Sashe 33
Ali Dan Tsoho Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Bai zame ko ina ba se gidan su yay horn megadi ya buɗe masa kofa ya shige da motar, nan harabar gidan yayi parking. Kallon Mubina yay yaja tsoki ya beƙa hannunsa ya ɗauki bottle ɗin water yaji akwai sanyi sosai, buɗewa yay ya matsa dab da fuskar Mubina, ya ɗaga bottel ɗin sama ya kwarara mata a fuskarta da kirjinta, zuwa shafaffan cikinta. Wata irin raunaniyar ajiyar zuciya Mubina ta sauke da karfi... Ta zabura jikinta na wani irin kyarrrrrma, ta fara ƙoƙarin bude idanunta wanda suka mata mugun nauyi, ga zafi tana girgiza kanta da karfi, amman ta kasa buɗe idanun kurma ihuuu tayi da karfi" Wayyo Allah na!! Umpah bana gani wlh bana gani umpah ƙishi nake ji ka bani ruwa." ta faɗa tana kecewa da kuka jikinta na karkarwa gag-gag. Kamal ya rankwafa yay mata rumfa da kirjinsa ya sanya tattausan hannunsa ya riƙo kafadunta, ya tallafo kanta ya sanya hannunsa ɗaya saman zara-zara gashin idanunta wanda suke kwance luf ya shafa, ya shiga hura mata iskar bakinsa ya meƙa hannunsa ɗaya ya janyo botteI ɗin water ɗin ya riƙota sosai jikinsa ya kafa mata bottel ɗin a ɗan karamin bakinta, da sauri ta fara haɗiyar ruwan ta dora hannunta saman nashi tana shan ruwan sosai. Kamal ganin batada niyar dena shan ruwan ya janye robar ruwan daga bakinta. Ta sauke ajiyar zuciya ta nitsa kanta kirjinsa tana maida numfashi, kuma sai tayi wata irin zabura, ya riƙeta gam itako se ƙoƙarin fizgewa take. Bakinsa ya kai dab da kunnenta Cikin ƙasa da murya yace"ke! maras kunya nutsu kisan da wa kike tare ko yanzu na sake tsinka maki lafiyayyun mari wlh , karamar ƴar rainin hankali." ya faɗa yana shafa idanunta da suke a rufe ruf, jikinta se rawar sanyin yake. Inajin murya a dodon kunnena sai naji wani irin mugun tsoron sa ya shigeni nan take ban taɓa tunanin zan ji tsoron mutum ba haka... Amman yau naji mugun tsoron sa fiye da kome... Sbd ni kadai nasan azabar da naji lkcn da ya tsinkamin marin karshe... Shiru nayi jikina na karkarwa ina jin wani irin sanyi yana shiga jikina se rawar sanyi nake na kasa kwakwaran motsi... Kamal ganin Mubina tayi shiru ta fasa hauka sai rawar sanyi take, yasa yaji mugun tausayin ta ya darsu a zuciyarsa. Jikinsa ya shigar da ita sosai yana shafa gashin kanta. Can ƙasan makoshi yay mata magana dab da kunnenta yace"kina jin sanyi ko?" ya faɗa yana shafa lallausan gashin kanta. Cike da tsoro na ɗaga masa kaina ina nitsa kaina cikin kirjinsa ina rawar sanyi. Murya sa naji yace"Am sorry my kanwar nine na mareki har kika suma ko?" tsintar kaina nayi da girgiza kaina ina kara ɓoye kaina kirjinsa, dan Allah ya gani bana son ko kallan fuskar shi ji nake banida makiyi a yanzu da ya wuce shi se dai a sannu zan rama cikin ruwan sanyi ta bayan gida, dan a yanzu bazan iya masa rashin kunya ba ya ɗarsa min tsoron! sa a zuciyata... Amon muryasa naji cikin kunnena yana cewa"Ok to waye ya mare ki idan ba Kamal ba?" ban iya bashi amsa ba hawayen baƙin cikin tunawa a tsakiyar makaranta yaci mutunci na! hawanye takai ci ke sauka kan fuskata... Ji nayi yana mgn cikin tsawa"Ke!! Maida hawayen ki yanzu nan." ya faɗa yana zaro handkerchief me wani