← Book details Triplets Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 68 OF 121

Sashe 68

Triplets Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan sun kammala Areef ya biya kuɗin suka fito daga wajen suka nufi super market, suna tafiya suna hira, sai bata labarin Washington DC Areef yake yi, tana ta murmushi. Tasha ruwan mamaki lokacin da suka je super market ɗin nan, kayayyakin da take mutuwar so Areef ya rinƙa zaɓa mata, sai tunani take yi a kan waye ya gaya mishi abin da take so kenan, har da takalma high heels irin wanda take so ya kwasa mata, ta sha sayayya iya sayayya ba karya, a nan ne Aseef yake gaya mata ai shi ma ya saya mata kaya, har da abin wuya irin nasu da ya ce zai sa a buga mata, to ya bugo ya zo mata da shi, yana cikin wannan akwaitin da ya ce ta ɗauka jiya bata ɗauka ba, ba ƙaramin daɗi ta ji ba, cike da murna ta ce su koma gida, dan ta je ta kalli kayan, to suka amsa mata tare da nufar wajen biyan kuɗi.

Areef ne ya biya, ma'aikatan wajen suka É—auka masu kayan zuwa wajen motarsu, a gidan baya suka sanya kayan, kamar yadda suka zo, ita da Areef a kujerar gaba, shi kuma Aseef driver, haka suka sake shiga suka nufi gida, sun manta da batun gyaran gashi.

Suna tsaka da tafiya a hanya daddy ya kira number Aseef, ya sha ruwan mamakin ganin call ɗin daddy da safiyar nan, yana can yana tunanin ko lafiya daddy ya kira shi, sai da wayar ta kutsa matsewa, ya yi maza ya ɗauka tare da sanyata a hand-free dan yana tuƙi. "Hello daddy good morning?".

Wani irin mahaukacin tsawa ya daka mishi wadda ya sanya shi taka birki a tsakiyar titi, saura kaÉ—an motar dake biye da su a bayansu ta dake su, sai Allah yasa ta kauce, daga Rimsha har Areef sai da kansu ya bugu da jikin glass É—in motar, saboda irin birkin da ya ja babu excuse.

"Michael wace ce ta ɗauki wayar Romeo yanzun da na kira shi?! Na sake ina kiran shi baya ɗagawa, shin a ina ma kuke tukunnan?!!". A razane ya ɗago yana kallonta, dan yasan ita ce ba makawa, daddynsu bai taɓa yi musu magana cikin irin wannan matsanancin siga mai cike da tashin hankali ba, to menene matsalar?.

Nan take shi ma tsantsar bala'in ɓacin rai ya bayyana a saman fuskarsa, tabbas yasan yau ba ƙaramin yaki za'a sha ba a Washington DC, dan kuwa idan daddy ya san suna Nigeria akwai bala'i ba kaɗan ba, sun ce mishi suna Spain ne wajen James, ba zai taɓa yarda su yi nisa har Nigeria ba, fatansu dai Allah yasa kada ciwonsa ya tashi, shi kansa Areef yau idan ransa ya yi dubu to ta ɓata mishi, ina ga kuma Romeo? Shi da ta ɗaga kiran na shi, Aseef jikinsa har rawa yake yi saboda tsantsar ɓacin rai, ji yake yi yau idan bai ɓalla yarinyar nan ba, ba zai sami kwanciyar hankali ba, yarinya bata ji sam, me ya kai ki taɓa waya ke da akace ki karɓo kuɗi?.

"Daddy am coming". Yana kai karshen maganar ba tare da ya jira me daddy zai ce ba ya yi diff ya katse kiran, a fusace ya juyo da kallonsa kanta, cikin ɓacin rai da kakkausar murya ya fara magana "Me yasa kika taɓa wayar Lion? Kin san abin da zaki jawo mana kuwa?!". Ɗaga mishi hannu Areef ya yi alamar ya yi shiru, ba musu ya yi shirun, da hannu ya sake nuna mishi hanya a kan su tafi sun tsaya a kan hanya, kunna motar ya yi zuciyarsa na tafasa, bawan Allah baya son ɓacin rai sam, amma yau sai da Rimsha ta ɓata mishi rai, shi ma Areef dannewa kawai ya yi dan ko sun ce dukanta zasu yi ma, a cewarsa me zai daka a jikinta, abu kamar ka lometa ka kora ruwa.

Tsantsar bakin ciki ya hana Areef magana, dama kunsan ance mai hakuri, shiru shiru, mai fara'a, bai iya shiga ɓacin rai ba, idan ransa ya ɓaci sai ya jijjiga kowa dake kusa da shi, hakan yasa ya daure ya yi shiru yana karanta

لَا إلَهَ إلَّا اللهُ وحْدَهُ لَا شَرِيكَ لهُ، لهُ المُلْكُ ولهُ الحَمْدُ، وهُوَ عَلَى كُلِّ شَيْءٍ قَدِيْرٌ. [عشر مرات](١)أو [مرة واحدة](٢).

Dan ya sami zuciyarsa ta yi sanyi cikin ƙanƙanin lokaci, idan ba haka ba, zai iya yi wa Rimsha mari ɗaya ba tashi, dan kule shi, fitinarta ya yi yawa.

Shiru suka yi babu wanda ya sake ce da wani ko uppan, haka har suka isa gida, suna parking na motar ta fito ta nufi cikin gida dan ta je ta yi wanka ta cire kayan jikin nan nata, ice cream ya ɗan zuba mata a kan kayan, har ta kai kofar shiga Palo, sai kuma ta juyo da sauri ta dawo, Areef yana tsaye ya ɗan jingina da jikin motar yana binta da kallo, shi kuma Aseef ya zagaya ta wajen pool a in da yake zaton zai sami Lion a wajen, gaban Areef ta dawo, cikin sanyin murya ta fara magana "Yaya Areef dan Allah kayi hakuri, ba zan sake ba, ka bawa yaya Aseef hakuri, dan naga ransa ya ɓaci sosai, In Sha Allah ba zan sake ba". Tana magana tana murza ƴan yatsun hannunta.

