← Book details Ali Dan Tsoho Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 124

Sashe 34

Ali Dan Tsoho Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yana fitowa parlo ba kowa se su Ameer da gudu ya fice dan karsu riƙe shi. Yana zuwa ya boɗe motar tana nan yanda ya barta, se dai tana rizgar kuka tana kiran umpah. Kamal ya shigo ya zauna ya ciro hijab ɗin a leda ya kamota ya saka mata yay ma motar key ya nufi get. Yana fita daga gidan, jin taki daina kukan ya janyota jikinsa bai yi magana ba ya shiga bubbuga bayanta da hannunsa ɗaya ɗayan yana driving, jin ta tsagaita kukan ta lafe jikinsa tana sauke ajiyar zuciya, yasa ya ɗan kara mannata jikinsa ya cire hannunsa daga bayanta, ya ɗauki wayarsa ya shiga neman layin Sageer. Bugo ɗaya Sageer ya ɗaga tare da sallama. Kamal ya sauke ajiyar zuciya da karfi yace"Sageer pls ina son ganinka yanzu da fatan kana hospital?" daga can Sageer ya bushe da dariya yace"Kangiwa ango me zan samu? Gani fa cikin makaranta..." Kamal yaja tsaki yace"To kazo hospital ɗinku yanzu yanzu mu hadu mu dubata." yana faɗin haka ya tsinke kiran, ya maida hankalin sa kan driving. Mubina ta fashe masa da kuka tin karfi. Kamal yace"Ya Salam me ye to kuma? don Allah kibar zuciyata ta huta haka haba ina dalili, ba hospital ɗin zamu ba ko idon ya buɗe ne? Mubina ta girgiza kai tana kara shigewa jikinsa tana sauke ajiyar zuciya. Hannunsa ya sanya yana buga bayanta...
Kai tsaye hospital É—in da Sageer yake Kamal ya nufa. kusan tare suka iso da Sageer dan yana cewa su hadu su dubata yaji gaban sa ya faÉ—i. gashi yana kiran Mubina ba'a É—auka, ya fito a guje ya shiga mota ya nufi hosfital É—in. Kamal na parking Sageer na parking......

*Labarin nan na kudi ne kan farashi me sauƙi, book 1&2 zaku same shi akan 200N kacal, ga mutanan mu na Niger zaku biya 400F, ba tsauwalawa hakan ta faru ne saboda masoyana na asali, karfa ku sake ayi baku wannna salon na daban ne, wannan karon bana cewa kome kune zaku faɗa insha Allahu, duk me bukatar siya zaku tuntuɓeni ta wannan*
*Lambobin👉🏻+22796515805/ +22792589446, karku manta nera 200 kacal zaku karanta book 1&2 ,Real ladingo na maraba da masoyanta har kullum💃🏻💃🏻💃🏻*
*💖😭KAMAL NE😭💖*

*Book 1*

NA

*Real ladingo*
*Sweet Baby💋*

Ƴar Mutan Niger🤙🏻

```Aslm masoyan Littafin Kamal ne... Dubun gaisuwa da fatan Alkhairi a gareku, nasan dayawa zasu shiga ruɗanin abinda zai faru a cikin wannan pagen... so abinda nake so daku 🙏🏻don Allah kar wacce ta bini pc dan ƙorafi ko shawara ko gyara nace a mafarki abin ya kasance, wlh bazan saurare kuba! Dan haka na tsara labarina kuma ina dalilina na yin hakan, dan haka don girman Allah tin wuri idan kinsa zaki saya domin ki dameni da jaje ko korafi, to na yafe ki riƙe kuɗin ki na riƙe book ɗina, se kuma ku wanda kuka biya kudi, don girman Allah kada ku cazamin kai ko isheni da korafi, kuyi hakuri ku biyo ni muje cikin labarin Kamal ne... Bayan wuya se dadi kuma mutum baya tsallake ƙaddarasa...````

*Daga yau pagen kyauta ya kare.*

*Bismillahir Rahamanir Raheem*

*Ƙarhen😅👉🏻 Free Page😉*

