Sashe 119
Triplets Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ya É—an É—auki Æ´an mintoci da zasu kai a kallah biyu yana kallon hoton kafin ya fita daga kan hoton, sai ya kallima ashe a WhatsApp na mutumin aka turo mishi hoton, É—ago kai ya yi dan ya kalli guys É—in, sai ya kalli wayam sun gudu, dan su da kansu ba su ga wajen da zasu tinkara suce ya basu wayarsu ba, kuma sun san su masu laifi ne, dama duk wani mara gaskiya da ya ji É—an motsi zai gudu.
Ganin basu nan yasa ya dawo da kallonsa kan wayar ya fara bin chatting na guy ɗin da wanda ya turo mishi hoton, dan ya ga me hoton Rimsha yake yi a wajensu? Me kuma za'ayi da ita?. Voice dake saman hoton, wadda aka fara turowa kafin hoton ya buɗe, cikin harshen Hausa mutumin ya yi magana, da wata muryarsa kamar na hamshakan bugaggu ƴan kwaya ya ce "Ni ban san in da take ba, kawai dai ku nemota, iya abin da na sani shi ne, ita Jehan ta turawa video na da ta ɗauka, dan haka ku nemota, ku tabbatar kun karɓa mini video na, idan taki ku kasheta, ni zan ji da Jehan tun da tana prison, dolema na san hukuncin kisa za'a yanke mata tun da Abubakar jaja ya mutu, zan turo muku hotonta wadda na sha bakar wahala kafin na samu, na wahala kafin na gane ƴaƴan Nawazudden ne, akwai wan da ya ce mini tabbas ya taɓa ganin ita Rimshar a Kaduna, na tura mishi hoton ta ne sai ya ce wlh tana Kaduna, shiyasa na nemo ku, dan haka ku nemota, idan kuka kuskura kuka bari video na ya fita wlh sai kun mutu". Shi ne abin da yake cikin voice ɗin, sai dai kafin ya gama jin voice ɗin wayar ta shiga key.
Kashe hasken screen ɗin wayar ya yi tare da zubawa screen ɗin idanu yana karantar wajajen da aka fi yawan taɓawa a kan screen ɗin, sune zasu iya kasancewa password na wayar, dan in da ake yawan taɓawa dan buɗe password ɗin, dole zata yi daban da sauran jikin screen ɗin. Ganin babu haske sosai da zata ishe shi ya kalli abin da yake son kallah ne yasa ya nufi gida dan ya buɗe wayar ya yi bincike a cikinta.
A bakin gate ta waje ya isko Mark, da mamaki ya tambaye shi me yake yi a waje kuma? Bawan Allah ɗan amana sai ya ce kawai ya fito ne dan hankalinsa ya kasa kwanciya ogansa yana waje, shi ne ya fito dan ya jira shi a nan ya kuma duba lafiyarsa, har cikin ransa ya ji daɗi sosai, umarni ya yi mishi a kan to suje ciki, hannu yasa yana ƙoƙarin ɗaukar Brady da ya wani kanainaye wuyar Lion ɗin kamar wani ya ce zai kwace mishi shi, da yake Mark mutuminsa ne, sai ya saki Lion ɗin ya koma wajen Mark ɗin yana yi mishi kuka a hankali alamar yana bashi labarin yaga hoton Rimsha a wani waje, da yake Mark ɗin ma ya yi mishi farin sani sai ya ce da Lion me Brady ya gani, shiru Lion ɗin bai tanka mishi ba, hakan yasa ya gane abin bai shafi kowa ba kenan, case ɗin na ogan nasa ne shi kaɗai.
Palo suka nufa, tun da ya sako kai cikin palon daddaÉ—ar kamshin kayan tea É—in da Rimsha ta dafa mishi a Abuja ya daki hancinsu dukkansu biyu, harta Mark ya ji mugu mugun daÉ—in kamshin, shaka suka yi suka lumshe idanu, bai yi magana ba har sai da suka shiga tsakiyar palon.
Suna kaiwa tsakiyar palon ya juyo tare da sauƙe dara daran idanunsa a kan Mark ɗin, ya kuma dakata daga tafiyar da yake yi.
Ƙasa da kai Mark ɗin ya yi tare da fara ƴan kame kame, tun ba'ayi mishi magana ba ya yi saurin fara magana cikin girmamawa. "Sorry sir am not the one and I don't know how it happened, it might be prof sister". Shiru ya yi bai yi magana ba, bai kuma ɗauke idanunsa ba, bai kuma juya ya cigaba da tafiyar da yake yi ba, da alama tunani yake yi a kan hakan.
Almost 5 mins suna a haka, gently ya mayar da kallonsa izuwa hanyar kitchen na Æ´an sakanni babu ko kyaftawa, daga bisani kuma ya juya ya cigaba da tafiya dan zuwa in da yake da niyar zuwa wato bedroom nasa. Sauke Brady Mark ya yi tare da nufar kitchen É—in dan ya ga waye ne ya yi wannan aiki da ya canzawa gidan daga kamshin abincinsu zuwa na kayan tea, ba kowa bace ta yi aikin nan fa ce Rimsha, ganin Mark É—in baya kitchen É—in ne yasa ta zo ta tafasa tea É—in ta abinta, shi ne kamshi ya bule daga kitchen É—in har palon.
