← Book details Ali Dan Tsoho Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 124

Sashe 32

Ali Dan Tsoho Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Damƙar wuyanta Kamal yay yana huci cikin ɗaga murya yace"Ashe haka kika iskance? Kike yawo a haka? matsayin ki na ɗiyar musulmai kuma gidan mutunci , kowane jaki na kallon ki... Kina tallar kanki sbd da ke sangartacciya , taɓara ta miki yawa yau zan koya miki hankali ." ya faɗa yana damƙar gashin kanta ya jata ya nufi motarsa da ita. tana kwarara uban ihuuu tana tirjewa, tana kiran umpah. Ɗai ɗaikun ɗaliban makarantar da suke shawagi, suka zuba masu idanu cike da mamaki suna tamyar kansu, sanin Kamal bai fiye shiga harakar mutane ba, maybe itama ko dan tana ɗalibar sa ce tayi wannan shigar yake hukuntata...? Mubina tace "wayyo Umpah na makance bana ganin kome wai me na tsare maka arayuwa? Ina ruwanka dani ne? Me na maka yanzu ka makantani? Wallahi bazan taɓa yafe maka ba! Da duk wasa ne yanzu ne zan ɗauki fansa ta kirki , daman na raga makane darajar Aunty amman yanzu ba yafiya tsakanin mu , se na rama..." kara damƙe wuyanta yayi, ya sake ɗauketa da mari wanda ta kasa koda iya ihun sai wani guntun fitsari da taji na shirin zubo mata... Se lokacin ta fasa wani gigitaccen ihuuu ta tafi luuuu ya tarota jikinsa ta fada saman kirjinsa, ta sauke ajiyar zuciya da karfin gaske, kawai se numfashinta ya tsaya cak, ta langwaɓe a jikinsa bata ko motsi... Kamal baki ya taɓe ya ɗauketa cak kamar baby ya nufi mota. Ai Basma ta fashe da kuka ta riƙe iyamu, iyamu bakinta na rawa tace"Ki...ru...fa...ma...na...a...si...ri...kar...ya...dawo wajanmu mu gudu kawai."ta faɗa suka rumtuma a guje... Kamal duk abinda iyamu ta faɗa karaf a kunnen sa, dan iyamu akwai katuwar murya kamar kato. Ya buɗe motar set ɗin gaba ya kwantar da kujera ya kwantar da Mubina wacce take a sume. Ya waigo ya buga masu wata uwar tsawa, "Kai!! Kuzo nan yanzu ko jikin ku ya faɗa maku" da sassarfa suka ƙaraso suka zube a gabansa, iyamu ranta in yayi dubu ya ɓaci yanda take ji da kanta ya wani tozarta su... Kamal yace" Ashe Basma Isma'il haka kike kema kin lalace? ashe ba abinda iyayanki suka turo ki ba kike? Yanzu gidan uban waye zaku a haka? kuka ma iyayanku karyar kuna lecture kuka yi shigar ƴan iska ko kishin kan ku ba kwayi a matsayin ku na ɗiyan musulmai?" ya faɗa yana hararan iyamu ya nunata da hannu yace"Keko katuwar banza yanzu wannan yaran sa'o'inki ne? Ko kunya bakya ji uwa dake kin sako wando babu kyan fasali , kinzo zuwa yawo ina ne zaku?" ya faɗa yana ƙura mata tsumammun idanunsa masu shegen haske da wani irin abu a cikin su. Iyamu duk tana tsorace hakan bai hanata ganin tsantsar baiwar kyawun da Allah yama Kamal ba, ga kwarjini, kayan jikinsa suka tafi da imaninta yanda kwarinsa yake waje mai cike da gashi, kayan sun masa kyau matuƙa... Marin da Kamal ya zafga matane ya dawo da ita haiyacinta. Basma kuwa ta sake ruɗewa jikinta sai ɓari yake. iyamu taji zafin marin matuƙa a ɗan tsorace!! Tace"Sir kayi hakuri Laweesa ce take party shine ta gaiyyace mu." ta faɗa tana sadda kai. " Kamal yace" ba zaku ba tashi maza kiba mutane waje maza ki wuce gidan da kuke zaune , idan iyayan ki suka ajiye ki ki kama kan ki kiyi abinda ya kawo ki , kuma kika yarda a cikin makaranta na sake kamaki da irin wannan shigar hum ,get out." ya faɗa yana buɗe mota. A guje iyamu tabar wajan. Ai kuwa tsirarun ɗalibai na mata dariya ƙasa-ƙasa suna mamakin duk karyar tata ma ashe matsoraciya ce. Kamal ya shiga mota ya zauna ya waigo yace da Basma "Marasa kunya maza wuce ki shiga mota na maidaki gida na shiga har gidan naku na faɗi iskancin da kuke a makaranta , ba karatu kuke ba yawon party kuke yi." ya faɗa yana murza key jikin motar. Basma ta fashe da kuka tace"Sir ka rufa min asiri Abba yanka ni zaiyi kuma wlh bama zuwa yauma Mubina ta matsa min amman insha Allahu bazan sake ba na tuba." ta faɗa tana miƙewa ta shiga set ɗin baya ta zauna. Kamal ya fizgi motar ya nufi get a guje tin bai isoba megadi ya buɗe masa get ya sulala motar waje. Iyamu kuwa ta shiga gidan da suke zaune ta fada saman katifa ta kece da kuka tana buga kanta a bango, tace"Sir baka dubi irin sonka da Allah ya dora min naka ba kaci zara fina a filin makaranta ka tozartani sbd kanwar matar se kace nice na koya mata iskancin , to wlh yanda ka sani kuka se nasaka se na rama ta in da baka zato se na tozarta ka se kaji kunyar da tafi tawa baka san iyamu ba." ta faɗa tana shasheƙar kuka ta kira number Leeza se da ta kusa yankewa ta ɗauƙo gurin cike da hayaniya tace"Iyamu wai ya haka ne guri ya cika taro yakai taro fa..." Iyamu ta fashe da kuka tace" Leeza Sir Kangiwa ya tozar tani cikin ɗaliɓai ya wankamin mari ya kirani yar iska ana min dariya saboda wannan yarinyar wlh se na saka shi kuka da idanunsa..." Leeza tace"Jar uban can wai kina nufin a anan gaban kowa da kowa? Tab dijam ai kuwa se mun ɗau fansa ki share kawai ki fito zaki ji dadi a wajan." Iyamu tace"No kome baya min dadi bazan iya farin ciki ba ko nazo na hakura , idan kun gama kizo kawai muyi shirin ramuwa ta ruwan sanyi ni an min dariya ko shi ihu za'a masa." ta faɗa tana tsinke kiran ta miƙe ta shige toilet.

