← Book details Ali Dan Tsoho Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 63 OF 124

Sashe 63

Ali Dan Tsoho Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hafsat idanu ta zaro cike da mamaki ta riƙe Mubina wacce fitsari ke bin ƙafafunta, jikinta na kyarrrrma tana neman sume mata, tace"Ya salam Mubina ki nutsu ni baƙuwace gunki nazo , Auntyn Abokin ki ce ɗan kurma." ta faɗi tana girgiza Mubina ɗin.
Ai kuwa Mubina a take ta sauke wata ƙatuwar ajiyar zuciya, ta ririƙe Hafsat ɗin tana sauke ƙatuwar ajiyar zuciya, ta ɗago da kanta, ta zubama Hafsat shanyayyun fararan idanunta, wanda suka rikiɗe suka fara yin Ja.
Cike da kunya ta janye jikinta tana sauke ajiyar zuciya, kunya ta gama cikata, cikin sanyi murya tace "Ina yini to ya kika san gidan mu?" Hafsat tayi murmushi ta kama hannun Mubina suka nufi gun motar.

Mubina duk a tsorace! Take da Hafsat, dan tana kallo yanayin Kamal a tattare da ita sosai.
Hafsat tace"Haba Mubina ki yarda dani mana nifa macace ta ya zan cutar dake , wlh ɗan kurma ya aiko ni." ta faɗi tana buɗe mota ta dauko gorar ruwa ta iso gun Mubina wacce ta kafeta da idanunta, dan ta gama gano Hafsat tsaf. Ta beƙa ma Mubina gorar ruwan tace "Amshi kisha ki nutsu mgn zamu akan ɗan kurma." Mubina sam taki na'am da Hafsat, gabanta se faɗuwa yake, tana amsar gorar ruwan ai kuwa ta sheƙa da gudu ta nufi get ɗin gidan su, tana buɗe kofa ta shige ta tsaya tana maida numfashi, ta leƙo tace da Hafsat,
"Ke!! Ni zakima wayo ba wani ɗan kurma ƙaryar banza da ta hofi ke ƴar gidan su Kamal ce , ga kama nan kuma haihuwar Zakiyya da muke yawan shiga wollah na ganki , a gidan , kuma ai Kamal zai girmeki tafi can wa zaku yaudara ku bani ruwan jaraba nasha cikin ya zube ko? To baza a shaba , shi ɗan jaraba har ya sami lbrn abokina kurma ko? To kice masa wlh yabi a sannu idan na kamashi wlh idan ya bari ya shiga hannuna , zai raina kansa, kuma cikin sai an haifeshi mugun banza katon kwarto dashi kawai,😜 to ɗan kurma nah yafi karfinsa, zansa ya ɓabɓallashi yasin , kice masa Mubina ba sakar mace bace ina da wayo da kaifin basira, kice ya shirya kamuwa da ciwon zuciya, ɗansa se yazo duniya😜. Ta karashe mgnr tana mata gwalo ta rufe get da karfi, a cikin ma gudu take tana kira Mamu da Umpah da Ablah....

Yo Hafsat me zatayi idan ba dariya ba! Dariya take sosai ta shiga mota tana ƙokarin turama Kamal video ɗin da ta ɗauki Mubina. Tana tura masa ta whatsapp, ta kirashi wayar switch off, key tama motar tabar gurin, tana dariya harda kwalla take, ga tausayin Mubina fal cikin ranta.!

Mubina haka ta nufi ciki da gudu tana kiran su Mamu, Baba megadi na tambayarta bata saurareshi ba! Ta wuce. Parlon ta shigo Mamu zaune tana waya, Mubina ta fado kanta, tana maida numfashi. Mamu ta tsinke kiran tace"Subahanallahi! Baby ke dawa kuma? Baki tafi ba?" Mubina ta ruƙumƙume Mamu tace"Mamu Kamal ne ya turo wata ta saceni, Allah ne ya tsareni ni na fasa zuwa gidan su Basma ɗin ma, bari naje na cire rigar fitsari na mata fa." ta faɗi tana sakin Mamu ta miƙe ta nufi sama. Mamu tace"Mubina fitsari kuma? Inane kika ga wacce zata sace kin? Kawai de kinji tsoron cewar yana gari ne." Mamu ta faɗa tana mikewa tabi bayan Mubina ɗin.

