← Book details Triplets Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 89 OF 121

Sashe 89

Triplets Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gidan baya maman ta shiga, ita kuma Ayla ya sanya ta a gidan gaba, dan baya son barinta ta je wajen mama ta cigaba da yin kukan nan nata, tana ɗaga mishi hankalin, shiyasa ya rabasu, kunna motar ya yi ya nufi gida, an fasa zuwa yawon, har lokacin sai kuka Ayla take yi, ita ma maman nata sai hawaye take yi, da yake yanzu ba hira suke ba, sai ya zuba gudu sosai da motar, cikin ɗan ƙanƙacin lokaci suka isa gida, kai tsaye part ɗin Abbi suka nufa, yaki yarda ya bar Ayla ta je jikin mamanta, dan baya son kukan da take yin nan ko kaɗan, dan haka sai ya rungume kayansa suka shiga cikin palon.

Aunty ce kawai a ciki tana zaune saman sofa bayan sun kammala cin abinci kenan, tana ganinsu ta miƙe tana yi musu sannu da dawowa, ganin wata a tattare da su yasa ta kara faɗaɗa fara'arta tana yi musu sannu da zuwa, saman sofa daddy ya zauna da Ayla a jikinsa sai aikin rarrashinta yake yi, ita kuma maman nata zata zauna a kasa ya ce mata a'a ta zauna a saman sofa, ganin Ayla na cin uban kuka haka yasa Aunty ta kariso wajensu da sauri tana tambayar ko lafiya, cike da kulawa daddy ya gaya mata abin da ya faru, sannan ya ɗaura mata da cewa ta kai maman Aylar ɗaki ta yi wanka ta ci abinci, ta huta zuwa anjima zasu yi magana, daga karshe ya tambayeta ina Abbi? Ya fita ta bashi amsa Kafin ta nufi maman Aylar tana faɗin "Muje ko? Ki dai'na kukan haka ya isa". Allah sarki Aunty baiwar Allah, ita dai ba ruwanta, koma waye aka kawo, in dai mijijta da ƴan uwansa ne, hannu bibbiyu take karɓarsu, bata da wata matsala a rayuwarta, ba kyashi bare hassada, haka ta riƙo hannun maman Aylar, bata damu da dattin da yake jikinta ba, ta wuce da ita zuwa ɗakin Hanan.

Shi kuma daddy rarrashin babyn nasa ya cigaba da yi yana gaya mata ai murna zata yi, wannan abin faranciki ne ya same su, dan haka ta kwantar da hankalinta, shi ya fi kowa ma murna, dan ko ba komai yanzu zai san su waye familyn babyn nasa da har take masa kama da tsohuwar matarsa wato mummyn Jelly. Da kyar ya lallaɓata suka wuce bedroom nasu dan ya je ya sakata tayi barci kada kanta ya yi ciwo, yasan yanzu tana lokacin barci ne saboda cikin nata, da ta kwanta kaɗan sai barci, abin ba sauki sam.

A ɓangaren matafiya kuwa.

Rimsha tun tana iya ganin mutane har ta dai'na, gabaɗaya sun fita garin Kaduna sun ɗauki hanyar Abuja, tsoro ne ya kamata, amma tuna cewa duk wuya ba zai taɓa cutar da ita ba, yasa ta hakura ta lafe a jikin kujerar motar, shi kuwa sharara uban gudu yake yi tamkar ba gobe, ban da hanya babu abin da yake kallah. Dai'dai wajen checkpoint na sojiji bayan ka fita Kaduna ta wajajen jare, a nan suka tsayar da su, a lokacin ma ta yi barci abinta.

Tun da ɗaya daga cikin sojojin nan ya dallah wutar torch light ɗinsa ya kalli motarsu, yasa a ransa sun yi kamu zasu samu kuɗi, dan kuwa ba ƙaramin mota bane wannan, nufarsu ya yi kai tsaye, da yake glass ɗin motar a sauke take kasa, sai ya danna musu torch light a cikin motar kai tsaye, har sai da Lion ya ɗan rintse idanunsa saboda bala'in hasken light ɗin.

Da sauri sojan ya haska Rimsha bayan ya haska Lion ɗin kenan, da mamakinsa sai ya ga ita chocolate color ce, shi kuma Lion Bature kamar ka taɓa jini ya zuba saboda haske, ga shi ita karamar yarinya, bugu da kari tana barci, fusataccen face ɗin Lion kuma idan ka kallah wani lokaci zaka rantse irin bakaken mugayen nan ne masu kashe mutane ba gaira ba dalili, dan haka sai sojan ya tuhume shi da satar yara, wato ya sato Rimsha kenan, kuma a yanayin da suke ɗin nan dole za'ayi mishi irin wannan tuhuma, cikin wannan dare ya ɗauko ƴa mace sun nufi Abuja, kuma kunsan dole wanda bai san su ba ya yi tunanin hakan, to da yake shi ma soja ne, yasan a kan aikinsu suke, sai bai wani nuna musu karfi ko ya dake su ba, hakan da suka yi dama shi ne dai'dai, gently ya ce musu wannan sister sane cikin Abuja zasu je, kwata kwata baya son a gane waye shi, dan shi bai zo Nigeria dan a gane ne yana ƙasar ba, yasan idan ya cire face mask na face nasa to tabbas ko basu san face nasa ba zasu san shi ne.