Kamal driving ɗinsa yake a nutse, Basma ko ta rufe bakinta banda kuka ƙasa-ƙasa babu abinda take, hankalin ta a tashe yake ganin Mubina asume kuma bai damu ba driving ɗinsa yake a nutsu. Muryar Kamal tajiyo yana cewa"Ki kama kanki ki min shiru ko jikinki ya faɗa maki wlh , ina ne gidan naku?" Basma ta haɗiye kukanta ta ɗago da kanta tace" Muna unguwa ɗaya ne da Mubina nan tsallake titi muke kwana ta farko." Tsaki Kamal yaja yaci gaba da tukinsa. Yana shigowa unguwar Basma ta rinƙa kwatanta masa har suka zo kofar gidan, yay parking. Basma tace"Sir na tuba kar ka faɗama Abbana wlh bazan kuma saka wando ba ko yinƙurin zuwa party wlh sir." ta faɗa tana shasheƙar kuka. Kamal yace"Ok naji share hawayen ki maza shiga gida." da sauri Basma ta goge hawayen fuskarta ,ta buɗe motar tana kallon Mubina tayi tsaye ta kasa tafiya. Kamal yace"Zaki rufe min mota na tafi ko ko ya ne na fito mushiga na faɗa ne?" Basma ta girgiza kai ta rufe motar tana share kwalla ta nufi get ɗin gidan su. Kamal ya fizgi motarsa yabar wajan a guje.

Amrah ce ta fito daga ɓangaran laure ta shigo parlon, ta isko Mamu da lubah a tsaye Ablah taba lubah abu a leda se godiya take, zata tafi. Amrah ta iso parlon tace"Don Allah Mamu me yasa kuka bar Baby ta fita da shigar banza daga gida? Wlh ko ban ganiba naji kunya sosai , a ce mijin da zai aure ni yaga abinda ba mai kyau bane har ya kira ya faɗa min haba dan Allah Mamu." ta faɗa ta zama. Mamu tace"Amrah ban son rainin hankali ni zaki ma faɗa ai daman nasan dole za'a zage mu wlh , Lubah muje na taka miki bakin mota." Ablah ta tafa hannunwa tace"Nusaiba tsine muku dai akayi ba zagi ba , shin meye a jikin Mubina na saka idanu? daman tace min yaron ya sa mata ido a makaranta." Mamu ba ta sake magana ba suka fice da Lubah Lubah na murmushi da mamkin rigimar Ablah, ga haskuya kiri-kiri ta hana a faɗa... Amrah ta miƙe tana hararan Ablah tace"Wlh kiji taoron Allah ki fasa wannan abinda kike sam bai dace ba..." Ablah ta miƙe da sandarta tana bin Amrah Amrah ta haye sama tana faɗa, tabar Ablah na bambami se kumfar baki take... Mamu kuwa ko da ta dawo daga rakiya ta isko Ablah na masifa ta bayan kujeru ta duƙe ta shige bedroom ɗin umpah na nan ƙasa ta ɗan kwanta kan a kira la'asar, tana me jin haushin Ablah dan ta san idan Mubina ta lalace ita za'a zaga ba kowa ba...!
Chapter 32 · 0% Book details