← Book details Triplets Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 57 OF 121

Sashe 57

Triplets Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A ɓangaren Rimsha kuwa, kofar ɗakin Imran ta nufa, da sallama ɗauke a bakinta ta tsaya a bakin kofar tana jiran izinin shigowa, daga ta cikin ɗakin jelly ta amsa mata da "To ƴar anace, yaya Imran yana wanka, idan kina son yin magana da shi, sai ki jira shi a waje ai". Ta kai karshen maganar tana jan tsaki.

Har cikin zuciyarta maganar ta yi mata zafi, kuma hakan ma kaÉ—an ne daga maganganun da jelly É—in ke gaya mata, yanzu ma da tasan baya cikin É—akin ba zata je wajen ba, dan tana jin zafin maganganun jelly sosai, kuma kunsan halin jelly, number 1 ce a rashin kunya.

Rai a ɓace ta juya ta koma cikin ɗakinta, tason ta yi magana da Imran akan zuwa gyaran gashin nan nata, dan kan nata na damunta, ta kuduri niyar ba zata sake zuwa wajen Imran neman wani abin ba, dan tana zargin da gangan ɗazun jelly ta ce mishi lallai su je gidan Abbi, dan kawai ta ji yace zai kai Rimshar gyaran gashi, shi ne ta bijiro da nata dan kada a kai Rimshar, ta yanke wa kanta hukunci zata rinƙa fita da kanta ta je tunda yanzu ta yi free, zata tambayi Akila sunan anguwar da ake gyaran gashin dan ta rinƙa kai kanta da kanta kawai zai fi mata.

Tana shiga bedroom nata zuciya cike fal da tunani, toilet ta wuce dan ta yi wanka, bayan ta kammala ta shirya cikin É—aya daga cikin É—inkunan da Imran ya yi musu, dogowar riga ce É—inki ya zauna mata sosai a jikinta, fesa perfume nata ta yi tare da É—aukar wayarta ta nufi garden na gidan.

Tana zama cikinta ya fara kukan yunwa, shiru tayi tana sauraron yadda cikin nata ke ƙu,lu,lu,lu, wato kuman yunwar kenan, tunani take yi a irin rayuwar da zata shiga yanzu kuma, ji take yi tamkar ta roƙi Areef yasa a mayar da ita kusa da daddynta, ko kuma ta koma gidan Akil, wani ɓangare na zuciyarta ne ya bata amsa da ita ma Umaisha kishi take yi da ke ai, tamkar zata yi kuka tuna hakan da ta yi, a kule ta ce wai me yake faruwa da ita ne? Ko wace mace sai ta ce tana kishi da ita, to ita tace tana son mazansu ne? Abin gwanin ban tausayi, can wani ɓangare na zuciyarta ya tuna mata to ko dai ta koma gidan Abbi ne?, Nan ma ɗayar ɓangare na zuciyar tane ya bata amsa da anya zata iya yin nisa da Saif kuwa? Anya zata iya jure wuni guda ba tare da ta ganshi ba kuwa? Anya hakan zai yiwu kuwa? Bama Saif ba, shima Areef anya zata iya rabuwa da shi kuwa?, Tuna hakan yasa ta fara ruwan hawaye, ga yunwa, ba wadda zata iya gayawa tana ji, yaya Imran ne kawai, shi kuma yanzu jelly ta yi musu tsakani.

Tana cikin wannan hali sai ga jelly da Imran sun nufo garden É—in, sunci kwalliya, Imran na sanye da kananan kaya, wato wandon jeans baka da t-shirt blue, ita kuma jelly riga da skit ne a jikin nata, skit É—in ruwan kasa da ratsin fari, riga fari, kayan sun É—an kamata, amma ba sosai ba, ba karya sun yi kyau sosai, yau Imran ya sanyata dole sai ta saka É—ankwali a kanta, hakan yasa bata ji daÉ—i ba, sai turo baki take yi, ita a dole ta ji haushi.

