Sashe 106
Triplets Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Dan haka nan take ta buɗe musu aiki mai gabaɗaya "Ni ban taɓa yin aure ba, Aliya shegiya ce kuma ga ubanta nan a gabanku yanzu aka gama labarai a kansa, yanzu ni bana jin komai a raina, ko yanzu na mutu hankalina ya kwanta, ABUBAKAR SALAHUDDEEN bakin azzalumin, kune kuke kallonsa kamar mutumin kirki, saboda ya sanya fatar ɓauna ya lulluɓewa duniya laifukan da yake aikatawa, da Abubakar da Farooq wlh ko sun tuba sai sun ɗanɗani azaban Allah, dan kuwa akwai da yawan al'umma da suka mutu ta sanadiyarsu, waƴan nan azzaluman guda biyu, wlh sai Allah......" Bata kai karshen maganar ba A'A ya ɗaga hannu zai zabga mata mari, cak ta riƙe hannunsa tana kare mishi kallo.
"Saboda ina faɗar gaskiya a kan ubanka shi ne zaka mare ni? To kai kanka ka kalli kanka da kanka ka kalli Aliya dake kwance tana barci zaka iya banbanta fuskarka da tata ne? Bari ka ji idan kayi kuskuren marina, wlh, wlh, wlh, sai na kwantowa gabaɗaya juri'arku ruwan da ba zaku iya tsayar da shi ba, wlh sai na bankaɗo dukka laifukan ubanka da ɗan uwansa wa duniya, sai ya zama baku da idanun fita ku kalli jama'a saboda kunya, wasunku ma bakin cikine zai kashe su, idan kuma kace ba haka ba to Bismillah zaka gane shayi ruwa ne wlh, dama na rufe ne dan saboda kada ya kashe mini ƴa ta, na ɓuya ne dan kada ya kalli Aliya ya kasheta, shiyasa ban fito na nunawa duniya ɓarnar da suke yi ba, amma yanzu kabi a hankali!!". WANNAN SHI NE TASHIN HANKALI, BABBAR MAGANA.
Wani irin azababben kululun bakin cikine yasa A'A zubewa kasa tamkar gawa baya numfashi, kansa su Abbi suka yi suna ambatar sunansa, amma ina ko motsawa bai yi ba, ruwa Irfan ya É—auko mai sanyi a fridge ya zo ya zuba mishi, amma ina ko motsi bai yi ba, daga karshe dai suka kwashe shi zuwa asibiti dan ceto rayuwarsa.
Ita kuma maman Ayla sama ta haura ta nufi ɗaki abinta, dan yau zuciyarta fes, Aunty kam taga tashin hankali yau, Hanan kuwa tun da aka fara hayaniyar ta bar palon, ta koma bedroom nata, dan bata son hayaniya ita ma,. Yanzu babbar abin tambayar a nan shi ne, a ina maman Ayla ta san mahaifin A'A? Menene yasa kuma ya ce ba cikinsa bane? Akwai lauje cikin naɗi, amma muje zuwa, zata warware mana komai ta bamu labarin yadda akayi komai, yanzu dai bari mu leƙa gidan Lion dan ganin wani hali suke ciki, wata kila kafin mu dawo wannan family sun ɗan sami kwanciyar hankali.
Misalin karfe 8 na safe, shirye suke cikin shiga iri É—aya, sai dai wandon Areef ya fi shiga kalar brown sosai, na Aseef ya yi light, zaune suke a garden da alama dai shirin zuwa wani wajen suka yi, zubawa Aseef dara daran ash eyes nasa ya yi yana kallon yadda fuskarsa take wani kyalli, da alama yana cikin farinciki over, sai aikin latsa waya yake yi.
