Sashe 45
Triplets Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kwashe kayan abincin tas ta yi tare da ficewa daga É—akin ta nufi waje, kitchen ta fara komawa ta ajiye kayan kafin ta wuce garden wajensu Akila.
Tasha ruwan mamakin ganin Imran da Areef a wajen, duk da cewa tasan wajen zamansu ne, amma bata yi zaton ganinsu yanzu a wajen ba.
Kusa da Akila ta je ta zauna, da fara'a Areef ya ce ya mata "Our Queen gaskiya yau kin yi kyau over". Ba ƙaramin faduwar gaba Akila take ji ba a duk san da ta saurari muryarsa, to me yake nufi da ya nuna bai gane ta ba? Ko dai ya fi son ya kai kansa da kansa gida ne? Sai jerowa kanata da kanta tambayoyi take yi.
Wayarta dake hannunta ne ya ɗan yi kara alamar shigowar saƙo, jikinta duk a mace ta kunna hasken screen ɗin wayar dan ta duba saƙon wanene.
Ganin saƙon ɓoyayyen masoyi ne yasa ta ɗago da sauri ta kalli Areef, kansa na duke a kan wayarsa yana latsawa, da alama dai shi ma wani saƙon yake turawa, ko yake rubutawa, dawo da kallonta a kan wayar tata ta yi, password ɗin wayar ta fara cire wa, kai tsaye saƙon ta buɗe. "My heartbeat sarkin ruɗu da son sanya ƙwaƙwalwarta a cikin tunani, yanzu me na tunanin ni ne ko bani bane? Bayan kin rigada kin san ni, shiyasa fa tun farko naki turo miki hotona, dan bana son ki ganni a wani waje ma ki gane ni har sai na kawo miki kaina gida, amma kika takura mini na turo miki hotona, duk da haka sai kin sake shiga ruɗu a kai na?". Zaro idanu ta yi tana karanta saƙon, da hausa ya rubuta mata kamar yadda ya saba, ita kam gaskiya yanzu ta kara tsorata da lamarinsa, ta sare sosai, anya zata iya jurewa ta cigaba da nuna mishi tamkar bata gane shi ba kuwa? Anya ma zata iya cigaba da soyayya da shi kuwa? Ta tambayi kanta, wani ɓangare na zuciyarta ne ya bata amsa da cewa, to ya zaki yi tun da kina son shi, ko dai akwai wani da kike yi wa rabin son da kike yi mishi ne?. Shiru ta yi ta rasa ina zata sanya rayuwarta ta ji daɗi, har lokacin sai dukan uku uku kirjinta yake yi, su Rimsha sun lula duniyar hira sun barta a duniyar tunani, kwata kwata bata jin me suke faɗe, daga karshe ma miƙewa ta yi ta nufi waje, Imran na kiranta amma ina bata ji ba, bata tare da su.
Binta da ash eyes nasa ya yi yana kare mata kallo har ta fice, dawo da kallonsa a kan wayarsa ya yi tare da cigaba da abin da yake yi na latsa wayar, da sauri Rimsha ta miƙe ta bi bayanta, su kuma su Imran suka cigaba da hiran da suke yi.
A ɗaki zaune saman tsakiyar gado ta iso ka, kusa da ita ta zo ta zauna tare da taɓata tana faɗin "Aunty Akila lafiya kuwa?". Ƴar firgita ta yi tare da juyowa suna fuskantar juna, idanuwanta cike tap da kwallah, babu ɓoye ɓoye babu komai ta fara bawa Rimsha labarin halin da take ciki, yanzu ta rasa mafita, tana magana tana hawaye.
Dafata Rimsha ta yi ta fara bata hakuri, wani saƙon ne ya sake shigowa wayar Akilar a wannan lokacin, kin buɗewa ta yi, ta ce ita ko mutuwa zata yi sai dai ta mutu, amma ɓoyayyen masoyi ta hakura da shi, karɓar wayar Rimsha ta yi ta buɗe saƙon, rubutu ne kamar haka. "Am so so sorryyyyyyyyyy my heartbeat, na san nayi wasa sosai da ƙwaƙwalwarki, amma ki yi mini afuwa, ba zan sake ba, wlh waya ta yi kaɗan wajen ɗaukar sorry dake cike a bakina, girman laifin da nayi, sorry a waya ya yi kaɗan ya goge shi, ki bani dama gobe kamar yadda na faɗa zanzo har gida, na yi alkawarin zangoge dukkan laifukana, dan Allah kada ki yi fushi dani, kin san cewa kece bugun numfashina ko? Tun ba yau ba ina gaya miki hakan, kin ɗauka wasa nake yi ne ko kuma kawai kalamai ne irin na masoya da suka saba faɗa? To idan haka kike ɗaukar kalamaina ki daina, duk abin da zan gaya miki na kalmar soyayya, wallahil azim da gaske nake yi, da gaske daga karkashin zuciyata take, ni ban taɓa soyayya ba sai a kanki, tun hotonki na farko da Prof ya turo mini na kamu da son ki, ban sanki ba, ban san halinki ba, amma zuciyata ta kamu da masifaffen Kaunarki, mace ta yi mana illar da ba za mu taɓa mancewa da shi bane, Shiyasa dana kamu da sonki na zaɓi na gwadaki ta wannan hanyar, ban taɓa yarda da mace ba sai a kanki ke da Rimsha, dan Allah ki fahimceni, ki gane abin da nake nufi, ki gane abin da ya sanya na saka miki idanu da kuma duk wani motsin da zaki yi ina gani, ki gane dalilin da ya sanya naki gaya miki ni waye, ina son ne ki soni domin Allah ba dan wani abu ba, ina son ne ki soni kamar yadda nake son ki, hakan yasa nayi miki wasa da hankali na kuma ki gaya miki waye ni, amma ai hotona na gaskiya na tura miki dan bana son ganinki cikin damuwa, kin shiga damuwa sosai a kan kina son gani na, hankan yasa na baki hotona tun na 22 years, na tuba My Heartbeat, ki fahimceni bugun zuciyata, wlh ba zan sake ba, yanzu komai zan rinƙa gaya miki gaskiya ne, ba zan sake ɓoye miki komai ba, i really love you more than anything except my TRIPLETS and Prof, idan kika ciresu, kece mutun ta farko a zuciyata, wlh ban taɓa rokan wani abu a wajen wani ba sai soyayyarki, ban taɓa cewa wani sorry ba sai a kanki, ki yi hakuri ki karɓi sorry na dan kinyi breaking record ɗin TRIPLETS, yau na ce miki sorry". A karshen massage ɗin ya sanya mata emojin kuka da kuma tambarin zuciya.
