Sashe 75
Triplets Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tsayuwa ya yi yana kallon yadda ruwan ke kwarara tamkar da bakin kwarya, kamar ance mishi ya kalli kasa, can ya hangota kamar wata kifi tana juyi a cikin ruwan, É—an waro idanunsa waje ya yi yana kallon ikon Allah, abin da ya faru shi ne, suna tsaka da hira da su Areef ruwan saman ya kece, shi ne ta tashi a guje ta yi waje, sun É—aukama wani abin zata É—auko, suna zaune suna jiranta, ita kuma ta je ta shige cikin ruwa abinta, idan baku mance ba akwai ta da son shiga ruwan sama ba kaÉ—an ba, bata ganin ruwa ta hakura bata shiga ba.
Sosai ya tsareta da dara daran blue eyes ɗin nan nasa babu ko kyaftawa, ta yi kyau sosai a cikin ruwan, har da wani ɗaga kai sama take yi ruwan na zuba mata a fuska, ba ƙaramin nishaɗi take ciki ba.
"Rimsha sarkin son ruwa". Cewar Malika da ta bayyana a yanzu, da sauri ta juyo, ganin Malikar yasa ta saki kayatatcen murmushi tana faɗin "Malika ai kema kina son ruwan, kullum a kayi sai kin shiga". Ɗan dariya ta yi kafin ta ce "To shikenan dai yanzu dai ya isa haka wanka a ruwan nan, fita kada mura ya kama mini ke". Da mamaki Lion ke kallota, shi a iya ita kaɗai yake gani, bai ga Malika ba, ga shi sai zuba surutu take yi tana dariya, tunani ya fara yi anya kuwa yarinyar nan kanta ɗaya? Anya babu wani motsi a kan nan nata kuwa?, Wani ɓangare na zuciyarsa ne ya amsa mishi da to kai me naka a ciki? Guntun tsaki ya ja tare da juyawa ya bar waje zuwa cikin bedroom nasa, saman bed nasa ya haye, cikin sauri Brady ya daka tsalle ya haye jikinsa, bargo ya ja musu ya rufesu zuwa daidai ciki, shi kuma Brady iya kansa ne kawai a waje, a hankali ya lumshe dara daran blue eyes ɗin nasa, ba jimawa barci ya yi awon gaba da shi.
Ita kuma Rimsha sai da Areef ya ji shiru ya biyota wajen, ba ƙaramin ruwan mamaki ya sha ba ganin ta a cikin ruwan, tasata a gaba ya yi tare da yi mata faɗa akan shiga ruwan da ta yi, hakuri ta fara bashi, sam bai ji daɗi ba, ya ce ta je ta yi wanka da ruwan zafi ta canza kaya kada mura ya kamata, sai su je sayan abinci, okey ta amsa mishi da shi, ta wuce sama sai ɗigar da ruwa take yi, shi kuma ya wuce bedroom nasa, zuciyarsa cike taf da tunanin irin ganin da ya yi mata a jike da ruwa, komai na ga halittar ta ya bayyana saboda kayan sun manne da jikinta, gabaɗaya tula tulanta sun bayyana sosai, abin ya tsaya mishi a rai, shi kuma Aseef waya ya ɗauka tare da kiran Akila ya wuce bedroom da ta kasance mallakinsa, dan su zuba soyayya da Heartbeat nasa.
Yana shiga ya haye gado tare da shigewa cikin bargo yana manna waya a kunne, "Hello My heartbeat"..............
â¤ï¸â¤ï¸TRIPLETSâ¤ï¸â¤ï¸
💋HEARTBEAT+ HEARTBEAT 💋
E31-32
Yana shiga ya haye gado tare da shigewa cikin bargo yana manna wayar a kunnensa, "Hello My heartbeat". Daga ɗayan ɓangaren tana daga cikin bargo ita ma saboda ruwan dake zuba tamkar da bakin kwarya, gari ya yi mugun sanyi, "My Shagwaɓati tamkar ta shiga cikin zuciyata kasan kewarka nake yi a yanzu haka". Kasa ya kara yi da murya, "Ai zuciyoyinmu a haɗe suke, dole zan san wani halin bugun zuciyata take ciki, yanzu dai yasu Ammie?"
