Sashe 70
Triplets Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Shi kuma Aseef yana riƙe da waya yana magana da daddy, da kyar ya samu ya kwantarwa da daddy hankali ya kuma bashi hakuri na abin da Lion ya yi mishi, shi kam Areef ko a jikinsa, dan ma laifi daddyn ya gani, saboda ya sani sarai Lion baya son shi, yana hakuri ne kawai yana yi mishi biyayya a matsayinsa na uba, amma ya zo ya tsaya yana yi mishi hayaniya a kai, ai dole ta kwaɓe musu dama, sai ka ce bai san halin ɗan nasa ba, ya san komai domin ai renonsa ne yaran, shi ya ɗaurasu a kan wannan turba, tun suna yara ya basu horon kada su yarda wani ya ɗaga musu murya, to dama ita rayuwa haka take, duk abin da ka koyawa yaro a kwana a tashi watarana sai ya yi maka, shiyasa ake so ka ɗaura yara a kan turba mai kyau, dan idan suka tashi yi maka ka ga mai kyau, Allah dai yasa mu dace.
After some hours.
Da yamma misalin karfe 4:30, sanye da wando jeans pink color da riga fari mai ƙaramin hannu ta fito Palo, ta ɗaure wannan kyakkyawar bakin gashin nata, sai kyalli face nata yake yi, hannunta na riƙe da wayarta, da alama ta ci kuka har ta ƙoshi, dan ga idanunta nan sun kumbura, sun yi jawur ta kasan.
Palon kasa ta nufa, babu kowa, gidan shiru, ko'ina a gyare yake tsab tamkar hannu bai taɓa taɓa komai dake wajen ba, kamar daga leda aka ciro komai, fitinannen kamshi air freshener ne ke tashi ta ko'ina, ga blue light da sanyin Ac, abin ba'a magana, ya ƙayatar ba kaɗan ba. Sai buga hammar yunwa take yi, dan bata ci abincin rana ba, ta sha barci kamar ba gobe, shi kuma Imran ya tafi shopping shi da Jelly, dan ta matsa mishi a kan lallai suje su sayi kaya, shi ne ya ɗauketa suka tafi.
Mark na kitchen yana aikinsa, kamar dai kullum fuskar nan tasa tamkar na ogansa, babu annuri ko kaɗan, basu san wani abu wai shi murmushi ba, bare dariya kwata kwata a rayuwarsu, ɗaure fuska da bada umarni kawai suka iya. Kallo ɗaya ta yi mishi ta kawar da kanta, dan haushin kowa na gidan take ji, tun da Lion ya taɓa mata tula tula shikenan ta tsani kowa, yanzu ma yunwa ne ya fito da ita, ba dan haka ba, ta ce ba zata sake fitowa waje ba, ba zata sake kula kowa ba, yarinta kenan, shi kuma Areef bawan Allah lokacin da take barci sau biyu yana zuwa ya dubata bata tashi ba, lokacin cin abicin rana ya je ya dubata, dama zai ce mata su je su sayi abinci ne, sai ya samu bata tashi ba, ita kuma ashe fushi take yi da kowa, har da su masu saya mata abincin ma gabaɗaya.
(Wayyo cikina wlh Rimsha zata kashe ni da dariya 🤣 ƴar kaniya idan ta yi fushi da su to waye zai saya mata abincin?🤣 Kuruci dangin hauka)
Tana fita harabar gidan suka yi ido huÉ—u da Brady dake tsaye a harabar gidan, tun safe da Areef ya kwancesu bai sake É—aure su ba, akwai ta da bala'in tsoron kare, bare kuma Brady da ya kasance renon soja, ai sai a hankali, Lion ya rene shi a irin halin sojoji, akwai shi da faÉ—a na bala'i, baka kula shi ba ma zai kula ka, idan ba TRIPLETS ba, baya ragawa kowa É—an banzan karen nan.
Ihu ta kurma tare da juyawa a guje ta koma cikin in da ta fito, ai kuwa shima da gudu ya bi bayanta yana daka haushi, dama kunsan ka'idan karnuka ne hakan, idan mutun ya gudu zasu bishi, bare shi Brady da dama ko bata gudu ba sai ya bita É—in dan bala'in faÉ—a, a guje ta haura sama tana ihu, shi ma a guje ya haura yana haushi.
Daidai tsakiyar palon suka ci karo da Lion ya fito zai sauƙa kasa, yana shirye cikin wasu shegun tsadaddun kananan kaya, da alama fita zai yi, yau ma kamar jiya, sarkarsa na saman riga ba a ciki ba, black glass ne a idanunsa, sai tashin kamshi yake yi kamar anyi ɓarin turare a jikinsa, ya yi kyau over tamkar shi ya yi kansa.
Bata lokacin da ta ƙanƙame shi da iya karfinta tana ihu ba, a guje Brady ya yi kanta yana ƙoƙarin kai mata cizo, wani irin mahaukaciyar damka ta yi wa Lion ɗin a kirjinsa, da alama bata ma san waye ta rungume ba, hankali ya tashi sosai idanunta sun rufe, bata gani, ita dai a rabata da wannan bala'in, wato Brady.
Yana ƙoƙarin kai mata cizo Lion ya tare shi da hannu ɗaya, gently ya yi mishi magana da English a kan ya bari, tsalle ya yi ya taka kafaɗarta ya haye jikin Lion ɗin yana wani girgiza kamar wadda ya je farauta ya dawo, ɗan banzan balaƴaƴen kare, ko da yake a haka a hore shi.
