← Book details Ali Dan Tsoho Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 122 OF 124

Sashe 122

Ali Dan Tsoho Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zuba mata tayi cikin babban cup ta saka mata sugar, ta kamo hannunta suka fito parlon. Zaunar da ita tayi tace"Amshi maza sha abinki zan kama Kamal zai sani ne." Mubina a hankali tace"Nagode Ummah." Ummah tace"Sha to bari naje na maki girkin ki me daÉ—i." ta faÉ—i tana komawa kitchen. Mubina Ummah tana tafiya ta fara shan kunun da sauri sauri tana tanÉ—ar baki, gashi tanajin zafi amman kunnun yay mata daÉ—i sosai, Samha tayi ta mata dariya.
Ummah girke² masu rai da lafiya taima Mubina, kuma taci sosai se da tayi sallar la'asar tace zata cikin gidansu. Ummah tace ta gashe mata da Mamu da Ablah. Parlon koda Mubina ta shigo ba kowa a cikinsa, zama tayi ta shiga ƙiran "Mamuna Ablah kuna ina ne...?" Mamu ce ta fito daga bedroom ɗin ƙasa, tace"Ah Auta ce?" Mubina ta ƙwaƙwaɓe fuska tace"Tin yaushe nazo ba kowa."Mamu tace"ƙarya kike Auta yanzu Abbanki ya shigo ina falon amman kice kin jima."ta faɗi tana zama kusanta. Mubina ta faɗa jikinta, tace"Mamu ina Umpah ɗin? Da Ablah?" Mamu tace"Ablah tana ciki, Baby yau kwana 8 har kin fara fita ya jikin naki?"Mubina tace"Mamu kimin tausa don Allah kinji." ta faɗi tana rungume Mamu. Mamu ta cire mata mayafin ta fara mata tausar tana lumshe idanunta tayi luf jikin Mamun. Umpah ya fito yace"Oyoyo Babyna ya jikin naki?" Mubina ta ƙwaƙwaɓe fuska taba Umpah hannunta. Zama yayi ya kama hannun nata a shagwaɓe tace"Umpah yanzu shine baku zuwa kuna duboni haka ake kun barni ni ɗaya bare." Umpah yay murmushin farin ciki ganin yanda ƴarsa ta warware ta murje tayi kyau sosai, yace"Sannu auta Allah ya raba lfy yi haƙuri mumyi laifi nida Mamu zamu gyara, ya Kamal ɗin yana lfy ko?" Mubina ta ɓoye kanta ƙirjin Mamu tace"Eh Umpah, har gidan anty munje fa."Umpah yay murmushi yana tausa mata jikin nata yace"Ai su jiya suka zo nan."Mubina tayi ƴar dariya tace"Nima kullum nazo ai."Mamu tace"Uhm sannu to Baby..."Ablah ce ta fito tace.
"Mubina saboda Allah kinzo ko ki nemeni? Oh rayuwa."Mubina ta mike zaune tace"Ablah kiyi haƙuri ke ta wajena ce fa, anamin massage zo kimin to." ta faɗi tana miƙewa, daga kusan iyayan nata ta koma, kusan Ablah ta zauna, ta rungumeta tana dariya, Umpah ya masu sallama ya fita. Sai dare bayan sallar isha Kamal yazo ɗaukar Mubina. Se da suka koma gidansu sukama Abbu da Ummah sallama suka tafi. Koda suka tafi gida basu zauna ba, sabida fushin da Mubina take da Kamal sai kumbure² take taki masa mgn, dole ya mata dubara, sukayi wanka suka shirya Kamal ya ɗauki abarsa, suka shiga yawon shaƙatawa, ya kaita gurare daban² yana nuna mata ita ɗayace a zuciyatsa babu wata, tin tana fushin har ta sauka, basu suka dawo gidaba sai 11 pm, suna zauwa wanka sukayi suka kwanta.
Kwance take saman ƙirjinshi, yana mata tausa, a shagwaɓe tace"Habibina shine ɗazu kasaka zanyi ɓari ni karka sake ƙiran sunan Umaimah." ta faɗi a shagwaɓe. Murmushi yay ya fara canza salon tausar yace"Sorry Sweetie bazan ƙaraba kaina bisa wuyana kinji sanyin idaniyar Kamalu." ya faɗi yana zura harshensa cikin kunnenta, yana tsotsa, hannunsa, ɗaya saman ƙirjinta ɗaya mazaunanta. Ashagwaɓe tace"Wayyo Habibina bacci zanyi kabar lagudani zakasa na fara murza gimbiyata fa."ta faɗi tana ƙamƙameshi. A cikin kunnenta yace"Yes sweetie oya murza abunki." idanu ta lumshe ta maƙale kafaɗa takiya, amman ta sakar masa jikinta yana laluɓeta da tsotsarta har tayi bacci. Kamal saida yaji yanda yakeso ya barta ya rungume Abarsa yay bacci mai cike da nishaɗi, son Mubina shi yasan daga Allah shine ya haɗa jininsu, suke ƙaunar juna kamar zasuci junansu...

