← Book details Ali Dan Tsoho Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 74 OF 124

Sashe 74

Ali Dan Tsoho Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tafiya ce mai tsayi su Kamal suka sha a cikin jirgi, kafin cikin hukuncin Allah ami kowa me komai ya kasu birnin london fafiya, karfe uku da rabi na dare jirginsu ya sauka. Iya gajiya Kamal ya gaji ga wani bacci da yake ji na uban mamaki dan baya iya bacci cikin tafiya.
Bayan sun sauko daga cikin jirgi an gama bin cikar su yana jaye da trollyn sa ya nufi gun idan ake tarbar wa inda suka zo. Cikin nutsuwa Kamal ke takunsa na nutsuwa yana lumshe idanunsa saboda tsabar gajiya. Tindaga nesa ya Makel ya hango Kamal, da ɗan gudu ya ƙarasa yana murmushi, suka rungume juna, cikin harshen turanci Makel yama Kamal sunnu da zuwa yace.
"Sir ka ƙara kyau da girma." Kamal murmushi yay ya maida masa da harshen turanci "Please Makel muje ina buƙatar hutu." Makel yace "Ok Sir." ya faɗa yana amsar trollyn hannau Kamal, suka nufi parking space. Kamal dai murmushi yake mai cike da gajiya. Wata rantsatsar mota mai numfashi, Makel ya buɗema Kamal gidan gaba mai zaman banza, ya shiga ya zauna ya rufe ya zagaya ya zauna mazaunin direba ya mata key suka ja suka bar Airport ɗin.
Kamal idanunsa ya lumshe ya jingina kansa da kujera ya fesar da zazzafan numfashi.
Makel sai hira yake masa yana basa labari akan Mubina, dole Kamal ya buɗe idanunsa yana mai cike da farin ciki yana sakin murmushi haɗe da ƙarema haɗadɗan babban titin da suke kallo yanda motoci ke ficewa jama'a kamar ba talitalin dare ba. Wata rantsatsar hotel, me suna *London House hotel* Makel ya tsaya gaban gate ɗin hotel yana honr. Katoton gate ɗin aka wamgame masa ya cinna hancin motar ciki.
Parking spece yay parking, ya fito Kamal ma ya fito, yana ƙarema compound ɗin hotel ɗin kallo, "Masha Allah ya furta a hankali yana murmushi, saboda komai na london house hotel yay masa. Makel ya buɗe both ɗin motar ya fito da trolley ɗin suka nufi ciki. Hawa na uku suka hau sama, Makel ya zura hannunsa cikin aljihu ya zaro key ya buɗe kofar, soka saka kai cikin haɗadɗan parlon. Idanu Kamal ya lumshe haɗi da sauke ajiyar zuciya, saboda wani irin sanyi daɗi da ƙamshi da ya daki hancinsa, yana ƙarema parlon kallo. Makel cikin bedroom yakai masa trollyn ɗinsa ya dawo, Kamal na zaune saman wata lumtsumemiyar kujera, Makel ya masa magana da harshen turanci"Sir da fatan kome ya maka na gun har ka gama abinda ya kawo ka?" Kamal ya jinjina kai. Yana miƙewa tsaye. Makel yace bari ayo maka oder abin da zakaci." Kamal yace.
"No bacci zanyi a kawo min coffee ya isa."ya faɗi yana shiga cikin bedroom. Makel ya fice. Kamal ya rage kayan jikinsa ya ɗauki sabon towel ya nufi bathroom. A gaggauce yay wanka ya dauro alwalla ya daura towel ya fito. Shiryawa yay cikin kayan bacci ya fesa sansanyan turaren sa me ƙamshi, ya fito parlo Makel zaune na jiransa. Coffee ɗin ya amsa ya a gaggauce sukayi sallama da Makel ya tafi shiko ya murza key kofar parlon, ya nufi bedroom, yana shiga ya fada saman bed ya shige cikin blanket yana riƙe da waya ya shiga cikin gallery, pics ɗin Mubina ya ƙurama idanun yana sakin murmushi, yana shafa sajan kyakywar fuskarshi, bai jima baccin gajiya ya ɗauke shi...

Washegari misalin karfe 7:30 am, Kwance Mubina take saman bed, ta naɗe cikin blanket sai rawar sanyi take haƙoranta na gamewa waje ɗaya tana nishi sai lumlumshe idanunta take ahankali.