Mubina tana shiga ta iske Amrah tana waya se wani lauɗi taje. Kayanta ta cire ba kome jikinta, tace da Amrah " Wlh ki kiyayi maza fa tau." ta faɗi kai tsaye bathroom ta wuce ta watso ruwa, ta fito ɗaure da towel. Mamu ta iskota a tsaye, Mamu tace"Baby wacece tazo sace ki?" Mubina ɗan ƙaramin bakinta ta zumburo gaba batayi mgn ba, ta nufi wardrobe ta ciro siket dogo ta saka ta ciro vest ta saka ko bra bata saba ta saka pant, ta ɗauki wayarta ta iso gaban Mamu tana ɗaga mata hannun, tace"Mamu goyani ni goyo nake so." ta faɗa tana diddira ƙafafunta. Mamu ta kama hannunta suka nufi kofar fita, Mamu tana cewa "Bazaki faɗamin waye ya tsorataki a waje ba." Mubina tayi shiru tana turo baki. Amrah da idanu ta bisu tana dariya har suka ɓace mata.

Suna sakowa ta maƙalkale Mamu tana kukan sangarta se ta goyeta. Ai fa dole sai da ta goyeta tana zagawa da ita a parlo tana kyalkyala dariya, tama manta abinda ya faru awaje, dan akwai son goyo, duk fushin da take kana goyata zata shiga farin ciki. Haka Ablah tazo ta same su, Mamu tana goye da Mubina suna zagaya parlo tana kyakyala dariya, daɗi kamar ya kashe Ablah, se tausayin yarinyar fal zuciyarta, ashe kamar Mubina na ɗauke da cikin shege, amman sam bata damuba wai dan ta ƙuntatawa wanda yama cikin....

Misalin karfe 8:00 pm Su Iyamu suna zaune, ita Leeza a parlo Iyamu tayi murmushi tace " My Leeza kinsa kuwa Tukur da Mounkaila suna so su raina mana hankali kuwa?" ta faÉ—a tana kallon Leeza. Leeza tace,
"Au se yau kika sani kenan basuda lkcn kiranmu se zasu cimu fa, kuma alkawalin kudinmu sun cinye gashi burinsu ya ciki Kamal baya gari , kuma wlh kwana biyu company nasu ya bunƙasa fa sosai..." Iyamu zatayi mgn kenan wani yaro ya kwada sallama tsakar gida. Leeza ta leko tace"Uban wa kake nema?" yaron yace,
"Aunty wani Alhaji ke sallama a kofar gida." Leeza tace "wa yace maka?" yaron yace "Bai ce min ba..." Leeza tace "Muje na gani." ta faÉ—a tana fita kanta ko É—ankwali babu.
Iyamu ta leko tana cewa"Durin uwa yasin se naje nima naga waye." ta faÉ—a tana bin bayan su.
Tsaye yake jikin motarsa ya haɗe cikin wata ɗanyar shadda gizna maroon coulor yayi kyau sosai, duk da ƙarancin hasken wajan bazaka gaza gane yanda yay kyau ba.! Leeza tin kafin ta iso yawunta ya tsinke a kansa, bata san lkcn da tace,
"Wow gaskiya wannan mutumin ya hadu kamar shine ranar muka hadu a cikin keke napep?" ta faÉ—a tana isa gunsa da sassarfa, ko jan aji ma babu Leeza ta isa gunsa, da sallama.
Murmushi yay yace"Ƴan mata ykk ya jin daɗinki?" Leeza tai fari da ido tace"Wlh sumul ƙalau." Iyamu ce ta isu gun tana kallo Ibrahim tace" Hy ykk?" murmushi yay yace,
Lau nake, yauwa ke nake son gani daman yanzu zan tambayi ƙawarki ko yayarki oho maku." ya faɗi yana watsa mata shu'umin kallo. Iyamu cikin murna tace"Wow naji daɗi sosai gani kuwa, pls my Leeza ki shiga ciki har mu gama yana son mgn dani Ok."
Leeza ta haɗe rai kaɗan taji wani baƙin ciki da kishi ya turnuke mata zuciya, amman ta waske ta saki murmushi tace, "Ok sai kin shigo." ta faɗa tana juyawa, ta nufi ciki.

