← Book details Triplets Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 121

Sashe 36

Triplets Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai murna suke yi, an kawata gidan tamkar ba gidan ba, sun yi amfani da tsafinsu wajen sauya gine ginen dake a cikin gidan, sun fito da sabbin gine gine tare da sabon penti, ga wasu baloon da kayan kyalkyali da aka zuba, tamkar wajen party, kai idan ba ance maka nan DAULAR MUTUWA bane ba zaka taɓa ganewa ba, saboda tsantsar kyan da ya yi, su barbushi duk sun zama kyawawan matasa masu jini a jika, ma'ana sun koma aihanin halittar da Allah ya yi masu, kyawawan matasan kabilar Ebo ne, duk wanda ya san Ebo ya sansu da tsawo da kuma ƙiba, mafiya yawancinsu farere ne kuma kyawawa, to suma haka suke, fararene tas kyawawa, ga tsawo da ƙiba, suna da kirar karfi tamkar masu ɗaka karfe, ma'ana masu yin gym, kuma ba wani gym da suke yi, halittace kawai da mafiya yawan mazan Ebo haka suke.

Fadar QUEEN an kawata shi da wani irin mahaukacin kyakkyawar zazzafar kwalliya, komai na cikin fadar Navy blue ne, ga wasu tsala tsalar kujeru da suka yi amfani da tsafinsu wajen kyara su, idan ka kalli fadar QUEEN sai ka yi zaton wani katafaren Daula mai tarin arziki na wani hamshakin basarake ne.

A cikin fadar akwai wani hawa step 3 haka, a saman step É—in ne a ka kawata wa QUEEN kujeran da zata zauna, sai dai kujerun guda biyu ne a wajen ba É—aya ba.

Sai shagali ake yi, su baba da yake sun saba gani duk shekara sai basu wani damu ba.... WAI SHIN MENENE MAKASUDIN HASSASA DAULAR MUTUWA NE? kamar yadda na gaya maku a baya, ta kabilar Ebo ce, sun hassasata ne ma dan tsafe tsafensu na samun makudan kuɗaɗe, suna ɗebo yara daga arewa zuwa wajen, da wuya ka samu ɗan gudu a cikin waƴan da ke cikin gidan, ko da gigin wasa ba zaka taɓa gani sun yi kuskuren kamo ƙabilar tasu ba, suna tsafi sosai da jikin mutane, ba iya yara ba, har da manya wanda ya yi sake da addininsa, yanzu matsafa sunyi yawa a duniya fiye da tunanin mai tunani, sai a riƙe ibada dan a tsiranwa gaidinsu, suna shan jini sannan kuma suna cin namar mutane, suna sayarwa wasu gidan matsafar wani sassa na ɗan adam idan suka buƙata dan yin tsafinsu, a caf faɗin kasar nan da wuya a samu gidan matsafa da suka kaisu girma da komai da komai, sun shahara ta wannan ɓangaren ba kaɗan ba, duk wanda ya shiga wannan gida baya fita, an rufe babinsa.... MU KOMA KAN LABARIN MU.

Murna a wajensu ba'a magana, wata kyakkyawar halitta ce ta fito daga wani katafaren kyakkyawar ɗaki, wannan halitta mace ce, a shakaru ba zata wuci 22 years ba, tana da tsawo sosai, amma bata da ƙiba sosai, ga shape kamar ita ta yi kanta, fara ce tas, ga hancin nan ɗan siriri kamar karas, ya zauna sosai da kyau a saman kyakkyawar farin fuskar tata, ɗan bakin nan nata ɗan karami, lips nata launin dark purple, kyau iya kyau wannar matar ta yi, sanye take da doguwar riga launin black color, rigar tata tana ja har kasa, rigar irin weeding gown ɗin nan, kanta babu ɗan kwali, ta zuba gashin nan nata har gadon baya, tamkar ita ta bawa kanta wannan kyakkyawar gashin, ga shi irin gashi mai gazar gazar ɗin nan ne, sai ya kwanto mata har baya. Wannan mata ba kowa bace fa ce QUEEN.

Saman É—aya daga cikin kujerun da aka tana da mata ta nufa, ga wasu kyawawan fararen samari guda biyu suna take mata baya, sai kasa da kai su barbushi suke yi alamar girmamawa, a gabaÉ—aya cikin fadar QUEEN É—in ita ce karama, amma kuma ita kowa yake durkusawa dan girmamawa, har sai da ta zauna a saman kujerarta suma suka zazzauna a nasu kujerun.

Tana zama bai fi da minti 5 ba, mahaifiyarta ta fito, wadda ita kuma dattijuwa ce da a kalla zata iya kai 45 to 50 years haka, da kallo É—aya zaka yi mata kasan cewa yes tabbas ita ta haifi Queen, ba komai zai sanya ka yi tunanin hakan ba face muguwar kamannin dake a kan fuskokinsu.

Tana takawa bodyguards guda biyu suna take mata baya kamar dai yadda suka rako QUEEN, har sai da ta zauna bodyguard É—in suka juya zuwa ta bayansu suka tsaitsaya dan tabbatar da tsaro a kansu.

Cikin yarensu mahaifiyar QUEEN ta buɗe musu taron, kowa yana zauna saman tsadaddun kujerun, sun sha kwalliya na ƙin karawa, suna da yawa sosai, a kallah sojijin ko in ce dakarun QUEEN zasu iya kai su 50 haka, dukkansu babu wani yare na daban a ciki, duk yarensu ne, hakan zai tabbatar maka da ba ƙaramin shiri suka yi wa wannan bakin azzalumin gidan ba.

