Sashe 97
Triplets Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Jin ihunsa yasa ƴan'sandan dake bakin gate suka nufo ciki da gudu, ita ma mai aikin da gudu ta nufo ɗakin, laɓewa bayan wani ɗaki Jehan ɗin ta yi, tana ganin ƴar'sandan suka wuce zuwa ɗakin nasa, bayan sun wuce ne ta fito a guje gabaɗaya jikinta kermar tsoro yake yi, gudun cetar rai zata yi, fitowar da ta yi kuma ashe mai aiki ta ganta, da gudu ta kira ƴan'sandan tana gaya musu gata can gata can, kafin su zo ma tuni ta isa bakin gate, sai dai gate ɗin a rufe yake da kwaɗo, tsabar bala'in tashin hankali da take ciki, bata san lokacin da ta kama gate ɗin ta haye ta dira waje ba, gabaɗaya wayoyin saman ginin sun ji mata ciwo, amma bala'in da take ciki yafi wannan, tasan idan suka kamata a cikin wannan gida to sai dai gawarta ya fita, ta san wadda ta yi wa wannan aika aikan ba ƙaramin mutun bane, ƴaƴan Farooq ne uwa ɗaya Uba ɗaya, idan baku manta Farooq wanda ya yi kokarin lalata rayuwar Hanan a Katsina na ba, to yayansa ne wannan alhajin..........Dama idan bala'i ta yi balai zaka yi abin da ba ka taɓa zaton zaka yi shi ba, yanzu dai bala'i tasa Jehan haura saman gate, dama haka ne, in kaga bala'i ba abin da ba zaka iya yi ba, san da zaka yi ma, ba zaka sani ba, sai daga baya bayan ka samu natsuwa zaka yi ta mamakin ya akayi kayi abu kaza? Allah dai ya raba mu da bala'i.
A guje ƴan'sandan suka buɗe gate ɗin suka rufa mata baya, a haukace ta hau saman hanya tana gudu ga kanta babu ɗan kwali, saura kaɗan wata danƙareriyar mota ta takata, har ta ɗan bugeta ta faɗi kasa ma, da alama ta ɗan ji ciwo, dan ma dai Allah yasa driver motar ɗan hannu ne, ya iya tuki sosai, shiyasa ya yi nasarar taka birki a cikin wannan yanayi, ganin ta faɗi kasa ne yasa matukin motar ya fito da sauri ya nufo ta, dan ya ganta karamar yarinya ce, ba wata babbar mata bace. Zaro dara daran brawn eyes nasa ya yi yana faɗin "Areef kazo ka kallah ta ɗan ji ciwo fa, ka zo ka dubata, kuma ka ga wasu ne suke binta".
Yana zaune a gaban mota, shi dai burinsa azo a kai shi wajen heartbeat yau ya ganta su gaisa, amma Aseef zai ɓata musu lokaci, tun da bata ji ciwo ba sosai ba Allah ya tsare basu bugeta sosai ba, ba sai ya wuce su tafi ba, me na wani kiran shi ya zo ya ganta. Dama sun ce da Akila suna zuwa ne, yau za su je su gaisa da Ammie, ita kuma Akila ta gaisa da Areef, shi ne suka shirya tsab za su je.
Ganin sai kiransa Aseef ɗin yake yi ne yasa shi fitowa yana jan tsaki, Aseef ya ɓata mishi rai, dai'dai lokacin kuma ƴan'sandan suka iso wajen, da yake unguwar na manya ne, kun san babu jama'a, kowa yana cikin gida..........
Yaya makomar wannan lamari zai kasance? Anya alhajin nan zai rayu kuwa? Shin Jehan ta kyauta kuwa? Aseef, Areef zasu taimaka mata kuwa? Alhajin zai kyaleta kuwa? Ga kuma kaninsa Farooq dama yana nemanta, Jehan ta tara maki ta ko'ina, Ya makomarsu Adiva? Shin Lion zai kama wadda ya je nema kuwa? To bari dai na barku haka sai mun haÉ—u on Monday idan mai dukka ya kaimu
â¤ï¸â¤ï¸TRIPLETSâ¤ï¸â¤ï¸
*Duk wace ta karanta mini littafina ba tare da ta biyani hakkina ba Allah ya isa ban yafe ba, sai Allah ya tsayar da mu ranar da bata da abin da zata biyani face ladarta*
E41-42💋
Ganin sai kiransa Aseef ɗin yake yi ne yasa shi fitowa yana jan tsaki, Aseef ya ɓata mishi rai, dai'dai lokacin kuma ƴan'sandan suka iso wajen, da yake unguwar na manya ne, kun san babu jama'a, kowa yana cikin gida, kallo ɗaya ya yi mata ya kawar da kansa yana faɗin "Me yasa kake ta kirana ne wai?". Ita kuma buguwar da ta yi nan ne yasa ta ke ganin jiri jiri bata wani jin me suke faɗe sosai.
Miƙewa ta yi tana wani tangal tangal kamar zata faɗi, ta gaji over, ga uban gudu da ta sha, baiwar Allah ga dirar da ta yi ta saman gate kafarta na ciwo, bugu da kari duk ta kukkuje jikinta da wayar dake saman gate ɗin, ta ji ciwo,. A sugwane Aseef ya ce "Areef wlh she is resembling uncle face, they look alike, i think sister Rimsha ce, daughter uncle ce ita ma, kalli face nata ka gani". Hararar shi Areef ɗin ya yi yana faɗin "Zaka wuce mu tafi ne ko kana gaya mini she look like Uncle,? Wai ka manta nan kasarsu uncle ne? To dole akwai masu kama da shi over, so please let's go ina son mu dawo na kira Lion dan nayi magana da my Rimsha, ina missing nata over, tun safe bamu yi magana ba fa".
