Sashe 42
Triplets Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Shi kuwa Areef cikin dariya ya ce "Yes kai Sa'a na ne mana, abokin wasa kuma ai daga kai da Aseef sai Prof". Shiru ya yi bai sake tanka musu ba, dan ya lura idan ya biyewa Areef yana iya yi mishi illah, ko kuma su yi faÉ—a, dama an samu shekaru basu yi faÉ—a ba, a lokacin da suke Æ´an 22 to 23 years, kullun na Allah ne sai sun yi faÉ—a, lokacin shi ma Areef akwai zafin zuciya, Lion bala'in zuciya rashin hakuri, Aseef zuciya, kun san lokacin ciwonsa, to haka zasu yi ta faÉ—a duk gidan ba mai iya raba su, sai sun jiwa kansu ciwo sun daku iya dakuwa ga junansu, sannan su hakura idan sun gaji, idan suka fara faÉ—a ko Uncle T tsoron tinkararsu yake yi kada su haÉ—a da shi, daddy kuwa har kuka yake yi idan sun fara, dan yasan ba shakka sai sun jiwa kansu ciwo, dan dukkansu ba baya ba wajen karfi ga zuciyar bala'i, É—aya ya ce ba zai hakura ba, idan aka mishi sai ya rama, idan ya rama shima wadda aka rama ya ce ba zai bari ba, babu hakuri ko É—aga kafa, haka zasu yi ta yi, amma yanzu Alhamdulila sun samu tsawon shekaru a kallah 6 basu yi faÉ—a ba, kuma duk da wannan faÉ—a da suke yi fa basu cin abincin idan har É—aya daga cikinsu baya nan, a tare suke komai, har kwana É—aki É—aya suke yi, gado ne uku a cikin É—akin nasu a lokacin, tun ainahi suna kaunar junansu fiye da tunanin mai tunani, sai dai kunsan dama ana samun faÉ—a irin haka a tsakanin Æ´an uwa, musamman ma twins or Triplets.
STORY💋
"Yauwa Prof menene Aduwa?". Cewar Areef. Shiru ya É—an yi yana tunanin menene ma wannan aduwar.
Katse mishi tunani ya yi da cewa "To koma menene ka haÉ—a da aduwa da goribar ka kawo mini da wuri fa" "Tom za'a kawo yau ma zan je kasuwar barci ba za'a rasa ba". Okey ya amsa da shi, daga nan ba su sake yi wa juna magana ba, suna kwanta shiru.
Can after some minutes Areef ya ce "Prof na mance ka ce da sister ta shirya zuwa Monday ta koma school". ÆŠan satar kallon Lion dake kwance yana fuskantar gefe da su ya yi, kafin ya ce "Okey amma naji matukar daÉ—i over wlh". Ya kai karshen maganar tare da shafa kyakkyawar dark black curly hair Lion É—in.
Juyo da blue eyes nasa ya yi a kansu. Ganin irin murmushin dake a kan fuskar Imran da kuma ɗan uwan nasa yasa ya ji daɗi sosai, yana son ganin Imran cikin farinciki kamar yadda yake son ganin TRIPLETS nasa, har cikin ransa yake jin Kaunar shi, bai taɓa son wani bayan TRIPLETS nasa kamar yadda ya so Imran ba.
Haka suka cigaba da nishaÉ—i suna hira, duk da bai sanya musu baki ba, yana matikar jin daÉ—in yadda suke hira da dariya haka.
AFTER SOME DAYS GIDAN HAJIYAR DAÆŠI ðŸ˜.
Tsawon kwanaki uku kenan yau su JEHAN suna rufe a cikin toilet, babu ruwa babu abinci, duk sun fita hayyacinsu, duk kyankyani irin na Jehan jiya sai da ta sha ruwan famfom toilet ɗin dan ta ceci rayuwarta kada ta mutu, sai kuka Adiva take yi, Allah sarki bata saba ba, ga yinwa ga kishin ruwa, sun yi ƙoƙarin buɗe kofar toilet ɗin amma abin ya ci tura, idan baku mance ba ta baya Zinariya suka rufe su, duk sun yi tsuru tsuru da su abin tausayi, sun fita hayyacinsu, tsabar yunwa tasa basu gani sosai, A'isha dai ta yi dana sanin biyewa Jehan, sun buga kofar toilet nan har suka gaji, ko motsin mutane basu ji ba, tamkar basu a duniya, tamkar babu kowa a gidan, Jehan ta yi kokarin buge wurar dake jikin window toilet ɗin dan taga me a wajen, sai taga akwai karafuna ta waje a jikin window, ba halin fita, kuma duk a cikin gidan window yake, ba a waje bane.
