Sashe 108
Triplets Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ko da suka isa prison da aka kai ta, wani ganduroba ne ya yi musu jagora zuwa ciki, sai mamaki Rimsha take yi, wai ba da ance ba za su sami damar ganinta ba? To ya aka yi da kansu suke yi musu jagoranci zuwa ciki kuma? Sai tambayar kanta take yi, bata san cewa duk da ba kasarsu bace suna da daman yin abin da ya fi É—an kasa, saboda sun fito daga babbar kasa, kuma ga His excellency ai dole ma a yi musu abin da ya fi na É—an kasa, sun fi Æ´an kasa samun Æ´anci.
Office É—in ogansu ya wuce suka zauna, idan ba dan su manya bane, yaushe za'ace yarinyar da ta kashe É—an takarar shugaban kasa ace har wasu zasu iya samin damar ganinta, kai abin da abin mamaki.
Har cikin office ɗin Mark ya bisu, dan hakki ne a wuyarsa da ya kula da Areef kada ya bari wani abin ya taɓa shi, saman doguwar kujerar dake cikin office ɗin Areef da Rimsha suka zauna, shi kuma Mark yana tsaye tamkar wani robot.
Ba'a ɓata musu lokaci wajen fito da ita ba, da gudu Rimsha ta miƙe zata je wajenta, cikin sauri Areef ya riƙeta yana girgiza mata kai, shi tun daga farkon case ɗin ma ya fahimci akwai zalinci a ciki, na farko a kallon da ya yi wa jenan bata kai shakarun da za'ayi mata irin wannan hukuncin ba, na biyu yadda suka zuba mata tsaro kamar wata kungurumiyar ƴar ta'adda, na uku yadda suka wuce da ita prison kai tsaye tamkar dama jira suke yi su kamata, akwai wasu kananan dalili dai, amma waƴan nan sune manya, yadda case ɗin nata ya tafi ma sam ba tsari, dan sun yi abin ne a yunwacen suna son kamata, sai kuma suka fitowa da duniya hakan, mai basira tsab zai iya gane ina suka dosa, sai dai fa Areef bai damu sosai ba, dan yana ganin kamar mu kuma dokokin kasar mu ce a hakan kenan, shiyasa bai damu ba, ya fi son ya ji magana daga bakinta, dan ya yi imanin gabaɗaya jikin Nawazudden ba zasu yi karya ba, ya yarda da su, ya yi wa Uncle nashi kyakkyawar yarda.
Kasan carpet dake wajen ta zauna, hannunta na sanye cikin sarka wadda ya tafi har kafarta, shiru Areef ya É—an zubawa sarkar idanu yana kallonsu, shi dai ya san gunguma gunguman Æ´an ta'addan kasa da kasa suke É—aurewa da irin wannan sarka, amma an tashi an lafkawa Æ´ar yarinyar da bata wuce goyo ba a cewarsa.
Wani ganduroba É—aya daga cikin waÆ´an da suka fito da ita ne ya ce "Sir kuna da only 10 mins". Bai bi ta kansu ba, dan bai ga uban da ya isa ya saka mishi time a rayuwarsa ba, idan suka yi wasa ma sai ya ce ba zai bar nan ba sai da ita ya ga karshen iskanci, idan ya ce lalllai ba zai tafi ba sai da ita, ai dole Lion ya zo, kuma dole His excellency ya saka baki, dan sufa kasar American tsuntsuwar kasarsu ma ranta na da muguwar daraja bare kuma mutun É—an cikin kasarsu, mutun É—in ma jika ga His excellency ai dole ma su tursasa kasar Nigeria a bawa Areef Jehan dan ya bar wajen kada wani abin ya same shi, amma ba zai yi hakan ba, dan yasan doka kuma ba zai taka ba, saboda suke faÉ—a kullum abi doka, suke kama masu karya doka su hukunta, to idan su basu bi ba, waye zai bi kenan? Ai kowa ma take dokar zai yi, idan ba doka kuma ai ba al'umma.
Cikin sanyin murya ya tambayeta ya sunanta, kin magana ta yi, tamkar bata ji shi ba, sai kallon kasa take yi abinta, kallon Rimsha ya yi yana faɗin "Our Queen bata magana ne?" "Wlh tana magana yaya Areef, bari ka ji na tambayeta". Sauƙowa kasan ta yi kusa da ita, tana hawaye ta fara magana tare da riƙo hannunsu cikin na juna "Jehan dan Allah ki yi mishi magana, ki gaya mishi gaskiyar abin da ya faru, wlh zai taimaka miki, kinga shi ya taimaka mini ya kuma taimakawa daddy, nasan kema ba zai barki ba". Jin ta ambaci daddy yasa Jehan ɗin ɗago dara daran idanunta da suke farare tas babu ko alamar ɗigon hawaye, suna bushe garau kamar bata san me ake tuhumarta da shi ba, har wani haske idanun nata ma suka kara, shi kansa Areef ya sha ruwan mamaki dakiya irin nata, gata yarinya karama, ga ta a prison, sannan jikinta duk ya sha sarkuna a ɗaure kafa da hannu, amma a haka ko a jikinta, bugu da kari gata mace, abin dole a jinjina mata, kuma ayi mamaki, idan da wata mace ce ai ta rinƙa ihu kenan ganinta a hannun hukuma.
Shi ma dai sauƙowa ya yi dan ya kama Rimsha ta dai'na kuka, mamaki ne ya kama Mark yadda Areef yake bala'in kaunar su Rimsha, ko a mafarki bai taɓa tunanin ɗaya daga cikin TRIPLETS zai yi hakan ba, ya sauƙo ya zauna a saman carpet sabida Rimsha, abin dole ga wadda ya sansu a baya ya yi mamaki over.