Cikin yaren su suka gudanar da komai, sun É—auki tsawon lokacin suna magana, wadda a kallah zai kai awa uku zuwa biyar haka, sai tattauna suke yi, da alama suna kara yin shawara ta yadda zasu kara buÉ—a gidan ne, ta yadda zasu inganta shi ya kara girma fiye da tunanin mai tunani, shi ne abin da suke tattaunawa, kowa yana kawo shawararsa a kan ga yadda zasu yi.

QUEEN dai shiru bata ce ko uppan ba, mahaifiyar ta ke magana, daga karshe ma mahaifiyar tata ce ta yanke shawarar ga matsayar da zasu tafi a kan shi dan su kara faÉ—aÉ—a gidan nasu...... BASU SAN CEWA ALLAH BAI YI ALKAWARIN TALLAFAWA AZZALUMAI BA, ALLAH BAYA BARCI, YANA GANIN KOMAI DAKE FARUWA, WANNAN TSINANNEN GIDA BA ZAI CIGABA BA, YA DAI CIGABA A BAYA, SUN CI LOKACIN SU DA DAMARSU A BAYA, A YANZU IN SHA ALLAH SAI YA RUGUJE, BA ZASU SAKE YIN MASARA BA, BA ZASU SAKE KASHE KOWA BA, BA ZASU SAKE TSAFI DA KOWA BA, AZZALUMAI TSINANNU.

Duk wannan taron da suka yi babu Duna babu alamar sa, wai shin ina duna É—in? Ina suka kai shi? To muje dai zuwa, koma me zamu ji a gaba.

Sai da dare ya tsala sosai suka tashi taron nasu, sun ci sun sha, sun ƙoshi sun yi hani'an, an cashe anyi murna sun sha sharholiya, abin ba'a cewa komai.

Sai bayan sun tashi taron mafiya yawa daga cikinsu suka koma kamanninsu na matsafan dan sun ce yafi yi musu daÉ—i, wasu kuma sun zauna a ainahin kamannin da suke da shi na kyawawan matasa.

QUEEN ma bata koma kamannin tsafi ba tukunnan, haka ita ma mahaifiyarta, da alama su kam basu son wannan tsiffa tasu ta matsafar, to koma yaya ne zamu ji a gaba,.

Da ainahin kamanninta Queen ta bar wajen zuwa katafaren daular yin barcinta, tana barin wajen taro ya watse, kowa ya wuce bakin aikinsa.

TO KUN JI ABIN DA YAKE FARUWA A DAULAR MUTUWA, BARI MU LEƘA WASHINGTON DC DAN JIN YA AKE CIKI NE.

WASHINGTON DC💋

Tafiya suke yi a cikin mota, Aseef da kansa yake tuƙa motar, shi kuma Musharraf yana gefensa suna hira.

"Kana ji uncle Hosain? Dama ai na gaya maka, sai na kwashi rabin kuɗin account ɗin uncle T na yi ta sadaka da su, ko Allah zai dube shi da idon rahama yasa ya musulunta, wannan kafurar zuciya ta ragu, to in gaya maka yau a account nasa na kwashi kuɗi na zuba a nawa, nan da anjuma zaka ji ya kirani akan me zan yi da uban kuɗin da na ɗeban nan, ai tun da suka sanar da ni sirrin bankin su, wlh ko ba su so sai sunyi sadaka, musamman ma uncle T da Uncle Herry, basu taɓa kyauta wa wani ba, sai pastor, shi kawai suke bawa kuɗin su".

Dariya Musharraf ya yi sosai kafin ya tsagaita ya ce "Wlh Aseef ka zama lashe money, ina ga nan gaba kaÉ—an sai sun canza gabaÉ—aya tsarin bankinsu saboda kai, duk sai ka talauta mutane ko? To kai ma dai Allah ya sanya ka gama karatun nan lafiya ka fara aiki ka tara naka kuÉ—in, sai ka fita daga layin lashe moneys".

Yana ƙoƙarin juya kan motar ya sauƙa daga kan titin da suke izuwa titin kasa ya ce "Uncle ba zaka gane bane, basu yin sadaka ne shiyasa nake yi masu, kuma ai kuɗin su ba zai kare ba tun da kullun wasu ne suke shigowa, duk cikin mu fa, daga Saif sai Areef ne kawai suke yin sadaka, shi ma daddy da kake ganin nan, wlh pastor kawai yake bawa kuɗinsa, bayan pastor kuma sai ni da nake cin kuɗin, ko suna so ko ba su so, kuma dole su bani na ci". Kara faɗaɗa murmushinsa ya yi "My Aseef ka cigaba da yi musu addu'a, In Sha Allah everything will be okey nan ba da jimawa ba".

ÆŠan É—aure fuska kaÉ—an ya yi. "Uncle Hossain wlh wannan bakar zuciya da kake gani, ni nasan daga wajen wannan Roshan É—in suka gado shi, ko ban ji tarihin kakan nan namuba, nasan shi ne mai shegen bakar zuciya tamkar shaiÉ—anun farko, kai uncle Hossain baka ji sunansa bane? Wai fa Roshan, daga ji kasan anyi tsiya ba na wasa ba, ni ban ma son jin tarihinsa, ban son sanin komai, dan nasan bakin mugune da wani idanunsa a wajen, ya ma yi Sa'a Allah yasa idanunsa irin na Lion blue color, dan hakan yasa nake raga mashi, ba da ban haka ba, da sai na ce Allah ya kara mishi azaba tun da bai musulta ba ya mutu". Yana magana yana É—aure fuska.

(Kai jama'a to me kakansu kuma ya yi mishi da ya kare mishi tanaji har haka?🤔 Allah ya shirya Aseef Wlh, wai da ya ce Allah ya kara mishi azaba🤣 to ai ka riga da ka faɗa sai dai kar a kara🤣)
Chapter 36 · 0% Book details