Katse su Æ´an'sandan da suka iso yanzu suka yi da cewa "Ke wuce mu tafi". Maganar da suka yi kuma yasa Areef da Aseef É—in gabaÉ—aya juyo da kallonsu a kansu, da kallo É—aya Areef ya yi musu ya fahimci marasa gaskiya ne, shi ma Aseef a nasa tunanin ya san dole wani abin zasu yi mata, duba kuma da irin shigar da yake jikinta, wata kila fyaÉ—e suka yi kokarin yi mata ta ki yarda, shi ne ta gudu suka bita, a tunanin Aseef kenan, shi kam Areef kai tsaye yasan basu da gaskiya.
Kokarin kamata suka yi Aseef ya ce ba zai yi wu ba, wlh babu wanda ya isa ya kamata, dan ta yi mishi kama da uncle Hosain sosai, ko da ba Æ´ar uwarsa bace, to dole zai taimaka mata saboda albarkacin kamar da fuskarta ta yi da shi, dan haka sai ya tsaya tsayin daka a kan lallai ba zasu tafi da ita ba.
Jingina da jikin motar Areef ya koma ya yi, tare da goya hannayensa a saman faffaÉ—ar kirjinsa yana kallon karfi hali irin na Aseef, shi ya dage a dole lallai sai ya tafi da ita, yarinyar da bai san ta ba, kawai daga ganin wasu sun bi yo ta a cikin daren nan ya wani tsaya shi dole sai ya taimaketa, ga shi ba shi da karfin ko na É—aga kwalin sweet, su kuma Æ´an'sandan da suka biyota sun ce lallai sai sun tafi da ita, domin kuwa ta aikata laifin da dole su kasheta.
Wani dogon tsaki Areef ɗin ya ja Aseef yana ɓata mashi lokaci, ya ƙosa ya koma gida ya kalli ya Rimsha ta wuni yau su yi video call, yana kewarta sosai da sosai.
Yana tsaka da tunani bai ankara ba sai jin wani kara na sauƙar mari mai sauti ya yi.
Cikin sauri ya É—ago kai tare da kai kallonsa kansu Aseef É—in, É—aya daga cikin Æ´an'sandan ne ya wanke Aseef da wani mahaukacin mari, da sauri Aseef É—in ya dafe kuncinsa da hannunsa, idanunsa sun yi jajawur domin ba karya ya maru sosai. Kan ka ce me É—ayan ya sake kwashe kafafunsa a in da ya zube kasa a waje, nan fa suka yi yunkurin yi mashi É—an iskan duka domin su tafi da ita.
Wani irin mugun bakin ɓacin rai Areef ya ji wadda tasa bai ma san lokacin da ya raba jikinsa da jikin motar ba ya yi kansu a zafafe.
Cikin zafin nama ya hau jibgansu tare da watsi da su kamar an aikosa, nan take ya koma ainahin waye shi, wato ya koma jam'in C.I.A cikakkun jarumai masu bada rayukansu akan al'ummarsu, kafin ma su shiga aikin sai sun sanya hannu akan sun sayar da rayukansu, ba su tsoron a mutu ko ayi rai, jininsu a tafashe yake a ko da yaushe, sun sami horo iya horo na wuce misali.
Rai a matukar ɓace ya yage rigar jikinsa domin tana takura mashi wajen jibgarsu yadda ya kamata, haka ya cigaba da ba su a jikinsu.
Shi kuma Aseef sarkin tausayi, bai ma damu da wani hali Areef ɗin yake ciki ba, bayan kuma shi ya jangwalo faɗar, miƙe wa ya yi abinsa ya riƙo hannunta yana yi mata sannu. Duk ilahirin jikinta sai kerma yake yi, dama a tsorace take, ganin suna faɗa kuma yasa ta kara tsorata sosai, ta fara kuka.
Hannunta ya ja suka karisa wajen motarsu yana faÉ—in "Kada ki ji komai tsab Areef É—ina zai yi masu dukan mutuwa, ke dai yanzu shiga mota bari ya gama jibgansu ya zo mu maida ke gidanku..." Bai kai karshen maganar ba ya ga an wurgo mutun kusa da shi, ai kuwa a guje shima ya shige cikin mota yana faÉ—in "Ya Subhanallah, Allah ka rufamin asiri da irin wannan duka na Areef, ka kama mutane sai jibga kake yi kamar an aiko ka, ni dai ina daga ciki, ka tabbatar ka ba su jikinsu sosai kafin ka zo mu wuce, amma fa ka yi sauri dan ina kewar My Rimsha wlh, zan je na kirata video call". Da yake ita Jehan É—in ta É—an bugu kuma ga tashin hankali da take ci, sai bata ma sauraron abin da suke faÉ—e, ta dafe kanta da hannayenta dukka biyu, ban da wash babu wani abin da take furtawa, kan nata ne dama ya bugu da jikin motar tasu.
Lilis Areef ya yi wa Æ´an'sandan kafin ya taho ya shiga cikin motar, a kujerar gaba ya zauna yana É—an dafe wajen ciwonsa, dan É—aga hannunsa da ya yi ta yin nan ya É—an ji zafin ciwon ba kaÉ—an ba.
Yana shiga Aseef ya ja motar suka koma gida, da yake ma basu da nisa da gidan, daga in da suke suna hangen gidan, dan fitowarsu kenan suka ci karo da ita. Sai da suka shiga cikin gida kuma Aseef É—in ya ce "Areef ai da mun fara mayar da ita gidansu kafin mu dawo ko?" Fita daga cikin motar Areef É—in ya yi ba tare da ya yi magana ba, burinsa kawai ya karisa cikin gida ya shafa maganinsa ya kuma sha na shansa dan ya fama ciwon nasa.