```Page biyu ne na haɗa```` 👉🏻 🅿️2️⃣1️⃣

Kamal yana gama parking ya fara ƙoƙarin janye Mubina daga jikinsa, ta wani tunzuro baki gaba ta saƙala hannunta wuyan shi, tana gujin kuka alamun bata so ya cireta daga jikinsa. Kamal ya zuba mata tsumammun idanunsa, ya fara mgn me cike da rauni yace"Mubeena mun iso hospital ɗin fa tsaya mana na sauka na kamaki mu shiga ciki ok." ya faɗa yana ɓanɓareta daga jikinsa, ya buɗe motar ya zuro kyakyawar ƙafarsa waje, ya hango Sageer na nufo gun motar sa, karasa fitowa yayi ya rankwafo ya kama hannun Mubina yace"Oya tashi muje" Mubina ta kwakwaɓe fusa tana shirin kuka tace"Allah Sir se ka ɗaukeni ni bazan iya tafiya ba bana gani salon na faɗa rami..." Kamal yace"Wane irin rami kuma? Ai ina riƙe da hannunki oya tashi muje." Mubina ta ɓangare baki ta saki kuka tana jijiga kanta tana diddira ƙafafunta... Kamal yace"Ok yi shiru bari na ɗauke ki shi kenan ko...?" Mubina ta ɗaga kanta. Kamal ya sunkuya ya cicciɓeta ya fito da ita ya rungumeta kirjinsa, ya fara ƙoƙarin rufe motar, Sageer ya iso gurin a guje ganin Mubina ce. Yana isowa yace"Subahanallahi me ya sami babyn my one kawota muje to" ya faɗa yana ƙoƙarin amsarta a hannun Kamal. Kamal ya kauce yana kallon Sageer fuskar shi ba walwala, yace"kuji ni da mutum kaine ka kawota ne zaka wani amsheta muharamarka ce?" ya faɗa yana ƙara manneta a kirjinsa. Sageer ya zaro idanu yace"Babban yaya harda gori? To afuwa muje."ya faɗa cikin yanayin damuwa. Mubina kuwa jin murya Sageer ta saƙala hannunta wuyan Kamal ta ƙamƙameshi ta fara magana dab da hancin sa, har tsinin hancin su na haduwa na gugar na juna, hucin numfashin su ya haɗe waje ɗaya, tana mgn a sangarce"my one Sir ne ya mareni bana gani..." Kamal yay saurin saka tattasan hannunsa saman bakinta ya rufe mata baki, suka nufi ciki. Jama'ah se kallon Kamal da Mubina suke yanda suka yi wani irin kyau suka dace da juna.