Ibrahim yace " ƴan mata ykk ya jin daɗinki? Ni sunana Ibrahim ni mutumin Kebbi ne nazo wani business ne da wani hamshaƙin ɗan kasuwa , se dai kashh kuma baya gari amman zan jira shi har yazo, but bama wannan ba, tin ranar da na ganki cikin keke napep kika shiga raina shine nayi yanda na biyo ki har naga gidan ku, da fatan zan samu karbuwa a zuciyarki.?" ya faɗi yana kallonta.
Cikin farin ciki marar misaltuwa iyamu tace"Wlh nima tin ranar kake manne a zuciyana kawai de dan naga baka ko kallemu ba shiyasa na hkr, ashe ina manne a ranka." ta faɗi tana ƙoƙarin shiga jikinsa.
Da sauri ya matsa yace"Kibar sauri mana ina zuwa kan wannan gaɓar, yanzu de zan wuce tinda na ganki." ya faɗa yana buɗe gaban motar ya ɗauko leda shaƙe da kayan ciye ciye ya bata haɗe da zunzurutun kudi har 50000F wato jaka hamsin cefa. Iyamu dan murna rungumesa tayi tana ƙoƙarin masa kiss, ya kwace jinsa yana mai farin cikin yarinyar zai sayeta da wuri.
Mota ya shiga yace" sakamin number ki zan kiraki." ba tare da ɓata lkc ba Iyamu ta saka ma Ibrahim number ta, ya mata sallama ya tafi, yana murna zai samu lbrn kome ta hanyar sakar mata kudi, dan bazai fara shashanci ba da ita.

Leeza da take laɓe tana kallon duk abinda ya faru, kishi ya turnuketa ganin Iyamu ta nufo ciki da murna tayi maza ta shiga ɗaki ta kwanta.
Iyamu da ihu ta shigo tana cewa"my Leeza yasin nayi kamu me kyau ke kinga mutum ba baƙin ciki ga maƙuddan kudi ga siyayya." ta faɗa tana zama. Leeza ta shiga murna tana cewa"kai naji daɗi Allah ya sanya alheri." nan Iyamu taba ma Leeza lbrn yanda sukayi da Ibrahim ɗin, nan suka baje suna cin kaza dasu ice cream
ana murna banza ta samu😂...

Ibrahim yana barin kofar gidan su Iyamu ya kira Hafsat, yana faɗa mata yanda yayi da yaran da ya hadu dasu yaji ɗayar ta ambaci sunan Kamal. Nan Hafsat ma bata ɓuye masa kome ba game da abinda Kamal ya gaya mata, harda cikin da ke jikin Mubina da irin abin dariyar da Mubina ta bata yau, har video ɗin ta tura masa, se dai sam ta manta da wani Mounkaila da ya faɗa mata. Nan ya faɗa mata yasan mgnr fyaɗen se dai bai san na cikin ba! Dan haka jin harda ciki ya baiyana Ibrahim yaji babu daɗi amman ganin video ɗin Mubina yarinyar ta bashi dariya sosai haɗe da tausayi, ya ɗauki damarar gano gaskiya sai ya samu gaskiyar al'amari...
Chapter 63 · 0% Book details