Ganin su yasa ta yi saurin goge hawayen fuskarta tare da ƙaƙalo murmushi dole dan kada Imran ya gane komai, tasan yana yi mata iya iyawarsa, baya bari ta shiga kunci, yanzu ma duk abin da yake faruwa tsakaninta da jelly bai da masaniya a kai, idan ya sani zai ɗauki mataki, ba zai bari hakan ta cigaba da faruwa ba, idan baku manta ba, kunsan jelly da iya makirci da kirsa, to bata yi wa Rimsha abu a in da ta san Imran ɗin zai gani ko kuma ya ji, sai ta faki idonsa take tsula tsiyarta, ɗazun ma da yake toilet ta yi wa Rimsha wannan maganar, ta san cewa ruwa na zuba, karar ruwan ba zai bari ya ji maganar ba, shiyasa ta yi.

Ganinta a garden É—in yasa shi sakin kayatatcen murmushi yana faÉ—in "Rimsha yaushe kuka dawo?" "Yaya Imran yanzu ba jimawa muka dawo". Kusa da ita ya zo ya zauna "Ai mun dawo daga gidan Abbi na tambayi Areef ina kike, sai ya ce mini kun fita ke da Aseef, fatan dai kun dawo lafiya?" Jinjina mishi kai ta yi tana faÉ—in "Lafiya lou Alhadulillah".

"Kina jin yunwa ko?" ÆŠan satar kallon Jellyn ta yi kafin ta gyaÉ—a mishi kai alamar e "Am so so sorryyyyyyyyyy, gaskiya rayuwar gidan nan akwai wahala a gareki, ke baki iya cin abincinsu ba, su kuma basu son warin naki, ni kinga na iya cin abincinsu dan a kasarsu nayi karatu, amma ba komai ai kwanaki kaÉ—an ya rage mana a nan É—in, zaki jure ko?" GyaÉ—a mishi kai ta yi alamar e.

"Good to tashi ki ɗauko mayafinki mu je gidan Akil a tare, tun da dai ke kince baki son abincin restaurant, ai aiki ya gammu da yawon zuwa gidan Akil ko gidan Abbi ɗaukar abinci". Ɗan motsa lallausan lips nata ta yi tamkar wadda take son yin murmushin, nan take dimple nata dukka biyu suka lotsa, wani irin fitinannen kyau na ɗaukar hankali ta kara, tana ƙoƙarin mikewa ta nufi cikin gida dan ɗauko mayafin nata, sai ga Aseef da Areef sun jero tamkar wasu taurari, sai walwali suke yi, Lion ya gaji da surutunsu ya haɗasu da Allah su fita mishi a ɗaki, sanin girman Allah yasa suka hakura suka kyale shi ya sha iska, ba dan haka ba, yau ba zasu rabu da shi ba.

Har wani daddaɗar nauyayyar ajiyar zuciya ta sauƙe ganinsu, ta rasa me yasa take jin tsantsar farinciki idan ta gansu, ta rasa me yasa take jin duk wani damuwarta ya gudu da zarar ta yi tozali da kyawawan fuskokinsu masu ɗauke da annuri ta murmushi. A ɓangaren shima Areef, ganin ta a wajen yasa ya sauke nauyayyar ajiyar zuciya da ta sanya Aseef juyowa yana kallon shi.

Gefenta ya je ya zauna shi kuma Aseef ya zauna a wani kujera na daban, ita kuma jelly tana ta faman kumbura kuma tu, ita a dole ta ji haushin kula Rimsha da Imran ya yi.

"Our Queen me yake damunki? Waye ya taɓa mana ke?". Cewar Areef, da kallo ɗaya ya yi mata abinku da jami'i, tuni ya fahimci akwai abin da yake damunta.