"Sunanan lafiya lou ina su Rimsha?". Shiru ya É—an yi kafin ya ce "Hmmm Rimsha ta Saif uwar rigima ba, tana É—aki, yanzu ta gama zuba mana rigima, amma in tambaye ki mana?". "Allah yasa na sani". Ta bashi amsa, "Kina tsoron karnika ko baki yi?" "Tab ai ni idan na gansu a kusa da nima zan iya suma". Dafe kansa ya yi yana salati a cikin zuciyarsa, Rimsha part two kenan, shi yanzu ya zai yi? Ga shi dai ba zai iya rabuwa da su Lucky ba gaskiya, duk wuya, duk daÉ—i suna tare, yana kaunar kayansa.
"Shagwaɓati ya kayi shiru?". Shagwaɓe mata murya ya yi tamkar zai yi kuka "Heartbeat sanyi nake ji sosai, ki zo mu kwanta tare, na san idan kina nan for sure ba zan ji sanyi ba". Kara jan bargonta sosai ta yi, cikin sigar soyayya mai tafiya da tunanin mutum ta ce "Tom shikenan ka yi mana addu'a In sha Allah ba za'a sake yin wani ruwan sama ban zama mallakinka ba". Nisawa ya yi, ba ƙaramin daɗi maganarta ya yi mishi ba, yana son kullun ya rinƙa jin kalmar zai mallaketa, idan ta gaya mishi hakan ji yake yi tamkar ya kamota ya mayar da ita cikin cikinsa ko zai sami natsuwa.
"Heartbeat In Sha Allah ke mallakina ce, nan ba da jimawa ba hakan zata faru, yanzu dai a ina zan sami Abba?". "Banki, yana banki a can zaka same shi". "Okey tom gobe zan zo gida da yamma me zaki bani?" Kara lafewa ta yi a gadonta, ta kule cikin bargon. "Me kake so?" "Ke mana my heartbeat, ke nake so". "Kai my shagwaɓati to ai ni taka ce". Jawo pillow ya yi ya rungume da kyau a kirjinsa, ji yake yi tamkar ita ya kankame, ga yadda ruwan saman ke zuba abin ba'a cewa komai, "Heartbeat kina shagwaɓa ni sosai fa".
Turo ɗan bakin nan ta yi kamar biro "To ai dama kai my shagwaɓatina ne, dole zan shagwaɓa ka sosai". "Serious?" jinjina mishi kai ta yi tana faɗin "Yah seriously, dole na shagwaɓa ka, sai ma munyi aure, zaka sha soyayya, sai ka kasa fita waje".
Kukan shagwaɓa ya saka mata, a hankali ta fara ambata sunansa "My shagwaɓati, my shagwaɓati!" Kin amsa mata ya yi, sai uhm uhm yake ce mata. "Please my shagwaɓati ka yi magana mana". Shiru ya ɗan yi kafin ya ce "Ni gaskiya ba zan yarda ba, Allah aure nake so, ni dole a aura mini ke". Kwaikwayar maganarsa ta yi ta maimaita abin da ya faɗa "Ni gaskiya ba zan yarda ba, Allah aure nake so, ni dole a aura mini ke".
"Ni Heartbeat serious nake gaya miki, ki dai'na wasa". Ya yi maganar tamkar zai fashe mata da kuka, sake kwaikwayarsa ta yi, daga muryar har maganar da ya yi, "Ni Heartbeat serious nake gaya miki, ki dai'na wasa". "Uhm uhm kai heartbeat ki dai'na kwaikwayona nace miki ko?" Sake kwaikwayon na shi ta yi, kuka ya saka mata tare da katse kiran.