Hannun nata ya kamo cikin nashi, "Ba komai ki rinƙa kula Kinji? Laifi nane da na aike ki ɗakin, da ya kamata naje da kaina ne, laifin ki ke kuma da kika taɓa wayar, ki sani zuciyar Lion ba irin tamu bace, mu muna iya controlling namu, shi kuma ba haka yake ba, idan kika yi mishi abin da ya ɓata mishi rai, a lokacin zai buɗe miki aiki, kuma na sha gaya miki hakan, kada ki kuskura ki shiga gonarsa, yanzu kinga dole zai ɓata rai, ko in ce miki zamu ɓata rai, daddynmu bai san muna Nigeria ba, ba zai taɓa yarda mu zo Africa ba, dan ta yi nisa da shi sosai, yanzu yana tunanin muna Spain ne, shiyasa ya hakura ya daure ya zauna a Usa, daddy ba zai iya nisa damu har haka ba, bai taɓa ba kuma ba zai iya ba, idan har yasan Nigeria muke, ba zai taɓa yarda ba, zai ce sai ya biyo mu ko kuma mu dawo yau yau ɗin nan ba sai gobe ba, kuma kinga akwai aikin da muke yi a nan, yanzu dai shiga ciki, amma dai akwai matsala". Duk jikinta ya yi sanyi da jin maganarsa, ta yi kuskure, su kuma basu son daddy ya ce zai zo Nigeria, dan yanayin jikinsa, tafiya mai tsawo ba karamar wahala zai sha ba, jiki a mace ta nufi cikin gidan dan yin wanka, tana shiga bedroom nata ta wuce toilet.

A ɓangaren Aseef kuwa, yana isa wajen pool ɗin shi kuma Lion yana fitowa zai nufi cikin gida, a tare suka jera zuwa cikin gidan, kwata kwata bai gaya mishi abin da yake faruwa ba, a palon kasa suka rabu ya wuce bedroom ɗin Areef, shi kuma Lion ya haura sama zuwa nasa bedroom.

Yana shiga cikin ɗakin ya ɗan tsaya shiru yana tunanin me ya kawo wannan yarinyar yau kuma ɗakinsa, dan ya tsinci kamshin perfume nata a cikin nasa, dressing room nasa ya wuce. After some minutes ya fito sanye da wandon jeans fara tas zuwa gwiwarsa, sai riga polo t-shirt ita ma fara tas, ba ƙaramin kyau ya yi ba, saman bed nasa ya zo ya zauna, sai tashin kamshi yake yi, ɗan bakin nan nasa kamar ya sanya jan janbaki, sai wani kyalli ɗan bakin nasa yake yi.

Wayarsa ya É—auka, ya sha ruwan mamaki lokacin da ya kalli miss call É—in daddy almost 10, shiru ya É—an yi kafin ya cire password É—in wayar, É—an waro idanunsa waje ya yi lokacin da ya kalli an yi picking na first call da daddy ya yi, bai kawo komai a ransa ba, ya yi tunanin ma Aseef ne ya yi picking, cikin kwanciyar hankali ya fara kiran daddyn video call, tamkar jiransa dad yake yi, bugu É—aya ya É—auka, fuskar nan nasa a É—aure tamau, yau ya fito a ainahin dangerous Boss É—insa, zuba mishi idanu Lion ya yi yana kallon shi, bai ce ko uppan ba. "Who is she Romeo?" Shi ne tambayar da ya fara yi mishi, shiru ya yi bai amsa ba. "Me haÉ—inta da kai? Meyasa wayarka zai kasance a hannunta?" Nan ma shiru ya yi bai yi magana ba, sai bin daddyn nasa da ido kawai yake yi.

Tsawa daddyn ya daka mishi "Am i not talking to you?!" ÆŠan zaro idanu kaÉ—an ya yi yana mamakin, wai yau shi daddy yake yi wa tsawa har haka lallai. "Romeo am i your mate?!" Nisawa ya yi kafin gently ya fara magana "Daddy i don't know what to say, because i don't know what you are talking about ".

"Romeo how comes za'a ce mace ta É—auki wayar ka kuma ka ce you don't know her, how this can be possible?". Shiru ya yi dan shi ba zai iya wannan surutu na daddy ba. "Romeo a ina kuke yanzu haka?" Kai tsaye ya amsa mishi da "Nigeria". "Nigeria kuma?" Jinjina mishi kai ya yi alamar tabbatarwa. "Okey yanzun nan ku haÉ—a kayanku ku dawo, yau ba sai gobe ba, kuma i really hate this girl that a saw koma wace ce".

"Ba zai yiwu ba daddy, sai na kammala abin da nake yi zamu dawo". Ya yi magana a nitse cikin kwanciyar hankali.

A fusace dad ya miƙe tsaye, cikin fushi da kausashiyar murya ya fara magana, "Romeo I'm your father who born you not your friend or your Triplets!! So is better for you ka san irin maganar da zaka rinƙa gaya mini".

Shi ma a wannan karon ranshi ya ɓaci, baya son hayaniya ko kaɗan, daddy ya zo yana ta wani daga mishi tsawa, a fusace ya miƙe tsaye, cikin tsawa da ɗaga murya ya mayarwa da dad amsa kamar haka "I'm so what dad, am so what if it is you had born me? Take me back to your womb!" Tashin hankali da ba'a sama mata date.

"Romeo are you hard what you said? Are you forget who you're talking with?!!".
Chapter 68 · 0% Book details