← Book details Triplets Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 86 OF 121

Sashe 86

Triplets Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ita kuma bayan ta fitar da kayan abinci, dawowa ta yi dan ta yi aikin da ya sakata, gadonsa ta fara nufa, abin dariya abin tausayi, girman gadon ma ta fara tsayawa tana karewa kallo, yanzu ita ta yaya zata shinfiÉ—a wannan gadon? Ta tambayi kanta, zazzakar sexy voice nasa ne ya daki dodan kunnenta a in da yake ce mata ta É—auko wani sabon bed sheet É—in daga dressing room nasa, sai ta cire na saman gadon ta shinfiÉ—a sabon, okey ta amsa mishi da shi tare da nufar room É—in,.

Ba karamar ƴar kallo ta zama ba lokacin da ta shiga cikin room ɗin, dan ma bata ga na Washington DC ba, wannan ai kaɗan ne, dama idan baku manta ba, shi ɗan gayu ne, ɗan son kwalliya ne, akwai kaya over, komai na shi a shirye suke datsan datsan gwanin ban sha'awa, ko mai wajen ajeyesu daban, set by set, agogon nan suna jere cikin wani tsadadden show glass mai bala'in kyau, babu kalar agogon da babu a wajen, haka takalma, kaya ne masu bala'in tsada shirye a wajen, kamar an ce ta ɗago kai, idanunta suka sauƙa a saman ɓangaren shot nasa, ita kanta ba zata iya kirga yawansu ba, ga fararen singlet a gefe da yawa, mafiya yawan kayan dake wajen farare ne, yau dai ta zama ƴar kauye a dressing room na shi na Nigeria, idan ta ga na Washington DC kuma ina ga kasa fita zata yi idan ta shiga.

Da kyar ta iya gano wajen sets na bed sheets ɗin, babu ƙaramin bed sheet ko ɗaya a wajen, dukka manya manya ne masu duvet, da kyar ta iya ciro wani kato launin milk color, yana cikin jakarsa mai bala'in kyau, ko da ta ciro shi ta kasa ɗauka, ya fi karfinta, yanzu a kalla ta ɗauki 20 mins a cikin dressing room nan tun daga shigowarta zuwa yanzu, ta rasa ta yadda zata ɗauki duv ɗin nan dan yafi karfinta, daga karshe dai ta yanke shawarar jan shi a kasa zuwa bakin gadon sai ta buɗe ta fito da su ɗai'ɗai, haka kuwa ta yi, yana zaune ya ganta sai faman jan abu take yi kamar mai jawo akuya, ko sannu bai ce mata ba, har bakin gadon ta kawo, sannan ta buɗe zip ɗin jakar ta fara ƙoƙarin fito da kananan irin su rigar pillow cases da sauransu, badan tana da tsowa ba, da Lion ya ce shekarunta 11 a duniya, ga rashin karfi, abin gwanin ban dariya yadda ta jawo bed sheet ɗin.

Sai da ta fitar da su pillow cases ɗin kuma, sai ta tuna ashe bata cire bed sheet ɗin dake saman gadon ba, mayar da su cikin jakar ta yi tare da fara ƙoƙarin cire wannan katon bargonsa dake saman gadon, irin waƴan nan bargon ne wadda idan mutun ya shige ciki ma ba za'a taɓa zaton yana ciki ba, saboda girma da tudun bargon, ga shi kuma jikin bargon mai irin jikin magen nan ne, bala'in laushi gare shi kamar me.

