← Book details Ali Dan Tsoho Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 124

Sashe 29

Ali Dan Tsoho Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Kamal tinda ya fita bai dawo gida ba se 10 pm na dare nan ya baje parlo ya fara aiki cikin laptop sbd wasu gadaje ne da za'a sarrafa su nan kamfanin sa yake aikin binci ke. Se 11:30 pm ya gama yaje yayi wanka ya shirya cikin kayan bacci ya kwanta ya shiga neman number Amrah, kiranta yay ta fara ringing. Lkcn Amrah ta gaji da jiran sa har sako ta tura masa ba reply, bacci ya ɗauketa ta ajiye wayar kusanta. Mubina tana cikin hira da Sageer se ɓangala dariya take tana ɗaga ƙafa ta dorama Amrah, itaki Amrah akwai nauyin bacci. Mubina taga wayar Amrah na alamun kira ganin sunan *My Hubbina💋* Na yawo saman screen ɗin wayar yasa Mubina ta ɗauki wayar tai picking ɗin call ɗin, ta janye wayar da suke da Sageer ta tsinke kiran ta kai wayar Amrah kunneta cikin lankwasa murya tayi kamar Amrah ce sak ta kwaikwayi mgnr Amrah tace"Hello my hubbina ykk bakai bacci ba? Allah ni nayi fushi ma shine zaka wani shanya ni ina jiranka tin yaushe." ta faɗa cikin wata siririyar murya haɗe da shagwaɓa. Kamal sosai murya ta daki dodon kunnensa, se da ya lumshe idanunsa ya gyara kwanciyar sa yana sauke sansanyar ajiyar zuciya... Mubina jin baiyi magana ba ta cire wayar ta bushe da dariya tana rufe bakinta tace"kunji kwarto ko yazata Anty ce bari naga iyakar iskancin sa se na kamshi wlh idan dan iskana bazan bari ta aure shi ba." ta faɗa tana maida wayar kunnenta se ta tsinto muryarsa mai daɗin sauraro cike da rauni yana cewa"Wow my cutie angel i love u kiyi hkr wlh naje unguwa ne da na dawo kuma nayi aiki se yanzu na sami kaina , amman yau nafi jin dadin muryaki a waya fiye da baya Muahhhhh my angel tawan." ya faɗa yana kara sakar mta sansanyan kiss ta wayar. Mubina idanu ta zaro ta toshe bakinta ta janye wayar tace" Lah wlh ɗan iskane fa su Umpah basu da labari har auntyn ma , gurgu akwai jaraba wlh..." ta faɗa tana maida wayar kunnenta ta lankwashe murya tace" Uhm-uhm my hubbina ni kana zautar min da kwanyata kana hargitsamin lissafi , kana rikirkitani sosai kana sakawa naji duk maza maza matane , a fannin soyayya kana sakawa na kara dulmiyawa cikin tafkin kogin sonka da kaunar ka , Hubbina i love u woyyo ni angel ,irin wannan zazzafan kiss haka ni dai ka daina kar ka lalatani gaskiya My Hubbina." ta faɗa a shgwaɓe tana masa
wani ɗan kukan sangarta tana harba ƙafafunta saman gado. Kamal ya sake rumtse idanunsa yana jin wani irin abu na tsirga masa tin daga tsakiyar kansa har zuwa ɗan yatsar ƙafarsa, bai taɓa sanin angel ta iya shagwaɓa haka ba. Amon zazzaƙar muryata yaji ta daki kunnensa tana masa kukan shagwaɓa harda shasheƙa, tana kiran"My Hubbina banza kayi dani ko to sai da safe..." da sauri Kamal ya bude idanunsa cikin tattausan lafazi yace" Am sorry my cutie angel wlh yau duk kin canza mani ne ina sonki sosai wlh duk kin rikitani ne angel am nace faɗamin me yasa kika min karya baki faɗamin gaskiyar cewar kina maradi ba , kuma kika ki faɗamin sunan ki na gaskiya Oya my angel faɗamin" ya faɗa yana sauke mata numfashin sa cikin kunnenta ta cikin waya. Mubin taji wani zirrrr a jikinta ta lumshe idanunta tana fesar da numfashi mai dumi tana zumburo baki gaba.... Muryasa ta sake bugun dodon kunnenta, a hankali taji yana kiranta "My cutie angel tawan faɗamin mana pls bana son yaudara fa?" Mubina idanunta ta buɗe ta zaro su waje ta ciro wayar daga kunnenta ta ƙurama wayar idanu tana nazarin abinda zata faɗa masa, dan bata san maganar da suka yi ba da Aunty Amrah....... Afuwa ba Editing Sosai.

