Sashe 47
Ali Dan Tsoho Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kwance yake saman makeken gadonsa wanda yaji lallausan zanan gado, tinda ya dawo daga masallaci, daga shi sai gajeran wando ko riga babu a jikinsa faffaɗan kirjinsa mai yalwar gashi a waje sanyi Ac sosai na ratsa murɗadɗan jikinsa ta ko ina, ɗakin sai sansanyan kamshi ke tashi, idanunsa a lumshe se zazzafa numfashi yake saukewa yana motsa jajayen lips ɗinsa, a hankali baka jin abinda yake faɗa. Wayar sa da take gefen sa ta ɗauki ringing, bai ko buɗe ido ba bare yaga me kiran, se ma birkitawa da yayi yayi rigingine ya matse pillow kirjinsa, still idanunsa a rufe, wayar seda aka kira sau biyar bai ɗauka ba, aka kira ɗayar ma sau biyar, yama ƙi buɗe idanunsa, dole aka hakura.
Ummah na zaune parlo tana girgiza Fatima na kuka Samha kuwa da Zakiyya suna kitchen, wai alala suke. Abbu ya shigo da sallama. Ummah ta amsa tana kiran"Ke Zakiyya rabu da alala nan kizo gun Æ´arki jibi dai zata garinsu can tama kakaninta rigima." ta faÉ—a tana murmushi. Abbu yace "Fatima ina Kamalu?" Ummah tace"Yana ciki ko." Abbu baiyi magana ya haye sama. Ummah tan masa mgn bai de saurareta ba ya haye.
Umpah cittè ya biya dan shine ke driving ɗin suna zuwa kofar gidan Baffa Inusa yayi parking suka fito, yana riƙe da hannun Mubina suka shiga.
Parlo suka shigo sallama. Inna na zaune yara sun zagayeta tana raba masu gyada ta amsa. Amrah ta ruga ta faɗa kanta. Mubina tace"Kai Aunty karki kashe min ita mana, inna ina Baffa ne?" Umpah ya sunkuya har ƙasa ya gaishe da inna" Inna tace"Abdulrahim kaine da rana haka? barka zuwa, ke Amara kike ko wama? ɗagani karki karyani Mubina zo mu gaisa." Mubina ta karasa ta zauna cinyar inna tana dariya tace"Inna wai ina Baffa ne?" Amrah tace"yana yawon nasa da ya saba ko..." Umpah yace kinci gidanku..."Inna tace"Barni da ita jari ina Fatima ɗin?" Umpah yace"Duk suna gaisheku." inna tace"muna amsawa kunzo kuwa ya fita sunje madaroumfa gun gaisuwa nasan yanzu suna hanya ma." Umpah yace"To a gaishe su su Mubina zasu dawo masa ban gajiya." ya faɗa yana zaro daurin yan dari dari ya ajiye masu yace"Ku tashi mu isa kar a fara ruwa akwai hadari sosai." Inna tace"Masha Allah Allah yayi maka albarka ku gaishe damutanan gidan." ta faɗa tana ɗaurama Azeema gyada ta bata. Umpah yaba su habiba da Nura da sauran yaran jikokin inna ɗiyan kannin Mamu jaka guda, sai murna suke suna ihu. Suka masu sallama suka fito, inna har kofa ta rakosu tana riƙe da hannun Mubina har mota se da suka tafi taja tawagarta cikin gida, tana sakama Umpah Albarka...
Umpah suna fita kai tsaye *Kalla transa mall* ya nufa domin jidarma Æ´aÆ´ansa duk abinda suke so, ya samu de gobe Mubina ta koma makaranta.