Lion kuwa yana shiga bedroom nasa ya iskota ta ajiye mishi abinci tana jiransa, ta wutsiyar idanu ya kalleta kafin ya wuce zuwa dressing room nasa, Jim kaɗan ya fito sanye da pajama launin white color, dama already kafin ya fita neman Network ya yi wanka ne ya zura jallabiya bai tsaya shiryawa ba, dan yana matuƙar son ya yi magana da Tyrone.
Zama ya zo ya yi a in da ya saba zama, calmly ya ce ta kawo mishi laptop nasa, da sauri ta ɗauko ta miƙa mishi, abincin ya ce ta zuba mishi kafin ya shiga ƙoƙarin buɗe wayar mutumin, tana tsaka da zuba mishi abincin ne zazzakar sexy voice nasa ya daki dodan kunnenta a in da yake ce mata "Daga yau ban yarda ki sake fita ko ina ba, school Mark zai kai ki ya kuma ɗauko ki, shi ma school ɗin idan kin je kada ki kuskura ki yarda da kowa, ko wani ya kira ki kije ko makamancin hakan, ko da su Areef ban yarda ki sake bi ki fita ba". Okey ta amsa mishi da shi, can kuma wani tunani ya faɗo mishi, to me zai hana ya haɗa ta da soja ɗaya kawai ya rinƙa tsaronta a school ɗin, tun da Jehan ta rigada ta jefa mata rayuwarta cikin haɗari, yanzu sai Allah kaɗai yasan adadin mutanen da wannan azzalumin ya turawa hotunanta a kan su kamota ta kawo video da Jehan ta zuba mishi karya akan ta turawa Rimshar, idan baku manta ba, lokacin da Jehan ta yi wa Alhajin can na gidan hajiyar daɗi video, ta ce mishi ta turawa ƴar uwarta Rimsha, to kuma dama kunsan manya mutane irin waƴan nan ba zasu bar abu makamancin haka ya fita ba, dan idan ya fita sun san shikenan rayuwarsu tana kwale kwale, shi ne to yasa aka nemo mishi hoton Rimsha yanzu kuma yasa a kamota a karɓa mishi videonsa, shi kuma zai ji da jehan.
Gaskiya Jehan ta tara makiya ta ko'ina, yanzu ga shi ta tsundumo Rimsha da bata san komai bama a ciki, shiyasa wani lokaci ake son kafin ka yi abu ka yi tunani, tunani ma mai zurfi a kan me zai je ya zo, Jehan ta yi babban kuskure a nan tun da ta san babban mutun ne, ba zai taɓa rabuwa da ita tana riƙe da videonsa tsiraicinsa ba, to ya kamata mu rinƙa tunani wani lokaci kafin mu yanke hukunci.
Abincin ta zuba mishi ya ci mai ɗan yawa kafin ya cigaba da abin da yake yi, ta miƙe zata kwashe kayan abincin ya ce mata idan ta kai ta dawo, okey ta amsa cike da mamaki ta nufi wajen. Tana shiga kitchen ɗin suka yi ido huɗu da Mark, ga shi yau bai sanya glass ba, Hazel eyes nasa dara daran nan yau dai a waje suna shan iska, mamakin idanun nasa ta yi, bata taɓa ganin irinsu ba, ajiye kayan abincin ta yi bata kula shi ba kamar dai kullum, zata fita ya ambaci sunanta, da mamaki ta juyo, wai dama Mark mai kama da robot ɗin nan dumkum ba magana nan ya san sunanta ne? Ta tambayi kanta da kanta.
Tambayarta ya yi a kan waye ya ce ta yi girki a kitchen É—in nan? Turo baki ta yi kafin ta ce mishi Areef ne ya ce ta yi, daga haka ya yi shiru bai sake yin magana ba, sa kai ta yi ta wuce abinta, É—akin Lion É—in ta koma dan amsa kiran da yake yi mata.
A gefensa ta je ta zauna abinta, ya sha ruwan mamaki yadda ta wani zauna a gefensa ko a jikinta, can kuma ko me ta tuna ne ta miƙe da sauri ta fito zuwa bedroom nata, cup ɗin tea ɗinta ta ɗauka ta dawo bedroom ɗin nasa, in da ta tashi ta koma ta zauna.
A hankali ta fara shan tea É—in tana jiran ta ji kiran me ya yi mata, shi kuma ya buÉ—e wayar mutumin sai bincike yake yi a ciki, a hankali hankali kamshin tea É—in ta yake dakan masa hanci, har cikin zuciyarsa yake son kamshin, akwai daÉ—i sosai.
Almost 5 mins suna a haka, da yake tea É—in akwai zafi a hankali take sha, Juyowa ya yi suna fuskantar juna tare da juyo da laptop nasa mai É—auke da wani hoto, "Kin san wannan fuskar?" Ya tambayeta, shiru ta yi tana kallon mutumin, shi kuma ya tsareta da idanu yana kallon sleeping eyes nata, sai dai kuma nazari yake yi a kan face É—in nata, "A'a ban san shi ba". Dama ya san da wuya ta san shi, dan ita ko Media bata damu da hawa ba, daga karatun boko sai na Islamiyya, shi ne kawai abin da take yi kullum, ko kallon film bata damu da yi sosai ba, idan kaga tana kallo to labarai ake yi a kan jaruminta GAR wato shi kenan.