Sashe 89
Ali Dan Tsoho Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ummah kuwa suna zuwa gida suna shigowa parlo, sukaga Abbu cikin manyan kaya sai washe baki yake shida ibrahim da Abbansu Hafsat da Goggo da Sumaiyya da Hafsat, sai murna suke. Samha ta rungume Abbu tace.
"Abbu da gaske an aurama yaya Kamal Mubina?" Abbu ya jinjina kai yana murmushi yace ku barni da Kamal zai sani ai." Ummah tace.
"Abba sannunku Goggo Ashe duk kuna nan ina makota tayin murna ashe murna agidana...?" Ta faÉ—i tama zama.
Dariya su Hafsat sukayi, Goggo ta rangaɗa guɗa tace"Don Allah ku bani number Kamalu nice zan ƙirashi. Abba ya miƙe yace"To nidai na wuce kasuwa."Abbu ya miƙe zai rakashi. Ibrahim yace"Abba Allah huta gajiya numa zuwa zanyi na huta, tinda yaƙi ya ƙare."Goggo tace"yarona Allah yama albarka kam."Hafsat tace.
"Ameen bari na ƙira Kamal dan yanacan hankalin sa a tashe, na ƙurasa yau duk ban samesa ba."Ummah tace "Ai kuwa kam."Sumaiyya tace"Allah sarki ni wareni ake."ta faɗi tana kumburo fuska. Ibrahim yayi dariya ya miƙe yana cewa"ni na wuce gida."Ummah tace"Alƙah dai yamaka albarka me gidana."Dariya yayi ya wuce.
Da Abbu suka haɗu a compound ɗin gidan sukayi sallama, ya wuce shikuma ya nufo ciki ya ƙira Kamal ya wanke shi tass. Abbu yace"Fatima kinada number Kamal ta london?" ya faɗi yana kallonta. Ummah tace.
"Eh jiya ya ƙirani gata a wayar." Hafsat tace"Dan Allah Babban yaya karka masa faɗa, kaima kayi soyayya lokacin aunty Fatima ƴar buzuwa."Goggo tayi dariya tace"Ai ki bari ya masa tass wlh."Abbu ya amshi wayar Ummah yana murmushi ya fara duba gun ƙira ya ga number ko suna babu, yay dialing ɗin number ya manna a kunnensa. Wayar switch off, Abbu yace"Ja'irin yaro ya kashe wayar, ai kuwa duk motsi zanyi ta gwadawa har ta shiga."Dariya su Hafsat sukeyi Samha kuwa murna take sosai ta kasa zama waje ɗaya, Abbu yace"Saura ke nan kusa keda anwar."Da gudu Samha ta nufi sama tana dariya. Haka ƴan uwan suka kasance cikin raha tare da mahaifiyarsu cikin farin ciki, har suka watsa basu sami Kamal ba wayarsa a kashe...
*Can kuwa A london*
Kamal wuni yayi tunkur yana bacci sbd a daran jiya bai rumtsa ba, dakyar yay tashi yay sallar Azuhur ya sake komawa, bacci Mubina manne a zuciyarsa. Makel har ya gaji da zuwa yana knocking, haka yayi ƙokarin zuwa makarantarsu Mubina amman shiru bata zoba, cikin sa'a kuwa lokacin da aka fito da ita za'a kaita hospital, yana kusan gidansu a laɓe, dan yayi niyar idan yaga fitowarta sai ya saceta da wayo ya kaima Kamal, ganin sun futa a mota yasa yabi bayansu har hospital ɗin da sukaje, kuma yayi ƙoƙarin ganin room ɗin da aka sata, ya juya ya sake komawa hotel ɗin da Kamal yake, ya gaji bugun kofa shiru ya ƙira waya shiru, nan ya fara tasar da hankalinsa kar aje ko mutuwa Kamal yayi....? Kamal sai karfe yamma lis ya farka bakinsa ɗauke da salati yana miƙa ya buɗe manyan tsumammun idanunsa, tar yana kallon ɗakin ya lumshe idanunsa da suke masa wani ɗan zafi kadan ya waiga ya kalli agogon bango, idanuwa ya zaro haɗe da cewa"Ya Rabbi! Har 5 banyi sallar la'asar ba?" ya faɗi yana zuro kyawawan ƙafafunsa ƙasa ya saka takmin toilet ya kama handle ɗin kofar bathroom, yaji anata knocking ɗin kofar. Kamal yace"Makel wayyo Mubinata Allah yasa ka ɗan samomin labarinta a yau." Ya faɗi yana juyawa ya nufi parlon. Yana zuwa ya murza key ɗin jikin kufar ya buɗe. Ido hudu sukayi da Makel. Makel ya faɗa jikin Kamal ya rungumeshi yana sauke ajiyar zuciya da harshen turanci yace.
