Sashe 113
Triplets Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Jinjina mishi kai ta yi tana faɗin "E wlh ni kullum na kalli hoton sai in kalli kamar mutun ɗaya ne a wajen, ido ne kawai yake banbanta ku, na rasa wlh, sai dai Lion ya fiku cika, kuma kaman ya fiku tsawo ma". Kai mata ruwan bakinta ya yi ta karɓa ta fara sha. "Kin san menene?" Girgiza mishi kai ta yi tana kan shan ruwan. "Da ni da su ko a cikin duhu Rimsha tana iya banbanta mu, mafiya yawan lokuta daddy da ya haifemu idan yana magana a palo da Areef dake cikin bedroom, idan na amsa daga cikin bedroom ɗin a madadin Areef, to wlh baya gane ni na amsa, basu rabe muryata da ta Areef, duk duniya dama Lion ne kawai yake iya rabe muryoyinmu, na sha ruwan mamaki lokacin da Rimsha ta iya rabe muryoyinmu a rana ta farkonta da ganinmu, to haka take banbanta mu ko a cikin duhu, wani lokaci idan na rufe mata fuska ta baya zaki ji ta ambaci sunana, idan na ce waye ya gaya miki Areef ne fa ba Aseef ba, zata kafe lallai dole ni ne ba Areef bane, , shi kan shi Areef ya sha ruwan mamakin banbanta mu da Rimsha take yi a cikin duhu, bare ma masoyinta Lion, bata haɗa shi da kowa ba, karfi da ya ji ta rabamu, ko cikin zolaya idan na ce mata Saif ne bayan na rufe mata ido, zaki ji tana cewa, kai ina GAR ya fi haka, kai in takaice miki kome kika yi wa Rimsha dan ki rikitata a kanmu sai ta rabe miki mu tsab wlh, na rasa wani irin baiwa ke gareta, shi ma Areef ya gwadata har ya gaji ya hakura, su uncle T duk basu rabeni da Areef idan nayi magana, amma ita ina raba mu take yi tsab".
Dariya ta kwashe da shi tana faÉ—in "Kai ai dole Rimsha ta yi muku farin sani kafin ganinku, kasan yadda take kaunar Lion kuwa? Hmm banga laifinta ba dan ta ce muku bata haÉ—a shi da kowa ba, ai kai ma ban haÉ—a ka da kowa ba, gaskiya sosai Rimsha akwai kwakwalwa na wuce misali, gata da natsuwa sosai".
Hannayenta ya riƙo bayan ya ajiye robar ruwan, tsareta da idanu ya yi yana faɗin "Wace Rimshar ce mai natsuwa? Sai dai idan wata Rimsha a gidanku, amma mu na gidanmu kamar battery ake saka mata, tana da fitina ga neman rigima wajen Saif, watara Allah sai ya sumar da yarinyar nan ina da tabbaci". Murmushi ta yi tana wasa da ƴan yatsun hannunsa masu bala'in ɗaukar hankali, "Duk abin da kaga Rimsha tana yi wa Lion ni na gaya mata wlh, ni na san cewa yaro mai kiriniya yana da saurin shiga rai, na san idan tana yawan shiga harkarsa tana taɓa mishi abubuwa bai aiketa ba, dole watarana ya ɗago ido ya kalleta, a kwana a tashi dole ya fara sonta, Allah Rimsha ta sha bakar wahala akan soyayyarsa, idan ba shi ta aura ba, wlh aurenta ba zai taɓa zuwa ko'ina ba, tun tana da 9 years a duniya take haukar kallon shi a Tv, ni nasan a yadda yake ɗin nan, ba zai yi saurin ɗaura hannunsa a jikin mace da sunan duka ba, shiyasa na bata wannan shawarar ko kuma in ce maka kullum nake kara bata hakan idan mun yi waya, ta dai'na jin tsoronsa, ta rinƙa taɓa mishi wasu abubuwa nasa ba zai taɓa dukanta ba, amma a nawa ganin da nake masa fa kenan, bacin haka, wlh Rimsha nitsatsiya ce sosai, kuma idan ka lura ai Lion ɗin kawai take yi wa rashin ji ɗin, to ni nake zugata".
Nisawa ya yi yana faÉ—in "Yes da wuya Lion ya É—aura hannunsa a jikinta da nufin duka gaskiya, ko ni ai ba zan daki mace ba, to wai me ma zaka daka a jikin mace? Ka je ka sumar ko ka kashe Æ´ar mutane a banza, mace ai bata da wajen duka a jikinta, shi Lion ma ya ce faÉ—uwa ce babba ga namiji ya sanya hannunsa a jikin mace da sunan duka, yo Allah na tuba Lion da yake mari manyan zaratan maza su faÉ—i su suma ina ga Rimsha kuma? Ai idan ya mareta sai mutuwa, gaskiya ma ba zai yiwu ba, duka kam a'a ba zai daketa ba, idan ta cika matsa mishi dai, sai dai ya bata punishment irin su frog jump da sauransu". Ya kai karshen maganar tare da kai hannunta dake cikin nasa saitin É—an bakinsa ya sumbata.
