← Book details Ali Dan Tsoho Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 60 OF 124

Sashe 60

Ali Dan Tsoho Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Mubina kuwa jin Kamal yay shiru yasa tace"Deen bazaka min mgn ba? Allah zan tsinke kiran." ta idar da maganar a shagwaɓe. Kamal tsinke kiran yay jikinsa na rawa ya tura hannunsa daku cikin gashin kansa, yace"Wlh ba zanyi kaffara ba Mubina cikina gareta tabbas cikine da ita, kuma cikina ne ni shedane..... Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un!! Da sauri ya tura mata text kamar haka. ```"Baby Yaushe rabonki da kiyi peroad ne? kuma da aka kai ki Hospital me aka ce kinada shi? Ƴan gidanku hankalinsu ya tashi da aka ce kina da wani abun? Pls ki bani amsa yanzu...?"```. Haka ya tura mata. Mubina kuwa da ta gama cika tayi fam ta miƙe tin lkcn da Kamal ya tsinke kiran ta shirya kanta cikin kayan bacci, ta ɗauki wayar zata nufi ƙasa taga sakon ta buɗe tana gani ta murguda baki cikin tsiwa ta tsaya ta tura masa haka. *😏"Ban saniba mun ɓata kabar ɓata lkcn ka wlh wlh bazan faɗa maka ba koma meye, na fasa da naso faɗa maka irin zalumcin da wani shegen gurgu yamin ya gudu daga ƙasar, amman na fasa ka nemi wata ƙawar ni na fasa, tinda kai ɗan wulaƙanci ne dan kaga ina son murmushin ka na sani jin farin ciki, shine zakana mani wulaƙanci kuma kana kashin kira, na faɗamaka damuwata baka tayani jajeba ko neman magani, zaka wani kawomin gulma wai ya ƴan gidan mu suka ji haushi to sokaji tafi can na fasa abontar kuma zan kashe wayana yanzu nan ma."🤨🤨🤨* haka ta tura ma Kamal ta kashe wayar tana zumburo bakinta gaba, tana jin bazata iya dogon fushi ba da ɗan kurma tana buƙatar murmushinsa tana jin daɗi sosai. Haka dai ta fito ta nufi ƙasa.

Kamal yana ga sakon Mubina ya dafe kansa ya miƙe tsaya yay dailing ɗin number ta amman Switch Off. A hankali ya furta "Am Sorry Mubee kinada cikina ko tantama bana yi, Kuma Wallahi ina son abina , ina son cikina se nabi duk hanyar da zanbi karki zubar min dashi, wlh ina son abuna, halamu sun nuna min Mubee bata san tana ɗauke da cikina ba sam..." ya faɗa hawaye na kwaranya kan fuskarshi. Zirganiya ya fara cikin katon parlon sai kai komo yake murɗaɗɗɗan jikinsa mai ƙirar ƙarfafan maza haɗe da faffaɗan kirjinsa mai yalwar gashi sai sama da ƙasa yake, yana zagaya parlo yana faɗin "Mubina cikina a jikin ki ba a banza ba naji na damu dukan lamarin ki kin tsayamin ciki Qalbina , ashe gudan jinina ke yawo a jinin ki." ya kai ƙarshen maganar yana dailing ɗin number Hafsat, bugo ɗaya ta ɗaga tare da sallama. Tace"Kai My son bakayi bacci ba yanzu garinku dare fa yayi ko?" Kamal ya tura hannunsa cikin lallausan sumar kansa muryasa a raunane yace"Momy don Allah wani aiki zan saki pls ki temaka min karta zubar min da cikina, dan nasan iyayanta sunada Tauhidi sosai baza su fara kisaba amman ita idan ta gano ko saboda tsantsar kiyayyar da take mani zata iya zubar min da cikina , niko wlh ina son abina ɗan kaddara ne wannan yaro ko yarinya ina sonsa sosai fiye da kaina wlh momy..." Hafsat jikinta ya ɗauki rawa cike da mugun mamaki ta miƙe ta matsa daga parlon dan tana tare da Maheer mijinta.

Tana shiga bedroom ta rufo kofa tace"Anya da Kamal nake waya kuwa?" Kamal yace"Nine Momy zan maki bayanin kome yanzu abinda ya faru dani har Abbu yace nabar garin da yanda nake kiranta har muka shaƙu a zaman ni kurma ne... Kuma yanzu na gano ciki ya shiga kuma ko shakka banayi ciki nane." Kamal ya zaiyya nema Hafsat abinda ya faru shida Mubina da barinsa gari da zuwa yau da ya gano cikine da ita.

