Sashe 26
Triplets Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ranar da Amarya ta dawo, tun da su Abban Imran suka yi ido biyu da ita, shikenan suka tare a gindinta suma, ta mallakesu, amma kuma Allah da ikonsa ta kasa mallake daddyn Rimsha da kuma daddy Anaya, ƴan biyun nan ƴan baiwa ne na gasken gaske kuwa, sam abin bai yiwa Amarya daɗi ba, domin ita burinta ne ta mallaki daddyn Rimsha dan ta sami abin da take buƙata, kuma duk mallake babansu da ta yi, baya hana shi kula su Daddy Rimsha, saboda su dai maganin bai kamasu ba, wani lokacin ma Amarya tana kiran shi ya zo su kwanta, zai ce a'a shi yau da yaran shi zai kwana, haka zai wuce ɗakinsu daddy Rimsha, su kaɗai yake kulawa a cikin ƴaƴansa. Sam amarya ta gaza samun sukuni, hakan yasa ta fara neman mafitar ta yadda zata salwantar da rayuwar yara biyun nan.
Dududu amaryar fa shekarunta 25 a duniya, iyayenta ke shirya mata duk wata manakisa, su burinsu cin dukiya, da ta je gidan ne ta gaya masu abin da su Abba suke yi mata, har da dukanta da Abba ya yi, shi ne mamanta ta kai sunan su Abba ga malaminsu aka mallakesu dan su samu su mulki gidan, su ƙori Naura su mamaye komai dukiya da kyawawan fararen turawan ƴaƴan.
A na tafiya a haka har cikin Naura ya kai wata 9, wata ranar Friday da ta kasance rana mafi bakin ciki a garesu, ranar da daddyn Rimsha ya gaza mancewa da shi, ranar data sanya Naura haihuwa ta shiri, ranar da ta kulla gaba tsakanin su Abba da daddy Rimsha, shi ne ranar da Amarya ta yi wa daddyn Rimsha wani mummunar sharrin wai yana nemanta da iskanci, kuma ta yi galaba akan shi ne ta haryar tabbatar masu da shaida, abin da ya faru shi ne.
Kiran shi ta yi É—aki akan zata aikesa, a lokacin yana tare da mummynsa yana yi mata tausa, bawan Allah bai san komai ba sai Kaunar mummynsa da Æ´an uwansa, ba in da ya sani a garin Kaduna sai school nasu, shopping da kuma gidansu, shi kuma Hassan yana ta faman shafa cikin mummyn nasu yana lissafa abin da zata haifa masu, kani ko kanwa, abin gwanin ban sha'awa da burgewa, duk wanda ya kalli yadda suke sai ya ji sun burge shi saboda yadda suke ta zubawa mummynsu hira, har lokacin kuma basu jin hausa sai turanci, suna bala'in kaunar juna tare da cikin mummynsu, sai murmushi suke yi abinsu, su Abbi kuma suna bedroom nasu.
Da farko da Amarya ta ce yazo, sai ya ce ba zai je kiran ba, sai da mummynsa ta sanya baki, shi ne ya je.
Yana zuwa ta rufe kofa, da karfi ta cire mashi kaya har sai da suka yi kokawa, jin ya fara ihu ne yasa ta fishi ɗaga murya wajen fara ihu ita ma, ta ɗauki kwalbar turaren humra ta buga mashi a goshi da karfin gaske, nan take wajen ta fashe, jini jajawur ya fara wanke mashi fuska, da haka ta gayawa Dr Salman ai shi ya shigo zai yi mata fyaɗe, a garin kare kanta ne ta buga mashi kwalbar turare, da yake ta mallake su Abba, sai suka amsa da haka ne da Dr Salman ya tambayesu, Abba har da cewa ai ranar ma ya ga daddyn Rimsha ɗin yana wasa da gabansa a cikin ɗakinta, ita kuma bata nan lokacin, shi kuma Abbi cewa ya yi ai ranar ma ya gan shi yana ta wasa da breziyarta yana kissing na bra ɗin........ Innalillahi wa Inna ilaihir rajiun 😠Allah ka tsinewa asiri albarka.