Dukka iya karfinta ta sa zata ja bargon kasa, ai kuwa sai gata a saman gadon baki ɗayanta, dan kuwa bargon yaki jawuwa, yana da girma over ga bala'in nauyi, sautin dariya ta ji daga bayanta, ko bata ɗago ba tasan Aseef ne, shi kuwa Lion tamkar babu shi a ɗakin, aikinsa kawai yake yi. Ba ƙaramin dariya ta bawa Aseef ba, bare ma yadda bargon ya rinjayeta ta faɗa saman gadon, Rimsha ba karfi sam, karisowa wajenta ya yi yana dariya, cikin zolaya ya ce "Ki zo na ara miki karfina ƴar piritu". Da kyar ta iya miƙewa, a shagwaɓe ta ce "Allah yaya Aseef bana so, ai ina da karfi, bari kuma ka gani sai na cire bargon nan yau"

Sake da karkarewa ta yi wajen jawo bargon dan ta sauke shi kasa, a karo na biyu ma sai gata a saman gadon ta faɗa, bushewa da dariyar zolaya ya yi har sai da ya sanya Lion ɗagowa ya kallesu, wayarsa ya ciro yana faɗin "Oya sake gwada ɗagawa bari nayi miki video, zan ajiye tarihi ne, idan kin yi aure kin haihu zan nunawa yaranki, in ce musu mummynsu raguwa ce ta karshe, babansu kuma jarumi ne na karshe, sannan uncle nasu Aseef ma jarumi ne". Ya kai karshen maganar yana dariya, kumbura kumatu ta yi a shagwaɓe "Yaya Aseef na ce maka bana so ko?" Ta yi maganar tamkar zata saka mishi kuka.

"Oh, oh, oh our Queen ba sai kin yi mini kuka ba, bari na sauke miki kin ji ko ƴar sistotonmu?". Ya kai karshen maganar tare da sanya hannunsa dukka biyu na ɗauki bargon, bin shi da kallo ta yi tana mamakin wannan uban nauyin dukka ya ɗauka, saman sofa kusa da Lion ɗin ya ajiye bargon tare da dawowa ya tayata cire bed sheet ya kuma fito mata da wadda ta ɗako daga cikin jakar ya ɗaura mata a saman bed ɗin yana faɗin "Tom na gama aikina ko?". Murmushi ta sakar mishi tana faɗin "Yaya Aseef nima fa zan fara koyan training dan nayi karfi kamar kai". Nufar Lion ya yi yana faɗin "Tom shikenan, nan ba da jimawa ba zaki fara koya". Okey ta amsa mishi da shi tare da juyawa ta fara ƙoƙarin warware ƙaramin bed sheet ɗin dan ta shinfiɗa.

Abin dariya abin tausayi, sai haɗa zufa take yi ta kasa shinfiɗa gadon da kyau, sai ta jawo nan ta ga can ya ɓaci, tamkar zata saka ihu, shi kuma Aseef ya koma kusa da Lion ya zauna, hankalinsa na a kan wayarsa yana chatting da Heartbeat, baya kallonta bare ya zo ya taimaka mata, ta zagaye gadon nan yafi sau goma ta kasa shin fiɗa bed sheet ɗin, daga karshe dai, ta saman gadon ta fara bi dan kafafunta sun gaji da zagayawa ta nan ta kuma zagayowa, ga gadon da uban girma.

A wannan hali Areef ya shigo ya same ta, ba ƙaramin dariya ta bashi ba, sai uban haɗa zuba take yi baiwar Allah, dawo da kallonsa kan su Lion ya yi, aikin gabansu kawai suke yi tamkar basu san da ita a cikin ɗakin ba, karisowa ya yi yazo ya sanya hannu suka fara yi bibbiyu, sai murmushi yake yi mata, duk ta firgice kamar wadda ta wuni tana tikar aikin wahala.

