Sashe 34
Triplets Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Suna tsaka da hira misalin karfe 4:30 bayan sun yi sallar la'asar, masoyin É“oye ya kira Akila, cikin sauri ta É—auki kiran, tare da manna wayar a kunnenta.........â¤ï¸â¤ï¸TRIPLETSâ¤ï¸â¤ï¸
E13-14
Suna tsaka da hira misalin karfe 4:30 bayan sun yi sallar la'asar, masoyin ɓoye ya kira Akila, cikin sauri ta ɗauki kiran, tare da manna wayar a kunnenta.
"Heartbeat yau fa tun da safe da muka yi magana ba mu sake yi ba, ina ka shiga ne?" Kamar dai kullun kun san a shagwaɓe ta yi Maganar.
Daga ɗayan ɓangaren ya amsa mata shi ma a shagwaɓe. "Am so so sorry my heartbeat, nasan na yi laifi, to amma ba Rimsha ta ɗebe maki kewa ba? Ai Rimsha ta fanshi laifi na ko?". Turo baki ta yi tamkar tana a gaban shi. "Yanzu Heartbeat ita kuma Rimsha a ina ka santa? Yaushe kuma kasan mun haɗu da ita?". "Kai heartbeat to ai ita Rimsha kanwarmu ce, yanzu dai bar zancen Rimsha yakika wuni? Ya fama da kewa na?". Shiru ta yi a cikin zuciyarta tana maimaita kalmar ita Rimsha kanwarsu ce? Me hakan yake nufi kuma?.
Jin tayi shiru ne yasan ta faÉ—a duniyar tunani, idan ya canka daidai kuma, tunani take yi a kan maganar da ya ce na Rimsha kanwarsu ce, dan haka sai ya katse mata tunani da cewa "Heartbeat kamar yadda kika ji na faÉ—a Rimsha kanwar mu ce, yas kanwar mu ce kamar yadda kike kema kanwa a gare ni, abin da yasa nace Rimsha kanwar mu ce kuma, ba komai bane face dan saboda na fita shekaru, kuma kema kin fita shekaru, kin ga kuwa ai kanwarmu ce ni da ke ko? Wai kin manta duk abin da kike so nima zan so shi ne? To idan kin manta na tuna miki, a cikin zuciyata na ji cewa kina Kaunar Rimsha sosai, shiyasa na kirata da kanwarmu kai tsaye".
Murmushi ta sakar mashi kafin ta ce "Wai ka saya mini goribar da nace ne?". Kai tsaye ya ce mata "Prof bai kawo ba tukun nan". Da yake bata san waye suke cewa Prof É—in ba, sai ta ce "Tom shikenan ka ce mishi ya haÉ—o mini da aduwa". Maimaita sunan aduwar ya yi kafin ya amsa mata da okey.
Ita dai Rimsha kamar Tv haka ta mai da su, sai kallon ikon Allah take yi, ji yadda Akila take wani tsuke fuska tana zuba shagwaɓa tamkar wata baby, lallai ma, abin mamaki ma ya bawa Baiwar Allah nan Rimsha.
Ita kuwa Akila da alama ta mance da Rimsha a cikin ɗakin, kamar yadda suka saba da sahibin nata, ta zage sai zuba hira da shagwaɓar ta take yi har sai lokacin sallar mangariba suka yi sallama, ɗagowa da zata yi already Rimsha ta yi barci a gefenta, bata san time da ta saki cool murmushi ba.
A hankali ta tashi Rimsha É—in akan su je su yi sallar mangariba ba, da kyar ta iya tashi dan barcin yana a idanunta sosai.
Bayan sun yi sallah ne suka koma suka zauna a saman gadon suka cigaba da zuba hirarsu kamar yadda suka saba.
Wayar Rimsha dake ɗaure saman bedside drawer ne ya fara kara alamar shegowar kira, kasan cewar Akila ta fi kusa da wayar sai ta ɗauko ta miƙa mata. Anaya ce mai kirar tata, cike da farinciki da zumuɗi ta ɗauki kiran.
