← Book details Triplets Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 72 OF 121

Sashe 72

Triplets Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Masu karatu shin ku a tunaninku me ya sami D.P.O ne?, ko dai ta mance wace ce ita ne? Anya lafiya kuwa? Akwai cakwakiya gaskiya, in dai haka ne Hajiyar daɗi ta ɗauki hakkin jama'a sosai a kanta, da alama rufewa mutane baki take yi, ba ji ba gani, dole sai maganarta kawai kowa zai bi, sai Allah ne kaɗai yasan adadin mutanen dake cikin gidan nan wadda basu son zaman gidan, Allah ne kaɗai yasan adadin matan da suke kuka a cikin zuƙatansu basu son wannan harka, wlh ba kowa zai so yin harkan nan ba, kunga ita ma Jehan bata zo da niyar son wannan harka ba, hasalima yakarsu ta yi niyar yi, amma sai ga shi reshe ta juye da mujiya, da alama ta koma tana supporting nasu fa, ko ya makomanta zai kasance cikin wannan bakin gida? Mu dai je zuwa, mu waiwayi gidan Abba mu dawo.

GIDAN ABBA💋

A bakin kofar palo mai gadi ya ajiyewa Akila trolley tsarabar da Aseef ya kawo mata, da kanta ta ja zuwa cikin palon, yadda ta bar Ammie hakan ta dawo ta same ta, tsakiyar palon ta jawo akwatin ta kawo shi, zuba mata idanu Ammie ta yi tana kallon ikon Allah, bayan ta ajiye akwatin ta koma ta É—auko kwalin goribarta, shima a tsakiyar palon ta ajiye shi, sai wani sakin uban murmushi take yi baki yaki rufuwa, har lokacin Ammie bata tanka ta ba.

"Ammie heartbeat ne ya kawo mini wannan tsaraba fa". "To Akila heartbeat kuma?" Gyaɗa mata kai ta yi baki yaki rufuwa, "Waye shi heartbeat ɗin?" Kusa da ita ta zo ta zaune tare da kwantar da kanta a saman cinyar Ammien nata tana faɗin "Ammie zan baki labarinsa daga baya, yanzu dai ya ce zai zo ya gaishe ki idan ya sake dawowa, har da Abba ya ce zai je ya gaidar, bari dai na buɗe tsarabar nasa in gani". Ta kai karshen maganar tare da miƙewa ta nufi trolleyn, zuba mata idanu kawai Ammie ta yi tana mamakin ƴar tata, wannan murmushi dake a kan fuskar ya isa ya bayyanar da tsantsar kaunar masoyin nata da take yi.

Kwantar da trolley ta yi, tare da zuge zip É—in, da wata katuwar teddy ta fara cin karo, teddyn nan ta haÉ—u tamkar É—an mutun, fari tas da ita, a gaban teddyn daidai wajen wuyarta an yi rubutu da jan kala, Heartbeat+ Heartbeat, wani irin haÉ—aÉ—É—en murmushi ne ya kubce mata, yasan abin da take so ashe, ya santa da teddy akwai amana, ga wannan teddy ma ta tsaru iya tsuruwa, da alama shi ya bada yadda yake so aka buga mishi, sai kamshin perfume É—in Lion take yi, tsabar murna, jikinta har rawa yake yi wajen ciro teddyn daga ledarta, ta wani rungume a kirjinta tamkar Heartbeat É—in nata ta rungumi, da yake Ammie ta san halinta da shegen kaunar teddy's, sai bata yi mamaki ba, in dai a kan teddy ne fin haka ma zata yi, a wajenta wannan teddy ya fi mata komai dake cikin akwaitin, da kyar ta yarda ta ajiye shi ta fara fito da sauran kayan.