Idanuwan Jehan sun ƙanƙance sun yi jawur, da akwai dama, da ta yi kuka ita ma, amma ta daure tana rarrashin Adiva, banda sunan Allah babu abinda take kira, ta rasa madafa, sai yanzu zantukan daddynta ke dawo mata a cikin kunnenta, lokacin da yake neman takara, yana yawan gayawa uncle Shitu, idan zaka yi gyara ko kana son dakatar da wata ɓarna a ƙasar nan, to kada ka yarda ko da sunan wasa ka fitar sa nufin ka, dan akwai wasu shegun kuraye da dama da basu son a kawo gyara, su burinsu kawai a ɓata, kansu kawai suka sani, idan zasu ji daɗi to kowa ma ya mutu in yana so, idan ka kuskura ka fitar da nufinka na kawo gyara, to zaka ɓata, kuma ɓata ta har abada, za'a rufe babinka, za'a shafeka tamkar ba'a taɓa yin ka ba, jama'ar dake goya maka baya ma, duk zasu juya maka baya, a kullum jama'a suna amfani da abin da suka ji, ko kuma abin da aka shirya musu karya a kansa suka kalla, ba zasu taɓa yin tunani da kwakwalwarsu ba, da zarar ka shirya musu ƴar karamar karya tsab zasu yarda su hau kai su zauna, sai ka rasa wani irin kwakwalwa ce da mutanen mu, sai ka rasa me yake damunsu, ga gaskiya suna gani sai su take, shi ne babbar matsalar ƴan kasarmu, da suna da zuciyar tsayawa a kan gaskiya, dagiya a kan adalci, cire son zuciya, cin hanci da rashawa, su daina duba ɗan karamin abin da za'a basu, su duba al'ummarsu, su duba cewa wannan ɗan abin da za'a basu zai kare su sake komawa wahala, amma idan suka tsaya tsayin daga a kan ayi adalci, a kawo gyara, a dakatar da ɓarna, to ko basu sami komai ba, adalci ta tabbata zasu ji daɗin rayuwa fiye da tunanin mai tunani, a ƙasar nan ba'a yaki da rashin gaskiya gaba da gaba, idan ka kuskura ka yi gigin yin hakan, to zaka yi danasanin zuwarka duniya, ta karkashin kasa ake yakar tsinannu shegu, ta karkashin kasa ta in da basu zata ba, ta nan zaka yaki duk wasu kuraye marasa adalci masu tauye gaskiya.
Tuna zantikan daddynta yasa ta fara hawaye, yau ne ta tabbatar da abin da daddyn nata yake faɗe, sai dai kayi yaƙin sunkuru da rashin gaskiya, ba dai ka yi gaba da gaba ba.
Ganin tana hawaye yasa Adiva ta dafata tana faÉ—in "Jehan lafiya kike hawaye haka?". Girgiza kai ta fara yi kafin ta fara magana. "Adiva daddy ya yi gaskiya, yanzu kinga da muna nuna zamu yaki gidan nan ta karfin tsiya, kinga mun kare a cikin toilet, daman daddy ya ce ta karkashin kasa ake yakar rashin adalci, yanzu na gane nufin daddy, hawayen da nake yi kuma saboda daddyna nake yin shi, daddyna ina yake? Yana raye ne ko ya mutu? Bana jin ya mutu Adiva, bana jin hakan a jikina, na fi zaton yana wani wajen yana rayuwa, ya Allah ka kare mini iyayena da Æ´an uwana, Rimsha Æ´ar uwata É—aya tilo a duniya, ko a ina take yanzu Oho, ita ma ina ji a jikina tana raye, tana wani wajen, Allah sarki, Allah ka kawo mana mafita". Ta kai karshen maganar tana goge hawayen fuskarta.
A cikin wannan kwana uku da suka yi a rufe, sallah ma a zaune suke yin shi a cikin toilet É—in, ita Jehan azumi take É—auka a gabaÉ—aya kwana ukun, shiyasa abin ya yi mata sauki, su A'isha kuwa, ruwan toilet É—in suke wuni sha ba abinci, cikinsu ya yi ta ciwo kamar zasu mutu, haka zasu wuni suna hawaye, da daddare kuwa, Adiva da Maryam cikin baf É—in wanka suke shagewa su kwanta, ita kuwa Jehan a zaune take kwana, idan barci ya kwasheta har faÉ—uwa take yi wani lokacin, Aisha kuwa, a kasa mai gabaÉ—aya take kwanciya dan suna wanke toilet É—in, Bayin Allah nan abin tausayi, duk wanda ya gansu sai ya matsa musu kwallah, har wani shegiyar rama suke yi.
Su kuwa su Zinariya, suna can suna harkokin gabansu, sun kawo sabbin ƴan mata da wasu sabbin matan aure ƴan hannu, kuɗi nata kara shigowa kamar ba gobe, sun bar bayin Allah a cikin toilet, tamkar ba rayuka suka rufe a ciki ba, Allah dai ya yi mana maganinsu ya toni asirin tsinannu shegu. In Sha Allah sai sun girbi abin da suka shuka, zasu ɗanɗani ƙuɗarsu kuwa.
WANNAN KENAN A GIDAN HAJIYAR DAƊI BARI MU LEƘA GIDAN LION DAN JIN YA AKE CIKI.
AFTER SOME DAYS.
Yau ma dai tsala wanka suka yi, suka shirya cikin kananan kaya, a yau ne kuma Imran ya tafi karɓo musu ɗin kinsu dake wajen tela, yana fita ba jimawa suka shirya cikin wando jeans ash color mai shegen kyau, ta ɗan kamasu daga ta sama, ta kasar kuma ta buɗe, riga kuma top ce pink color, sun yi kyau sosai kamar ka sace su ka gudu da su, Rimsha zata ɗaure gashin kanta Akila ta hanata, wai ta sake shi kamar ba Indiya, kuma kun san yadda gashin nata yake, sak gashin kakanta Na'urat, abin ba'a cewa komai sai dai Masha Allah.
Haka ta biyewa Akila ta saki gashin har gadon baya, perfume ɗin Akila suka sanya a jikinsu, Rimsha ta fito kamar baturiya sai dai hasken fatar ne kawai da bata da shi kamar nasu, ita kuma Akila da yake gashin ta bai kai na Rimsha tsawo ba, sai ta ɗaure shi tare da sanya ɗan ƙaramin handkerchief ta ɗara a gaban goshinta, tsakiyar kanta a waje.
Da farko Rimsha ta ce ba zata fita babu ɗan kwali ba, daga ƙarshe kuma da Akilar ta yi ta zugata, sai ta yarda suka nufi waje a hakan.
Babu kowa a palon sama, dan haka sai suka sauƙa kasa, nan ma babu kowa, waje gabaɗaya suka nufa, ita kuma Jelly tana can tana barci abinta.