"Jehan wlh daddy ya yarda da shi sosai, ki yi mishi magana kin ji". Cewar Rimsha, kuma da harshen Hausa ta yi maganar nata, jinjina mata kai Jehan É—in ta yi alamar to. "My name is Jehan Nawazudden Salman Sultan". Ta bashi amsa, nauyayyar ajiyar zuciya ya sauke dan kuwa har voice nata sak na daddynta ne, babu in da ta baro shi, hannun Rimsha ya kama suka koma saman sofa suka zauna, baya son ganinta tana kuka.
"Okey Jehan zaki iya gaya mini a kan wani laifi suke tuhumarki da kuma gaskiyar abin da ya faru". Ba musu ta gaya mishi a kan laifin kisan kai suke tuhumarta da shi, ba ƙaramin tsorata Rimsha ta yi ba, shi dai Mark ya zuba musu idanu ne yana kallon ikon Allah, Jehan na magana kamar wata babbar jarumar soja, babu tsoro ko ɗarɗar a muryarta, kai tsaye ta ce kisan kai lallai.
"Okey to da gaske kece kika yi kisan ne?" Jinjina mishi kai ta yi alamar e ita ta yi, Rimsha bata san lokacin da ta kurma ihu ba, da karfi ta ce "Wlh karya ne, ni nasan wacece ƴar uwata, tana da faɗa sosai, amma wlh ko kaza ba zata iya kashewa ba, karya ne". Rungumota Areef ya yi yana ƙoƙarin miƙewa dan komai ya lalace tun da Jehan ta amsa da bakinta ita ta yi kisan, shikenan kuma. Har zai miƙe sai kuma ya koma ya zauna yana karewa Jehan ɗin kallo, yarinyar nan ko a jikinta wai an yakushi kakkausa.
Mark ne ya yi gyaran murya cikin girmamawa ya ce "Sir am sorry to say amma wannan yarinyar ba ita ta yi kisan nan ba, ko da ita tayi to akwai dalili mai karfi ko kuma by mistake ne". Jinjina mishi kai ya yi alamar ya gamsu, shi ma ya yi tunanin hakan shiyasa ya fasa tafiya ya dawo ya zauna, cikin sanyin murya ya sake tambayarta ko zata gaya musu ya akayi ta yi kisan, nan ne kuma Rimsha ta yi shiru ta nitsu tana son jin ta ya akayi hakan ta faru.
Ba musu ta gaya musu tsab, sai dai bata gaya musu daga ina ya ɗauko ta ba, ta dai ce musu ya ɗaukota ne da nufin ya yi mata fyaɗe ya kai ta gidan shi, shi ne ita kuma ta yanke bananarsa, dai'dai lokacin da ta furta ta yanke bananan nan, gabaɗaya gandurobobi uku dake wajen sai da suka sanya hannu a gabansu dan su ji nasu yana nan kam ko, harta shi kan shi Mark sai da ya sanya hannu a saitin gabansa yana mamakin karfin hali irin na yarinyar nan, har zata iya kallon gaban babban namiji ta saka wuƙa ta yanke?, Wannan da horon sojoji ta samu ba karamar soja mara imani za'ayi ba a duniya, sai ta kafa tarihi a duniyar hukuma, wai ta yanke, ko a jikinta ta faɗa kai tsaye, Areef bai taɓa shan ruwan mamaki irin na yau ba, suna hukunta masu yin fyaɗe ta wannan hanya na yanke musu gaba, amma ita fa mace ce kuma yarinya karama, abin ya bashi mamaki sosai, bare ma yadda ta faɗi komai dallah dallah a nitse cikin kwanciyar hankali, ita kam Rimsha tsit ta nasu ta ji abin da ya goge mata lissafin ƙwaƙwalwa yau, lallai jenan ta wuce tunanin mai tunani.
Gyaran murya ya yi, lokacin guda kaunarta ya shiga ransa, yana bala'in son mutun jarumi mai dakiya, son gaskiya, adalici da taurin zuciya, mai ƙoƙarin kare kansa a koma ina ne, shi abin da Jehan ta yi, ta yi mishi dai'dai, hakan kuma yasa ya ji sonta a cikin zuciyarsa, ta burge shi ba kaɗan ba.
"Lokacin da abin ya faru, waye da waye ne a cikin gidan?" Nan ma ba musu ta bashi amsa tare da É—aura mishi da cewa ai Æ´an'sandan ne suka biyota shi da Aseef suka bugeta da mota, sai yanzu ya gama fahimtar case É—in ma, ashe da bakin hukuma mutumin yake lallata Æ´aÆ´an mutane, a dole dama su yi wa Jehan irin wannan sharri, dan idan gaskiya ta fito, har su kansu hukumar sun shiga uku, dan sune masu tsaron mutumin ai.
"Okey tom ba damuwa zan sake dawowa zuwa anjima or gobe dan in yi miki wasu tambayoyi". Ya bata amsa tare da miƙewa ya riƙo hannun Rimsha, binsu da ido ta yi, har ya ɗan yi gaba sai kuma ya dawo ya tsugunna a gabanta tare da riƙo haɓarta ya ɗan ɗago suna fuskantar juna, "Kyakkyawa mai kama da uncle na, ki kula sosai dan nikam na samu jarumar sister". Ya faɗa tare da miƙewa, kun san shi dama da wasa da dariya idan ya yi niya, harara ta wurga mishi, kashe mata ido ɗaya ya yi yana ɗan murmushi, jawo hannun Rimsha ya yi yana faɗin "Muje hai sister, wannan mai kama da uncle ɗin mafaɗaciya ce sosai". Rufa musu baya Mark ya yi, ita kuma Jehan suka mayar da ita cikin prison ɗin.