Nan ta sake cin karo da wani haÉ—aÉ—e flowers mai girma, ya kusa kai girman teddyn nata, flowers yana nan round, an shirya shi datsan datsan, ba karya shi ma ya yi, dukka kayan cikin akwaitin nan kamshin perfume É—in Lion suke yi, perfume É—in da idan ya kama kaya baya saki, sai dai abin mamaki Ammie bata ce bata son kamshin ba, sai ma shaka da take yi tana lumshe idanu, amma kuma da alama kamshin ya canza abubuwa da dama daga cikin gidan, duk wasu aljanu dake kusa sun gudu, har wani haske gidan ya kara yi, to me hakan yake nufi? Ita dai Ammie duk abin da waÆ´an nan dodannin basu so, suna sawa ita ma ta ji bata so, to ya akayi take son wannan kamshin, su kuma sun gudu da suka jita? Akwai ayar tambaya a nan gaskiya, ba mai amsa mana kuma sai ita Ammien da kanta, mu dai je zuwa.

A jikin flower an rubuta i really love you my heartbeat, da farin kala aka yi rubutun, shi kuma flower ja ne, a wannan karon Ammie ta kasa hakuri sai da ta ce "Heartbeat hala Bature ne ya kawo miki wannan kyauta?".

Cikin sauri da mamaki ta gyaÉ—a kai tana faÉ—in "Ammie shi ne ya aka yi kika gane to?". Karo na farko da ta saki cool murmushi, cak Akila ta tsaya tana kallonta, yau tsawon shekaru 15 kenan rabon da taga Ammiensu tana murmushi, kullum fuskarta a É—aure, tun tana yarinya da take mata wasa da dariya, daga ta fara girma Shikenan duk wata annuri ta kau daga fuskar mahaifiyar tasu, Allah sarki abin tausayi.

"Akila kenan ai soyayya da Bature daban yake da kowa a duniyar nan, su duk in da zasu yi soyayya baza su ɓuya ba, haka zalika kyautarsu a soyayya bata ɓuya, abin da zance miki na karshe shi ne ki shirya wajen tara flowers, dan zaki samesu babu adadi, idan ba Bature ba waye zai tsaya irin wannan soyayya, bahaushe zai wani sayo miki flower ne? Ai su ɓata lokaci da shirme ne a wajensu, yanzu idan kika ji uban tsadar wannan flower dake hannunki sai kin tsorata, da za'a canza kuɗi da kuɗin Nigeria, sai ya saya miki ƙaramin gida, tab ai ni nina san Bature, ke baki san tarihin Abbanki ba ko,? Lokacin da muke soyayya da shi, bashi da babbar kyauta biyun flower, a lokacin ma kakanku tana nan, kinga shi ma Abbanku har ya yi girma ya yi wayo yana cikin turawa kafin su dawo nan, to yanzu ne zama cikin Hausawa ya sauya shi, amma duk wani ɗabiunsa a baya irin nasu ne, shima Bature ne ai kinga ni".

Zaro wannan dara daran idanun nasu na gado ta yi, tana mamaki, ba abin da yafi bata dariya da mamaki wai Abbanta ma soyayyar flower ya yi, dan iya shege sai ta rufe idanu tana imagine ga Abba nan ya zo ya duƙa yana miƙawa Ammie flower, kamar wata zararriya haka ta tuntsure da dariya har da faɗuwa kasa, Ammie kamar wata aljana, ta san me take yi wa dariyar, sai ta shareta tamkar bata sani ba.

Sai da ta yi mai isarta ta tsagaita tare da ajiye flower ta cigaba dan fitar da sauran kayan, set na wasu É—ankara dankaran shegun chain ta fitar, a jere suke guda goma sha biyu, dukkansu na zallar madarar zinari ne babu mix, sai wani irin bala'in kyalli suke yi, suna É—aukar ido ba karya, ko wanne da irin design nasa, ita kanta Ammie ta tsorata da ganinsu, tsadar bala'i gaske suke da shi, ko wani guda É—aya bala'in tsada ke gare shi, ga shi har goma sha biyu set É—in baki É—aya ya saya mata, innalillahi wa inna ilaihir rajiun, ai Ammie bata san lokacin da ta tambayeta da É—an waye take soyayya ba, É—an shugaban kasa ne ko waye, da yake ita Akilar bata san tsadar chain É—in ba, sai bata wani É—aga hankalinta sosai da ganinsu ba,.