Cool murmushi ta saki tana faÉ—in "ÆŠan rigima kawai, nima ai na iya". Ta kai karshen maganar tare da fara kiran layin nasa tun da ya buÉ—e mata, wayar ta yi ringing har ta katse bai É—aga ba, tana katsewa sai ga shi ya biyo kiran nata, "ÆŠan rigima" ta faÉ—a kafin ta É—auki kiran.
"My heartbeat i want to see your face now". Shi ne abin da ya faɗa bayan ta ɗaga kiran, "Video call?" Ta tambaye shi, yes ya bata amsa, "Okey in kira ka ne ko zaka kira ni?" "No bari ni na kira ki". Okey ta amsa mishi da shi, juya kiran ya yi zuwa video call, cikin zumuɗi ta ɗaga, dan ita ma tana mugun son ta kalli face nasa, bata gajiya sam sam ga ganinsa, ya haɗu ne ta ko'ina, irin mijin da take burin aura kenan su kashe juna amma da soyayya da kauna tare da shagwaɓa.
Kayatatcen murmushi suka sakarwa junansu lokacin da suka sauke idanu a kan juna, cikin sanyin murya ta ce "My shagwaɓati ka yi kyau sosai, kasarmu ta karɓe ka".
"Ba dole Kasarku ta karɓe ni ba, tun da kina cikin kasar, yanzu dai ɗan yi kasa da bargon nan bari naga face naki da kyau". Kara jawo bargon sama ta yi har zuwa wajen idanunta, cikin sigar zolaya da shagwaɓa ta ce "Ni kunyarka nake ji". Rumtse idanu ya yi, kasa kasa ya furta "Wato ba zaki dai'na yi mini irin wannan wasa bako? For sure watarana sai kin saka ni zuwa gidanku 2 na dare".
Ɗan zato idanu waje ta yi "To ai da gaske kunyarka nake ji my shagwaɓati". Turo mata ɗan bakin nan nasa ya yi "Uhm uhm wai fisabillilahi ba zaki bari ba? So kike yi ki sanya ni kuka ko?" Ɗan gangaro da bargon zuwa kirjinta ta yi, tana murmushi tare da faɗin "Sarkin rigimana to ai gani nan ka ganni, yanzu dai ba shikenan ba?". Shiru ya yi bai yi magana ba, ya zuba mata idanuwansa babu ko kyaftawa, "Lafiya kake kallona haka?". Gera ɗaya ya ɗaga mata tare da kashe mata ido ɗaya, ɗan zaro idanu ta yi tana kallonsa, "Wai me ya faru ne shagwaɓati? Kayi magana mana". Nisawa ya yi tare da shagwaɓe fuska kamar zai yi kuka, bai ce mata komai ba.
"Shagwaɓati wai ba zaka yi magana ba?". Ji yake yi tamkar ya jawota ya rungume, shi kaɗan yasan me yake ji a cikin zuciyarsa, ta yi matukar tafiya da imaninsa, ya tsareta da waƴan nan idanuwan nasa, a hankali ya lumshe su ya sake buɗewa a kan face ɗin nata, ba ƙaramin rikita ta ya yi ba yadda ya lumshe idanun, sai ya kara kyau over, tsantsar madarar kyau ne ya bayyana, ga zara zaran eyelashes nasa wadda suke tamkar ya kara dana kanti saboda tsawo, sak irin na Lion, kuma irin na Josephine.
"Heartbeat ban san me zance miki bane, shiyasa na yi shiru, idan nace zan yi magana zan iya yin kuka, kina rikitani sosai my one and only". Kara kudundunewa ta yi a cikin bargon, murya kasa kasa kamar wani nayi mata laɓe ta ce "Heartbeat kai ne kake rikita ni dayawa wlh, ban san ya zan kwatanta maka yanayin kyanka ba, ni na rasa ma me zan ce". Sake lumshe idanunsa ya yi zuciyarsa na kara macewa a kanta, ya kara narke mata sosai.