"Wai Aseef yana ga sai wani fresh kake yi ne? Seriously Naija ta karɓeka kai da Lion, sai wani kyalli face naka take yi, zo ka gaya mini me sirrin ne?". Bai ɗagoba, yana ta faman aikin latsa waya, sai murmushi yake yi Heartbeat ta yi kira. "Kana ji Areef, Heartbeat ce ta yi mini ciki, shiyasa kaga nake wannan kyan". Ya kai karshen maganar tare da miƙewa dan Akila ta ce yazo yanzu. Areef ya gama fahimtar tun da Aseef ya fara soyayya ya dawo mara mutunci, da an yi mishi magana zai shere mutane, ko kuma ya mayar musu da amsar iya shege, yanzu me na wani cewa wai heartbeat ce ta yi mishi ciki daga tambaya? Gaskiya abin da ban haushi.
Yana can yana tunani sai ya ji tashin motar ɗan uwan nasa, alamar da gaske barin gidan zai yi, tafiya zai yi kenan, miƙewa ya yi da sauri ya nufe shi dan tare zasu je su gaida Ammie ya kalli heartbeat ɗin shi ma.
Lokacin da ya isa wajen, Aseef É—in ya kashe motar ya fito zai nufi cikin gida, "Ina kuma zaka je mu tafi mana?" ÆŠan juyowa ya yi yana faÉ—in "Yauwa Areef zo dan Allah, zo muje ka kallah wani abin". Ba musu ya bi bayansa, kai tsaye É—akin da Jehan take suka nufa, ita kuma Rimsha, sai zuba barci take yi abinta, shi ma Lion haka, da alama dukkansu a tsananin gajiye suke.
Da sallama ya shigo cikin ɗakin, tana zaune a bakin gado ta farka, tun da Areef ya ɗaura idanunsa a kanta ya ce tabbas gaskiyar Aseef ne, duk yadda aka yi wannan jinin Uncle Hosain ce, akwai alaƙa mai ƙarfi a tsakaninsu, dan kamar ta yi yawa, amma bari su je wajen heartbeat su dawo, tun da Rimsha tana nan zata warware musu komai ai.
Sannu suka yi mata, sai binsu da idanu kawai take yi, tana mamakin me kuma ya kawota gidan Turawa? Ko dai a kasar turai take ne? To yaushe a ka kaita can? Iya saninta a Nigeria take. Ganin taki yin magana ne yasa Areef ya ce "Kila bata magana ne, yanzu dai muje mu dawo, zan gayawa sister ta kula da ita kafin mu dawo sai mu san abin yi". Okey Aseef ya amsa, ya kuma ji matsananci daɗi da Areef ya yarda da cewa tabbas tana da alaƙa da uncle ɗin su, ya yi murna da hakan, juyawa suka yi suka fice daga ɗakin zuwa na Rimsha, ganin sai zuba barci take yi ne yasa Areef ya rubuta massage a wayarta a kan idan ta tashi akwai bakuwa dake ɗakin Imran, ta ɗan taimaka mata kafin su dawo, daga haka suka nufi waje dan su je wajen heartbeat, Lion kuwa tare suka yi sallar asuba da shi, dan haka sun san yana lafiya yana barci, sai ba su shiga ba bare su tashe shi suka wuce.
Sai misalin karfe 9 Rimsha ta farka daga barcin gajiya da take yi, da kyar ta sauko kasa ta nufi toilet dan yin wanka.
A gurguje ta yi wanka tare da shiryawa cikin kananan kaya ta fito da nufin ta duba su Areef dan su ci abinci yunwa take ji, ganin babu kowa a gidan ne yasa ta dawo cikin É—aki ta É—auki wayarta dan ta kira Areef É—in, a nan ne ta ci karo da sakon da ya ajiye mata na bakuwar da suke da ita, fasa kiran nasa ta yi ta ce bari ta fara duba bakuwar tana zuwa, fitowa ta yi ta nufi bedroom É—in.
Bakinta ɗauke da sallama ta shiga, a sukawane ta sanya hannu tana murje idanunta dan ta tabbatarwa da kanta abin da take kalla gaskiya ce ko ba gaskiya bace, ita ma Jehan ɗin a razane ta miƙe tsaye tana mai murza idanunta dan ta tabbatarwa da kanta ba mafarki take yi ba.