# Ai kuwa ran Dr Salman in ya yi dubu to a ranar ya yi mugun ɓaci, a nan ne kuma ya furta kalamai masu zafi a kan ɗan nasa, nan take ya ce ya yafe shi wa duniya, kuma sai an kai shi prison, sai ya yi zaman yari na shekaru goma, da yake su dokar turawa suka sani, ba na Nigeria ba, wani irin Mahaukaciyar razana da shiga tashin hankali Naura ta shiga, domin tasan dokan turawa ya fi namu a nan tsauri, su idan suka yanke hukunci fa, to sai an yi wannan shekarun, kuma ta ji har shekara goma ɗan nata zai yi a prison cewar babansa, bata san Nigeria kam ɗan ma zai iya gudu daga prison ɗin ba. In takaice maku labari, a wannan ranar dai Allah ne ya kaddara Naura kwananta na gaba, da sai dai a kwashi gawarta, saboda tsantsar bala'in tashin hankali da ta shiga, su Abba kuwa tsab suka bi bayan babansu da Amarya suka share Mummynsu, da alama ma sun mance ita ta haifesu, sai zaginta suke yi ita da daddyn Rimsha, yana jin suna zagin mumnynsa, shi sharrin da akayi mashi bai wani damesa sosai ba kamar yadda Abba da Abbi ke zagin mummynsu.
Suna ganin Naura na kuka, amma ko a jikinsu saboda basu a hayyacinsu, tashin hankali da damuwar kada a rufe mata yaro ne yasa ta ɗebo kuɗi masu yawa wadda ita ma bata san adadinsu ba, ta zuba kuɗin a cikin jaka, a lokacin Dr Salman ya kira ƴan'sanda, basu kai ga isowa ba, sai dukan daddyn Rimsha yake yi kamar zai kashe shi, da kyar Naura ta iya kwatarsa, ita kuma Amarya tana ɗaki abinta, yau ranta fes, Hassan kamar zai yi hauka, shi ne kuma ya taya mummyn nasu karɓar Hossain nasa, su Abba suna tsaye suna kallon me yake faru, ko a jikinsu.
Da kyar ta ja Daddyn Rimsha zuwa ɗakinta, ga ƙaton ciki wadda da alama ma ta fara naƙuda, tana kuka kamar ranta zai fita, haka shi ma Hassan, tamkar ransa zai fita yake kuka, shi kuma daddyn Rimsha ba'a magana, duk Dr Salman ya fashe mashi baki, ga gaskiya suna gani amma suka take. Ɗakin Amarya Dr Salman ya koma ya kwanta yana jiran dirowar ƴan'sanda dan su tafi da Hossain.
Suma su Abba kowa ya wuce ɗakinsa, lallaɓawa Naura ta yi tana naƙuda ta ɗauko jakar kuɗin nan ta bawa daddyn Rimsha ta ce ya gudu ya tafi, da yake shima a zuciye yake a lokacin, ya tsani kowa, sai ya karɓi kuɗin ya gudu, mai gadi ya so tare mashi hanya, ai kuwa ya sakarwa mai gadin kunamunsu na twins ya gudu ya fita daga gidan, bai san ko'ina ba, bai san kowa ba, dan ma dai Allah yasa yana da wayo sosai ga kuma ilimi, sai kuka Hassan yake yi yana cewa shi zai bi ɗan uwansa, amma Naura ta riƙe shi gam, da yake dama sun san yana kuka, sai basu kawo cewa Hossain ya fita ne yasa yake kara wannan mahaukacin ihun ba, sai suka bari a kan dukan da babansu ya yi wa Hossain ɗin ne yasa Hassan ke wannan ihu haka. A TAKAICE DAI WANNAN SHI NE SANDIYAR RABUWAR HASSAN DA HOSSAIN, WANNAN SHI NE ABIN DA YA FARU, SAURA LABARI