Suna shiga Sageer ya kai su wani room me kayan gwaje-gwaje komai akwai a ciki. Ya kalli Kamal yace"Wai Kangiwa me ya sami babyn tawa ne?" Kamal ya nufi gun gadan ya kwantar da Mubina yana jona mata wata na'ura, tako saki kuka ta riƙe hannunsa gam, Kamal ya riƙe hannunta gam ya zuba mata lumsassun idanunsa yace"To meye kuma? ba dub ki zamuyi ba pls daina kukan kinji kanwas." ya faɗa yana shafa fuskarta. Mubina ta damƙe hannunsa a cikin nata tace"Sir ni de my one zai duba ni bana so kai ka duba ni ko nayi ta kukan." ta faɗa tana ɓare baki zata saki kukan, Kamal yace"Ok shiru bari ya duba ki" ya faɗa yana sakin hannunta, ya juyo ya kalli Sageer yana tsaye dab dashi duk ya zama wani iri... Kamal yace" Abokina ka dubata da kyau karka biya sangarta ta pls." Sageer yace "Ok wai da gaske bata gani ne?" Kamal yace"ka dai jona mata na'urorin se mu tabbatar." ya faɗa yana lumshe tsumammun idanun da ya buɗe kofar ya fice. Direct masallaci Kamal ya nufa dan yayi sallah. Sageer ya jona mata na'ura a kanta ya haska mata wani abu a idonta, kamar fitila me hasken gaske gaban sa na faduwa yace"Babyna wlh ko da hakan ta kasan ce ina sonki ina kaunar ki , banga halin da zaki shiga bana na rabu dake zan kasance dake har abdan insha Allah , baby." ya faɗa yana cigaba da aikinsa kusan 1 hour. Kamal kuwa yana nan kofar room se kai komo yake gaban sa na bugun uku-uku kar abin ya zama gaske ina zai shiga da kayan kunya? Tabbas da yaji kunya ba karama ba.!! Se kiran sa ake a waya yaki ɗagawa, dan baya da nutsuwa.
Sageer ya sauke nauyaiyiyar ajiyar zucuya, ya cire ma Mubina na'ura da ya ɗaura mata ya zauna kusanta ya ɗagota ya zaunar da yace"Me yasa kika yi karyar idanu baby haba baby me ma wai ya faru ne?" Mubina ta buɗe idanunta tar ta dorasu kan Sageer tace"My one don Allah kamin alfarma karka cema Kangiwa ina gani so nake na rama abinda yamin cikin ruwan sanyi , nasa yaji kunyar da bai taɓa jiba a duniya na bashi wahala ya kasa sukuni ya rasa nutsuwar sa da kwanciyar hankalin sa..."Sageer yay saurin rufe mata baki da hannunsa yace"haba baby mijin yayarki ne fa to meye ya maki ma faɗa min naji idan ya cancanci hukuncin sai mu masa?" Mubina nan ta kwashe kome ta faɗama Sageer yanda abin ya faru... Ta dora da cewa "my one ka yarda ko da sati ɗaya ne na rama kaji." ta faɗa a shagwaɓe tana narai-narai da idanunta. Sageer ya riƙe hannunta, ya ƙura mata idanu yana girgiza mata kai yace"No baby ina sonki bazan so abinda zai cutar dake ba ko na rasaki , kina ɗaukan abin wasa zai iya zama gaske dan Allah babu ruwansa..." ta sakar masa kuka tana riƙe hannunsa tace"pls my one ka temakamin na ƙuntatama Kangiwa pls..."Sageer yace"ke ni fa ba ɗan iska bane najawo abinda nine zan kwana a ciki... Ta yaya zan ɗauki wuka na dabama kaina...? Ko baki san za'a iya cewa a fasa auran sa da Amrah ya aure ki tinda shine ya nakasa ki ba..." Mubina ta zaro shanyayyun idanuta wanda suka rine waje tana kallon Sageer tana turo baki. Sageer yace"eh wlh da gaske dan haka abar mgnr ki bari bayan auran sa se na faɗa maki abinda zaki yi ki rama cikin ruwan sanyi ai baza mu yafe ba tinda yaci zalinmu..." Mubina tace"my one ka tabbatar kuwa zamu rama?" Yes baby kibari se bayan auran yanzu ajiye ɗaukar fansar , kuma nima se na mare shi yayi fitsari wlh kangiwa ɗan iskane zai yi bayani ai." Mubina ta bushe da dariya ta kwanto jikin Sageer tana riƙeshi tace"Wayyo ciki ashe my one kaima mugune amman zan so naga fitsarin gurgu yasha mari wai niko kasan me? zan masa gobe a makaranta? Wlh karkashi zan zuba a roba na jiƙa shi naje saman bene nabi na zuba a matatakala ya fado nasan nan ma kara jirgewa zai yi."ta faɗa tana ruƙumƙume Sageer. Sageer ya janyeta jikinsa sbd yadda yake jin wani irin abu na tsirga masa, ga nonuwanta sai gugarsa suke. Ya bushe da dariya yace"wai baby A'A kibar kome a hannuna har ayi biki lfy zan baki shawara yanda zamu rama kuma bene a bashi ɗaya ba ke da office ko kin manta? Ai sai muyi barna dayawa kibar kome hannuna kinji" Mubina tace"Eh naji" Sageer yace"yauwa autar mata ƴar lelena yanzu dai ki hkr ok?" Mubina tace"Ai na yarda da kai bari nayi sallah." ta faɗa tana kama Sageer ta sauko daga saman gadon. Sageer yace"Au baki yi sallah ba?" kai Mubina ta ɗaga ta shiga toilet. Sageer ya miƙe yana jinjina kai irin rigimar baby darduma ya shimfiɗa mata, ya buɗe kofa ya fito.
Chapter 34 · 0% Book details