Can parlo kuwa gaba ki É—ayansu suna zaune ne akan dinning table, inda suke gudanar da break fast, cikin nutsuwa.
ÆŠago da kai Ummi tayi tare da duban Azeema, cikin nutsuwa tace.
"Azeema jeki k'irawo Auntyn ki, tagama shiri me takeyi, da har yanzu bata fito ba."

Majeed dake zaune yana tsakalan chips, ya É—ago kansa, duban Azeema shima yayi tare da cewa.
"Yauwa maza kiyi sauri ki k'irawota, tazo nai dropping, d'inta don nima sauri nake zan wuce wajen aiki."
Da "To" Azeema ta amsa musu sannan ta nufi, d'akin Auntyn tata.

Dagudu ta k'arasa har bakin k'ofar d'akin, inda ta bud'e k'ofar ta shiga, ganin Auntyn nata kwance akan gado, yasa cikin sauri ta k'arasa gareta, tana fad'in.
"aunty Aunty, ki tashi Ummi na k'iranki, kuma Yaya Majeed ma yace kiyi sauri."

Mubina dake kwance, shiru tayi don bazata iya magana ba, kasancewar jikinta na wani irin kakkarwa, sannan hak'waranta har had'ewa waje d'aya suke.
Azeema kuwa ganin Auntyn nata bata ce komai ba, yasa ta k'araso inda ta d'an yaye blanket d'in da Mubina ta rufu dashi. Ganin jikin Aunty Mubina'n na rawa, yasa cikin sauri had'i da gudu gudu, ta nufi parlo, kaitsaye dinning table d'in ta koma, cikin yanayi na sauƙe numfashi tace.

"Ummi naga Aunty tana ta rawan sanyi, haƙwaranta suna gamewa."
Majeed dake rike da cup, zai sha tea, cikin sauri ya miƙe yana faɗin cewa.
"Subahanallahi meya same ta, ko shiyasa naji shiru bata fito ba, don dai nasan baby tun ƙarfe 7 take fitowa na sauƙeta amakaranta."
Yana gama faÉ—in haka ya aje cup É—in dake hannunsa, cikin hanzari ya nufi É—akin Mubina'n.
Ahankali ya tura ƙofar ɗakin ya shiga, ae kuwa kwance ya hangota, nannaɗe acikin blanket, sai faman rawar ɗari take, tamkar wanda ruwa yayiwa duka.
Cikin hanzari ya tako zuwa gaban gadon, muryar É—auke da damuwa yace.
"Baby lafiya kuwa kike, meke damunki?."
Ya ƙare maganar yana mai yaye blanket ɗin da ke jikinta, hannunsa yakai kan fatar wuyanta, nan kuwa yaji jikinta ya ɗauki zafi zau, hankalin Majeed atashe, ya zauna nan gefen gadon, ɗagota yayi inda ya mannata ajikinsa, cikin kulawa haɗi da tsananin tausayinta yace.
"Baby meke damunki ne haka, ummmm faÉ—amin kinji baby!"
Cikin zafin ciwo, haɗi da zallan shagwaɓa, ta saƙala hannunta akan wuyansa.
Murya asanyaye tace.
"Yayana zazzaɓi nakeji, please ka lulluɓeni sanyi nakeji."

Dubanta yayi, nan yaga daga ita sai ɗan mini skirt, kasancewar ta kammala shirin makarantar ta kenan, ko kaya bata sanya ba, zazzaɓin ya rufeta, ajeta yayi tare da miƙewa, gaban sif ɗin kayanta ya ƙarasa, nan ya zaro mata wata, baƙar abaya mai adon pink ɗin duwatsu, wato "stones".
Shida kansa ya zura mata rigar ajikinta, nan ya yafa mata ɗan madaidaicin ɗan kwalin kayan akanta, sungumarta yayi tamkar wata ƴar tsana, haka ya sata acikin ƙirjinsa, kai tsaye ya nufi parlo da ita, Ummee da papa Saleem dake zaune, ganin Majeed ya fito da Mubina'n saƙale ajikinsa, yasa su mimmiƙewa.
Duban Majeed É—in Ummi tayi, tare da cewa.
"Lafiya kuwa Majeed?."
Cikin raunin murya Majeed yace.
"Wallahi Ummi zazzaɓi ne, jikinta kamar wuta."
"Subahanallahi, maza hanzarta mu wuce hospitall, idan mukaje aka bata magani sai musan abunyi, idan akwai yiwuwar zuwa school É—in yau to, idan ma dai sai gobe, duk Allah ya kaimu."
Cewar Papa Saleem.
Cikin kulawa Ummi tace.
"Bana É—auko mayafi na, muje tare."
Nan agurguje Ummi ta ɗauko mayafinta, inda ta ƙarasa kimtsa, Azeema da Aleem, wanda aka saka musu kayan makarantar su, atare su dukansu suka fito daga compound ɗin gidan.
Bayan Ummee tace da Tani mai aiki, ta kula da gidan, su zasu kai Mubina hospitall, sannan kuma daga can zasu kai su Azeema makaranta.