Bayan sun shin faɗa ƙaramin bed sheet ɗin, sai ya ɗauko mata duvet ɗin ya gyara shi da kyau kafin ya shinfiɗa, dan yasan ba zata iya shin fiɗawa ba, ya yi mata girma, ba ƙaramin kyau gadon nan ya yi ba, ba'a taɓa shinfiɗa wa gadon bed sheet milk color ba sai yau, kullum daga fari sai sky blue mai haske, banbancinsa da farin kaɗan ne, ita ta jera mishi kananan pillows dake zuwa da bed sheet ɗin, su kam ta iya jerasu ba kaɗan ba, ta ɗauki wannan mai design of heart ɗin ta sanya a gaba tsakiyar masu four corner, sai ta ɗauko dogon kuma ta sanya a bayan masu four cornern, mai Heart ɗin dai ya zamana shi ne a gaba, shi kuma Areef wucewa ya yi ya cicciɓo wannan uban bargon, a tsakiyar ɗakin ya tsaya ya maɗe bargon gida huɗu, sannan ya ɗaura saman gadon kusa da pillows ɗin daga ɗan gefe, wani uban tudu bargon ya yi naɗe shi da aka yi, shi ma Areef ɗin da kyar ya naɗe saboda ciwonsa, dan ma ɗazun ya sha magani ya kuma shafa magani a wajen, shi ne ya ji wasau ta ɗan sake shi, ba laifi kuma ciwon tana warkewa sosai ba karya.

Bayan sun kammala ya koma kusa da Æ´an uwan nasa dake ta faman aikin gabansu ya zauna, Lion yana fama da laptop shi kuma Aseef waya, tamkar babu su a cikin É—akin, ita kuma kayan shara da mopping ta É—auko, yadda kasan ta iya aiki sosai, sai wani zagewa take yi, shara ta fara yi, har ta gama bata ga datti ko É—aya da ta sharo ba, mamaki ma take yi, wai a hakan kuma kullum sai an share É—akin har sau uku, ko me suke sharewa oho, mutun ne sai shegen bala'in kyamar datti kamar me, sai zancen zuci take yi har ta fara mopping É—in, shi ma dai ka tulluka, dan babu wani abin da ta goge, ko'ina tsab yake, amma dan bala'i da shegen son tsabta wai sai an share an yi mishi mopping, kai wannan Saif É—in akwai kusfa da kakale kakale.

Da ta kammala har zata fita waje, sai kuma ta tuna ai bata sanya musu turare air freshener ba, ta san halinsa sarai yanzu duk kamshin dake karaɗe da ko'ina a cikin ɗakin nan, zai iya cewa bai yi mishi ba sai an kara, wannan ba dan ta gan shi da kafufunsa yana taka kasa ba, da sai ta ce baya taka kasa kuma bai taɓa takawa ba, dan abin nasa ne sai shi ɗin, dama mai yin aiki a karkashinsa ai sai ya shirya ba kaɗan ba, sai ya kai zuciya nesa can kololuwa, kayi kuskure kaɗan kasha bakar wahala, dan ma dai yanzu ba aikin take yi a karkashin sa ba, akwai dalilin na zuwanta ɗakin, ya fi karfin ya tambayi Musharraf abu shi ne yake amfani da ita.

Dressing room ɗin nasa ta koma bayan ta mayar da kayan sharar, turarruka kala kala ta samu, wasu ma da alama bai san ya kamshinsu yake ba, ya dai sa an sayo mashi ya zube su a wajen, kuma kullum air freshener ɗaya yake amfani da shi, dan yafi son kamshin sa, bai taɓa gwada sauran ya ji ya suke ba, tun da wancan ta yi mishi ai shikenan kuma.

Dubawa ta fara yi, dan ita bata ma san da wanne yake amfani ba, ɗaya baya ɗaya ta rinƙa ɗauka tana buɗewa ta ji kamshin ya yake, dukkansu suna da bala'in daɗi, har da mai kamshin mangoro a cikinsu, nitsuwa ta yi ta zaɓa mishi dai'dai da ra'ayinta, wadda ya kwanta mata a rai ta kuma ji daɗin kamshinsa ba kaɗan ba, cikin zumuɗi ta ɗauke shi ta fito cikin ɗaki, lungu da saƙo ta fara bi tana fesawa.
Chapter 86 · 0% Book details