← Book details Triplets Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 121

Sashe 30

Triplets Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ɗan satar kallon Ummi ta yi kafin ta miƙe tsaye ta nufi hanyar ɗakin nasu ba tare da ta yi magana ba, murmushi ya saki while ita ma Ummi murmushin ta yi, tana faɗi a ranta cewa, ai ba zata sake shiga tsakaninsu ba, jiya haka suka yi mata, a kitchen suna aiki ya shigo wai zai taya su, A'AFIA na ɓare maggi zata saka a miya, da ya sanya hannu zai taya ta, sai ta ce "Ummi ki ce yaya Nawid ya bar mani kayana bana soz bai iya ba, baya ɓarewa dukka, yana barin sauran Maggi a ciki". Ita kuwa Ummi sai ta shiga, ta ce ya bar mata kayanta, ai kuwa kafin ta gama ɓare maggin nan ita da kanta ta ce "Yaya Nawid to ɗauka muyi bibbiyu". Daga nan Ummi ta fita harkarsu, bata shiga faɗarsu, yanzu ma da ta shiga ta ce A'AFIA bazata je ɗakin ba ko makamancin haka, ai da sun sake bata kunya, tun da ga shi dai ta miƙe ta wuce ɗakin dan kanta, so ba'a shiga tsakanin mata da miji, idan ma mace ta kawo maki kukanta akan mijinta, kiyi mata addu'a kawai ki bata hakuri, wlh idan kika kuskura kika tayata zaginsa da faɗar laifinsa, tofa zata iya biye maki a lokacin tun da sun yi faɗa da mijin, amma kuma da zarar sun shirya, ki tabbatar abin da kika faɗa na zaginsan nan tsab a kunnensa zata gaya Mashi, idan munafuka ce ma, wlh sai ta kara da karya, kuma zata yi ta riƙe ki a rai na kin zagi mijinta, haka dayawan mata suke, Allah dai yasa mu dace mu kuma gyara.

Bin bayanta ya yi, a tsakiyar gado ya iskota ta kwanta ruf da ciki tare da kifa kanta a kan pillow.

Saman gadon ya haye shi ma, a hankali ya sanya hannu ya ɗago kanta, Subhanallah zaro idanuwansa waje ya yi yana kallon yadda take hawaye sharɓa sharɓa.

"Aafia lafiya kike kuka? Me ya faru kuma?" Ya yi maganar fuskarsa É—auke da damuwa tare da kulawa a gareta sosai.

Shiru ta yi mashi ba tare da ta yi magana ba. "Dan Allah matata ki gaya mini, shin nayi miki wani laifi ne?" Ya kai karshen maganar tare da É—agota da kyau ya mannata da kirjinsa.

"Yaya Nawid kwana fa ka ce zaka je kayi a asibitin, kuma fa ai naji mace ce fa ta kira ka, daman kenan akwai number mata a wayarka?". Allah sarki da yake ta jima tana som shi, hakan yasa take bala'in kishin kayanta, shi kuma bai san hakan ba.

"Am so so sorryyyyyyyyyy Matata, na tuba, yanzu dai to tashi muje Asibitin tare domin ki ganewa idanunki, ayi komai a gabanki, mu je tare kuma mu dawo tare ko, amma ki yi shiru dan bana son kukanki". Cikin sauri ya ɗago tana kallon shi, jin ya ce zasu je hospital a tare, ba ƙaramin daɗi ta ji ba, ganin ta tsare shi da ido ne yasa ya jinjina mata kai alamar tabbatar mata da abin da ya ce.

Cikin sauri ta diro kasa saga saman, ta nufi waje tana murna, miƙewa shi kuma ya yi ya hau shirin zuwa hospital ɗin.

Tana fita É—akin jelly ta wuce, har lokacin Ummi tana Palo tana kallonta. Hijabin jelly ta É—auko tare da wasu kayan, doguwar riga abaya fara tas, da mayafinta, ta sanya rigar, ta É—aura mayafin a matsayin É—an kwali, ta É—aura É—an hijabin please call me É—in a saman, shi ma hijabin fari ne tas, ta yi kyau sosai abinta.

Lokacin da ta dawo ɗakin shi ma ya kammala shi, hannunta ya riƙo a kan su tafi, karɓar jakar hannunsa ta yi tare da rataya shi a kafaɗarta, suka nufi waje.

A Palon suka tsaya suka yi wa Ummi sallama, addu'a ta yi masu tare da fatan nasara da kuma a dawo lafiya, sosai dai ta yi masu addu'a, sai Amin Amin suke amsawa da shi.

Suna fita harabar gidan ya É—an rungumota a jikinsa, lokacin kuma karfe 6 daidai gari ya É—an yi duhun mangariba.

Da kansa ya buÉ—e mata gidan gaba na motar ta shiga, bayan ya mai da marfin ya rufe, ya zagayo ta mazaunin driver, ya shiga ya zauna.

Zuba mata idanu ya yi ba tare da ya kunna motar ba, jin shiru bai tashi motar ba yasa ta ɗan ɗago dan ta saci kallonsa, karaf suka haɗa idanu, ƙasa ta yi da kai tana Murmushi.

"Me ya yasa ki murmushi?". Girgiza kai ta yi alamar babu komai. Matsowa kusa da ita ya yi tare da rankwafo da kansa sai tin tata. "Kin taɓa ganin anyi abu babu dalili ne?". Nan ma dai girgiza mashi kai ta yi alamar a'a.

"To menene dalilin?" Nisawa ta yi kafin ta ce "Saboda kayi kyau sosai ne yasa nake murmushi, amma kuma....." Sai ta yi shiru. "Amma kuma menene? Ki karisar da maganar mana?" "Amma kuma bana son wata ta ganka a haka, bana son taga kyan da kayi". "Kenan kishi kike yi?" Girgiza mashi kai ta yi alamar A'a.