irin daddaɗan ƙamshin sa me sanyaya zuciya, naji saman fuskata yana goge min hawayen. Shiru nayi nayi lamo jikinsa ina sauke raunaniyar ajiyar zuciya da karfin gaske, ina shaƙar daddaɗan ƙamshin sa. Hannunsa naji saman fatar idona yana shafawa yace"Oya buɗe idanunki maza." ya faɗa yana shafa gashin idona. Ƙoƙarin buɗe idanuwana da suka min nauyi na fara yi, amamn na kasa buɗewa... Muryasa na tsinto tsakiya kunnena ya kirani *Mubeena*" da sauri bakina yana rawa nace "Sir... na... Ka... sa... bu... ɗe... idon... na...wa" na fada ina hawaye. Kamal jin abinda Mubina ta faɗa gaban sa ya yake ya faɗi jikinsa na rawa ya ɗago da kanta ya riƙe fuskarta da hannu biyu ya kai bakinsa saman idanunta kawai sai ya fara lasar idanun nata ya shiga tsotsa a hankali yana shafa lallaunsa gashin kanta. Wani irin abu na fara ji na tsirgamin jikina tin daga ɗan yatsana zuwa tsakiyar kaina, nayi saurin ƙamƙameshi ina girgiza kaina nace"Sir ina jin zafi zan iya buɗe idanuna yanzu bari na gwada kaji Sir."na faɗa ina tusa hannuwana tsakiyar sumar kansa mai taushin gaske ina sauke ajiyar zuciya, ina ƙamƙameshi sosai jin yadda yake tsotsar min fatar idanuna, idan ya tsotsi na dama ya saki ya tsotsi na hagum. Kuka na sakar masa da karfi ina dukan kirjinsa. Kamal bakinsa ya janye daga idanun Mubina yana murmushi ya tallafo kanta murya can ƙasan makoshi yace" Ok *Mubee* oya buɗe idanun naki na gani kinsa gabana faduwa wlh." yafaɗa yana shafa fuskana yana huramin iskar bakinsa saman idona. Bakina na zumburo gaba, na fara ƙoƙarin buɗe idanuna amman sam na kasa kirjinsa an fada ina girgiza shi na kece da kuka nace"Sir Kamal wlh bana gani na kasa buɗe idanuna sam..." Kamal da sauri ya rufe mata baki jikinsa ya fara kyarrrma yace"Pls Mubeena ki rufa min asiri wlh buɗewa zaiyi , me zance ma Umpah da wani ido zan kalle su haba Mubee buɗe kinji."ya faɗa yana ɗaga min fatar idanuna na kara sakin kuka da karfi. Kamal yace" Ok yi hakuri yi shiru muje hospital ko?kai na ɗaga masa na tura kaina kirjinsa ina sauke ajiyar zuciya. Hannunsa naji tsakiyar bayana ya zagaye bayana ya dora kansa wuyana, yana gogamin habarsa a dede setin keyata, yana sauke ajiyar zuciya ajere a jere, naji bakinsa cikin gashin kaina, yana cewa"Mubeena ki daina min irin wannan wasan nasan lafiyar ki kalau dan ki rama ne, to pls kiyi hakuri na tuba me kike so yanzu na baki ko na saya maki ki hakura , muje na saya maki na kawo ki gida da kaina har gaban umpah da Mamu cikin ƙoshin lafiya yanzu zan maki ko meye amman pls bari min wasan ido kinji My Mubee kanwata?" ya faɗa yana bubbuga bayana, ya maido bakin sa dab da wuyana numfashinsa na sauka a wuyana ina jiyo bugon zuciyarsa da karfi tana bugawa... Duka na kai masa kirjinsa na saki kuka nace"Wlh Sir Kangiwa bana gani wayyo umpah kazo ya kasheni..." da sauri Kamal ya dora hannunsa saman bakinta yana murzawa a hankali, ta lafe luf jikinsa. Kamla yace"Innalillahi wa'inna ialaihir raji'un!! Mubeena muje hospital ko?" kai na ɗaga masa ina zubar da hawaye. Kamal ya goge min hawayen fuskata, ya kwantar dani saman kujera yace"Ok bari na shiga na ɗauko maki hijab nayi alwalla kinji Mubee." ya faɗa yana shafa fuska. Kai na