← Book details Ali Dan Tsoho Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 101 OF 124

Sashe 101

Ali Dan Tsoho Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Daga nesa Umaimah ta hango Kamal cikin haÉ—adÉ—iyar shigarsa irin ta saudiya, sai wata Æ´ar matashiyar balarabiya siririya tana biye dashi, itama ba'a ganin kome nata sai ido da tafin hannunta. Kawu Jafar da Anwar cikin farin ciki suka nufeshi.
Umaimah murna ta koma ciki ganin Kamal É—inta da balarabiya, ta gane matarsa ko kuwa watace daban? Tsaye tayi taga yanda Kamal suka
Rungume juna shi da Anwar ya sakeshi ya rungume kawunsa yana dariya. Kawun ya sakeshi yana ma Mubina magana, da harshen larabci"Ɗiyata ina miki barka da zuwa ƙasa mai tsarki cikin garin manzon mu." Mubina ta sunkuya tana gaishe da kawu dattijon ya mata kwarjini jinsa tayi kamar Umpah da Abbu ne. Ɗagota yayi yana murmushi yace"Ba sai kin duƙaba." Anwar yace.
"Mubina ko" to sannu da zuwa ya london?" cikin kunya tace "Lafiya lau." haka da Umaimah ta gani ne ya nuna mata cewar Mubina ce amaryar Kamal, cikin jin haushinsa ta ta taho da sassarfa ta ƙarasa da gudunta, ta faɗa ƙirjinshi ta saki kuka ta rungumeshi ƙam, tana cewa."Yayana sannu da zuwa i miss u..." Kamal yace"Oh Umaimah to tarbar yayan ne da kuka haka?" ya faɗi yana bubbuga bayanta, yana ƙoƙarin janyeta gabanshi na mahaukacin bugawa, tare da Addu'ar Allah ya rufa masa asiri kar Mubina ta masu tsiya. Iatako
Mubina wacce tayi mutuwar tsaye, ta zuba masu shanyayyun idanunta, wanda a take suka rikiɗe sukayi ja jikinta har wani tsuma yake. Kamal janye Umaimah yana sakinta. Kawu yace"To muje kuyi sallah ku cika tumbinku sai ku kwanta ku huta." Umaimah tana ƙoƙarin kama hannun Kamal yayi saurin kama hannun Mubina yana cewa" Ƙanwata baki gaishe da yayarki ba matana ce fa." Umaimah ta basar kamar bataji ba. Kawune yace"Ke!! Umaimah kinci gidanku, bakiji me Kamal yace ba?" baki ta turo ta daure tace"Aunty sannu da zuwa." cikin harshen larabci ta faɗi.
Mubina ta tattaro nutsuwarta ta amsa da "Yauwa ƙanwata." haka suka nufi gun motar Anwar ne ya zuba trolleys ɗinsu both ɗin motar ya rufe kawu da Anwar na gaba Kamal suna baya Mubina zauna tsakiya gefen da Umaimah bazata raɓi Kamal ba. Suna fara tafiya Kamal yaga Mubina bata ko kalleshi ba, sai Umaimah ce ke masa surutu. Kamal janyota yayi ya rungumeta yana mata raɗa narkewa tayi jikinsa ta ɗora hannunta kan fuskarshi tana shafa kwantaccen sajan fuskarshi ta ƙura masa idanunta wanda sukayi ja.
Kamal ya mata magana a hankali yace"Sweetie menene bacci ko?" kai ta girgiza masa tana murmushi mai kashe zuciyar masoyi, tayi magana yanda Umaimah ce kadai zataji tace"Mijina" Kamal ya amsa da "Na'am Sweetie nah."waigawa tayi taga su Kawu zasu iya ganinsu, sai tayi saurin janyewa jikinsa tana dariya tace"Bari zan faÉ—a maka." Umaimah kuwa mutuwar zaune tayi ta cika tayi fam. A hak suka iso gidan, bayan sun shiga Anwar ya kwaso kayansu suka nufi parlo.