"Hello Anaya? Ykk?" Da fara'a ita ma Anaya ta ce "Lafiya lou Rimsha yasu Yaya Imran naki?" "Suna nan lafiya lou ina su yaya Feroz da mummy, daddy, Uncle Shitu da Zaira?" "Suna nan lafiya Uncle Shitu gobe da asuba zai je Maiduguri ya duba su Gwaggo Aisha, tun da suka koma Maiduguri basu sake dawowa ba, ina kewarsu wlh, gobe daddy ne zai kai mu school dan ya zo yau, da uncle Shitu ya gaya mashi zai je duba su Gwaggo Aisha, shi ne ya zo dan ya kula da mu kafin uncle Shitu ya dawo nan da kwana biyu". Ta kai karshen maganar tana É—an dariya.
Nasan baku gane suwa ye Anaya take Magana a kai ba, Gwaggo Aisha dai ba kowa bace fa ce Gwaggon Jehan, sai mummyn su Rimsha, na san zaku yi mamakin ya aka yi suka haÉ—u da Uncle Shitu da kuma daddy Anaya, to ku saurara, ya akayi suka haÉ—u da daddy Anaya zai zo maku a gaba, shi kuma uncle Shitu dama kun san already yana tare da daddy Anaya kafin su mummy su zo, wai shin menene yake tsakanin Uncle Shitu da su mummyn Rimsha? Uncle Shitu yaya ne ga mummy'n Rimsha, É—an bappanta ne, sai dai shi Mahaifin mummy Rimsha ya yi wayo ne a Niger ba'a Nigeria ba, tun yana saurayi ya tafi Niger kasuwanci, daga nan bai sake dawowa Nigeria ba har sai da ya auri mahaifiyar mummyn Rimsha wadda ta kasance Æ´ar Niger É—in ce, bayan auren nasu ne ya É—aukota zuwa Maiduguri Nigeria dan taga Æ´an uwansa, lokacin da ya zo kuma ya samu yayan sa Mahaifin uncle Shitu ya samu karuwar yaro wato uncle Shitu, a lokacin har ya yi wayo, dan zai shekaru 10 haka, da suka zo komawa Niger ya so komawa da uncle Shitu, amma yayan nasa yaki, ba dan yaso ba ya koma ba tare da uncle Shitu É—in ba, tun daga lokacin kuma bai sake zuwa Nigeria ba har sai da suka haifi Mummyn Rimsha tana da shekara biyar a duniya suka zo Nigeria, a lokacin uncle Shitu yana da 15 to 16 years, da suka tashi koma a wannan karon, sun tafi da uncle Shitu É—in, dan ya je ya ga in da suke ya yi masu hutu ya dawo, ba Æ™aramin jin daÉ—in zaman Niger uncle Shitu ya yi ba, ba dan yaso ba ya dawo NIGERIA, tun daga nan kuma ba su sake jin ya su mummyn Rimsha suke ba, har bayan shakaru 7, lokacin mummyn Rimsha tana da shakaru 12 zuwa 13 a duniya, shi kuma uncle Shitu 22 to 23 years yake da shi kenan, a lokacin ya shirya yaje Niger É—in bisa umarnin Mahaifinsa akan ya je ya dubo mashi É—an uwansa ya yake, a lokacin yana 100 level karatu a Ahmadu Bello University, hutu yake zuwa Maiduguri, da yazo hutun ne ya je Niger duba bappan nasa, a nan ya sami mummunar labari na ce wa, bappansa Allah ya yi mashi rasuwa shekara É—aya da ta wuce, ya sha kuka ba kaÉ—an ba, ya so su dawo tare da mummyn Rimsha da mahaifiyarta, amma iyayenta wato kakannin mummyn Rimsha sun ki yarda, haka ya hakura ya dawo ya sanar da gida abin da ya faru, sun sha kuka sosai kuma sun ji haushin mahaifiyar mummyn Rimsha da ta kasa turo É—an aika ko ta nemi waya ta gaya masu