"Lafiya Ammie kike tambayata da waye nake soyayya?". "Akila kin san tsadar chain ɗin hannunki nan kuwa?" Girgiza kai ta yi tana faɗin "Ammie ba ɗan shugaban kasa bane, amma jikan shugaban kasa ne, kuma ke baki ganin news ma bare nace zan yi miki kwatancen shi ki gane shi, da kina kallon Tv ne idan na kira miki sunan ɗan uwansa zaki iya saninsu". Hannu tasa ta karɓi chains ɗin tana kara kare musu kallo, farkon soyayyarta da Abba ya saya mata irin shi guda ɗaya, ita kuma Akila set baki ɗaya tabɗijam.

Cigaba da watsa tarukucen kayan ta yi, a nan ta sake fito da diamond Ring mai bala'in tsada, kafin ta fitar da wani tambarin Heartbeat mai bala'in kyau fari tas, tamkar balo balo a ka hura, haka heart É—in yake, amma ba balo balo bane, yana da karfin da ba zai fasu ta daÉ—i ba har sai dai idan yanka shi za'ayi, Heartbeat+Heartbeat ne a rubuce a gaban heart É—in, an yi rubutun da jan kala, rungume heart É—in ta yi a kirjinta, ita duk tsadar waÉ—an nan abubuwa basu wani dameta ba, tafi kaunar teddy, Heart, da kuma flower nan, sun fi shiga ranta, Heartbeat nata ya san abin da take so da wanda bata so.

Miƙewa ta yi da sauri ta nufi bedroom nata ta bar Ammie da tulin kaya a gaba, har zata shiga sai kuma ta dawo ta ɗauki teddynta, sai murmushi take yi ta haye saman bed nata tare da fito da wayarta, massage ta yi mishi a WhatsApp a kan ya kirata yanzu.

Ba'afi minti ɗaya da shigar massage ɗin ba, sai ga kiransa da numbersa na ainahi ba unknown number ba, cikin zumuɗi ta ɗaga kiran, a shagwaɓe ta fara magana.

"Heartbeat, heartbeat Allah har na fara kewarka over". Cikin shagwaɓa shi ma ya fara magana "In zo in ɗauko ki mu dawo gidan mu ne?" Da yake su Turawa a wajensu dan budurwa ta dawo gidan saurayi da zama ba wani laifi bane, bai san nan kam Nigeria bane, kasar musulci, ko za'ayi hakan ma sai dai a ɓoye kuma ba da sanin iyaye ba, a takaice dai sai wadda iyaye suka yi wa baki ne zata yi hakan, wadda aka cewa jeki kya gani, Allah ka tsaremu da jin wannan mummunar kalma daga bakin iyayenmu masu albarka Amin.

"A'a Heartbeat ka zo dai mu yi hira, idan mun gama sai ka yi wa Abbana magana".

"Heartbeat ina nan zuwa wajen Abba, dole ne kuma nazo nayi magana da shi, dan gaskiya ba zan iya komawa ba tare da aurenki ba". Cool murmushi ta saki tana ɓuye fuska "Amma Heartbeat in tambaye ka mana?". Yana daga kwance ya miƙe zaune yana faɗin "To ina jinki". "Yanzu me kake yi?" "Ina kwance daga ni sai shot and single, kizo mu kwanta tare". Rufe fuska ta yi, ko me ya aiketa ta tambaye shi Oho, ai ga shi nan ta sami amsa daidai da tambayarta.
Chapter 72 · 0% Book details