"Sir ka saka naji tsoro ko wani abu ya sameka lafiya ka kashe waya nayi sau yafi goma nan har ma'aikatan hotel sun fara tuhumata." Kamal ya rungume Makel yana dariya yace.
"Ai ni wlh ka tsoratani nima bansan ya akayi nakai warhaka ina bacci ba, plesae Sanyin idaniyata taje school yau...?" Kamal ya tambayi Makel yana janye jikinsa ya ƙura masa tsumammun idanunsa. Makel yace"Yanzu dai kasamu kayi breakfast sai muyi magana tana lafiya." Kamal yace"Alhamdulillah Ala kullu halin'! Ok haɗomin koda coffee ne." ya faɗi yana komawa ciki da hamxarinsa. Makel kuwa ya sauka ya nufi rasturant ɗin hotel ɗin. Kamal yana shiga ya haɗama kansa ruwan dumi yayi wanka ya dauro alwala ya fito daure da towel, ya goge jikinsa ya saka jallabiya ya fesa turare ya shimfida dauduma ya tayar da sallah. Yana gamawa ya jima yana Addu'o'i ya shafa ya miƙe ya cire jallabiyar ya ɗora saman gado ya shafe jikinsa da lotion mai mutuƙar daɗin ƙamshi haka gashin ƙirjinsa ma ya murjeshi da mai na musamman, ya buɗe trolleyn sa wacce Mubina ta watsar masa da kayansa jiya, yana sakin murmushi ya girgiza kai a hankaƙi ya furta"Sweetheart rigima ga fitina ga kishi, wai uwani ko jaka ma tako oho." Ya faɗi yana sakin murmushi dannjiya gurin ya masa daɗi, ko nan yasan ana sonsa. Ciro wata ɗanyar shadda mai masifar kyau green colour ya saka ɗinkin dan ɗagwas dashi, bai saka hula ba, sumar kansa mai yalwa sai walkiya take tana fitar da ƙamshi tamkar balarabe, ya gyara sajan fuskarsa da ƙasumbarsa wacce ta ƙara masa kyau, yabi duk jikinsa da sansanyan perpumes masu shegen ƙamshi ya fesa, lungu da sako na jikinsa, yana gamawa ya manna farin glass kan fuskarsa ya sake wani irin kyau tsadaddan agogo ya ɗaura a tsintsiyar hannunsa, ya murza zobe guda biyu ɗaya azurfa ɗaya gold, ya saka wani mahaukacin takalmi, kai kyau fa Kamal yayi sa ayau ba ƙarya. Wayarsa ya ɗauka sai lokacin ya kunnata, ya nufo parlo. Makel da yagaji da jira yana zaune, ganin Kamal yace.
"Wow Sir kayi kyau sosai kamar ango."Kamal zama yayi yana dialing ɗin number Mubina, amman a kashe, tsaki yaja yace"Oh my god ko wane halima take, oho Makel tashi muje ka kaini wajanta."Ya faɗi yana miƙewa. Makel ya riƙeshi yace"Please Sir kaci wani abu ma tin jiya babu abinda kaci fa."Kamal ya yamutsa fuska, ya ɗauki cup ɗin tea mai shegen ƙauri da yaji madara yakai bakinsa yana sha da zafi² yana haɗawa da gasashiyar cinyar kaza yanaci yana yamutsa fuska, dan hankalinsa ya tafi kan Mubina. Agogo ya kalla yaga karfe 6 saura ƙiris ya jiye cup ɗin yana miƙewa yace.
"Tashi muje neman sanyin idaniyata." Ya faɗi Yana koma bedroom ya wanke hannunsa da bakinsa Makel ya miƙe suka fito Kamal ya murza key daga waje ya zare ya saka aljihun rigarsa suka sauko ƙasa. Anutsu yake tafiya irin ta cikakkun maza yanajin ransa sama babu dadi baisan halin da Mubina take ciki ba.!! Mota suka shiga Kamal ya kame a gaban motar yayin da Makel ke zaune gun direba yama motar key suka nufi get, aka buɗe masa gate ya fice a guje ya hau kan titi yana sasharara gudu, Kamal ya lumshe idanunsa yana kikiga ƙafafunsa, yana feso da zazzafar iskar bakinsa waje....
