Sashe 71
Triplets Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kusa da A'isha da bata ko motsi Adiva ta zo ta zauna tare da zuba mata idanu, bayan ta yi wanka ta fito, kayan Adiva ta sake sakawa a jikinta kafin ta haye gadon Aisha É—in, jugum jugum suka yi suna kallonta, fuskarta ya yi wani irin haske tamkar babu rai a jikinta, ga face É—in natan ya kumbura kamar an hura balo balo, tunani Jehan take yi anya ba wani cutar wani alhajin ya sanyawa A'isha ba kuwa? Ji yadda take ta kumbura kamar ana hurata, anya ma akwai rai a jikinta kuwa? Anya akwai sauran numfashi a tattare da ita kuwa?. Sai tunane tunane take yi, abin ya É—aure mata kai, ga shi ita ba iya gane matatciya da rayayyiya zata yi ba, basu da wata madafa, ba magani ba asibiti.
Sun jima zaune a wannan yanayi kafin a kira sallar mangariba, Jehan ce ta fara tashi ta É—auro alwala ta fito, tana fita Adiva ta shiga, daga cikin su Æ´ar gwal kuwa, babu wacce ta sake shigowa cikin É—akin nasu, basu sake jin É—uriyar kowa a gidan ba, tamkar babu kowa.
Bayan sun idar da sallar mangariba sai suka zauna saman daddumar suna karatun Alqur'ani mai girma, har sai da aka kira sallar issha suka tashi suka gabatar da sallah, Maryam da Adiva suka je suka É—auko musu abinci bayan sun idar da sallar kenan.
A tare suka ci abincin, Allah sarki yau ban da A'isha, abin gwanin ban tausayi, bayan sun gama ci, ko wace ta haye saman gadonta, ita kam Adiva gadon jenan ta haye dan tana tsoro, addu'ar barci suka yi, ba jimawa Adiva da Maryam suka yi barci, ita kuwa Jehan yadda taga rana, haka ta ga dare, ta kasa rintsawa, Allah ne kaÉ—ai yasan me take tunani da bata yi barci ba, har wa yau A'isha bata motsa ba.
Washegari da safe kamar yadda suka saba, bayan sun yi sallar asuba suka gyara ɗakin nasu, suka yi wanka sannan suka zo suka zauna saman gadajensu, sai latsa waya Jehan take yi kamar mai tura wani saƙon.
Da misalin karfe tara na safe, suna zaune jugum jugum sun tasa A'isha a gaba, har lokacin bata motsa ba. A hankali aka turo kofar ɗakin nasu, wata hamshakiyar mace ce, mace wadda ta amsa sunanta mace, sanye take da wata shegiyar lace wadda ta amsa sunanta lace, ta haɗu lace ɗin nan, da alama zata yi bala'in tsada, wuya da hannayenta duk shaƙe suke da kayan ado na gwalagwalai, fara ce tas, amma farin mai ce, tana da faɗin fuska sosai, kafarta na sanye da wani tsadadden haɗadɗen plat shoe mai bala'i kyan gaske, ta ko'ina a jikin matan nan dukiya ce a narke a wajen, kanta ba ɗankwali, ta zuba uban attachment har baya, da kallo ɗaya zaka yi mata kasan ba bahaushiya bace, in ma bayarabiya or Ebo, egala, ɗaya daga ciki dai, ga wani uban make up da ta sha, eyelashes nan ba'a magana, kamar bindin kaza, hancin nan nata a haje a fuskar tata, irin matan nan ne masu cika ido, idan ka gansu sai sun cika maka idanu ta yadda zaka kasa yi musu gardama a kan abu, akwaita kuma da katon tunbi kamar mai ciki wata tara, tana da kiɓa ba cancan sosai ba, idanunta dara dara, irin waƴan nan idanun da suke tamkar a waje haka, gula gula da su, gasu jawur tamkar ƴar shaye shaye, sai tashin wani irin warin maganin gargajiya take yi, da alama wani turaren magani ta banka a jikin nata, dan ga kamshin perfume nata a gefe, shi kuma maganin warinsa na gefe.
Babu ko sallama ta kutso cikin É—akin, zuba mata idanu suka yi har ta iso wajen bakin gadon nasu, tun da suka É—aura idanunsu a kanta suka kasa É—aukewa, da alama kuma gabaÉ—ayansu sunyi la'asar, duk jikinsu ya mutu tamkar wani abin ta yi musu, da alama dai ba haka kawai ta shigo ba.
Gefen gadon ta zauna, cikin sanyin murya ta fara magana cikin harshen turanci, da alama babu Hausa a bakinta, "My daughters ya kuke ta kallon mummynku haka? Tamkar kunga wata bakuwa daga wata duniya? Ba zaku gaishe ni bane? Mummynku ce fa, ni ce mahaifiyar ku yanzu". Har suna haɗa baki wajen ɗaga mata gaisuwa, har lokacin kuma basu kawar da kallonsu daga kanta ba, wani irin shu'umin murmushi ta saki "Yauwa daughters ko ku fa? Ai yana da kyau ku rinƙa respect na mum ɗin ku, Jehan me ya same ki naga bakinki kamar ya ɗan kunbura?".
Hannu ta kai ta taɓa bakin nata tana faɗin "Mummy babu komai" "No daughter ki gaya mini idan wata ko wani ne suka taɓaki a gidan nan, yanzu zan sanya ayi musu hukunci!" Girgiza kai ta shiga yi tana faɗin "Da gaske mummy babu komai".