*************** ******** ***************

*Bayan wata 7*
Kwanci tashi babu wuya su Mubina har sunyi wata 7 da tarewa, soyayya tsakaninta da Kamal kuwa kowace rana ƙaruwa take, ji suke kamar zasuci junansu, haka sukayi renon cikinsu yau da lfy gobe babu gashi Mubuna sosai cikin yake azabtar da ita, anyi bincike har an gaji ba'aga wani abuba tattare da ita, Kamal, kwata kwata bayada nutsuwa wata rana gaba zai sakata yana hawaye, itace zatana lallashinsa, tace kar yasa ta sare mana. To hakan yasa yaci gaba da bata kulawa ba dare ba rana, watan haihuwartane, cikinta yayi wani irin girman gaske, zama dakyat tashi dakyat kullum cikin tsammanin haihuwa suke, Kamal shike mata kome, cike da kulawa baya gajiya, tana samun kulawa sosai wajan iyayanta da surukanta, kowa ya ɗora ransa a kan acikin jikinta, sai Addu'a kawai suke ta kowane fanni dan ba ƙaramin wuya take shaba, Mamu haka kawai take jin yawan faɗuwar gaba, idan ta kalli ɗiyar tata ga wani irin fari na mahaukacin kyau da tayi . watani huɗu da suka wuce akasha bikin Samha da Anwar, wanda su Kawu Jafar sukazo aka gwangwaje, akayi shagali bayan biki da sati 2 suka ɗauki amaryasu suka koma saudiya, inda ta sami kulawa da siyayya fiye da tunanin me karatu, dan ba ƙaramin so Anwar yakema Samha ba, suna zuba soyayya tamkar zasuci junansu, ga kulawar da take samu wajan Yumna da kawu abin masha Allah idan kaga yanda Samha ta murje ta goge tayi kyau tayi ƴar ƙiba, ga madara daɗi na ratsata hummm.🤣 Umaimah ma an kawo kuɗin auranta an sanya biki watani uku masu zuwa. Amrah an goge fannin sex ba wasa, ta riƙe mijinta wani irin so sukewa juna ita da Sageer, yanzu haka cikine da ita wata 2 kacal amman baya bata wahala, sai abinda ba arasa ba. Haka Basma ma babu sauƙi suna zuba love gidansu, ga kulawa da yake bata, ga ta surukarta Mamu, itako cikinta ya fito sosai watansa 5 Kabeer Allah ya jarabeshi da son cikin, se muyi fatan sauka lafiya.