"Sake ni". Ya faɗa a nutse, shiru bata amsa ba kuma bata sake shin ba, ɗan duƙo da kansa ya yi a kan face nata, sai yaga ta sume mishi a jiki, ashe lokacin da Brady ya zo zai cijeta, bala'in tsoro yasa numfashinta ya ɗauke, ɗan ciza laɓɓansa ya yi tare da cewa Brady ya sauƙa mishi a jiki, ba musu ya diro kasa sai wani girgiza na iya shege yake yi.
Ji ya yi tamkar ya yi wurgi da ita kawai ya yi tafiyarsa, amma kuma sai ya kasa yin hakan, ɗan rage tsawonsa ya yi tare da ɗaukarta cak ya nufi saman sofa, har zai kwantar da ita a wajenku ko me ya tuna sai ya fasa, ya nufi bedroom nata, saman gadonta ya kwantar da ita, zai miƙe kenan sarkarsa ya dawo da shi, dan kuwa sarkar nasa ya makale a cikin nata sarkar dake ta cikin rigarta, ɗaukarta da ya yi yasa sarkar wuyarsa ya shiga rigarta.
Guntun tsaki ya ja tare da ɗan jan wuyar rigar nata kasa ya fito da nata sarkar, gently ya warware su ya zame nasa, miƙewar da zai idanunsa suka sake sauƙa a saman sunansa dake rubuce a tudun tula tulanta, shiru ya ɗan tsaya yana karewa sunan kallo, daga bisani kuma ya dawo da kallonsa a kan face nata, har wani shock ya ji lokacin da ya kallin face ɗin nata, yau taso ma ta yi mishi kama da Josephine, ɗan shafa kansa ya yi yana mamakin wannan fuskar tata, fuskar ce abu ta farko da ta tsaya mishi a rai, ya gane cewa ita ce ta kira sunan shi a gidansu Imran, dan ranar da ta kira Anaya a waya zata gaya mata cewa ya kallan mata breast, a ranar ya gane ita ta kira sunansa, da ta kira Anaya ta ce Anaya GAR ya kalla mini.. sai kuma ta yi shiru, yana cikin bedroom nasa yana jinta, yaji GAR da ta faɗa, tamkar a bakinta a ha halicci sunan, ta iya kira kamar ba gobe.
Gently ya juya zai bar É—aki, idanu É—uhu suka yi da Areef dake tsaye a bakin kofar shigo, tun lokacin da Lion É—in ya shigo da ita shi ma ya shigo, dan ihun da ta yi ta gudu Brady ya bi bayanta, lokacin yana garden, ya ji ihun nata ne ya biyo bayanta, yana haurowa Palon sama lokacin shi kuma Lion ya É—aukota zai kai bedroom nata.
Ko sannu bai ce da Areef É—in ba ya wuce ya fice abinsa, mamaki Areef yake yi, wai me haÉ—in breast É—in Rimsha da Lion ne, duk idan zasu yi karo to fa breast É—in nan nata ne a gaba, sai ya kallesu, wannan wace iriyar kaddara ce? Ya tambayi kansa, suku nasu kaddarar a haka tazo kenan?. Juyawa shima ya yi ya fita, a harabar gidan ya isko Lion É—in da Mark zasu fita, ga hadari na tasowa, alamar ruwan sama za'ayi, har walkiya ta fara wanzuwa a sararin samaniya, garden ya koma abinsa, shi kuma Lion ya wuce suka fita da Mark, Aseef kuma yana ta shararra barci bawan Allah.
A É“angaren gidan Hajiyar daÉ—i kuwa.......â¤ï¸â¤ï¸TRIPLETSâ¤ï¸â¤ï¸
E29-30
A ɓangaren gidan Hajiyar daɗi kuwa, ranga ranga suka kwashi Zinariya suka fita da ita daga gidan, sai Allah ne kaɗai yasan in da zasu kai ta, ita kuwa Jehan, bayan sun kaita ɗaki sun fito, miƙewa ta yi zaune tare da cewa Adiva, "Adiva zo ki kwance ni kin ji?". Da farko Adiva taki, ta ce tana tsoro kada su Zinariya su zo su mata ɗan banzan duka, sai da Jehan ɗin ta yi ta kara mata karfin gwiwa sannan ta yarda ya zo ta kwaceta ɗin, "Bani ruwan sha Maryam". Da sauri ta ɗauko mata ruwan a fridge, tun da ta kafa kai bata ɗaga ba har sai da ta shanye ruwan nan tas, sai faman sauke nauyayyar ajiyar zuciyar take yi, ita kanta ta wahala, ina ga su Zinariya kuma? Abin ai ba'a magana, sun wahala ba kaɗan ba.
Jugum jugum suka yi, dukkansu idanu sun rena fata, bare ma Adiva da bata saba da shan wahala ba, renon madara da ice cream, jiki duk madara, yau ta kare a gidan karuwai, wannan shi ne ake kira da rashin sani yafi dare duhu, ga iyayensu a can suna haukar nemansu, ga su sukuma a nan, ana ƙoƙarin lalata musu rayuwa a sakasu a harkar bariki, gabaɗaƴansu ma sun ɗauka iyayen nasu sun mutu, ya Allah kasa mu fi karfin zukatanmu.
"Adiva ina wayar nan taki? Ɗauko ki saka mana ita a charji, bana son komai ya sameta, dan akwai abubuwan da na ajiye masu mahimmanci a cikinta". Cewar Jehan kenan, da sauri ta miƙe ta shiga cikin toilet ta ɗauko wayar, dan a can suka barota, da kyar ita kuma Jehan ɗin ta lallaɓa ta shiga toilet dan ta yi wanka ko jikinta ya sami kwari.