"Menene wannan idan ba kishi ba?" "No yaya Nawid ba kishi bane, kawai ina kula da kai ne, wai ka manta amarka a ka bani ne?" Zaro ido ya yi yana kallon yadda take zaro magana kamar ba ita ba, eyee wato Amanar shi aka bata, kai jama'a, wasa wasa ita ma ta iya magana sosai.

"E kam gaskiya ne, tun da amana ta a ka baki, dole ki kula da ni sosai, yanzu dai bani sumbata sai mu tafi ko? Lokaci na kurewa". Kara faÉ—aÉ—a murmushinta tayi tare da matso da É—an bakinta sai tin kumatunsa da nufin ta sumbace shi.

Sai da ya bari ta kawo bakinta, sai ya juyo da face nasa ta sumbace sa a saman lips nasa, tana ƙoƙarin zamewa ya riƙota tare da zura harshensa a cikin bakin nata, ya fara kissing nata.

Sun É—an jima a haka kafin daga bisani ya saketa tare da kunna motar yana wani lumshe idanu, kumawa ta yi ta jingina da jikin kujerar motar, ita ma ta lumshe idanunta kamar mai barci, wani azababben son shi ne ke kara ninkuwa a cikin zuciyarta.

A hankali yake tukin, duk bayan minti sai ya juyo ya kalleta, har lokacin idanunta a lumshe. Kasancewar suna tuƙi a hankali sai ya sa basu isa Hospital ɗin da wuri ba.

Har suka isa kuma, ta ki yarda su haÉ—a ido, a tare suka fito suka jera zuwa ciki, sai janta da hira yake yi, tun bata biye mashi sosai, har ta fara biye mishi, dayawa daga cikin nurses É—in sun yi zaton kanwasa ce, domin basu san ya yi aure ba, kuma akwai kama ta jini a kan fuskokinsu, idan baku manta ba, da Hjy Turai da Hjy Hadiza Æ´a da kanwa ce, dole za'a samu kama ta jini.

Kai tsaye office nasa ya wuce. Bai kai ga shiga cikin office É—in ba wasu nurse guda biyu suka nufo shi da sauri, basu bari sun gama karisowa ba suka fara gaya mashi halin da matar da zaayiwa aiki take ciki.

Dawo da kallonsa kan Aafia ya yi, cike da kauna ya ce "Ki shiga office ki jirani ko, Bahijja ki raka ta, ki zauna ki kula da ita, ke kuma Ameera muje zuwa É—akin da aka kwantar da matar". Ya kai karshen maganar tare da wucewa gaba. Wadda aka kira da Ameera ta bi bayan shi, ita kuma Bahijja ta yi gaba tana faÉ—in "Ke muje ko?".

Binta da kallo Aafia ta yi kafin ta maido da kallonta izuwa kan mijin nata, bata kula Bahijja ba har sai da ya kurewa ganinta, sai binta da kallon banza da raini Bahijja take yi, dan bata taɓa tunanin Aafia matar Dr bane, tun da basu ji labarin auren nasa ba, abu ne da aka yi shi lokaci guda.

Sai bayan ya kurewa ganinta ne ta tura kofar office É—in ta shige, bayanta Bahijja ta bi, ta je zata zauna a ainahin kujerar da yake zama, Bahijja ta daka mata tsawa akan wai ta dako kujerar da patient suke zama ta zauna, kujerar Dr iya shi kaÉ—ai ne yake zama a kai.

Da yake Aafia ma yar yi ce, ko kallon in da take bata yi ba, domin Bahijja bata kai ta É—aga idanu ta kalle ta ba, wucewa ta yi ta zauna a saman ainahin kujerar tasa.

"Ke baki da hankali ne? Ina matsayin P.A na oga zan yi maki magana ki ki kulani, kanki ɗaya kuwa? Na gaya maki ba wanda yake zama a kujerar Dr sai shi kaɗai, dan haka ki dawo wajen da patient ke zama ki zauna, idan ba haka ba ranki in ya yi dubu zai ɓaci yanzun nan". Har lokacin Aafia bata ɗago ta kalleta ba, sai ma ɗauko wayarta da ta yi tana latsawa.

Bahijja ta fusata iya fusata, tun da ta kalli Aafia dama ta ji ta tsaneta, bata sonta, tana tsoron ta ce zata yi mata wani abu kuma, ya zamana suna da kusanci sosai da Dr ya yi mata hukunci, hakan yasa ta zauna a patient chair tana cika tana batsewa, ba dan ta so ba ta hakura.

Ita kuwa Aafia ko a jininta, ranta fes, sai ma massage ta yi wa Nawid akan tana son shan black tea kafin ya shigo, yana ganin massage É—in shi ma ya yi wa Bahijja massage a kan ta haÉ—awa matarsa Black tea ta bata kafin ya zo.

Ba ƙaramin razana ta yi ba lokacin data ga massage ɗin nasa, wai a haɗa wa matarsa tea, kenan Aafia matar sa ce? Ta tambayi kanta, "Kai ina ba matarsa bace, sai dai wadda yake son aura, tun da bamu ji ance ya yi aure ba" ta sake faɗa a cikin zuciyarta tare da miƙewa ta nufi wajen wani kyakkyawar show glass dake cikin office ɗin, kayan tea ne kala kala a ciki.

Ruwan zafi ta fara jonawa a hitter, kafin ta haɗa komai da zata buƙata a cikin cup mai shegen kyau.
Chapter 30 · 0% Book details