*Labarin nan na kudi ne kan farashi me sauƙi, book 1&2 zaku same shi akan 200N kacal, ga mutanan mu na Niger zaku biya 400F, ba tsauwalawa hakan ta faru ne saboda masoyana na asali, karfa ku sake ayi baku wannna salon na daban ne, wannan karon bana cewa kome kune zaku faɗa insha Allahu, duk me bukatar siya zaku tuntuɓeni ta wannan*
*Lambobin👉🏻+22796515805/ +22792589446, karku manta nera 200 kacal zaku karanta book 1&2 ,Real ladingo na maraba da masoyanta har kullum💃🏻💃🏻💃🏻**💖😭KAMAL NE😭💖*

*Book 1*

NA

*Real ladingo*
*Sweet Baby💋*

Ƴar Mutan Niger🤙🏻

*Bismillahir Rahamanir Raheem*

*Free Page*

🅿️1️⃣8️⃣

Amon daddaɗar murya Kamal na sake tsinta cikin dodon kunnena, cikin rauni yana ce min" My angel oya ki faɗamin me yasa da muka haɗu a fecebook kika min karya cewar kina dosso , kuma kika ki faɗamin sunanki na gaskiya amsa ina jira cutie nah...?" ya faɗa murya can ƙasa.
A jiyar zuciya na sauke da karfi... Se yanzu na gane Aunty daman da Kamal soke soyayya ta fecebook basu sani b...? lankwashe murya nayi na fara magana, ```"My Hubbi babban dalili na shine ina son na sami wanda zai soni domin Allah ta wannan hanyar, tabbas nasan idan ka soni ba tare da kasan kalar halittata ba , to ba shakka kai masoyine na gaskiya, haka zalika nima naji ina sonka tin ban ganka ba, da farko naso na bijire ma iyayena akan son da nake maka wanda nasan kaima kana sona , se naga babu ribar na bijirema iyayena akan namiji... Na gwammaci nayi biyayya na hakura dakai na rungumi wanda aka zabar min , se dai zuciyata ta kasa hakura na kasa jure rashinka , shine fa nace na faɗama gaskiya yaudara ka nake ashe wai kaine zabin raina... Kaga anfanin bin iyaye ashe ma mune masoyan yanar gizo na asali." na faɗa ina murmushi mai mutiƙar ƙayatarwa. ```

Kamal ya jinjina kai ya sauke sansanyar ajiyar zuciya, yana lumshe tsumammun idanunsa fesar da iskar bakinsa waje. Raunana muryasa yay yace"my sweetheart Amrah ina sonki naji daÉ—in kasancewar ki wacce zata zama uwar Æ´aÆ´ana tabbas ina sonki tin ban ganki ba , yanzu kuma ganinki da sanin halinki ya karamin sonki da kaunarki da kimarki a cikin zuciya na , insha Allahu nida ke mutu ka raba, yanzu kwanta ki huta u love u more." ya faÉ—a yana sakar min kyakyawan kiss mai ratsa jini da tsoka.
Baki na turo na shagwaɓe masa nace" My Hubbina" Kamal ya saki murmushi yace" Na'am My cutie angel menene?" sanin banida amsa nayi sauri cewa"Hubbina bacci nake ji ni sakani bacci to." nafaɗa a sangarce cikin irin murya Amrah. Murya shi na tsinto yana min sansanyar waka wacce ta sakani ƙamƙame jikina ina ina girgiza kai, ina murmushi idanuna a lumshe duk wakar buzanci ce ta Bonbino ce amman zaƙin muryasa tasa naji dadin waƙar sosai inajin wayata na ringing na kasa bude idanuna saboda baccin da ya fizgeni, na shige cikin jikin Aunty Amrah na manneta gam ina gyada kai. Ina haka ban ko san bacci ya ɗauke ni ba har wayar ta faɗi a hannuna se bacci. Kamal kuwa jin saukar numfashin ta yasa ya tsinke kiran yana murmushi, ya ajiye wayar gefen gado yana jinsa cikin wani irin farin ciki da wani nishadi, ya ɗago ya kara gudun Ac daman wutar ɗakin a kashe se ta gefen gado mara haske sosai, cikin blanket ya naɗe luf yana sakin murmushi. A haka har bacci ya ɗauke shi, Asuba tagari...
Chapter 29 · 0% Book details