Sashe 64
Triplets Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A palo ta haɗu da Ummi, zata wuce kitchen ta dakatar da ita ta hanyar cewa "A'a Aafia ki bar girkin zan je in karisa, ki je ki kula da mijinki tun da ya dawo". Kasa ta yi da kai, a dole ta ji kunya, sumui sumui ta juya ta koma, dama ita ma tana son zama ta kula da kayanta, dan kawai kada Ummi ta ce ta bar mata girki daga kai abinci ne yasa ta fito, badan haka ba, ta fiso mijinta ya ci abinci a gabanta, dan ta san adadin komai da yake buƙata, ma'ana tasan adadin cinsa da sauransu, dama kuma yana da kyau ku san adadin abincin da mijinku yake ci, dan kada ki rinƙa labta mishi abin da ba zai iya cinyewa ba, ki zuba mishi abin da ya fi karfin cikinsa, ko kuma wadda ta yi mishi kaɗan, sai ya zo yana a kara mishi ko daɗin ji babu, wai a kara.
Lokacin da ta dawo É—akin shi ma ya fito daga toilet É—in shirye cikin kayan data fitar mishi É—in, ya yi kyau sosai, ya fito a cikakken saurayinsa, duba time ya yi 5:30, in da ya saba zama ya je ya zauna, cikin natsuwa ta karisa in da yake, abincin ta fata zuba musu, bayan ta gama ne suka fara ci a tare, cike da so da kaunar juna, da kuma kula da juna, sai zuba mata hira mai shegen daÉ—i yake yi, ita kuma sai bin shi da murmushi take yi har suka kammala.
Miƙewa ta yi ta tattare kayan abincin ta nufi waje, Ummi tana kitchen tana faman zuba soyayyar nama a cikin miyar da Aafia ɗin ke haɗawa. "Ummi bari na karɓa miki". Ta faɗa bayan ta ajiye kayan abincin.
"A'a Aafia ai kin yi abinci, miyar kuma bari na karisa, ke dai jeki ki kula da mijinki, Allah ya yi muku albarka, ya dawwamar min da rayuwarku a cikin tsantsar farinciki". Amin ta amsa da shi tare da yi wa Ummin godiya ta juya ta koma É—akinsu.
Kwance ta isko shi saman doguwar kujeran, ya É—aura kafa É—aya bisa É—aya, ya zuba wa Tv dake manne a jikin bango idanu. Daidai saitin kansa ta zo ta sanya hannu ta É—an É—aga kannasa ta zauna tare da É—aura kan nasa a saman cinyarta, juyo da kallonsa a kanta ya yi suna fuskantar juna. "Sister kinsan duk wani abu da nake so, Allah ya yi miki albarka, kina sanya ni farinciki sosai da sosai, ba abin da zan ce sai dai nayi ta yi miki addu'ar fatan alkhari".
Hannu tasa tana shafa face nasa, cikin sanyin murya ta ce "Yaya Nawid farincikin da kake sanya ni yafi wadda nake sanya ka, fata na dai Allah ya kare min kai a duk in da kake, Allah yasa kada wata mace taga kyanka sai muni, ya zamana ni kaɗai zan ga kayana" "Eyee wato ma dai addu'a kike yi na kashe mini kasuwa ko? To ban yarda ba, haka kawai? Ni bana so, ina laifin ki ce mata kyawawa zuƙa zuƙa kamar ke haka, guda uku su makale suce sai ni, ai kinga......." Bai kai karshen maganar ba ta rufe mishi baki da hannunta, a kule ta ce "Haka ma zaka ce?" Girgiza mata kai ya yi alamar a'a, tun da ba halin yin magana, ta rufe mishi baki.
Miƙewa ta yi tare da kwantar mishi da kansa a saman sofa ta nufi gado ta kwanta, irin ta yi fushin nan, da sauri ya miƙe ya bi bayanta yana ambatar sunanta, kin kulashi ta yi, ta yi kwanciyar ruf da ciki, tare da kwantar da kanta a saman pillow.
Saman bayanta ya haye ya kwanta tare da kwanto da kansa a saman kafaɗarta, murya a sanyaye ya fara magana "Haba my sweetheart, me yasa zaki ɓata ranki bayan kinsan wasa nake yi miki, nifa ke kaɗai kin ishe ni, bana son wata, please tashi kiyi mini tausa kin ji ko? Na tuba ba zan kara ba".
Ɗan ɗago kanta ta yi, da sauri ya sauƙa a kan nata, pillow ta ɗauka ta fara bugun shi da shi, tana kumbura kumatu, sai dariya yake yi gwanin ban sha'awa, shammatarta ya yi ya haɗeta ita da pillow gabaɗaya ya rungume yana dariya, shigewa jikinsa da kyau ta yi tana murmushi,. "Eyyee ranar nace kishi kike yi, kin ce ba haka ba, to yau kuma menene? Ko dai shi ma wannan ba kishi bane?" "A'a yaya Nawid, ba kishi bane, ni bana kishi ai, na gaya maka kula da kai ne, wai ka manta amanarka a ka bani ne?". Hancinta ya ja zai yi magana aka fara kiraye kirayen sallar mangariba, shiru ya yi yana salatin annabi yayin da ita ma take yi, sai bayan an idar da kiran sallah ne suka yi addu'a da ya kamata.