Kin yarda sojojin suka yi, suka ce sam sai ya tashi Rimsha su ji daga bakinta, ya tasheta a gabansu, ta ya za'ayi yana Bature ɗan haure zai ce musu bakar fata kanwarsa ce,? Ai wannan hankali ba zai ɗauka ba, babu wata kama da take nuna wannan kanwarsa ce, ko suna da alaƙa da ita, dan haka ko ya tashe ta, ko kuma ya miƙa musu ita ya kawo wani abu na cin hanci kenan, sai su yafe mishi ya tafi ya barta a wajensu, da farko ya ɗauka faɗa suke yi a kan gaskiya, sai yanzu ya fahimci in da zancen ya dosa, ashe marasa gaskiya ne ma, ba suna faɗa dan kare kasarsu daga miyagu bane ma, dan aljihunsu suke yi ashe.

Cike da izza ya ce bai ga uban da ya isa ya tashi Rimsha a nan ba, kuma wlh su basu hanya su wuce ko kuma ya yi musu abin da sai sun yi danasanin zuwarsu duniya, cike da izza shi ma ɗayan sojan ya sanya gindin bindigarsa zai taɓa kumatun ta da shi ya tashe ta, ɗayan kuma ya ja kofar motar zai buɗe, sai surfa masifa suke yi, wai ai ɗan haure ne, ya hauro musu kasa ba ta hanyar da ta dace ba, dan haka sai ya ɗanɗani kuɗarsa yau.

Bai kai ga taɓata da bindigar ba ta farka saboda surutansu da ya yi yawa, shi kuma Lion sai ƙoƙarin dannar zuciyarsa yake yi dan abin da yake gabansa ya fi masa sauraran waƴan nan banzaye muhimmanci a cewarsa, miƙewa ta yi zaune tana murje idanunta. Tsawa sojan ya daka mata wadda ya sanyata firgita, shi kuma Lion wayarsa ya ɗauko ya fara latsawa, dan shi bashi da lokacin sauraran waƴan nan marasa hankali da basu san aikinsu ba a cewarsa,.

"Ke waye wannan kuma ina zai kai ki?" Ɗaya daga cikin soldiers ɗin ne suka mata magana cikin tsawa, a firgice cikin magagin barci murya na rawa ta basu amsa da cewa "Yayana nane ya ce zan raka shi wani waje ne, amma ni ban san wajen ba". Dawo da kallonsu kan shi suka yi, sai latsa waya yake yi, zasu yi magana wani daga cikin sojojin da alama babbansu ne ya kariso wajen, cikin girmamawa ya ce da Lion su tafi, ya samu kira daga sama, su kuma sojojin su bashi hakuri, bai jira wani hakurinsu ba, dan idan baku manta ba, ya tsani kalmar sorry a rayuwarsa, da gudun gaske ya ja motarsa ya bar wajen, yana barin wajen kuma suka sake samin kiran waya an soke aikinsu baki ɗaya, an koresu daga aiki kenan, gabaɗayansu da suke wajen, a nan dai ya yi musu amfani da karfin ikonsa ne ba karfin damtse ba, ya fahimci sojojin irinsu masu karɓar cin hanci, sam basu da wata amfani a hukuma, domin kuwa, ba kasa da al'umma suke yi wa aiki ba, aljihunsu da cikinsu suke yi wa aiki, to yana da kyau su bar aikin al'umma su je su nemi aikin cikin nasu, dan aikin soja aikin kasa da al'umma ne, da mutane masu kishin kasa kishin kansu da al'ummarsu ya dace ba banzaye irin waƴan can ba.

Cigaba da sharara gudunsa yake yi, sun yi nisa sosai har ma sun kusa shiga Abuja, sautin garuwar hakwaranta ne ya saka shi waigowa ya kalleta, tun da ya bar wajen sojojin nan ya ɗage glass ɗin motar saboda sanyi da ya fara sauƙa, amma a haka wai rawan sanyi take yi, da farko kamar ba zai kula ta ba, sai ya tuna idan wani abin ya sameta shikenan shirin shi ya ruguje, dan ba zata iya fita ba, tuna hakan yasa ya yi parking na motar a gefen titi ya cire jacket ɗin jikinsa ya rufa mata a jikinta, sai zuba barci take yi, kunna motar ya yi ya cigaba da tafiya dan sun kusa shiga, kamar a mafarki ta ji kamshin perfume nasa sosai yana ratsata, ga kuma ɗumi da ta ji, karayin lamo ta yi a jikin kujerar tana sauke numfashi a hankali hankali cikin kwanciyar hankali.

Misalin karfe 11 dai'dai suka shiga cikin garin Abuja, kai tsaye gidansu ya nufa, tamkar already ya san hanya, amma kuma bincike ya yi ya gane location na gida, sai ya yi amfani da google map, sai zuba barci take yi bata san ma sun iso ba, da yazo shiga babban gate na duplex apartment É—in sai da aka charje motarsa tsab, bai hanasu ba, dan ma baya son wasu su san ya shiga gidansu Rimsha É—in, baya son kowa ya sani.

Bayan sun gama charjewa, kai tsaye kofar gidan ya nufa, rufe take gate ɗin, ga wani zabgegen kwaɗo da aka sanya a babban gate na shigar da mota, parking ya yi a bakin gate ɗin, gently ya fito ya nufi wajen gate ɗin, ga mamakinsa sai yaga babu kura ko wata alama da zata nuna an jima ba'a shiga gidan ba, alamu sun nuna akwai masu zuwa gidan, shiru ya ɗan zubawa kwaɗon idanu, gently ya kai hannunsa har kamar zai taɓa kwaɗon, sai kuma ya fasa ya juya zuwa wajen motar tasa dake kunne, juyawa da zai yi sai ya kalli mutun daga gidan kusa da su ya leƙo ya kuma koma, bai bi ta kansu ba ya koma cikin motarsa.
Chapter 89 · 0% Book details