Sashe 41
Ali Dan Tsoho Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Can ko hospital Dr Khadija na yawan leƙa Mubina taga ko ta farka amman bata farka ba daga sumar. Suna isa hospital Kamal ya fito ya buɗe masu kofa suka shiga, Mamu tana tambayar Umpah"Wai Abban Mubina lfy?" Umpah yace "Muje dai." Dr Khaduja na fitowa daga room ɗin da Mubina take suka ci karo da dasu Kamal. Dr tace"Yauwa kazo ko bata farka ba amman zata farka da izinin Allah, muje ku ganta." ta faɗa tana shiga suka bita a baya Kamal har tuntuɓe yake. Kwance take kamar gawa se wata na'ura jone hancinta da drip a daure jikinta fuskarta fayau. Da gudu Umpah ya isa bakin gadon ya zauna.
kusanta ya rankwafa ya rungumeta ya saki kuka. Mamu tace ma Dr"Dr me ya sameta?" Khadija tace"momy kuma sha'anin amare se hakuri bai mata ta sauki bane harda ɗinki aka mata amman zata dawo haicinta insha Allahu..." A mugun tsorace!! Mamu tace "Waye bai mata ta saƙin ba?" Dr ta nuna Kamal tace"mijinta mana, kuma dan Allah karku mata hayaniya ku dubata kawai ku fito kubar sa shi kadai." ta faɗa tana fita ta janyo kofar. Mamu ta zuɓe nan ƙasa ta dora hannunta aka ta kece da kuka tama rasa wace Addu'a zata karanta. Abbu da ummah suka ƙarasa bakin gadon suka zuɓe ƙasa kan guiwarsu gaban Mamu. Amman bata ko kallesu ba. Kamal ma gabanta ya zube yana sakin kuka ya riƙe guirwata yace"Narantse da Allah Mamu ban..."Wasu gigitattun maruka masu kyau Mamu ta sauke masa kan fuskarsa guda uku, tana rusar kuka ta hankaɗe shi daga jikinta ta matsa baya da sauri, kuma se ta miƙe tsaye ta isa gun Mubina ta taɓata ko ina baya motsi a jikinta, tana kuka tace"Umpah Mubina fa inaga ya kasheta wlh bata motsi..." Kamal yace"Wlh inaji a jikina bata mutu ba insha Allahu bazata mutu ba, wayyo rayuwa ina ma na mutu na huta..."
Goggo ta rufe masa baki tana girgiza kai tace"Duk mummunin kwarai an sanshi da amsar kaɗɗara me kyau ko akasin hakan, don Allah kuyi hakuri abun nan kar a fasa kowa yaji tonan a sirin mu ne baki ɗaya..."Mamu tace"Wlh a gobe zan shigar dashi kotu narantse bazan taɓa yafe maka ba Kamal kaci amana ka zalumce mu, Allah ya isa..." Umpah ya rufe mata baki ya rungumota ya kece da wani irin kuka me tsuma zuciya yana riƙe da hannun Mubina yana girgiza kansa. Mamu ma kukan take Abbu kuka Ummah kuka Kamal ya ma fasa ya kifa kansa da guiwowinsa... Goggo tace"Kamal ka gama damu... Na'uran jikin Mubina ta dauki ruri Se gata ta fara motsi tana wani irin fizge-fizge da karfi har ta fizge drip ɗin jikinta kafin a farga. Kamal ya miƙe cikin farin ciki ya fita aguje kiran Dr se gata sun gamu a kofa suka shigo tare. Umpah da Mamu suka riketa gam suna tofa mata Addu'a cikin farin cikin farkawarta. Umpah yana kuka yace"Autana buɗe idanunki umpah ne kinji." Dr tace ku matsa ku bani guri wannan wane irin abune ko wace mace ai se ta dandana irin haka, se dai ita dan ya nuna karfine kawai matsalar." ta faɗa tana duba Mubina tai sauran haɗa alluran ta riƙeta sai fizge-fizge take tai saurun mata allura ta gyara mata kwanciya ta maida mata drip ɗin, nan take sai bacci. Dr tace"don Allah kubar hayaniya tana buƙatar hutu,kukan me kuke ne...? Nifa bana ganewa?" ta faɗa tana kallonsu. Kamal yace"Duk nine sila ni na saka su cikin wannan masifar yau iyayena na kuka sbd dani... Dr ba ma..."Umpah yace"Dan Allah kaiyi shiru Dr jeki kawai idan buƙatar kiranki ta taso zamu kiraki domin kula da ita..." Dr Khadija ta jinjina kai ta fara zargin wani abun, ta fice. Mamu tace"Wai Abdul me kake nufi ne? duk ina son da kake nuna mata ina kaunar ne...? Gashi kana ji kana gani an kashemu da ranmu amman ka wani zauna kana kuka bakada alamar ɗaukan mataki?"ta faɗa tana rungume Mubina tana kuka. Umpah yace"Nusaiba kenan ni a yanzu burina ma naga Mubina ta tashi cikin haiyacinta ta ganeni ta ganeki ta kuma kira sunayanmu se lkcn zan sami nutsuwa nama Allah godiya da kaddara da ya dora mana dan babu ta inda zamu tsallaketa , ta yaya kike so na baza irin wannan tozarcin da aka mata aduniya na ɓata mata sunah A'A bazan ce kome ba Nusaiba.... mu bari mugama abinda Allah zaiyi pls ki daina zancan ɗaukar mataki ba'aja da ikon Allah..."Abbu yace ma Kamal"Dan ubanka ka faɗa mana dalilinka na sakamu cikin wannan masifar, dama ka jima kana wannan mummunar sana'ar ne ta fyade ƴaƴan mutane?" ya karasa maganar da karfi... Kamal ya kasa mgn sam bema san ta ina zai fara ba...! Umpah kallonsu kawai yake baiyi mgn ba. Goggo ta sunkuya ta kama Kamal suka fita. Ummah ji take bata taɓa tozarta irin haka ba. Goggo ta sami guri suka zauna ta tisa Kamal gaba tace "Don Allah Kamalu me yasa kayi haka ne? Yaushe ka lalace haka?" Kamal sanin a yanzu ba me yarda dashi yasa ya fasa mgn dan bai san abinda zai ce ba sam, ya gama yankewa kansa hukunci. Babu yanda goggo bata yi dashi yaƙi mgn se hawaye. Haka suka kasance cikin ƙunci da baƙin ciki sai wajan goma na dare Umpah yace da Abbu su tafi gida kawai, Abbu yaki se lkcn suka yi sallah isha'i ma, har su Mamu ɗin. Suka ci gaba da zama har shaɗaya bata farka ba, har lkcn goggo ma ta kasa tafiya tana tare da Kamal dan mugun tausayinsa take wannan ba karamar azal bace ta faɗa masa, ga taga zubin uwar yarinyar ba yarda zatayi ba...!!
