← Book details Triplets Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 59 OF 121

Sashe 59

Triplets Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Babu kowa a Palon, kai tsaye waje ya nufa, su Ammie sun jima da yin barci abinsu, motarsa ya je ya shiga ya nufi gidansa. Lokacin da ya isa gida, tana zaune a palo sai kuka take yi, kwata kwata hawayenta ya dai'na zuba daga idanunta, sai shessheƙar ne kawai zaka ji, shi zai tabbatar maka da kuka take yi, amma hawaye kam ya dai'na zuba gabaɗaya.

Tana jin tsayuwar motarsa, amma ta kasa tashi saboda wani irin jiri da take ji yana ɗebanta, hakura ta yi ta cigaba da zama a in da take har ya shigo cikin palon, da farko bedroom nasu zai wuce, jin shessheƙar kuka a palo yasa ya tsaya tare da kunna wutar palon, ya tsorata sosai ganin yadda har idanunta suka kumbura, bai yi zaton kukan da Akila ta rubuta mishi a massage take yi ya kai har hakan ba, ya yi zaton irin kukan kullun ne da ta saba yi mishi. Da sauri ya kariso in da take yana ambatar sunanta, "Wife! Wife".

Kara rushe mishi da kuka ta yi, yana zuwa ya runhumeta yana É—an bubbuga bayanta alamar rarrashi tare da zama a gefenta, ina ai sai da ta gan shi ne ma ta ji sabon kuka ya zo mata mai karfi, yi take yi yana rarrashinta, sai da ta bashi wahala kafin ta tsagaita da kukan, É—aukarta ya yi suka nufi toilet, ko abinci bata ci ba, dan ta kasa ci É—in, wanka ya fara yi mata kafin ya fito ya shiryata cikin kayan barci masu kyau, sosai ya yi nadamar abin da ya aikata, bai yi zaton zata wahala har haka ba, da yanzu cikin nasu ya zube waye gari ya wayanwa to? Ya tambayi kansa da kansa, dan yasan damuwa tana É—aya daga cikin abin da take hana ciki zama a jikin mace.

Bayan sun shirya da kansa ya rinƙa bata abinci a baki yana rarrashinta, a wannan dare dai basu suka kwanta ba sai karfe 3 na dare, sai lokacin suka gama duk abin da zasu yi, sai sauke ajiyar zuciya take yi, har lokacin sai kara rarrashinta yake yi, ba shi ya sami kwanciyar hankali ba har sai da ya ga tayi barci cikin kwanciyar hankali kwance a kirjinsa tana faman sauke ajiyar zuciya, a sannan ne ya samu natsuwa tare da yin addu'ar barci ya shafa musu ita da shi baki ɗaya. ASUBA TA GARI.

GIDAN LION💋

Bayan ta yi sallar mangariba da issha, sai ta É—auki abincinta ta fito palo dan taci tare da Aseef, shi ne abokin yin ta dama, kuma dama kafin su rabu ya tafi masallaci ta ce mishi idan ya dawo zasu ci abinci tare, okey ya amsa mata da shi, to shi ne yanzu zata je garden su ci abincin a tare idan zai iya.

Duk da tasan babu kowa a garden ɗin, sai da ta tsara sallamarta irin ta addinin musulunci, tana sa kai zata shiga ciki, ita kuma jelly tana fitowa, karo suka yi, baya kaɗan ta yi tana ce wa Jellyn sannu, dan ita ce ta bugeta, rai a ɓace jelly ta ɗaga hannun zata mareta, dan dama haushinta take ji, kamar daga sama ta ji an riƙe hannun nata, Rimshar ta gama rintse idanunta gam tana jiran saukar mari sai ta ji shiru.

A hankali ta waro dara daran fararen sleeping eyes nata a kan jelly, da mamaki take kallonta, cikin sauri kuma ta ɗan juya gefenta ganin jelly'n na kallon hannun nata, muryarta har rawa yake yi wajen furta "Yaya Areef". Yana tsaye ya rasa wani hukunci zai yi wa Jelly yau, ji yake tamkar ya murɗe hannun nata ya karye shi gida biyu, yau sai ta ɗanɗana kuɗarta, dawowansa daga masallaci kenan ya ce bari ya zo garden ɗin, dan yasan da wuya ba zai sami Gimbiyar tasu a wajen ba, yanzu a gabaɗaya gidan bata da wani wajen zama da ya wuci wannan wajen, shiyasa ya nufo wajen kai tsaye da fara'arsa, cike da kwarin gwiwar zai same zaune tana cikin farinciki, Aseef da Imran sun wuce ciki, shi Aseef ya je ya yi wanka ya sako kayan shan iska, dan ya ce zafi ta yi yawa, shi kuma Imran wajen Jellyn ya nufa, dan bai taɓa tunanin a wannan lokacin zai sameta a garden ba, ya fi zaton tana ɗaki, dan ita sarkin kallo ce, sai ta wuni a cikin ɗaki tana kallon film a Tv dake cikin ɗakin, bata wani cika fitowa waje ba.

Sun kai almost 2 mins tsaye a wajen, ba ƙaramin razana jelly ta yi da ganin face nasa ba, tun da take da su a gidan sai dai taga wucewarsu, bata taɓa yin ido huɗu da su ba, kuma shi ma Areef dama da Rimsha kawai yake wasa da dariya har haka bayan TRIPLETS nasa da Imran, bai cika yiwa mutanen da suka zo baki magana ba, idan suka yi mishi magana, yana amsawa saɓanin Lion da ko kallon in da suke ma bai ishe shi ba, a takaice dai bata taɓa yin gaba da gaba da ɗaya daga cikinsu ba, sai dai bayansu take gani.