Dawo da kallonta kan A'isha dake kwance tamkar gawa ta yi, a É—an ruÉ—e ta furta "Oh my god, me ya sami my daughter A'isha kuma?". Cikin sauri Adiva, Jehan suka haÉ—a baki wajen cewa "Muma bamu sani ba mummy". MiÆ™ewa tsaye ta yi, da ganinta kasan anci duniya da tsinke, bariki ta zauna, goggiya ce, duk wani tantiranci ta iya shi, makirci, kirsa suma sara mata suke yi, nan take ta nuna musu ta birkice, ta shiga tsantsar tashin hankali da halin da A'ishar take a ciki, hankalin ya yi mummunar tashi, har da wani kyarkyatar karya, tare da ciro wayarta ta danna kira, cikin wani yare ta yi magana, bayan ta gama wayar ta koma ta zauna tare da fara shafa fuskar A'ishar tana faman ambatar "Oh my daughter, yau ina zan sa kai'na, dole a zo a kai mini ita Hospital, oloni". Bayin Allah sun É—auka da gaske ne, ko da yake ba wani abin da za su iya yi, ta rufe musu baki ruf, yanzu sai abin da ta ce shi zasu yi, ba su isa su tsallake maganarta ba....... INNALILLAHI WA INNA ILAIHIR RAJIUN JUSTICE FOR JEHAN, ADIVA AND MARYAM, SUN SHIGA KOMA SUMA, DUK WANI MAI IMANI DOLE YA YI MUSU KWALLAH, SUN SHIGA HANNUN WANNAN MAKIRA.ðŸ˜
Ba'afi minti 5 da yin wannan waya da ta yi ba, sai ga wasu mata sun shigo cikin É—akin su biyu, mata ne amma masu kirar maza, duk layinsu É—aya da hajiyar, cikin wannan yare nasu ta sake yi musu magana, tsawon minti uku suna maganar, daga bisani suka É—auki A'isha suka fita da ita, Jehan, Adiva, Maryam, babu wacce ta iya tambayar ina za'a kai A'ishar, sun zuba ido kawai suna kallo, har aka fice da ita, juyowa garesu Hajiyar daÉ—in ta yi. "My daughter's kada ku damu magani za'a je a yi mata, Hospital zasu kai ta, dole nayi jinyar daughter ai, kada ku ji komai, nan ba da jimawa ba, zata dawo gareku, yanzu dai kunci abinci ne?" Har wa yau cikin harshen turanci ta yi maganar. E suka amsa mata da shi.
Girgiza kai ta yi tana faɗin "No daughters bari na sa a kawo muku wani abincin, ai ina gidan nan, kada ku damu dole zaku yi abin da kuka ga dama, tun da mummynku ta dawo shikenan ai, zaku ji daɗi, Jehan idan kun gama cin abinci ki shirya mu je super market a sayo miki kayayyaki masu shegen kyau da kuma sauran duk abin da kike buƙata". Da murnarta ta amsa da okey, Allah sarki kun shiga koma sai addu'a.
Waya ta sake yi a kan a kawo musu wani abincin, a wannan karonma da wannan yaren nasu ta yi maganar ba da English ba, da alama dai bata son su san me take faÉ—e ne yasa take magana da wannan yare, hakan na nufin magana a kan A'isha ma wani abin ta shirya kenan, babbar magana, lallai wannan mata ta kai duk in da ake neman makira shegiya.
Matan da suka fita da A'isha, sune suka kawo musu abinci, tasa su ta yi a gaba da daɗaɗan kalamai masu ratsa zuciya, har sai da suka cinye abincin nan tas, daga maganar Hajiyar daɗi zaka san tantiriyar karuwa ce mai lasisi, dan ta iya tsara zance da daɗin baki sai ka ce karuwan zamanin farko, yanzu zata saye zuciyar mutun ko da bai yi niya ba, sai wanda Allah ya tsare, hakan yasa take samu galaba sosai a fannin jawo matan aure zuwa wannan tsinanniyar harka, da wannan daɗin bakin nata, ga shegen iya zuba zance, ta fito a tsohuwar karuwar tata, nan take take saye zukatan matan aure, ta halakar da su, ta kaisu ta baro, ya ilahi ya lillihi, Allah ka kare mu da mu da zuria'ar mu baki ɗaya, ya Allah kasa duk halin da zamu shiga imani da tsoronka ya tabbata a zuƙatanmu, ire iren su Hajiyar daɗi su suka fi komai yawa a rayuwarmu ta yau, Allah ka yi mana tsari da su.
Sai da ta tabbatar sun ƙoshi haniƙan, da kanta dan tsabar makircin ta buɗe musu ruwan sha tare da lemon kwalba, su kuwa bayin Allah komai tace, da okey kawai suke amsa mata, abin gwanin a zubar musu da kwalla, bayan sun kammala komai ta yi musu sallama har da basu sunbata a goshi, da wani bakinta da ya yi bakinkirin saboda busar shisha da su sigari da sauran kayan buguwa, basu ji kyamar bakin ba, haka suka bari ta sumbace su ta fice daga ɗakin tana wani cewa "Am going to miss you my daughter's, amma zan dawo nan da two hours". Har suna rige rigen amsa mata da okey.
Tana fita Jehan ta kwanta tana sauke numfashi cikin kwanciyar hankali, suma ko wacce ta haye saman bed nata ta kwanta, da alama sun mance da A'isha, an rufe musu babinta, sai murna jenan take yi zasu fita sayayya da mummynsu wato Hajiyar daÉ—i, tashin hankali da ba'a sanya mishi rana.