Sashe 58
Triplets Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Suna barin wajen Rimsha ta fara hawaye, tana mamakin jelly yarinya yar karama da ita ko a ina ta koyi wannan banza hali na kirsa da makirci oho, ɗan riƙota a gefen kirjinsa ya yi, yana goge mata hawaye tare da bata baki, da mamaki cike fal ransa Aseef ya miƙe ya dawo kusa da su dan ya ji wai shin menene matsalar.
Ɗan langwaɓar da kanta a gefen kirjin nasa ta yi tana mai jin bakin ciki a cikin zuciyarta, zama a gefenta a in da Imran ya tashi Aseef ya yi, fuskarsa ɗauke da damuwa ya fara tambayar me yake faruwa, ba ɓoye ɓoye Areef ya sanar da shi duk abin da ya fahimta, cikin sauri ta ɗago kanta daga gefen kirjin nasa, tana kallon face nasa, mamaki take yi waye ya gaya mishi abin da yake damunta, kashe mata ido ɗaya ya yi yana faɗin "Kina mamaki ne? Ina kaunarki ai, dole na iya gane me yake damunki, kuma duk da bana jin yarenku, ina fahimtar akan me kuke tattaunawa, yanzu dai jeki ɗauko mayafinki muje wajen cin abincin, Aseef zai ja mota, Lion ba zai hanani fita ba, dama abin da yasa yake hana fita, dan ni kaɗai ne, kada na fita wani abin ya same ni, ko kuma na fama ciwona, yanzu Aseef yana nan, babu abin da zai faru In Sha Allah, kuma daga yau kada ki sake tambayar Prof wani abu, duk abin da kikeso, Aseef yana nan idan ni ba na kusa, kin ji ko?".
Gyaɗa mishi kai ta yi alamar e ta ji. "Yanzu nauyinki a kan mu yake, dole mu kula dake tamkar yadda zamu kula da kanmu, Aseef ɗauko makullin mota ka sanar da Lion zamu je restaurant, ke kuma jeki ɗauko mayafi". Kusan a tare suka miƙe Ita da Aseef ɗin, hannunta ya riƙo suka nufi cikin gida yana tambayarta shekarunta, 14 years 3 months ta bashi amsa, sai mamaki yake yi, ƴar karama da ita, lallai akwai kura.
A palon sama suka rabu, ita ta shiga ɗakinta, shi kuma ya shiga ɗakin Lion. Jim kaɗan suka fito kusan tare, sake riƙe hannunta ya yi a cikin nasa yana faɗin "Wannan abin da kuke rufe jikinku da shi, ba karamin kyau yake yi muku ba". Sai murmushi take yi ba tare da ta yi magana ba suka nufi waje.
A yadda suka bar Areef haka suka dawo suka same shi, yana ganinsu ya miƙe a kan su tafi, fitowa balcony ɗakinsa Lion ya yi dan yaga tafiyarsu, yana ji da ƴan uwan nan nasa over, har ga Allah bai so Areef ya fara fita yanzu ba, saboda jikin nasa da saura, amma shi kuma yana bala'in son yaga ya fita, ya son ganin cikin Naijan nan ya take, Hakan yasa Lion ɗin ya hakura kawai ya kyale shi su fita.
Kiran Imran a waya Areef ya yi, ya tambaye shi a wani location restaurant É—in da suke sayan abincin yake, ba musu ya gaya musu, bai kuma tambayesu me zasu je yi a can ba, dan yasan ba makawa Rimsha zasu je sayawa abinci. Kunna goggle map Aseef ya yi a wayarsa tun kafin su bar gidan, Rimsha ta so zama a gidan baya na motar, amma Areef ya ce lallai ta dawo gidan gaba su zauna a tare, shi kuma Aseef ya tukasu.
Bata yi musu da shi ba, ta dawo kusa da shi ta zauna, duk abin da suke yi a kan idanun Lion suke yi, a kan idanunsa suka bar gidan, sai tsokanar Rimsha Areef yake yi, suna ta murmushi.
Kai tsaye wajen wani katafaren restaurant suka shiga, suna parking suka fito kusan a tare, nan take kallo ya dawo kansu, kun san mutanenmu idan suka ga Turawa, sai kallonsu jama'a suke yi, su kuwa kwata kwata basu son wannan kallo da jama'a suke yi musu, dama kuma kunsan kallo bashi da daÉ—i ko kaÉ—an, idan mutun yana kallonka gabaÉ—aya sai ka tsargu, sai ka fara tunanin ko dai wani abin da bai kamata bane a jikinka yasa suke kallonka.
Saman tsadaddun kujerun dake wajen suka zauna, nan take masu karɓar oder suka nufo wajen nasu.
"Rimsha ki basu oder abin da kike buƙata". Cewar Areef, shi dai Aseef ya yi kasa da kai yana latsa wayarsa, da alama chatting yake yi da Heartbeat nasa.
Daidai lokacin aka fara kiraye kirayen sallar mangariba, umarni Areef ya yi musu a kan su yi mata takeaway ne kawai su wuce da shi gida, mangariba ya yi, sai dai abin dariya kuma abin haushin shi ne, babu mai ko biyar a jininsu, kuma ba ta yadda zasu yi su yi wa masu restaurant ɗin transfer, ko da aka kawo musu takeaway ɗin da bill ɗinsu, kallon Aseef Areef ya yi, shi ma a lokacin ya ɗago kansa dan ya kalli ɗan uwan nasa, da wani kuɗi zasu biya to? Suka tambayi kansu da kansu a cikin zuƙatansu, ita ma Rimsha sai kallonsu take yi tana kankame da laidar takeaway ɗin nata abinta.
