ya buɗe ya kalleta ya miƙe zaune. Mubina cikin sanyin murya me haɗe da kasala tace"Umpah bacci kake ka tashi ka amso min taliya ko mu tafi ma gida naji sauƙi kawai." ta faɗa tana nufar toilet cikin sanyi take tafiyar jikinta ba kwari ko kaɗan. Umpah yace"Nusaiba mu tafi gida kawai gobe sai mudawo da safe tinda taji sauƙi..."Mamu tace"A'A mu zauna har goben kasan harakar laulayi fa, yanzu ma tsiro nake taci taliyar tayi amai , amman ba yanda zanyi, kaje ka amso mata yanzu."
Umpah yace" Ok bari naje amman don Allah karki faÉ—a mata bari se taci abunci ta koshi."Mamu tace"Eh na sani cikin siyasa zamu faÉ—a mata mu lallasheta har ta hakura ta amshi kaddarata." Umpah ya jinjina kai. Ya mata sallama ya É—auki makullin mota ya fice.

Mubina shower ta sakar ma kanta taji dadi sosai, nan ta goge jikinta ta mayar da kayanta, ta fito ta zauna ta kwanto jikin Mamu tana yamutsa fuska sbd yanda tashin zuciya ke damunta, ga yawu. Mamu jin shirun yayi yawa tace"Baby menene ko yunwar ce?" Mubina ta ɗaga kai ta miƙe ta nufi toilet ta zubar da yawu ta dawo, ta zauna ta ɗauki wayarta tana dubawa taga sako kusan biyar, kwanciyarta ta gyara, ta buɗe sakon taga kamar haka *Ina miki fatan Alkhairi a rayuwarki Babyn Sageer, pls ina kika shiga ne nagaji da kira baki ɗauka ba? Ko dai baki son abutar dani ne bazaki tausaya ma ɗan kurma ba? Babyn Sageer wlh haka kawai naji gabana na yawan faɗuwa a kanki, hakan ya bani tabbacin bakya jin daɗin jikin ki.... Kin faɗamin ne bakida lfy baki yarda da kurma ba? Ni banida baki, ba kowa zan faɗama ba pls faɗamin meke damun ki...? Na tura Sageer ya duba lafiyar ki yazo? Pls Mubee meke damun ki faɗamin ko na samu nutsuwa zcyt taki nutsuwa a kanki?"😭faɗamin ko nayi ta kuka😥.*

Idanu Mubina ta zaro se ta saki murmushi , ta duba sako na biyu kamar haka *bazaki kulani ba ko??🥺😰.* se na uku *Dan ina kurma shine kowa ya tsaneni hum waiyyo ni😰😰😰* Se na hudu *Ina son nasan halin da kike ciki ne.... amman kin ki kulani bari nayi ta kuka har na makance shikenan banida baki banida ido kowa ma ya huta😰😰😰.*

Mubina taji wani iri a ranta sai ta tsinci kanta da rubuta masa.
Chapter 55 · 0% Book details