rasuwar É—an uwan nasu, sun ji ba daÉ—i ainun, hakan yasa suka yi fushi suka ce ba zasu karÉ“o mummyn Rimsha É—in ba, sun yi fushi da mahaifiyarta, kun san Shuwa Arab su ma sun iya fushi ba kaÉ—an ba, daga nan kuma basu sake bibiyar ya Mummy Rimsha take ba, sun watsar da su, basu sake sanin ya suke ba sai yanzu da ta kai kanta da kanta ga dangin mahaifin nata, to shi ne suka sake sanyata a idanunsu..... KUNJI ALAƘAR DAKE TSAKANIN UNCLE SHITU DA MUMMY RIMSHA, YA AKAYI MUMMY RIMSHA TA AURI DADDY RIMSHA? YA AKAYI TA ZO NIGERIA? INA MAHAIFIYARTA? MEYASA BATA TAÆA ZANCEN MAHAIFIYAR TATA BA? MEYASA BATA KOMA NIGER BA BAYAN ÆATAR DADDY RIMSHA? DUK AMSA ZAI ZO MAKU DAGA BAKIN DADDY RIMSHA DA UNCLE SHITU, YANZU DAI NA FAYYACE MAKU ALAƘAR TA DA UNCLE SHITU NE A TAKAICE DAN KU GANE ME MATSAYINSA A WAJEN SU RIMSHA, DAN HAKA MU KOMA KAN LABARIN MU.
STORY💋
"Allah sarki Anaya ni dai ina son ganin Gwaggo Aisha nan naki, wlh ko dan takura mini da zancensu da kike yi ma dole naso ganinsu" . Ta yi maganar tana mai dafe kirjinta, ta rasa dalilin da yasa duk lokacin da Anaya take bata labarin ƴan uwanta sai ta rinƙa jin gabanta yana faɗuwa, kirjinta na bugawa da sauri sauri, wani lokaci har sai ta dafe kirji nata take samun sauƙi.
A ɓangaren ita ma Anaya duk lokacin data kalli Rimsha sai gabanta ya faɗi, da yake dukka dai yara ne sai ba wanda ya kawo komai a ransa, kuma sosai Anaya tana ganin muguwar Kamannin dake tsakanin Rimsha da kuma Gwaggo Maryam wadda ta kasace mummy Rimsha ɗin kenan, amma bata taɓa gayawa Rimsha ba, sau da dama tana zucci zuccin gaya mata tana yi mata kama da Gwaggon ta Maryam matar uncle ɗinta, sai dai idan sun haɗu sai hiran school ko hirar wani abin, Anaya ta na mancewa da zancen kullum.
"Rimsha In Sha Allah zaki kalli su Gwaggo Aisha, kin san me? ". A'a ta bata amsa. "Idan su Gwaggo Aisha suka sake zuwa zan ce daddy ya kawo ni gidanku mu ɗauko ki, kizo ku gaisa, jiya ma munyi waya da Gwaggo Aisha ta ce mini zasu zo azumi, kuma kinga azumi ya kusa, tun da an kusa babban zaɓe, to suna zuwa zan gaya miki, wlh suna da kirki kuma suna son mu sosai, musamman ma ni, gwaggon A'isha ta fi sona fiye da kowa, dan nayi kama da ita, naso su zauna damu a gidan nan, amma suka ce a'a, daddy ma ba yadda bai yi ba, sunki yarda suka ce sun fi son Maiduguri, shi ne kawai daddy ya barsu a can yana saya musu duk wani abin da suke so ya tura musu can, amma zan gaya miki gaskiyar meyasa basu son zama damu, wlh mummymu ce bata son su, tana zaginsu, shi ne suka ce zasu koma Maiduguri, kuma gwaggo A'isha ta ce kada na gayawa daddy mummy ta zagesu, da nace sai na gaya, amma sai na fasa dan kar gwaggo A'isha ta ji na daɗi". Anaya sarki magana, faɗi ba'a tambaye ki ba, sai mamaki Akila take yi na irin shegen surutun nan na Anaya, duk ta gama tune asirin gidan nasu kamar wadda aka tambaya, ta zube komai a faranti abinta.