← Book details Triplets Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 121

Sashe 54

Triplets Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sosai ta karajin kaunarsa ya ninku a cikin zuciyarta. "Heartbeat what of Rimsha? Last time you told me tha she is your sister, and then you didn't mention her a cikin pleasures naka, why?". ÆŠan juyawa ya yi ya kalli cikin motar tasa, da yake bakin glass ne, baka iya ganin mutumin da yake daga ta ciki, sai shi na ciki ne zai iya ganinka.

"My heartbeat idan nace my TRIPLETS i mean with her insert, Rimsha ita ce cikon TRIPLETS, In Sha Allah matar Saif É—in mu ce, kinga kuma idan babu Saif to babu TRIPLETS, idan akwai Saif to akwai Rimsha kuma akwai Triplets, fatan kin gane?"

Jinjina mishi kai ta yi almar yes ta gane, kuma ba ƙaramin daɗin maganarsa ta ji ba, gaskiya Rimsha ta sami gurbi mai shegen tsada a zuciyar Areef da Aseef, wannan gurbi da ta samu kuma, zamu iya cewa tafi daddynsu samun matsayi, tashin sense.

Ita dai Rimsha ta zubawa satautar Allah idanu tana kallonsu, har barci ya fara É—aukarta baiwar Allah.

"Heartbeat amma ya akayi kake iya controlling na wayata ko da yaushe, and then komai na yi kana gani". Shagwaɓe murya ya yi tamkar zai yi mata kuka. "Ke Heartbeat kin cika tambaya sosai, ni ba ɗaya daga cikin Triplets bane? Sakawa na yi a datsa mini camerar wayarki, a kayi yi mini connecting da laptop na, Tyrone babban yaron Lion ne ya yi wannan aiki, kuma na gaya mishi kada ya gayawa kowa, akwai sirri a tsakanin mu, shiyasa duk in da zaki je matikar kina tare da wayarki to sai na ga abin da kike yi, sai dai idan camerar wayar taki bata zauna saitin in da zan ganki ba, amma fa wani lokaci kawai ina cankar abin ne da kike yi ne da kai, dan wani lokaci a saman bedside drawer kike ajiye wayar taki, kuma ba kifa wayar kike yi ba, kina danne camerar a kasa, bana samin ganinki da kyau, sai na canka kawai, batun controlling na wayar ki ma Tyrone ne ya yi wannan aikin, so please stop asking me some questions kin ji?". Ya kai karshen maganar tamkar zai yi kuka.

"Amma fa Heartbeat ka yi wasa da kwakwalwata sosai, ba dan Rimsha ba serious fushi da kai zanyi, amma Rimsha ta ceceka". Ɗan langwaɓar da kansa ya yi a shagwaɓe ya ce "Heartbeat let's enter inside the car, ni na gaji da wannan ranar, serious tun ɗazun yake damuna, na daure ne saboda ke". Ɗan kallon motar ta yi kafin ta ce "No ni a ranar nake son ka tsaya".

Cool murmushi ya sakar mata "Okey i like everything you like, let's stay here ɗin kawai, kuma da kika yi magana ma ya fi daɗi". Murmushi ta saki ita ma, har cikin zuciyarta ta ji matuƙar daɗin zancensa, ya iya magana kamar ba gobe, dama ta ce su tsaya a nan ne dan ta gwada shi, dan taga shin zai iya yi mata gardama ko a'a, to ga shi dai duk abin da take so shi yake so, soyayya ruwan zuwa.

"Amma wannan hoton da ka turomini kana cikin Hausa mens É—in fa?" Shiru ya É—an yi kafin ya ce "Pic É—in Triplets na ne, ba ni bane, ni before bana son black peoples ko kaÉ—an, a baya mutun É—aya daga cikin mu ne yake kula kowa har da black peoples, to hoton sa ne ba nawa ba, ni da Lion bamu so, amma yanzu da muka musulta, muna son kowa, mun gane kowa É—an adam ne mai Æ´anci". Shiru ta yi tana tunani, tana son gane banbancinsa da hoton, ta dage dole dole sai ta gano banbancin dake tsakanin TRIPLETS, ga shi kuma iya kalar kwayar idanun Areef kawai ta sani, bata san na Lion ido da ido ba, bata san na shi Aseef É—in ba.

"My heartbeat you look so gorgeous more than everyday". Ya yi maganar kasa kasa cikin sigar soyayya da kauna, yana ji tamkar idan bai mai da ita cikin zuciyarsa ba, ba zai taɓa samin kwanciyar hankali ba.

Shiru ta ɗan yi kafin ta ce "My heartbeat am surprised lokacin da na ganka, ba zan ɓoye maka ba har yanzu na kasa yarda da cewa wai kamar kai ne kake so na, tun da na ganka, na tabbatar kai ne, daga nan na shiga ruɗu akan soyayyar da kake ikirarin kana yi mini". Tana magana tana wasa da yatsun hannunta.

Hannun nata ya riƙo cikin nasa, a hankali yake murza ƴan yatsun nata, har cikin tsakiyar kansa yake jin wani irin yanayi mara misaltuwa, a ɓangarenta itama hakan ne, wani irin baƙon yanayi take ji.