Kasa kasa kamar mai raɗa ya ce "I really love my heartbeat, kece bugun numfashina, idan bake to babu ni". Buɗe tafin hannunta ta yi tare da ɗaura nasa hannun a saman natan, yazama kamar sun tafa da juna kenan, cikin shagwaɓa ta ce "Promise me that ba zaka taɓa barina ba duk wuya duk daɗi". Matso da fuskarsa daf da tata ya yi "I promised you that ko me wuya ko me daɗi ni naki ne, a kanki zan tsaya ba ja baya". Cool murmushi ta saki har sai da gaf teeth nata suka bayyana
Heartbeat ya ambaci sunanta a tsananin sanyaye, ita ma a sanyaye ta amsa mishi, "Fito da harshenki dukka waje bari na gani". Ba musu ta fito da ita, tana da tsawo sosai harshen nata, nauyayyar ajiyar zuciya ya sauƙe kafin ya ce tom ta mayar, mayarwa ta yi tana tambayarsa menene yasa ya ce ta fitar, jan dogon hancinta ya yi yana faɗin "Sai gaba zan gaya miki dalili". Make kafaɗa ta yi a kan lallai bata yarda ba sai ya gaya mata ita dai, kara matsowa kusa da ita sosai ya yi har suna iya jiyo sautin numfashin juna, "Ba kin ce na dai'na irin maganar sai mun yi aure ba?". Jinjina mishi kai ta yi alamar e, "To kin gani ki bari sai mun yi aure sannan zan gaya miki dalili".
Turo baki ta yi taso jin meyasa ya kalle mata harshe, amma ba komai ai, yanzu ma da ya ce sai sun yi aure tun da ta ce ya dai'na irin wannan magana, ta fahimci ina ya dosa, sai dai bata san me na'amar hakan ba, ta dai fahimci duk zancene da ya shafi ma'aurata.
"My shagwaɓati zan koma gida kada Abba na ya dawo ya sameni a waje, zai yi faɗa sosai, Ammie ta ce kada na jima". Har cikin ransa sai da ya ji wani raɗaɗin zafi, amma haka ya danne tare da gaya mata kalamai masu daɗi dan kada ta shiga gida ta shiga cikin damuwa koma ta yi kuka, sai da ya tabbatar ya sanya ta farinciki sosai har da dariya kafin ya ce to suje ya taka mata zuwa bakin gate. A tare suka fito suka nufi gidan, sai hira yake zuba mata, burinsa ta mance da komai ta yi barcin cikin farinciki.
Sai da suka je bakin gate ne ya É—an jawota jikinsa ya rungume, dan su a kasarsu hakan ma sallama ce, É—an shafa lallausan kumatunsa tayi kafin ta raba jikinsu ta wuce zuwa cikin gida, binta da kallo ya yi har sai da ta shiga palo sannan ya bawa mai gadi dama ya rude gate É—in, ya juya zuciyarsa cike tab da bakin ciki, shi kaÉ—ai yasan me yake ji.
Cikin mota ya koma ya zauna tare da kifa kansa da jikin steering motar yana jin zuciyarsa na tafasa kamar zata kone, yanzu ko hawayen ma ya nema ya rasa, saboda bala'in ta kai mishi bala'i. Ya jima a haka kafin ya kunna motar zuwa gida, yana kan hanya ta kira shi a waya dan ta ji ko ya isa lafiya, kin É—auka ya yi har sai da ya koma sannan ya kirata suka cigaba da hira suna farantawa juna rai tare da kara nitsawa cikin kogin soyayyar juna. Shi kuma Areef yana can yana ta bincikensa, ya tasa hoton Jehan da ya É—auko daga laptop É—in Lion yana kare mata kallo, shi dai wlh ta shiga ransa ba kaÉ—an ba, musamman idan ya kalli idanun nan nata masu kama dana daddynta, suna matukar burgesa, abin da baku sani ba gabaÉ—aya TRIPLETS Allah ya jarrabesu da bala'in kaunar manya manyan idanu, suna É—aukar hankalinsu sosai, bare ma idan idanun suka kasance farare tas abin ba'a magana, ga family'n Dr Salman kuwa gabaÉ—ayansu ba baya ba wajen manya manyan dara daran idanu, shi ne yasa Lion yake bala'in son idanun Rimsha, sun kasance manya manyan farare tas, ga su sleeping eyes, ai dole ma ya so su, dan abin nasu a jini yake.
A ɓangaren Rimsha da Lion kuwa, barci gabaɗayansu suka koma, iska mai daɗi yana kaɗa shi, ita kuma sanyi iskar ya yi mata, a hankali yayyafin ruwan sama ya fara sauka a kansu, wajen akwai runfa ta yadda ruwa ba zai shiga ba, to amma ruwan da iska sosai yake tafe yasa iskar yake kaɗo ruwan har ciki yake taɓa su.
A hankali ya waro dara daran blue eyes nasa tare da sauko da kansa kaɗan, karaf sai saman kyakkyawar fuskarta ya sauƙesu, sai zuba barci take yi kamar ba gobe, lumshe idanun nasa ya yi tare da sake buɗe su a kan face ɗin tata, shiru ya yi yana tariyo makusantar Josephine da ya sani ko zai ga mai irin wannan face ɗin, shi dai yasan tabbas ya taɓa ganin matar tare da Josephine to wace ce? A hankali ya kwantar mata da kanta a saman sofa tare da miƙewa ya nufi wajen fridge dake wajen, ruwa mai sanyi ya ɗauko, dawowa ya yi ya zauna a saman wata sofa daban, nan take ruwan sama ta kece kamar da bakin kwarya, shan ruwan tas ya yi tare da ajiye robar ruwar ya kishingiɗa a saman sofar tare da fito da wayarsa ya fara latsawa, a haka har suka kai asuba, ga ruwan sama yaki tsayawa, yana son komawa cikin gida ya ɗauro alwala zuwa masallaci, amma ina ruwa kamar da bakin kwarya yake zuba.