Cikin shiri ya fito yana taka steps cikin nutsuwa tamkar ƙafarsa batada wata illa sai ka ƙura masa idanu zaka gane yana ɗan ɗingisawa, ba ras yake ba, wata ɗanyar Shadda milk coular ce me danƙo ɗunkin zamani kansa ba hula haka yaba lallausar kwantacciyar sumar kansa damar kaɗawa gashinsa baƙi suɗik mai sheki sai ƙadawa yake yana baza kamshi, ya gyara uwar ƙasumabar da ya tara ya tajeta haɗi da sajan da ya zagaye fuskarsa yayi masa kyau sosai sai baza kamshi yake, idanunsa baƙin glass ya saka baka ganin kwayar idanunsa, amman hakan bai hana zallar baiwar kyaawunsa fitowa ba. Yana saukowa ya isko Abbu da Ummah dasu Samha suna cin alala suna hira wasa da dariya, sannu ya masu suka amsa kamar kullum. Zakiyya ce ta miƙe tana cewa"Uncle zo kaci alale akwai dadi wlh..." Lallausan murmushi ya sakar mata yace"No Zakiyya tnx kici de Samha ba tayi ma?" ya faɗa yana murmushi. Samha tace"Wlh na fitarma bara na ɗauko ma." ta faɗa tana miƙewa. Kamal yace"No ku bari na dawo zanyi tafiya ne zuwa zinder gobe nake zauwa." Ya faɗa yana isa gun Ummah ya zauna ya rungumeta ya mata kiss yace"Se nazo goben, Abbu na tafi se goben ko?" Abbu yace "Eh Allah ya kaimu ka kula da hanya kayi tuki da nutsuwa." Kamal yace"insha Allahu Abbu." Ya faɗa yana rungumeshi ya sake shi ya miƙe. Ummah tace "Allah ya kiyaye sai ka dawo." Kamal yace "Ameen ummah sai na dawo Samha Zakiyya sai na dawo." ya faɗa yana ficewa daga parlon. Samha tace"Yaya Kamal karka manta ɗa Alkaki don Allah." daga can yace "Tom insha Allahu." ya faɗa yana karasa fita daga parlon.
Zungureriyar Jeep baƙa ya shiga, Garba ya iso yana masa kirari yayi murmushi yace"Garba manya yanzu amshi nasan ita akewa" ya faɗa yana bashi yan mille francs cfa guda biyar sababbi fil dasu. Garba ya washe baki sai kirari yake ma Kamal. Kamal ya rufe motarsa ya fizgeta yayi bakin get, yana zuwa aka buɗe masa get ya sulala motar waje ya kwasa aguje.
Kai tsaye ```Kalla transa mall```ya nufa domin sayan wasu abubuwa da zai buƙata a hanya.
Mubina bayan ta gama zaɓar jaka da takalmi, Amrah ta sata sosai suke jidar kaya ita da Amrah ɗin, Umpah dai tinda ya ma Mamu da Ablah sayayya ya koma gefe ya zauna yana jiransu su gama, dan sun nutsa can ciki dayawa. Mubina bayan ta kwashi coucolety kala kala sai ta kewaya wajan ice cream ta fara jida sai taji sha'awar sha sai ta buɗe roba ɗaya tana tafe tana sha ta nufi wajan turaruka taji Amrah na kiranta cewar an fara ruwa robar ice cream ɗin ta yar ƙasa, kayan ta fara turawa niki niki tana turo baki ta kasa ta barsu nan da sauri tayi kwana tana cewa"Aunty kayana bazan iya turawa ba ina masu aikin gun..."Bata kara saba ta afka jikin mutum tayi kwance kirjinsa. Jin mace ta faɗo jikinsa a zafafe ya ingijeta daga jikinsa yana huci ya kalleta, da niyar mgn, se yaga Mubina ce ta tafi luuuuuu zata faɗi ƙasa tana kiran"Wayyo Umpah" Idanu ya zaro bakinsa na rawa yace"Mu... Bi... Na... Ke...Ce...?" ya faɗa yana tarota cikin zafin nama, da sauri ta faɗo sama faffɗan kirjinsa ya tarairayota sosai cikin jikinsa, yace"Mubina Sorry ..."Mubina a mugun tsirace!! Ta ɗago kanta jikinta na kyarrrma, bakinta na rawa, tace"Ka...mal..." Dif numfashinta ya ɗauke ta sume masa ta langwaɓe a kirjinsa. Kamal ya rikice yana girgizata yace"Mubeena pls tashi wallahi babu abinda zan miki ki yarda dani, pls ki daina tsorona haka, Mubeena." Ya fada yana ƙamƙameta cikin jikinsa, zuciyarsa na mugun bugawa da karfin gaske, kamar zata fasa kirjinsa ta fito, sbd bugun da take da karfi... Kamal ya rikice ya rasa me zaiyi ya ma zaiyi jin muryar Amrah da umpah suna kiranta dan sunji ihunta. Kamal ji yayi sam bazai iya barin Mubina ba cikin wannan halin ya ɓuya, kawai Cak ya sumgumeta sama....