Misalin karfe shida na yamma, tafe suke a hankali yana suna zaga unguwa, dan ta motsa jikinta, riƙe da hannunta da kyat take takawa, sai ciza baki take, Kamal duk hankalinsa a tashe, dan tun jiya ya gama gano tana naƙuɗar tsaye ganin ya dubata a gida da saura saura shiyasa ya barta yake bata kulawa sosai kafin mai gaiyar ta taho. Kafaɗunta ya kama yace"Sweetie sannu ko haihuwarce tazo?" kallonsa tayi ta yamutsa fuska tai narai narai da idanunta a cikin sanyi murya tace"Habibina mu ƙarasa gida a titi fa muke."Kamal ya shafi ƙaton cikinta yace"Ok Sweetie muje." ya faɗi yana kama hannunta suna tafiya, damƙe hannunsa tayi sosai tana ciza bakinta. Kamal yace"Sannu" kai ta ɗaga masa.
Suna zuwa gida Kamal ya sakata mota yaje ɗauko duk abinda zasu buƙata na baby da mamarsa ya kwaso ya zuba both ɗin mota ya zagaya ya shiga motar ya zauna. Mubina ta kwantar da kanta saman kafaɗarsa tana ciza bakinta. Motar yaja yana horn ya nufo gate. Tin kafin ya iso megadi ya buɗe masa gate ya fita. "Sannu sweetie." yace mata yana driving. Kai ta ɗaga masa dan da saura kawai dai tanajin abin yana tsinkarta ne. Suna zuwa hospital ɗin su Mubina yasa aka ware masu room ta musamman, ɓangaran ƴan haihuwa, ya shigar da abarsa, zaune suke tana riƙe dashi tana ciza baki yana shafa cikinta zuwa bayanta, yana famar mata sannu. Mamu ya ƙira a waya da Ummah ganin naƙuɗar ta fara zuwa gadan gadan. Basu jimaba suka iso kusan tare hardasu Umpah da Abbu. Suna tsaitsaye daga waje. Mubina ta cukuikuyeshi jikinta na ɓari, ya rufe kofa yace sai ta haihu zai buɗe, gwara suyi naƙudar tare, sai famar sannu yake mata, bayan 30 minutes haihuwa tazo gadan gadan sosai Kamal yasama zuciyarsa dakiya yake temaka mata, duk ta yageshi yasha damƙa, tausayin Mubina ne yasa nabar ɗakin na dawo wajansu Mamu, wanda masha Allah sun kusa cika hospital ɗin. Ablah ce take bugun kofar Kamal yaƙi buɗewa, kuma tanajin kukan jariri, Abbu ya shiga ƙiransa suna bugun kofar. Kamar 20 minutes ya buɗe kofar yana sakin wani irin ihun daɗi ya faɗa jikin Abbu yace"Wayyo Abbu wlh mace da namiji ta haifamin." ya faɗi yana sakin Abbu ya zuɓe ƙasa yana sujada ta godiyar Allah. Mamu da Ablah da Ummah suka nufi ɗakin. Har ya yanke masu cibiya, ya naɗe yaran cikin towel ba wanka ba kome sai tsala kuka suke.
Mubina kuwa kamar gawa sai bacci take kirtawa ko na wuyane oho🤣 Ummah da Mamu, suka ɗauki yaran Macan Mamu ta ɗauka mai kama da Mubina sak kamar an tsaga kara, ita da uwarta, sai namijin shiko kamar an tsaga kara shida Kamal. masha Allah, yaran manya dasu. Inna ce da Ablah suka rangaɗa guɗa saboda murna, Mamu taba Ablah yarinyar, ta nufi toilet. Umpah da Abbu suka shigo suka amshi yaran suna murna kowa yayi mamakin girman yaran, Kamal ya dawo tare da nurse guda. Cikin awa ɗaya aka gyara Mubina da yaranta, Kunun kanwa mai zafi Mamu taje tayi daman akwai farfeson hanta kawai sai ta biyo mata dashi, dakyar taci saboda ciwon cikin da yake damunta, yaran ma dakyar da zare idanu Mamu ta matsa ta basu nono tana cizon lips saboda zafin da takeki.
Masha Allah kafin ƙarfe tara na dare hospital ɗin ta cika da ƴan uwa da abokan arziki, su Amrah Basma duk sunzo yaran akwai shiga rai jajir dasu ga gashi, Kamal kuwa duk wanda yasan suna harakar arziki ya sanar dashi haihuwar matarsa ƴaƴa biyu mace da namiji, su Sageer baki yaƙi rufuwa saboda murna, yaran ji yake daman shi. Kusan duk manyan ma'aikatan companyn Kamal sai da sukazo hospital saboda cewa yake duk wanda baizo ganin babys ba to ba masoyinsa bane. Umpah bayan Mubina ya nutsu ya rungumeta yana mata sannu dan ba ƙarmin ƙoƙari ƴarsa tayi ba, ga ɗinkin da aka mata.
Chapter 122 · 0% Book details