Majeed kuwa cikin sauri ya ƙarasa jikin motarsa, inda ya buɗe gidan baya, nan ya kwantar da ita, zaga yawa gefen driver yayi inda ya zauna, yana jiran ƙarasowar Papa Saleem da kuma Ummi.
Koda suka ƙaraso, Papa Saleem ne ya shiga gefen driver, inda Ummee kuwa ta shiga baya ita da yara, nan tajawo Mubina jikinta, tare da aza kan Mubina'n, akan kafaɗanta, yayinda har yanzu Mubina'n keta rawan sanyi, don zazzaɓin nata ƙara ƙaruwa yake.

Saida suka fara biyawa suka sauƙe su Aleem amakaranta tukunna, kafun daga nan suka wuce asibiti.
Suna isa hospitall ɗin, wasu nurses suka ƙaraso, su suka amshi Mubina daga wajen Yaya Majeed, kan wani gado suka ɗaura ta, kana sukai wani ɗaki da ita, nan likitoci suka shiga bata taimakon gaggawa, don zuwa lokacin har takai ga numfashinta, yasoma ƙoƙarin yankewa, wato yana seizing kenan.
Bayan babban likitan da ke kan nata yagama checking ɗinta, nan yagano cewa bawani babban ciwo bane, zazzaɓi ne kawai da maleria ke damunta, nan ya ɗaura mata drip, acikin drip ɗin, yayi wasu allurai wanda suke ɗauke da magunguna acikinsu, kasancewar alluran daya sanya acikin drip ɗin, suna da ƙarfi sosai, hakan yasa cikin mintuna kaɗan, bacci ya ɗauke ta, inda sannu ahankali zazzaɓin ke sauƙa, daga jikinta.

Can waje kuwa su Papa Saleem ne sukai jigum, gaba ɗaya damuwa ta bayyana akan fuskar Majeed, kowa da irin tunanin da yake saƙawa acikin ransa, jiran fitowar likita suke, don jin meke damunta.

Buɗe ƙofar ɗakin da akayi ne, yasa duka suka ɗago kansu, ganin Dr. ɗinne yasa sukayo kansa cikin, damuwa Papa Saleem yace.
"Dr. yajikin nata?".

Ajiyar zuciya Dr. ɗin ya sauƙe, cikin kulawa yace.
"Alhamdulillah, nayi mata duk wani abun daya dace, don tama samu bacci, ku kwantar da hankalin ku, bawani ciwo bane ke damunta, maleria ce kawai, don itace ma ta haifar mata da zazzafan zazzaɓin, amma yanzu idan ta farka, insha Allah zataji sauƙi."
Cikin gamsuwa suka shiga jinjina kansu, duban Papa Saleem da Majeed Dr. É—in yayi tare da cewa.
"Su biyoshi office."
Hakan kuwa akayi inda suka rufa masa baya.
Ummi kuwa É—akin da aka kwantar da Mubina É—in ta shige.

Magunguna Dr. ya rubuta musu, wanda zata na sha, idan ta farka.
Nan sukai masa godiya, tare dayin musabaha.
Majeed ne ya wuce pharmacy É—in dake cikin asibitin, nan ya sayo maganin sannan ya dawo.
Koda ya shiga É—akin, nan ya iske Papa Saleem da Ummi zaune, kallonsa ya kai ga Mubina, wanda ke kwance tana ta sharar baccin ta, yayin da ahankali ruwan da aka É—aura mata, ke É—iga bisa cikin jikinta.
Aje ledan maganin yayi, tare da É—an jingina bayansa da jikin bango.
Papa Saleem ne ya miƙe, duban Ummi yayi tare da faɗin.
Chapter 74 · 0% Book details