← Book details Triplets Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 121

Sashe 25

Triplets Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Su biyu ne ke wasa a wannan waje, kamanninsu ɗaya, daga gani kasan ƴan biyu ne, fararene tas tamkar larabawa, waƴan nan samari ba su kowa bane a fa ce Azharuddeen da kuma Nawazudden, a lokacin Bama a haifi daddyn jelly ba, haka zalika Hjy Batula, Zahradeen wato Abbi, da kuma Abdulkadir wato Abba, a lokacin suna makaranta, haka ita ma Gwaggo tana makaranta, Abba yana haɗa degreensa ta farko a jami'ar Ahmadu Bello University Zaria, a can zaria yake zama, sai idan an yi hutu ya dawo shi ma time to time ne, haka shi ma Abbi sai hutu yake dawowa, ƴan gata ne na bugawa a jarida, iyayensu na bala'in kaunarsu, suna shagwaɓa su, kome suke so cikin ƙanƙanin lokaci ake yi masu, Mahaifinsu hamshaƙin mai kuɗi ne ba na wasa ba, mahaifiyarsu kuma baturiya ce yar kasan Russia, kuma kamshakiyar mai kuɗi ce ita ma, lokacin da babansu ya je karatu a can suka kulla soyayya, har ya aurota ya dawo da ita, amma kafin su dawo Nigeria sun zauna sosai a Russia, dan sai da suka haifi Abba, Abbi, Gwaggo, da kuma twins, har ma su twins sun girma sun zama samari, a takaice dai su daddyn Rimsha ba'a nan Nigeria a ka haifesu ba, a lokacin da suka fara girma sosai ne kuma Mummynsu ta ce lallai sai sun dawo Nigeria dan su san familyn babansu, haka ba dan Dr Salman ya so ba, ya tattarosu suka taho Nigeria, a in da ya sai gida a Kaduna dan nan yake son zama, bayan ya dawo baifi da wata ɗaya ba, iyaye da ƴan uwa suka ce wlh ba zai yi wu ba, dole ya auri yar gida Nigeria dan kada turawan nan su kwashe komai ɗin sa, haka ba dan ya so ba ya yi wa Na'ura wato mummynsu kishiya da wata ƴar karin Bauci, wadda kuma ƴar kanin babansa ne, kuma shi kanin baban nasu ne ya haɗa wannan aure, Naura wato mummynsu shiru shiru ce, duk da take baturiya tana da halin kirki sosai, bata da yawan magana kuma bata son hayani, kamar dai daddyn Jelly take, shi kuma Dr Salman duk da yake da wannan fara'a fa to akwai shi da zuciyar bala'i, ga saurin fushi kamar me, idan ya yi fushi kuma baya sauƙowa ta daɗi, tun da suka yi aure da Naura bata taɓa yarda ta yi mashi wani laifi ba, dan saboda tasan halinsa ciki da bai, kuma an yi sa'a ita ma irin Aunty ta Abbi ce, bata magana, tana bala'in son ƴaƴanta da mijinta, saboda mijin nata ta musulta, da ta musulta kuma ƴan uwanta suka ce sun yafe ta, wannan dalili yasa tun da ta baro kasarsu bata sake komawa ba, kuma hakan ma yasa ta ce su dawo Nigeria, saboda bata son suna haɗuwa da ƴan uwanta kuma basu yi mata magana, tana jin babu daɗin hakan sosai, tun da tazo Naija bata ma sha'awar ta koma kasarsu, NIGERIA ya yi mata daɗi, in yanke maku labari ta koma gaje, tun da ya auri wannan yar Bauchi shikenan zaman lafiya ta yanke a cikin gidan, faɗar yau daban ta gobe daban, a lokacin Naura tana da karamin ciki, da zarar Amarya ta fara bala'inta Naura zata wuce cikin ɗaki abinta, ga shi a cikin yaranta dukka daga Hassan Sai Hossain ne kawai suke garin Kaduna, shi kuma Dr Salman gabaɗaya ya birkice a lokacin, ya juya ya koma wajen Amarya ya tare abinsa, ko kallon in da Naura take baya yi, yana fin wata bai haɗu da ita ba ko ajikinsa tun da yana da Amarya, kuma bata damuwa baiwar Allah, abin kai daga gani kasan shiryar wa Amarya aka yi daga gida, dan dama family sun ce ba zasu yarda baturiyar nan ta zo ta kwashe komai na ɗan su ba, kasan cewa yafi kowa kuɗi a cikin familynsu, Dr Salman farine tas, amma Naura ta haifo ƴaƴa farare irinta da chocolate irin dangin mijinta, mutanen Bauchi two colors ne, kanne Dr Salman gabaɗaya chocolate colors ne, shi ne kawai fari a cikinsu.

A na haka su Abbi suka dawo hutu, to dama gabaɗaya cikin yaran Dr Salman ya fi kaunar daddyn Rimsha da Hassan, sun fi shaƙuwa, ita kuma Amarya bata son hakan, tana jin haushin hakan, shiyasa ta tsani daddyn Rimsha fiye da misali.

Dawowar su Abbi gidan yasa suka takawa Amarya birki a kan cin mutuncin da take yi wa mahaifiyarsu, har iƙirarin dukan mutuwa Abba ya yi akan zai yi mata, a kwana a tashi Amarya bata daina ba saboda Dr Salman yana goya mata baya, ta mallake shi, sai kwasan dukiyarsa take yi tana turawa gida Bauchi, dan a cewarsu ai ita ma baturiyar tana kwasa ta aika kasarsu, dan haka ne ma suka turo Amarya da babban shirinsu, abin da basu sani ba shi ne, Naura kusan ma tafi Salman kuɗi, domin iyayenta hamshaƙan masu kuɗi ne, kuma kunsan turawa, tun ƴaƴansu na yara suke sakar masu kuɗi da komai da komai, dan su yi abin da suke so, hakan yasa tana da account mai ɗauke da dubbanin makudan kuɗaɗe, ga kuma zallar ruwan cash a gida.