KUMA ZAI ZO MAKU DAGA BAKIN ABBAN IMRAN, WANNAN MAGANA BA ZA SU MAIMAI TA SHI BANE YASA NA GAYA MAKU ABIN DA YA FARU, SHI KUMA DADDYN RIMSHA BAYAN FITAR SA GIDA INA YA JE? ZAI GAYA MAKU DA BAKINSA, INA NAURA TAKE? ME TA HAIFA A RANAR? YA AKAYI DADDYN JELLY YA YI RAYUWA DA DADDYN RIMSHA DA HAR YAKE IKIRARIN SUN FI KUSANCI DA HOSSAIN ƊIN? INA AMARYA? YA MAKOMARSU ABBA A WANNAN LOKACI? YA AKAYI WANNAN ASIRI DA AMARYA TA YI MASU ABBA YA WARWARE DA HAR A YANZU SUKA SAN KUMA SUKA GANE SUN YI WA DADDYN RIMSHA LAIFI? YA AKAYI DAGA BAYA SU ABBI SUKA RABU HAKA? SAURA LABARI YANA GABA, NA SAN A IYA WANNAN MA KAWAI KUN FAHIMCI IN DA ZANCEN YA DOSA, MU DAI JE ZUWA ZAMU HAƊU A GABA DAN WARWARE KOMAI A TARE.
STORY💋
💋GIDAN LION💋
Ajiye wayar Imran ya yi tare da kwanciya a saman gadonsa, tunani cike fal ransa, tabbas yana son sanin menene gaskiyar abin da ya raba iyayensu, meyasa daddyn Rimsha baya son haÉ—a inuwa É—aya da su? Amma kuma meyasa yake taimaka masu sosai idan suka shiga damuwa? Imran bai san abin da suka yi mashi bane ta tsaya mashi a zuciya da yasa baya son haÉ—a inuwa da su, jini ba wasa ba, tabbas yana kaunarsu shiyasa ma yake taimaka masu kuma yake bibiyar lamuransu, amma kuma duk lokacin daya gansu, ba abin da yake tunawa fa ce irin sharrin da suka murje idanunsu a gaban kowa suka yi mashi, wai yana neman matar babansa, waiya zubillah, ya kasa mancewa da wannan abin, yana da Bala'in zuciya sosai.
A ɓangaren Rimsha kuwa, bata sami barci ba har wuraren karfe 1, tun da Imran ya dawo da ita ɗaki take kuka, kuma ta rasa dalilin kukan nata, ta rasa me yake yi mata daɗi, da kyar barci ya yi awon gaba da ita.
Washegari da misalin karfe 8 wanka ta yi, ta shirya tsab cikin wando da riga kamar dai kullum, sai dai yau, Pakistan ta sanya, rigar ma ta É—an É—ara gwiwarta, wandon kuma yana da É—an faÉ—i, sai mayafin mai É—an girma, dukkansu launin sky blue ne, ba two colors bane.
Bayan ta gama shirin ta fes, sanya perfume nata ta yi, tare da É—aukar wayarta ta nufi Palo, idanunta har yanzu suna kunbure, saboda ba karya ta sha kuka daren jiya.
Ko da ta fito Palo, babu kowa, dan haka sai ta wuce kawai ta nufi garden É—in gidan. Da sallama É—auke a bakinta ta shiga, Imran ne kawai yake zaune a wajen.
Kayatatcen murmushi ta saki mashi kafin ta É—aga mashi gaisuwa, da fara ya amsa gaisuwar tata, kusa da shi ta je ta zauna, hira suka fara yi a tsakaninsu, cikin mutunta juna da girmamawa, sai murmushi suke sakarwa junansu gwanin burgewa.
Suna tsaka da hira suka ji diran motoncin a cikin gidan, nan take gabaÉ—aya gidan ya kauraye da jiniya tamkar yaki za'a tafi, jibga jibgan motoci masu numfashi kwara biyar ne cif, kuma dukka motocin sojiji ne masu rai, sabbi gal gal, haka zalika jibga jibgan fararen turawan sojoji ne a saman bayan waÉ—an nan motocin.