A bayyane Rimsha ta karanta mata komai, shiru ta yi har lokacin tana ruwan hawaye, tabbas tana yi mishi wani irin mahaukacin makauniyar soyayya, wadda ko kanta bata yi wa irin wannan soyayya, amma kuma har cikin ranta tana jin tamkar taraiyarsu ba zata yiwu ba.
To me yasa take jin hakanâ“
Sosai Rimsha take rarrashinta tare da bata baki, cikin sanyin murya tare da sigar rarrashi ta fara magana "Aunty Akila in dai ɗaya daga cikin TRIPLETS ne, in dai yaya Areef ne yake sonki, wlh ina mai baki shawara da iya gaskiyata da basirata, ina mai gaya miki ki yarda da shi, ba wai dan wani abu ba, ba wai dan ina bin bayansu ba, ni nasan waye yaya Areef a ɗan zama na da shi, wlh, wlh mutumin kirki ne da samun na biyunsa zai yi matukar wahala, ko yaya Imran ne ya ji wannan magana shawarar da zai baki kenan, ni san duk wanda zaki tambaya halin yaya Areef ba zaki taɓa samun ɗaya na banza ba, bashi da matsala ko kaɗan a rayuwarsa, ina da tabbacin duk wata mace mai bala'in buri a kan miji, to da zarar ta zo kan TRIPLETS burinta ya kare, su ɗin burin ko wace cikakkiyar hamshakiyar mace mai hankali da sanin ya kamata ne, su ɗin burin ko wace uwa ce, kowa zata so samun ƴaƴa irinsu, kaunar junansu, ba'a magana, wlh idan kika shiga cikin rayuwar TRIPLETS ba ƙaramin daɗi zaki ji ba, ina ga sau da dama zaki rinƙa mance a wata duniya kike, saboda kyawun halinsu da kuma kula da zaki rinƙa samu, ki sani yadda suke kaunar junan nan nasu haka zasu kaunace ki idan kika shigo cikinsu, wlh ina da tabbacin idan kika auri yaya Areef to harta yaya Saif sai ya soki, duk abin da ɗaya daga cikinsu yake so, ko da basu so suna hakuri su bi son ɗayan nasu, ta hakan suke kara tabbatar da kaunar dake a tsakaninsu, ni wlh ba zanso ki ce ki na fushi da yaya Areef ba, na san son shi kam ba zaki taɓa dainawa ba, ko me zai yi miki, dan haka suke da shegen shiga rai kuma basu fita, idan ma kika ce zaki ciresu, to mutuwa zaki yi a banza, tun last week nake ƙoƙarin cire son yaya Saif a raina, amma ina abin ma karuwa yake yi, dana matsa ma sai naji rayuwata tana barazanar barin gangar jikina, ba dan naso ba haka na hakura dolen dole, to nasan ba zaki taɓa iya cire son yaya Areef a zuciyarki ba, idan kika matsa sai kin cire ma, wlh zaki iya mutuwa, dan haka ki hakura kawai ki karɓe shi dan ya cancanci a so shi ɗin, ni dai Aunty.......". Bata kai karshen maganar ba Akilar ta rufe mata baki tana faɗin "Na yarda da zancensa da ya ce ke kanwarsa ce, ga shi yanzu kinzo sai yabon shi kike yi, dan Allah ki yi shiru ki kyaleni na ji da abin da nake ki kinji ko? Bakin ku ɗaya ai da shi, dama ya gaya mini ke kanwarsa ce, kinga kuwa ai ba zaki so laifin yayanki ba daman". Sosai Rimsha ta ji ba daɗi, maganar Akilar ta yi mata zafi, kenan Akila tana nufin bata sonta ne yasa take bin bayan Areef ko yaya?.
Miƙewa ta yi da nufin ta fice daga cikin ɗakin, da sauri Akilar ta riƙo hannunta tana faɗin "Kiyi hakuri Rimsha, da wasa nayi maganar kin ji ko?" Tana magana tana ƙaƙalo murmushi dole.
Da yake Rimsha mace ce mai kyakkywar zuciya, sai ta hakura ta dawo ta zauna, kuma har ga Allah tana kaunar Akilar over, musamman ma da yanzu ta san cewa Æ´ar uwanta ce, Æ´ar bappanta ce, sai son ya karun mata a ziciyarta.