Nan take ta sha jinin jikinta, tayi narai narai da ido, dan dama duk rashin kunyar mai rashin kunya sai dai idan bai yi ido huÉ—u da fusatattun fuskokin zakunan jikin William jacop ba, ga fuskokin nasu mai cike tap da bala'in kwarjini mai haukata mutane kamar me, ganin ya yi shiru bai saki hannun nata ba, bai kuma yi mata hukuncin da yake da burin ya yi mata ba, yana tunanin ya É—aga mata kafa saboda auren dake kanta ne ko kuma ya karyeta kawai?.

A hankali cikin sanyin murya Rimsha ta sake ambatar sunansa "Yaya Areef". Dawo da dara daran ash eyes nasa kanta ya yi, tare da sakin hannun jelly'n ya wuce zuwa cikin garden É—in, da gudu jelly ta watsa zuwa cikin gida, ita kuma Rimsha bayansa ta bi zuwa cikin garden É—in.

A ɗan gefensa ta zauna tana mai ɗaga mishi gaisuwa, nauyayyar ajiyar zuciya ya sauke, bai amsa gaisuwar tata ba sai ya ce "Daga yau duk wanda ya yi kuskuren marinki, in ma a gidan nan ko a waje, ki rama, idan kika kuskura kika bari wata ta mare ki baki rama ba, to gaskiya zan yi miki hukunci, ko Mark ne ya mare ki, ki rama ki ce ya zo ya rama a kai'na, kina ji na ko?" Gyaɗa mishi kai ta yi, sai faman sauke numfashi yake yi tare da nisawa, tamkar shi aka yi niyar mara, gabaɗaya ya ji babu daɗi, yaso ɓalle hannun Jelly wlh, bai so ta yi wannan babban kuskure na yunkurin marin Rimsha ya barta ba, yau dai taci albarkacin igiyoyi ukun dake kanta, ba dan haka ba, da yanzu haka tana gadon asibiti.

Suna tsaka da hitarsu sai da Aseef, sanye yake da gajeren wando jeans baki zuwa gwiwarsa, sai riga mai ƙaramin hannu sky blue, kusa da ita ya zo ya zauna sai tashin kamshi yake yi, kamar ko da yaushe, sai aikin latsan waya yake yi, yana chatting da bugun zuciyarsa.

Shammatarsa Areef ya yi ya kwace wayar yana faÉ—in "Tun da kazo kafi bawa wayarnan mahimmanci sama da ni, wai me kake yi ne a cikinta ne?". Dawo da kallonsa kan Rimsha ya yi yana faÉ—in "To ka duba mana ka gani, ba wani abu bane hira nake da matata faricniki na, our Queen ina abincin mu?". Ya yi maganar yana É—aga mata wannan kyakkyawar cikakken gerar tasa, gata baka kirin cike da gashi.

Zata yi magana kenan Areef ya katse ta da cewa "What? Me nake ganin nan, dan Allah da gaske ne abin da nake gani Aseef". Rimsha ce ta amsa mishi da "E mana yaya Areef da gaske ne, ai ni naga komai" tana magana tana dariya.

Ɗan leƙo face nata ya yi kafin ya ce "Wow our Queen kin ga ɗan bakin nan naki kamar baya magana ko? Ashe dai kin iya sa ido, wato kallona kike yi lokacin da nake hira da Heartbeat ko? Amma shi ne da na dawo cikin mota kika yi kamar mai barci ko? To Allah ya kamaki yanzu, har da wani cemin yaya Aseef ina son yin magana da Aunty Akila amma baka tashe ni ba, eyye wato barcin karya aka yi mini kenan? Ni ne ban gane ba, to ba zan bari ba, sai na zane ki".

Zata yi magana ya É—aure kyakkyawar farin yatsansa a saman lips nata yana faÉ—in shiiiiiiiiii ta yi mishi shiru.

Buge hannunsa Areef ya yi yana faɗin "Ba wani shirun da zata yi maka, ka jimin mutun, ka dai'na taɓa mata baki, zo nan ma ka gaya mini tun yaushe wannan abin ya fara faruwa ban sani ba, ka barni a gantale ban san komai ba, shi ne dan iya shege zaka wani cemin kana mafarkin mace ko? To dama kana zuba irin wannan kalaman soyayya ya za'ayi ba zaka yi mafarki ba, lallai ma ka sha da rabona".

Cikin sauri ta ce "Yaya Areef nasan komai, duk abin da ya faɗa wa Aunty Akila ina jinsa, ni zan gaya maka". Aseef zai sake yin magana Lion ya shigo wajen bakinsa ɗauke da sallama kasa kasa, yana sanye da pajama launin fari tas, tamkar yanzu ya fitar dasu daga ledarsu, yau shima sarkar wuyarsa tana a waje saman rigar kamar yadda Aseef yake yi, bai barta a ta ciki ba, ya yi kyau over, kujera daban ɗan gefe dasu ya je ya zauna, hannunsa na riƙe da laptop da kuma wayarsa.

Ganinsa yasa suka watsar da zancen shirmen da suke yi dan sanya Rimsha dariya, Areef baya son Lion ya rinƙa kallonta kullum a cikin shirme da yarinta, gwara su rinƙa yin abu serious a gaban shi, dan ya dai'na yi mata kallon small baby. Abinci Areef ya ce ta kawo musu suci, miƙewa ta yi ta nufi cikin gida, jim kaɗan ta dawo hannunta ɗauke da plates and spoons.
Chapter 59 · 0% Book details