Su kuwa masu karɓar kuɗi suna tsaye suna jira, dan kuwa ba zasu yafe ba, ice cream da suka sanyawa Rimsha ma kawai almost 10k bare azo kan saura abubuwa ga abinci.
Dariya ne ya subcewa Rimsha lokacin da ta gane me matsalar, zuba mata idanu Areef ya yi yana kallon yadda take dariyar, ba Æ™aramin burge shi ta yi ba, shi ma dai Aseef dariya abin ya bashi, wai su a dole sun zo sayan abinci, sun manta ba'a Washington DC suke ba. Babbar magana yanzu ya zasu yi? Su mayar da abincin ne ko yaya za'ayi? Ga shi ita kuma Rimsha ta kankame ledar ta abinta, jira kawai take yi su biya su tafi, har ta kotsa ta fara shan ice cream dake cikin, ga shi har da pizza ta ce a sanya mata...........â¤ï¸â¤ï¸TRIPLETSâ¤ï¸â¤ï¸
E23-24
Suna a wannan hali sai ga Mark ya shigo cikin wajen, fusataccen fuskar nan tasa tamkar face É—in shanu, yana sanye da wandon jeans black color da t-shirt maroon, faffaÉ—ar kirjin nan nasa a buÉ—e irin na ogan nasa, tamkar wani zaki, ya sanya bakar glass a idanunsa, ba wasa a tattare da shi ka É—igo, ganin shi ma kawai ya isa ya razanar da duk wata halitta mai rai.
Kai tsaye in da suke ya nufo, cikin girmamawa ya gaida su tare da miƙawa masu karɓar kuɗin rafar kuɗi ƴan dubu dubu, wadda a kallah zasu kai 100k, ko basu tambaya ba sun san Lion ya aiko shi, dan idan ba Lion ba, ba wanda ya isa ya sanya Mark fita daga gidan, ya bar bakin aikinsa, dama tun da suka fita Lion ya kira Mark ya bashi kuɗi a kan ya bi bayansu da shi, dan yasan basu da ko biyar a jikinsu, kuma yasan ba ta yadda za'ayi su yi transfer, su sun mance da hakan, amma shi tsabar kauna da kuma kula da su da yake yi bai manta ba, yana ankare dasu, shiyasa ya yi musu hakan, dan kada wata matsala ta biyo baya, Areef kawai yake jiyewa, ciwon nan nasa, tun da suka fita yake jin wani iri a ransa, yadda Areef ɗin ke jijjiga jikin nan nasa, ciwon nasa na jijjika, to shi ma haka Lion ɗin yake jin wannan jijjiga a jikinsa, tamkar ciwon a jikin nasa yake ba Areef ba, ya kyalesu su fita ne dan su yi farinciki, tun da sun nuna hakan suke so, bai taɓa hanasu abin da suke so ba, sai idan ya tabbatar da in suka yi abin zasu cutu matuƙa, shi ne zai taka musu birki, ba dan yaso ba, sai dan kada su cutu.
Tun da Mark ya miƙa kuɗin, Aseef ya riƙo hannunta suka nufi waje, shima Areef miƙewa ya yi ba tare da ya kalli in da Mark ɗin yake ba, ya bi bayansu.
Motarsu suka shiga, da gudu Aseef ya ja motar dan lokacin sallah ya yi, da mugun gudu shi ma Mark ya fito ya rufa musu baya, da motar da yazo da ita. Cikin ƙanƙanin lokaci suka isa gida, saboda irin uban gudun da suke shararawa, dama idan baku mance ba, Aseef ya iya guduwa da mota kamar ba gobe.
Suna yin parking ta fito ta nufi bedroom nata dan ta yi sallah, a tsakar gida suka yi karo da Lion da Imran zasu tafi masallaci, bin su Aseef da Areef É—in suka yi, zasu je su yi alwala a can É—in kawai.
A palon sama taci karo da jelly, ko sannu bata ce mata ba, da alama ta rako Imran ne, ta kula da shi har ya fita dan kada ya kula Rimshar.
(Kai jama'a Jelly duniya, wato har waje take rako Imran ta tsare shi dan kada ya kula Rimsha 🤣)
Bedroom nata ta nufa, binta da kallon banza jelly'n ta yi bata ce da ita komai ba. Tana shiga bedroom É—in nata, toilet ta nufa dan yin alwala, tare da É—aura ledar takeaway É—inta a saman bedside drawer. Bayan ta yi ta zo ta shinfiÉ—a dadduma ta tada sallah abinta.
A ɓangaren gidan Akil kuwa, wasa wasa har shabiyun dare shiru ba Akil babu labarinsa, Umaisha tayi kuka ne har ta godewa Allah, sai uban haɗa zufa take yi, duk da sanyin Ac dake gudu a cikin ɗakin, ta jigata sosai, ta kuma kasa yin barci, a ɓangaren shi ma Akil ɗin ya sha bakar wahala, dan bai saba kwana ba tare da ya taɓa tula tula ba, tun ranar da ya yi aure har zuwa yau, ya kasa runtsawa, sai juyi yake yi a saman gadonsa dake bedroom nasa a gidan Abba, ya jigata sosai, kuma yaga massage ɗin Akila, ya basar ne kawai, irin shi zai daure ya yi koda sati ɗayar nan ne haka, amma ina kwana ɗaya ma ya kasa jurewa, da ya gaji da kwanciya zai miƙe zaune yana haɗa zufa, gabaɗaya ya rasa ina zai sanya ransa ya ji daɗi, daga karshe dai miƙewa ya yi tare da zura jallabiya ya ɗauki makullin motarsa ya fito palo.