Hafsat tsabar kaduwa wayar ta kufce mata ta fadi ƙasa, sai da sunkuya ta ɗauka amman bata fashe ba. Kuka ta saki tace"Kamal me yasa kama ƴar mutane haka amman su waye suak haɗa maka wannan tugun dan nasan bayain kanka bane.?" Kamal yace su Mounkaila ne amman ku barsu a kullum a gaban kabah se na kai kukana gun Allah ya masu fiye da abinda sukamin, kuma nasan lkc na tafe, momy abinda nake so yanzu gobe kije can gidan su Abbu kiji suna lbrn cikin ko ba suda? ina son kisan yanda zakiyi ki sakata a jikinki don Allah kar ki bari ta ɓarar da cikin nan pls momy." Hafsat tace"Ai dole zani gida gobe kamar yanda suka ɓoye min zan ɓoye masu kome ai kuma ita bata sanni ba zan zo mata nice Aunty ɗan kurma na sakata jikina da izin Allah se ta haifo mana gudan jinin mu kuma sai ta soka so me zafi wanda a lkcn ko ta gane kaine Kamal bazata taɓa rabuwa da kaiba, zan nemi Sageer naji ko ya san kome.." Kamal yace"No momy bana son ta soni ta auri wanda take so burina ta yafemin laifinn da na mata, kuma ta haifamin ɗana ko ƴata bass ya isa Allah ya basu zaman lfy can su saka sani bai shafeni ba! Ta haihu na amshe yarona kawai..." Hafsat tace"Hummm Kamal kenan Tom naji hakan za'ayi se goben zakiji yanda mukayi zan je mata a matsayin Auntynka." Kamal yace"I love you momy good night." yana faɗa ya tsinke kiran, ya share hawayen fuskarsa, tausayin Mubina ya lunku a cikin zuciyar sa ya rasa me ke masa dadi sam. Saman kujera ya faɗa ya lumshe idanunsa, ya buɗe yay dailing ɗin number tata har yanzu switch Off. Kirane ya shigo cikin wayar sa, picking yay ya kara a kunnensa yana share hawaye cikin amon muryasa mai daɗin sauraro, yay sallama. Wata ƴar matshaiya ce mai nagartaccen kyau chocoulet coulor ƴar duma duma se bata breast manya ƴan kananu dasu, se dai taji dogon hanci da baki mai ɗan faɗi, bazata wuce 17 year ba! kananun kitsone a kanta jelar ta ɗan zubo iya wuyanta, kwance take saman katuwar katifarta, daga ita se ɗan gutun wando da riga na bacci ta lunshe idanunta, ta buɗe baki a hankali tamkar bata son mgn tace"Wslm uncle Kamal ina yini i miss u so much." ta faɗa tana raraba idanu. Kamal ya sauke ajiyar zuciya can ƙasan maƙoshi yace"Uhm Umaimah miss u too yasu Kawuna?" cikin farin ciki tace"Lfy lau nayi ta kiranka fa baka ɗauka ai nazata Dady bai faɗa m

aka ba ya sayan waya, ashe kasan muryata wayyo daɗi." ta faɗa tana murmushi. Kamal ya dafe goshinsa ya fesar da iskar bakinsa me zafi yace"Umaimah yanzu bana jin daɗi amman zan kiraki zuwa gobe insha Allahu muyi hira kinji ƙanwata." Umaimah tace"Ok Uncle ka kular min da kanka pls kaji?" Kamal ya dan sakar mata murmushi yace"Ok insha Allah ƙanwata bye se da safe ki fa yi karatu kinji?" Umaimah cikin farin ciki tace"Ok uncle love u so much." tana faɗa ta kashe kiran tana dariya tana brigima saman katifa.

Kamal kuwa baki ya taɓe ya miƙe ya nufi bedroom domin ya sake wanka ya fara bautar Allah dan bacci yake ji ga tarin damu a zuciyar sa, amman dole zai kai kukan sa wajan Allah da kuma neman gafarasa duk da yasan bashi laifi gun Ubangijinsa, tinda yayi abune baya haiyacinsa, ba kuma yasha kayan maye bane yana sane, amman dole zai ta istigifar, da Addu'ar Allah yasa abin cikin Mubina ya fito duniya lafiya...

Mubina kuwa bayan ta turama Kamal sakon ta nufi ƙasa cikin sanyi da jikinta yayi ga kasala da tashin zuciya na damunta ga wani irin feelings da take ji kan murmushin da ɗan kurma yake mata. A nutse take taka step ɗin tana zumburo baki, tana dab da saukowa taji Umpah na gaya ma su Mamu da Ablah da Kabeer da Amrah, yana cewa"Alhamdulillah jibi karfe 10 am jirginmu zai ɗaga zuwa London nida Baby da Abubakar Biza ta fito, don Allah kar ku bari Mubina tasan tana da ciki har sai munje can zan faɗa mata , na mata nasiya har ta fahimta tayi hakuri ta amshi ƙaddara kamar yanda muka amsa..." Ihun Mubina sukaji da uban karfi ta ɗora hannunta akai tana cewa"Umpah waye zaje London? kuma waye me cikin shege? ɗin nice mai ciki Umpah ni nakeda ciki...?" tafaɗa tana baya luuuuuuuu.........Wlh banji daɗin jikina, yau kuyi manage

*Wannan littafi na kudi ne ki biya kiyi karatu cikin salama, da kuma kwanciyar hankali, duk me so zaku tuntuɓeni ta wannan lambobin*
*👉🏻+22792589446/ +22796515805*alliya:
*KAMAL NE*

*Book 1*

*Bismillahir Rahamanir Raheem*

3️⃣5️⃣
Chapter 60 · 0% Book details