Yumnah ta tarbesu cikin walwala, ta rungume Mubina. Wacce ta gaisheta cikin girmamawa. Umaimah aka cire abaya sai kai komo take wai ita me duwawu. Anwar ya kai masu kayansu can part É—in da aka ware masu wanda yasha gyara, Umaimah ta kashe kanta ta gyarashi. Suna zuwa Kamal ya murzama kofar key, yana kallon Mubina ta cire kayan jikinta ta saka wata guntuwar riga iya guiwa ta kwanta nan saman carpet. Kamal yaje ya haÉ—a ruwan gumi yazo ya É—auketa caÉ—ak. Kuka ta saka mashi tana dukansa tana cewa.
"Ajiyeni karka sake taɓani wlh sai ka mayar dani gidanmu bazan zauna ba." Cikin ruwan ya nasa ya cire rigarta yace"Na tuba yi haƙuri bazan ƙaraba idan laifi nayi ajikinki zan iya bari kimin nisan awa 1 bare na rabu dake." Haka ya samu ya mata wanka ya gasata sosai tana kuka wiwi da shasheƙa, yasa tayi alwalla ya nadota a towel ya rungumo abarsa ya fito da ita, jikinta ya goge mata ya murjeta da body lotion sai kuka take. Ya buɗe trolley ɗinta ciro abaya ya zura mata, ya shimfiɗa mata sallaya, yace"Oya yi sallah kibar kukan kinsa dai ke ɗaya nakeso wallahi bana son wata bayan ke kuma babu shegiyar da zata shigo rayuwarmu sam bana iya haɗaki da kowa Sweetie." ya faɗi yana rungumeta ƙirjinsa yana manna mata kiss a goshi.
Ajiyar zuciya kawai take saukewa tayi lamo a ƙirjinshi ta lumshe idanunta, ita kadai tasan me takeji. Kamal ya ɗago kanta a hankali kamar me koyan magana yace"Sweetie nah"Shanyayyun idanunta ta buɗe yace"Oya yi sallah muyi break fast mu kwanta kina jin bacci ko?" Baki ta zumbora gaba a shagwaɓe ta koma ƙirjinsa ta ƙirashi" Kamal!" murmushi yayi ya janyeta ya gyara mata tsayuwarta ta kalli Alƙiblah, yace"Oya yi salla kar alwallar ki ta karya." yana faɗin haka ya nufi toilet. Murmushi ta saki ta bishi da kallo saida ya shige ta yayar da sallar Asuba.

Kamal bayan yayi wanka yayi sallah. Anwar yazo ƙiransu, Hannun Mubina ya kama suka fice. Girke² masu rai da kuma lafiya, aka shirya masa, nan ƙasa dukansu suka baje Umaimah ce tayi serving ɗin Kamal, da Mubina, Mubina a dole takeci darajar kawu haka suka shiga kwasar girki, Umaimah tana kusan Kamal sai zuba take masa kamar ta shige cikinsa, ta kalleshi tace
"Yaya Kamal na kusa mutuwa fa Allah ya taɓoni kuma shi kadai yasan me ya ɓoye, a tsakaninmu, Yaya Kamal ciwon so ya kusa kasheni wallahi." ta faɗi tana riƙe hanunsa. Kamal yace"Wai amman kuwa da na shigar da wanda sonsa yayi sanaɗin kashemin ƙanwa, to ki haƙura kawai ki nemi wani." Baki ta turo tace"Allah bazan haƙura ba tab dan bakasan sa bane, to ba kowa bane k..." Kawune ya daka mata tsawa yace"Ke!! Wlh zan saɓa maki, wai anya aljannu basu shafeki ba kuwa?" Yumnah tace"Ai nima naga abin akwai hauka ko kunyar matarsa bakyayi ni kam ba ruwana bama son rashin arziki." Anwar yace"Se yaune zaku mata faɗan ba daidai ba? Idan na doketa kuga laifina." Umaimah tace"Yaya kaga sun tsaneni ko?" Akan dole yake biye mata. Haka suke ci abunci kowa rai babu daɗi, kawu yaji kunyar abinda Umaimah tayi.
Mubina ita kadai tasan me zatama yarinyar sai ta kumsa mata baƙin ciki ciki, sai ta nuna mata daga kanta ba kowa zuciyar mijinta, dan ta gano son Kamal take, ko yanzu taci darajar kawune badan hakaba hannun da ta riƙe mata miji ma yaci ubansa....

Bayan sunci sunsha aka ƙara gaisawa, Kamal na kusa da kawunsa, yana masu nasiya su zauna da juna lafiya. Mubina na kusan Yumnah zaune, ta sadda kanta cike da ladabi take jinjina masu kai.
Umaimah kuwa tayi fushi ta tafiyarta ta kwanta, tana murna juyi take kan ƙatuwar katifarta tace"ko banza na kumsa ma matarsa baƙin ciki haka zan maida kaina kamar sakara, sai na aure mata miji na rabasu Kamal dani ya dace, ba wannan figagiyar balarabiyar ba me kwala kwalan idanu fari sai kace zabiya, yarinya sai na ƙwace Kamal..." ta faɗi tana dariya. Karfe 8 am suka ma su Kawu sallama suka shiga part ɗinsu.

Jallabiyar jikinsa ya cire ya saka kayan bacci wandon iya guiwar sa ne. Ya zabo wata fincikar riga iya cinya ya sakama Mubina, ya kalleta yace.
"Sweetie kinyi kyau." Bata tankaba ta haye jibgegiyar katifar ta shige cikin bargo.
Murmushi Kamal yayi ya kashe wutar ɗakin ya ƙara fesa sansanyan turare a jikinsa, ya ƙara gudun Ac ya haye katifar, ya janye bargon ya shiga ciki ya rufesu ruf ya rungumota jikinsa.
Bata tanka masa ba, jin shasheƙar kukanta yayi, da sauri ya juyo da ita ya tallafo kanta da hannunsa biyu yace.
Chapter 101 · 0% Book details