"Me yasa kika ce haka my heartbeat?" Yana magana yana kallon face nata sosai, nisawa ta yi kafin ta fara magana a nitse, "Naga ko rabin ka ban yi a kyau ba, kuma gaka kai Bature ne, wadda ya fito cikin kyawawan fararen turawan, wadda farinsu babu ko miss, idan muka tashi kwatance kyau a nan cewa muke yi kyakkyawa kamar baturiya, saboda kyanku yasa kuke bamu sha'awa, amma duk da haka ka tsallakesu kazo har Nigeria, Nigeria ma Kaduna, ka ce ni kake so, ni fa a haka fara ce a gidan mu, ko in ce a danginmu, amma yanzu kallah da na zo kusa da kai, na dawo baka, hasken ka ya dishashe nawa, wannan dalilin yasa naji zuciyata ta karaya, na ji anya kuwa ba mafarki nake yi ba? Ko kuma wasa kake yi mini ba, sannan bugu da kari, ga kuÉ—i mulki kai komai ma kun haÉ—a, dan Allah Heartbeat ka gaya mini gaskiyar me kake so a waje na? Ni nasan ba soyayya bace ta kawoka waje na, zuciyata ta tsorata wlh". Ta kai karshen maganar hawaye na zuba daga idanunta.

Shiru ya É—an yi kafin ya jingina da jikin motar tare da lumshe dara daran brawn eyes nasa, hakan yasa dogayen eyelashes nasa suka kara bayyana, zuba mishi idanu ta yi tana hawaye tana jiran amsa daga gare shi, kun sani na sani har ga Allah tana bala'in kaunar shi kafin ta san waye shi, ganin shi ido da ido yasa ta ji zuciyarta ta karaya, a nata ganin ya fi karfinta, sai dai idan wani abin kawai yake so da ita, dama jira take ta tabbatar da shi É—in ne, to yanzu ya kawo mata kansa, ta tabbatar da yes shi ne, a zahiri ma yafi kyau fiye da hoton, duk da hoton ma tun yana É—an 20 years ne, ta ruÉ—e da kyansa sosai, kuÉ—i, kwarjini, shiyasa take ganin kamar ba son gaskiya yake yi mata ba.

Almost 10 mins suna a haka, a hankali ya duƙo da kansa yana kallonta, ita ma shi take kallo, ya rasa da wani baki zai yi mata magana, mai da kallonsa izuwa kasa ya yi, da yake unguwa ce ta manyan mutane, titi har cikin unguwa, ga titin fes babu datti, hakan yasa ya zube gwiwowinsa a kasa a gabanta, duk wanda ya san turawa yasan yin hakan ɗabi'arsu ce, su zube gwiwowinsu a kasa dan bayyanar da soyayyansu.

A razane ta koma baya ganin ya zube gwiwowinsa a kasa a gabanta, duk da tasan ɗabi'arsu ce yin hakan, ba wani abu bane, amma sam bata yi tsammanin haka daga gare shi ba, dan a nata tunanin bata kai wannan matsayin ba, bata kai ya zube mata gwiwowinsa a kasa ba, duba da irin tarin dukiya da suke da shi, ita kanta Rimsha da ta san halinsu ta girgiza ganin ya zube gwiwowinsa a kasa, ta razana ainun, bata taɓa tsammanin hakan daga gare shi ba, ko a mafarki, bata san lokacin da idanunta suka washe ba, gabaɗaya barcin cikinsu ya gudu, zaro idanun nata ta yi tare da matsowa jikin glass ɗin motar sosai tana kallon wanan abin al'ajabin, yau ga ɗaya daga cikin TRIPLETS na THE GENERAL OF THE ARMY ya zube a kasa a gaban mace, ina ma wannan abin a Washington DC ta faru, da gabaɗaya gari ta ɗauka izuwa yanzu.

"My Heartbeat trust me, from the button of my heart nake sonki, serious babu wasa, ni bana son turawa, ke Allah ya zaɓa mini, kin san cewa ko TRIPLETS na ban gaya musu ina sonki ba, dama nace sai nazo Naija zan gaya musu, amma zumuɗin in zo in ganki ido da ido ya hanani tsayawa na basu lokaci na, muyi hira har na gaya musu, uncle Hosain kaɗai na gayawa, kuma shi ne ya kara mini confidence a kanki, he told me that ke ƴarsa ce, ƴar yayansa, kina da farar zuciya, zaki iya tambayarsa, da gaske nake sonki, yasan komai, please stop doubting a kai'na, kiyi hakuri ki yarda dani, ni bana karya, duk abin da nayi miki a baya na gaya miki dalilin yinsa, kuma idan da bana sonki ba zan ɓata lokaci na wajen zuwa in da kike ba, saboda ke na haɗa Exams uku a lokacin guda nayi, kuma ba rana ɗaya za'ayi su ba, ni ne nace dole a bani nayi a rana ɗaya, dan nayi miki alkawarin zan kawo miki kai'na yau, bana son saɓa miki alkawarin dana ɗauka miki, Shiyasa nayi hakan, ko kaɗan banji daɗi ba da zuciyarki ta fara tunanin ko ba da gaske nake sonki ba, please ki gaya mini wasa kike yi kinji ko?".

Ina ta kasa magana, har lokacin ganin abin take yi tamkar a mafarki, ta kasa yarda da abin da take gani, ji take yi tamkar ta gudu ta koma cikin gida, dan ta tsorata sosai.

Ganin bata yi magana bane yasa ya ɗan rarrafo da gwiwowinsa a kasa, ya matso kusa da ita, hannayenta ya riƙo cikin nasa, a wannan karon a shagwaɓa ya yi magana, "Please My heartbeat talk to me now, zuciyata tana bugawa da sauri sauri, ji nake yi like zan mutu, i need your amsa now please".
Chapter 54 · 0% Book details