ÆŠan zaro idanu Imran ya yi yana kallonta, har lokacin kuma shi dai bai ga alamar wata damuwa a face nata ba, shi ma Aseef da kallo É—aya ya yi mata ya ga damuwa kwance a cikin idanunta, da yake idan baku manta ba, Triplets akwai baiwa, akwai kwakwalwa, sun gaji brain wajen Dr William jacop.

"Yaya Areef babu abin da yake damuna fa". Ta yi maganar tana kara ƙaƙalo murmushi a kan fuskar tata, dan ta tabbatar musu da babu komai ɗin.

Kallon Areef Aseef ya yi while shima Areef É—in shi yake kallo, daga bisani suka juya suka kalli Imran wadda shima ya tsaresu da ido sosai, yana kallonsu, yana son sanin me yake damun kanwar tasa.

"Yaya Imran mu tafi ɗaki barci nake ji" muryar Jelly ce ta katse musu shirun da suka yi suna tunani, kallonta gabaɗayansu suka except Areef, shi dawo da kallonsa a kan Rimsha ya yi, a nan ne kuma ya fahimci jelly ce matsalar gimbiyar tasu, domin kuwa wannan magana da jelly ta yi, ta sake jefa fuskar Rimsha cikin damuwa da tunani, fahimtar hakan yasa ya ɗan yi shiru yana tunani mafita, tabbatas ba zai taɓa yarda da duk wani abin da zai sanya Rimsha cikin ɓacin rai ba, zai yarda da komai a gidan amma ban da hakan.

"Rimsha me zaki ci in sayo Miki". Cewar Imran, ya yi maganar ba tare da ya tanka maganar jelly da ta faɗa na su tafi ɗaki ba, sai dai bai gama rufe baki ba jelly ta kuma katse shi da su tashi su tafi ɗaki, ta yi hakan ne kuma dan kada Imran ya sahowa Rimsha abinci ko ya ɗauketa su fito, kishi kumallon mata, ko wace mace tana da shi, sai dai na wata ya fi na wata, ayi wa Jelly uzuri, ta ga hankalin yaya Imran ɗin ta na ƙoƙarin rabuwa biyu ne, ta ga yafi kula da Rimsha sama da ita da take matarsa, kuma take gani ita ta kasance kanwarsa, Rimsha kuma babu abin da ya haɗa su tun da bata ma san waye bappan nasu Hosain ba.

"Jelly ki bari bari na je ya sayowa Rimsha abinci ko na É—auko mata a gidan Akil, ki je É—akin ki kwanta ina zuwa". Babu kunya bare tsoron Allah ta sa mishi kuka wai cikinta na ciwo, shi dai Areef binsu kawai yake da ido yana karantarsu, shi kuma Aseef ganin tana kuka yasa ya tambayi Imran É—in menene matsalar, Shi Areef duk da baya jin Hausa, zama yau da gobe da su, yasa idan suka yi magana yana fahimtar in da maganar ta dosa, sannan kuma yana karantar yanayinsu, ta hakan yake gane a kan me suke maganar.

Kanta Imran ya yi yana tambayarta ko lafiya, kuka take yi tsakaninta da Allah, hawaye wani na bin wani ta dafe cikin nata.

A hankali Rimsha ta faki idanunsu ta miƙe tana son barin wajen dan kada zuciya ya ɗebeta ta kifawa jelly mari, dan kayan haushin jelly ya isheta, sanin halinta da zuciya yasa bata son haɗuwa da Jelly'n, dan bata son suyi faɗa a matsayinsu na ƴan uwan juna.

Sosai Areef ya ji babu daɗin hakan, dan yasan Rimsha bata da wanda yafi Imran, shine farincikinta a yanzu, amma wata tazo tana kutse a tsakaninsu. Tana miƙewa ya riƙo hannunta, da sauri ta juyo duk da ta san shi ɗin ne, girgiza mata kai ya yi alamar a'a ta dawo ta zauna, ba musu ta koma ta zauna, shi kuma Imran ya ɗauki jelly a kan zai kaita ɗaki ya rarrasheta ya dawo.
Chapter 57 · 0% Book details