*Wannan littafi na kudi ne ki biya kiyi karatu cikin salama, da kuma kwanciyar hankali, duk me so zaku tuntuɓeni ta wannan lambobin**KAMAL NE*
*Book 1*
*Bismillahir Rahamanir Raheem*
2ï¸âƒ£7ï¸âƒ£
Cikin zafi nama da kuzarin sa irin na Jarumai karfafan maza, yay saurin yin kwanar da Mubina ta fito, yana rungume da ita ko wacce irin Addu'a tazo bakin Kamal yi yake, na Allah ya kubutar dashi daga faÉ—awa wani Azal É—in. Wani É—an lungu ya shige da ita, gun tarin nunus ne a gurin, ko ka shiga ba me ganin ka.
Kamal jikin Nunus ya jingina Mubina ya tallafo kanta, cikin rikita da mugun rauni a tattare dashi murya shi na sarƙewa yace, "Mubina ki tashi wlh bazan iya barin ki na gudu ba sam, tunda garin zan bari ban san halin da zaki kasan ce ba..."
Ya faɗa a cike da rauni yay sauri riƙeta sosai ya kai fuskar shi dab da tata, ya tallafo kanta sosai yay saurin dora bakinsa saman ƙaramin pink lips ɗinta me laushin gaske, ya sanya hannunsa can ƙasan laɓɓan nata daga, ya ɗan buɗe su, ya shiga hura mata numfashin sa da sauri-sauri yake busa mata numfashin sa. Wata irin ajiyar zuciya Mubina taja da karfin gaske tana sauke numfashi da sauri-sauri tana shaƙar daddaɗan kamshin bakin Kamal, amman sam bata haiyacinta tana dai numfashi dai sama-sama, tana kara samun numfashin Kamal tana shaƙa sosai, hakan yasa take sauke ajiyar zuciya sauri-sauri cikin bakin Kamal, amman bata gama dawowa normal ba.!! Kamal kuwa jin Mubina ta sauke numfashi da karfin gaske, kuma tana numfashi yay saurin zare bakinsa anata, da sauri, kuma dai-dai lkcn su umpah suka yo ta wajan har da security a guje suna cewa"Anya ba ɗaukarta akayi ba...?
Ko aje a duba ta CCTV Camera" Ai kuwa Kamal ya kwantar da Mubina nan ƙasa ganin tana fitar da numfashi, yay saurin janyo katon Nunus me Kan kare kato ya zalzalo harshe ya saita shi nan tsaye kamar na gaske, ya kuma janyo ƙarami guda ya manna mata hannunta ya buɗe chocoulet guda ya gutsiri rabi, ya manna mata sauran a bakinta, ya shafi kyakyawat fuskarta ya riƙe tattausan farin hannunta gam cikin nashi, yace"Ina miki fatan Alheri Mubina na damu dake matuƙa tausayin ki ya mamaye min zuciyana, haƙiƙa na cutar dake bisa kuskure ki yafe min, nasan Sageer zai riƙe ki Amana zai kular min dake bazai miki kallon wata fuska , haka kawai nakejinki kamar wata ɓare a tare dani a yanzu, bansa me yasa ba, kiyi rsyuwa me kyau tare da Sageer Allah ya baki zuri'a dayyaba, bye Mubina." ya faɗa yana tsiyayyar da hawaye yayi saurin kai hannunta bakinsa ya sumbata, yay saurin sakin hannun, ya miƙe yana barin wajan ta ɗayan bangaran yayi saurin ɓuya ya laɓe yana fitar da hawaye.