Æangaran Mubina kuwa bacci kawai take, Ummi na gefe a zaune, tayi tagumi jin Umpah ya aura mata Kamal, ta jinjina lamarin kan irin bayanin da ya mata kan irin tugun da aka shirya masu ashe ba da gangan yaron ya rufar mata ba. Zaune ummin take tana riÆ™e da hannun Mubina tana bacci cikin nutsuwa. Majeed ne da Nabeel suka buÉ—e kofar suka shigo da sallama da kular abinci, da flask a hannun Majeed. Ummi ta amsa sallamar. Nabeel ya zauna kusan ummi yace"Bata farka ba tayi salla a tashe ta." Ummi ta murza lallausan hannunta tana Æ™iran sunata.
"Mubina tashi amraya kiyi sallah kici wani abun haba tun jiya bakyaci bakya sha oya tashi, Majeed ƙira nurse ta cire mata drip ɗin ya kusa gamawa, zazzaɓin ya sauka."Majeed ya fice yana mejin haushin da aka ɗaura mata da Kamal, dan Kabeer ya faɗa masa kome.
A hankali ta buÉ—e runanun idanunta da suka mata mugun nauyi ga zafi da suke mata ta sauke su kan ummi. Ummi ta kamata ta zauna, tana yamutsa fuska. Nabeel yace"Sannu Baby." Shiru Mubina tayi tana kallon ummi, da shanyayyun idanunta. Ummi ta haÉ—a mata tea mai zafi ta zuba mata haÉ—adÉ—iyar jalof É—in taliya da taji É—anyan kifi, bakinta takai cup É—in ta girgiza kai cikin sanyin murya tace"Ummi zanyi fitsari sai na wanke bakina É—aci yakemin." Ummi tace.
"Sannu bari acire drip É—in." Idanunta ta lumshe ta rungume ummi gam, tana sauke numfashi. Haka Majeed suka shigo da nurse ta cire ma Mubina drip É—in ummi tace.
"Muje to." ta faɗi tana kama hannun Mubina suka nufi toilet. Suna shiga Mubina ta shagwaɓe tace"Ummi kije zanyi da kaina ni har wanka zanyi jikina ciwo yake." ummi tayi murmushi tace"Gud amarya kina bacci har an ɗaura maki aure bakida lafiya." Wani irin fafuwar gaba, ya ziyarci Mubina tayi tagal² zata faɗi, ummi ta riƙota, ƙamƙame ummin tayi tace.
"Ummina da waye aka ɗauramin auren?" Ummi tace "Kinji Baby da wata tambaya waye gareki bayan Sageer da Sageer mana. Mubina ta waro manyan idanunta waje kamar zasu zazzago, sai ta jinjina kai ta ƙara shigewa jikin ummi ta lumshe idanunta wani irin raunine ya ziyarceta, jikinta ya ɗauki wani irin mazari, kawai sai ta fashe da rikitaccan kuka mai sautin gaske, cikin shasheƙar kuka take cewa"Tom ummi nayi farin cikin nima na zama matar aure, ummi ina Kamal ya sani ko? Kinga yanzu sai ya shafamin lafiya maye kawai." Ta faɗi tana ƙara sautin kukan haɗe da shasheƙa. Ummi jinjina girman son da Mubina take Kamal tayi, tausayinta ya kamata tace"Baby yi wanka ki fito kici abinci ki rama salloli sai na faɗa maki wani abu nasan zakiyi farin ciki, kinsa munata hira a toilet bayan babu kyau, yi haƙuri bari kukan kinji amarya oya yi sauri ki fito." Ta faɗi tana gogema Mubina hawayen da ke sintiri kan fuskarata yaƙi tsayawa. Dakyar ta samu Mubina tayi shiru ta haɗa mata ruwan gumi ta fito ta barta. Haka kawai Mubina taji zuciyarta na mata ƙuna wani irin tuƙuƙin baƙinciki takeji, ta rasa na meye, hawaye sai sunturi suke kan fuskarta, gazar² ɗin gashin idanunta kansu jagab suke sun jiƙe da ruwan hawaye, cire kayan jikinta tayi tana mejin zazzaɓin ya dawo maya, haka tana ciza lips ɗinta ta fara wankan....