Sauƙowa kasa ya yi daga saman gadon ya nufi toilet dan ya ɗauro alwala, ita ma sauƙowa ta yi ta fiddo mishi da jallabiya, bayan ya fito, ya ɗauki jallabiyar ya koma toilet ɗin, jim kaɗan ya fito sanye da ita ya nufi masallaci, amma kafin ya tafi sai da ya manna mata hot sumbata a kumatu, ita ma ta mishi reply, sannan ya wuce zuwa masallacin, ita kuma ta haye gado ta kwanta dan yau bata sallah.
A ɓangaren gidan Abbi kuwa.
DADDYN JELLY & AYLA.
Wasa wasa laulayi ya kankama, kwata kwata bata cin wani abincin kirki, cikin nata mai mugun zaɓar abinci ne, ga uban laulayi, cikin ƴan kwanakin da basu fi biyar da bayyanar cikin ba, har ta yi wani uban rama, kullun sai kwanciya a kasa tana bin sanyin tiles, ba wan da bai tausaya mata ba, shi kam daddy ma ba'a magana, kullum yana tare da ita, da ta yi motsi zai tambaye ta ko wani abin take so, ya dai'na fita ko nan da cikin gida wajen su Abbi, babban abincin da ta fi ci a yanzu shi ne yalo, dan haka daddy ya jibge mata su dayawa a cikin fridge, da yaga sun kusa karewa, zai sayo wasu, yana ji da cikin nan nasa, yana ririta kayansa, dama ko ban faɗa ba kum sani, kunsan Ayla raguwa ce number ɗaya, yanzu ma ragwancin take zuba mishi ba karya, haka zai yi ta biye mata, dama da lafiyarta ma shi yake yi mata komai, ina ga kuma yanzu da lalura ta samu, ai sallah ne kawai yake barinta ta yi da kanta, sai kuma shiga toilet, amma harta kaya, shi yake sanya mata bayan ya yi mata wanka, ta dawo jaririyarsa da gaske, dan ma yana da ƙoƙarin yi, baya damuwa, har rama shi ma ya yi saboda wahalar da cikin nan yake basu, da kyar yake iya lallaɓata ta ci abinci, nan ma sai ya nuna mata zai yi kuka, da zarar ta ci kuma zata yi ta kwarara amai tamkar zata amayar da ƴan hanjinta, tana azabtuwa ba karya.
Da misalin karfe 8 na safe, tana zaune a tsakiyar gadonsu, jikinta na sanye da wata Æ´ar shimin rigar barci da bata wuci zuwa cinyarta ba, hannun rigar Æ´an sirara ne kamar igiya, kayan suna da kyau sosai da sosai, ta rame ta yi wata fayau da ita, fuskar nan kamar ba ita ba, sai ido zaka gani.
Daddy na gaban mirror yana fesa perfume, yana shirye cikin kananan kaya, wandon jeans ash color da riga baka, ya yi kyau sosai, bini bini zai kalleta ta cikin mirror, ita ma sai bin shi take yi da idanu irin Allah sarkin nan, ganin tana ta kallon shi ne yasa ya juyo yana sakar mata murmushi. "Babyn daddy akwai abin da kike so ne?" Kayatatcen murmushi ta sakar mishi tana girgiza mishi kai alamar a'a "Ki tuna dai da kyau, idan akwai ki gayawa daddy yanzu zan kawo miki".
Nisawa ta yi kafin ta ce "Daddy wai dama haka ciki yake da wahala ne?" Ajiyar zuciya ya sauke tare da girgiza mata kai alamar a'a. "Ba kowani ciki bane yake da wahala baby, kinga cikin jelly kwata kwata bamu san ma da shi ba har sai da ya kai almost wata 3, a sannan ne ya bayyanar da kansa, to ko wani ciki da yanayin yadda yake zuwa mace, ke dai kiyi addu'a Allah ya baki lafiya, sannan kuma Allah ya bamu ƴaƴa masu albarka, next time In Sha Allah zai zo miki da sauƙi, yanzu ma da izinin Allah da ya kai wata uku zai rage miki duk wannan laulayin kin ji ko?" Gyaɗa mishi kai ta yi alamar e ta ji.
"Yauwa babyn daddynta, yanzu dai tuna da kyau babyna baya buƙatar komai?". "E daddy baya buƙata". "In kawo miki yalo?" Cikin sauri ta gyaɗa mishi kai alamar e ya kawo mata, ƴar murmushi ya yi yana faɗin "Ba baby ya ce baya buƙatar komai ba? Ya akayi yanzu kuma zai ci yalo?" Hannayenta dukka biyu tasa ya rufe fuskarta tana dariya.
Takowa ya yi ya nufi wajen É—an madaidaicin fridge É—in nasu, buÉ—ewa ya yi tare da fito mata da yalo guda biyu, a gefenta ya je ya zauna tare da É—an rungumota a jikinsa yana kai mata yalon saitin É—an bakin nata, kaÉ—an ta É—an gutsira ta fara tauna tana mai mugun jin daÉ—in yalon sosai da sosai. "Daddy kai ma kaci mana?" To ya amsa mata da shi tare da kaiwa bakinsa, kwata kwata baya son yalon, amma tun da ita ta ce ya ci, dole ya jarraba ko dan ta yi farinciki.