Zaman lafiya dai yaki samuwa a tsakaninsu, dan an turo amarya ce ta kori baturiya ta koma kasarsu, abu sai gaba gaba yake yi, yaki karewa.

Wata rana aka wayi gari Amarya ta yi yunkurin dukar Na'ura, a lokacin kuma cikin ta ya kai wata biyar haka, ba imani Amarya ta yi yunkurin dukanta, aikuwa Abba ya yi mata ɗan iskan dukan mutuwa wadda har sai da aka kwantar da ita a gadon asibiti, daga nan ne fa wannan tsohuwar gaba ta faro tushe, dan kuwa da Dr Salman ya dawo ya ce ba zai taɓa yarda ba, da hannunsa ya miƙa Abba a police station aka rufe shi akan ya daki amarya, a wannan rana tamkar Naura zata yi hauka, babban ɗanta a police station, idan ba kaddara da soyayya ba akwai wanda ya isa ya rufe mata yaro ne, gida dukka ya birkice da kuka, Abbi ne kawai baya kuka yake rarrashinsu, Naura tana yi, Hassan da Hossain suna yi, yau sun ga ɗan karamin yaki bayin Allah.

Sai da Abba ya yi kwana biyu a rufe aka sako shi, Naura ta jigata sosai da kuka, ta yi nadamar musulta da ta yi, ta bar family'nta, ta bar dukka uban gatanta, ta yarda da Dr Salman, ta biyo shi, yanzu ya ci amanarta, yana azabtar da ita, ta yi danasanin cewa su dawo Nigeria. Abin da bata sani ba, shi ma ba laifinsa bane, iyayensa ne da basu kaunarta, su ne suka shirya dukka wannan abin.

Bayan kwana biyar da faruwar abin da ya faru na dukan Amarya da Abba ya yi, masifar Amarya dai ba abin da ya ragu, sai ma abin da ya karu, iskanci kala kala, a ranar da aka sallamota daga asibiti ta dawo gida, tun da ta ɗaura ido a kan daddyn Rimsha Allah ya jarrabeta da wani mummunar nufi a kan shi, ko da yake ba Allah bane ya jarrabeta, ita ce ta ɗaurawa kanta wannan wahala, wani irin azababben sha'awar daddyn Rimsha take yi, domin duk cikinsu ya fi su bala'in farin jini, ga shegen saurin shiga rai kamar me, yadda dai kuga Rimsharsa, shi ta gado, duk in da ya je sai an so shi, ga zahiri kuma kungani, yadda su Lion basu karɓar baki, amma shi sun karɓe shi hannu bibbiyu, to haka yake da shegen shiga rai tun yana yaro, ga bala'in kyau kamar shi ya yi kansa.

Amarya dai ta yi iya yinta akan ta yi wa daddyn Rimsha fyaɗe, amma ina abin ya ci tura, duk da yana matashi kuma ɗan tubabbiyar baturiya, ya sami kula ta uwa, ya yi dacen uwa da ta yi mashi tarbiya mai kyau, duk da Naura ainahinta ba musulma ba ce, amma da ta musulta ta riƙi addinin sosai, ta kuma koyi abubuwa da dama tun kafin ta haihu, haka ta koyawa yaranta addini, suka yi riƙo da shi sosai, har ma sun fi ainahin musulman da ba mix.

Idan suka je Bauchi kowa baya sonsu, sai su rinƙa ce masu ƴaƴan kafura, kyamatarsu kakanninsu suke yi, suna hantararsu, ita kuma Naura baiwar Allah duk da haka bata hana su zuwa ga dangin babansu, Abba yana da bala'in zuciya kamar babansu, sai ya ce shi wlh ba zai sake zuwa ga dangin babansu ba, ai suna zaginsu, suna ce masu ƴaƴan kafura, idan ya je wlh idan suka ce mashi haka, sai ya yi masu dukan mutuwa, a lokacin yana tashen faɗa kamar hauka, ai kuwa Naura tayi ta yi mashi nasiha a kan kada ya kuskura ya tanka, ba kakanninsa bane masu zagin nasa? To ya yi hakuri komai zai wuce watarana, fir yaki yarda, ya yi ta cika yana batsewa, ya ce shi dai ba zai yarda ba, wlh sai ya sumar da kakan nan nasu in dai bata dai na zaginsu ba, gudun kada ya je ya sumar da tsohuwa a banza ya kara ja mata bakin jini yasa Naura ta yarda ta bashi goyon baya akan ya daina zuwa, haka suma su Abbin suka daina zuwa Bauchi gabaɗaya, daga wannan lokacin suka rufe babin family'n babansu, suka cigaba da rayuwarsu.

A kwana a tashi lokaci ya ja, cikin Naurat na da wata 8, Amarya ta je gida Bauchi ta yi sati guda ta dawo, har lokacin kuma babansu yana manne da ita, ya guji Naura, abin ya yi Baiwar Allah yawa, ga shi bata isa ta ce zata koma kasarsu ba, domin kuwa ta watsawa iyayenta da Æ´an uwanta kasa a ido, ta yarda da Dr Salman ta biyo shi, shi kuma ya ci amanar yarda, haka ta daure ta cigaba da zama cikin kunci tana kula da tarbiyar Æ´aÆ´anta.
Chapter 25 · 0% Book details