"Jehan". Rimshar ta ambaci sunanta, tare da tafiya da gudu ta rungumeta, ita ma rungumeta sosai ta yi suka shiga kewaye É—akin suna ruwan hawaye. "Rimsha dama kina raye?" Ta faÉ—a tana kwallah. "Ina raye Jehan, ina raye, dama kema kina nan Kaduna? Shi ne Sadiq bai gaya mini ba".
"Rimsha bana Kaduna, dogon labarine zan baki daga baya, yanzu dai ina su mummy?" Ta yi maganar tana raba jikinsu. "Ban san in da suke ba, daddy kawai na san in da yake". "What daddy kuma?!!" Ta faÉ—a tana zaro idanu kamar zasu faÉ—i kasa, "E Jehan daddy, yana nan, yana raye bai mutu ba". Zata yi magana kenan suka ji jiniyar motocin Æ´an'sanda ya karaÉ—e ko'ina a cikin anguwar, da alama jiga jigan Æ´an'sanda ne, da alama kuma suna da yawa, dan motocin nasu manya ne, jiniya ya karaÉ—e ko'ina tamkar filin yaki suka nufa, kallon juna suka yi, "Zo mu je waje mu gani menene". Cewar Rimshar, da yake Jehan bata da tsoro ko kaÉ—an a fili, ga karfin hali da dakiya sai ta bita suka nufi waje dan suga menene.
Daga bakin kofar palon kasa suka tsaya suna hangen gate É—in gidan, amma kafin su fito sai da Jehan ta sanya doguwar rigar Rimsha, dan idan baku manta ba, ba wani kayan arzikine a jikinta ba, daga three quarter sai Æ´ar vest, shiyasa ta ce ba zata fita a haka ba duk da bata san su waye ne a gidan ba, sai da Rimsha ta É—auko mata doguwar rigarta É—aya, ta sanya sannan suka nufo wajen.
Can suka hango gateman yana dirama da Æ´an'sandan a kan lallai ba zasu shigo cikin gidan nan ba, su kuma sun kafe sai sun shigo, daga Rimsha har Jehan basu san menene yake gudana ba, garama Jehan bata yi mamakin ganin Æ´an'sadan ba.
Waya gateman ɗin ya yi wa Lion da ƴan'sandan suka matsa, a lokacin shi ma ya tashi daga barci, ya fito daga wanka kenan, yana tsaye a gaban mirror ɗaure da towel a kugunsa, umarnin ya bawa gateman ɗin da ya bar ƴan'sandan su kama yarinyar tun da a kan aikinsu suke, shi yasan menene doka, dan sune doka, sune suke tsawatarwa da abi doka, tun da sunce kisan kai ta yi to su kamata, kuma sai ya ji dalilin da yasa su Aseef zasu kawo mishi mai laifi gida. To fa kada ku ga laifinsa, a kan dai'dai yake, doka ce dole a matsayinsu na masu doka su girmama dokan kafin na kasa da su subita, ba zai ce kada su kamata ba tun da shi bai san wacece ita ba, bai kuma san gaskiya a kan me ya faru ba, kuma kunga news ɗin da suka baza a gari a kan daɓa wa ABUBAKAR SALAHUDDEEN ɗin wuka ta yi a ciki, kuma ko su Aseef ne zasu yarda da yes ta daɓa mishi ɗin, dan kuwa a kan hanya suka ganta ana binta, basu san daga ina ta fito ba, sai dai idan sun yi bincike mai tsanani ne suna iya gane gaskiya, amma yanzu dai duk yarda zasu yi akan abin da ta yi kenan, babbar magana. WANNAN ABIN DA ƊAURE KAI YAKE AMMA MUKE ZUWA, DAN JIN DALILIN DA YASA AKA JUYA LABARIN YA KOMA KARYA, SUKA BINNE NA GASKIYAR.