Can gidan Mubina kuwa shaɗaya har da rabi na dare su Amrah na zaune a parlo cikin jimami, hankalin su a tashe ga suna kiran umpah da Mamu basa ɗauka, ga Amrah na kira Kamal yaki ɗauka. Yanzu ma kiransa tayi yaki ɗauka ta ja tsaki. Sabeelah tace "Wai ke dawa nene? Mu dogara da Allah mana, gashi sunki daukan kira bamu san inda suke ba bare muji halin da suke." Ablah tace "Masifar tace kawai, nifa gaskiya nagaji har yanzu shiru Mubina ga Nusaiba taki zuwa ga basa ɗaukan kira haba abin yayi yawa fa, dubi dare yayi sosai..." Majeed dake fitar da kwalla daga idanunsa ya janye Aleem kaninsa yace "Amrah Ummi Ablah wallahi muna cikin musifa fa duk da Umpah yace kar na faɗa maku amman se na faɗa ko kunsa cewar Mijin da Amrah zaki aura wai yama Mubina fyade, suna asibiti..." haba wa Amrah ta zage karfinta ta wanka ma Majeed mari ta kwala masa wayar a kansa saida gun ya loɓa. Cikin ƙaraji tace"Wallahi karya ne badai Kamal ba sam..."Majeed yace"Ni kika buga harda fasa min kai? A yanzu wa yake shedar ɗan Adam, Amrah na rantse da mahalilcina sun tafi asibita ya kaisu gunta a gabana ya faɗa yana kuka iyayansa suna kuka wlh Allah ya mata fyade..."Ablah ta fashe da kuka ta miƙe jikintana kyarrrma tace" Innalillahi wa'inna ilahir raji'un!! Mun mutu mun lalace kace ya kasheta kawai antafi gun gawarta kawai? Amman wannan katon yaron ta ina zai kusanci baby tayi rai.." ta faɗa tana nufar kofar fita. Sabeela ta fashe da kuka tace"Allahumma ajirni'fi musibatin wa'akilli khairan!! Mun shiga uku" ta faɗa tana bin Ablah ta rikota. Aleem da Azeema na biye da ummi suna cewa"ummi mutuwa akayi wa yamutu ne?" Amrah kuwa kamar gumki tayi tsaye kiƙam jikinta na kyarrrma ta kasa magana tana binsu da kallo. Sabeelah tace"Ablah tsaya bari mu kira Umpah ya faɗa mana sunan huspital ɗin sai muje." Daket tasamu Ablah ta tsaya ta kira Umpah amman bai dauka ba." ta faɗa tana sake kiran, cikin sa'a ya ɗauka tace"Yaya Abdul dan Allah meke faruwa mu gamu cikin damuwa ku faɗa mana asibitin muje yanzu ga Ablah ta tashi hankalinta." Umpah daga can yaja numfashi yana tsoron!! Fitinar Ablah amman ita mahaufiyar sa ce bazai iya boye mata ba dole ta sani. Yace" Ok bari ganinan zuwa yanzu na kawota ko kuma Haladu ya kawo ku Sauƙi clinique hospital ɗaki me lamba 10." yana faɗa ya tsinke kiran. Sabeela tace"To ku muje Haladu ya kaimu."ta faɗa tana kama Ablah. Majeed ya kama hannun Azeema da Aleem, yace da Amrah muje mana." Daket ta ɗaga kafarta ta biyo su suka fito. Ashe ƙafarta babu ko takalmi Majeed ne ya lura ya koma ya ɗauko mata takalmi ya kawo mata. Sai lokacin mata ta tuna ta saka suka shiga mota, Sabeelah ta faɗa ma Haladu hospital din yaja motar suka tafi. Ko a mota ba wanda yake magana se Aleem da Azeema suma Sabeela ta daka msu tsawa! suka yi shiru...