ɗaga masa ina zumburo ɗan karamin bakina. Kiss ya rankwafa ya manna mani a agoshi ya buɗe motar ya fito ya murza key daga waje dan sam zuciyarsa bata yadda ba cewar idanunta sun ƙi buɗewa, kawai dai wahala take son bashi. Murmushi ya saki ya tura hannunsa tsakiya sumar kansa ya shafi tattausar sumar kansa, jiya yi ana kiran sallah la'asar. Anutsu ya nufi ciki yana ƙarƙaɗa makullan motarsa. Garba ya nufo Kamal da gudu yana washe baki yace"Yallaɓai barka da zuwa kaga namijin duniya , ɗa ɗaya tilo wajan Abubakar Kan Giwa Mai Nasara..." Kamal yace"Garba a yanzu dai ka barni na sami nutsu ina cikin wata yar matsala wacce idan ta girma zanji kunya a idanun duniya na makanta...." ko me ya tuna yay saurin cewa"Bari na nutsu sai kamin kiraranin Ok." yana faɗin haka yay cikin gida. Garba yayi dariya yace" to wa ya tabo mana Oga kuma?" kofar parlon ya danna ɗan madanin ya shege da sallama. Samha ta tarbe sa tana dariya tace"Yaya Kamal gwara da Allah ya kawoka zo na zuba maka kunun alkama da nama Zakiyya da kaina , wlh yayi dadi." ta faɗa tana dariya. Ummah ta kurba ta ajiye cup ɗin hannunta tana dariya tace"Kamaluddin ya naga kana gama fuska naga ai kana son kunun ko baka jin yunwar yamma?" Hafsat tace "my son ya dai kai dawa wai?" Kamal ya saki hannun Samha ya kara sa wajan Hafsat yace"Wlh momy an ɓata min raina ne amman nima naga abin bai kai ya ɓata min raiba, amman wlh ya ɓaci gashi kamar zan shiga cikin wata ƴar matsala , pls idan kunyi Sallah yanzu ku sani a cikin Addu'a kada Allah yasa wannan abun ya zama gaskiya, momy yaushe kika zo ne ina yini bari naje na dawo , Zakiyya saura ki shanye kunun nan kiga yanda zamuyi uwar ci ina Ummah tane?" ya faɗa yana haurawa saman bene. Ummah tace" gata nan kuwa tana bacci ai yanzu zan tasheta na mata wanka , Ai Addu'a kullum cikin yinta muke ɗan albarka babu abinda zai sameka na sharri se alkhairi." ummah ta faɗa tana miƙewa. tace" Zakiyya tashi maza tinda kin koshi aje asha ruwan zafi." Hafsat tace"lallai fa kam Samha ya dai anyi shiru yayanki zai sha yace ransa ne a ɓace wai." Hafsat ta faɗa tana kallon Ummah. Ummah tace"Kamaluddin kenan ya huce ai shida abokan kasuwanci ai su kullum burin su su kuntata ma wanda zai sauƙaƙa kayansa cikin sauƙi domin talakawa suji dadi , to basa so." Zakiyya ta miƙe tace" Allah ya fisu." Hafsat ma ta miƙe domin ɗauro alwalla se su Ameer kawai suna wasa, dan ganin yanayin fuskar uncle Kamal ta hana su bishi sama.
Kamal yana hawa sama bedroom ɗin Samha ya shiga ya sato hijab dogo har ƙasa ya saka cikin leda ti kun ya fito ya wuce bangaran sa se da yayi wanka saboda yadda yake kin zafi ya ɗauro alwalla ya fito, ya shirya ya saka wani yadi ruwan ƙasa me shegen kyau ƙaramin ɗinki ne mai masifar kyau ya fesa sansanyan turare ya kwashi wayoyinsa da makullan motarsa ya fice...
Kamal yana hawa sama bedroom ɗin Samha ya shiga ya sato hijab dogo har ƙasa ya saka cikin leda ti kun ya fito ya wuce bangaran sa se da yayi wanka saboda yadda yake kin zafi ya ɗauro alwalla ya fito, ya shirya ya saka wani yadi ruwan ƙasa me shegen kyau ƙaramin ɗinki ne mai masifar kyau ya fesa sansanyan turare ya kwashi wayoyinsa da makullan motarsa ya fice...