← Book details Triplets Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 121

Sashe 14

Triplets Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tana fita bedroom nata ta koma, suka cigaba da hira da Akila, a nan AKILA take gaya mata Hjy Batula zata aiko mata da wasu kayan karin girman breast wadda ta haɗawa jelly, suna da kyau sosai, Hjy Batula ɗin ta ce zata bawa yaya Imran ko yaya Akil su kawo mata, idan sun kawo mata, zata ɗebawa yaya Imran ya kawo mata ita ma ta yi amfani da su, sosai Rimsha ta ji kunya, ta kuma amsa da to, sannan ta daɗa da cewa ta haɗa mata da su kanunfari, citta, kimba, da kuma su na'a'na'a, dan tana son ta rinƙa haɗa tea nata irin wadda mummynta take yi wa daddynsu mai shegen daɗin nan, bata son green tea ɗin su Lion, bata saba sha ba, sai ta ji babu daɗi, ga shi ita ma'abociya shan tea ɗin ne, to Akila ta amsa mata, tare da gaya mata zata bawa driversu ya sawo mata kayan a kasuwa, idan ya kawo mata, sai ta bawa yaya Akil ko yaya Imran su kawo mata, sai murna Rimsha take yi, sun sha hira kamar ba gobe, sosai Akila ta kara zugata akan ta rinƙa shan wanka da kwalliya, kada ta yarda Lion ya bar Nigeria ba tare da ta sato masu zuciyarsa ba, sai murmushi take yi jin Akila ta sosa mata in da yake yi mata kai kayi, ita kuma Akilar ta zage sai kara gaya mata lagon maza take yi, abin da bata sani ba shi ne, LION duk duniya abu ɗaya ya bari a kasani a matsayin rauninsa, wannan abu kuma ba komai bane fashe kaunar TRIPLETS nasa, kaunar ƴan uwansa kawai ya bari jama'a suka sani, bayan haka ko uban da ya haife shi, bai san me raunin ɗan nasa ba, shi Lion bai ma yarda yana da rauni ba a duniya, domin a nashi ganin komai ma zai iya yi, kuma zai iya jure komai ciki kuma har da rashin TRIPLETS ɗin nasa da jama'a suke ganin kamar shi ne rauninsa. TO FA ZAN SO GANIN MENENE RAUNIN LION GASKIYA.

Idan muka koma ɓangaren gidan Abbo kuwa.

Misalin karfe 5 na asuba Nawid ya farka, abin mamaki sai ya ga bata a kan gadon, a hankali ya miƙe tare da zuro kafafunsa kasan gadon, ya kunna wutar ɗakin, nan take haske ya gauraye ɗakin.

Can saman dadduma ya hangota, tana zaune tana karatun Al Qur'ani mai girma, baiwar Allah Akil ya riga da ya saba masu, ɗan zamanta da Akil ta koyi abubuwa da dama dan gane da addini, ciki har da su askar, yin karatun Al Qur'ani mai girma, tashi barci kafin lokacin sallar asuba domin ta gabatar da nafila na raƙatainil fajir, sannan ta gabatar da karatun Al Qur'ani, yin sallar dare, da dai sauransu, ba ƙaramin natsuwa da cigaba ta samu ba.

Miƙewa ya yi ya nufi toilet, wanka ya farayi, ya ɗauro alkawala, kusa da ita ya zo ya tsaya, ganin shi yasa ta miƙe hannunta riƙe da Al Qur'ani ta nufi saman sofarsa ta zauna.

Tsayuwa ya yi ya gabatar da sallar raƙatainil fajir, sannan ya nufi masallaci, ita kuma ta dawo saman dadduma dan gabatar da sallar Asuba.

After some minutes, bayan ta idar da sallah ta yi karatu har rana ya fito, ta yi askars ɗinta, ta miƙe ta nufi waje.

Tana ƙokarin fita shi kuma yana ƙoƙarin shigowa, karo suka ɗan yi, da sauri ta yi baya tana sunkuyar da kanta kasa.

Zuba mata idanu ya yi yana kallonta sosai.

Kasa ta yi da kanta, cikin sanyin murya da girmamawa ta fara magana "Ina kwana yaya Nawid?". Nauyayyar ajiyar zuciya ya sauƙe kafin ya amsa mata tare da tambayarta ya kwanan bakunta, cike da kunya ta amsa mashi da lafiya, gabaɗaya kunyarsa take ji, domin ta tashi barci ta tarar ya rabata da kayan jikinta.

"Ina zaki je yanzu da sassafen nan?" Ya yi maganar yana kara tsareta da ido. "Wajen Ummi zanje". "A nan É—in na takura maki ne?" Ya yi maganar cikin zolaya.

Girgiza mashi kai ta yi tana faɗin a'a. Wucewa ya yi, ya shige cikin ɗakin. "Zo ki yi kwanciyarki sai zuwa anjima sai kije, yanzu ko da kinje ma, tana barci, bata kai ga tashi ba". Kamar zata yi kuka, haka ta juyo ba dan ta so ba. Saman sofa ta zauna tana wani rakuɓe rakuɓe.

Da mamaki yake kallonta, ya rasa meyasa take gudun shi haka, tabbas ƙwaƙwalwarsa tana gaya mashi akwai dalili, domin kuwa shekaruntan nan ta wuce a ce sai an zauna ana yi mata wani karin bayani game da aure, 21 years take da shi a duniya yanzu.

Tsareta ya yi da ido, yana son karantarta, domin ya gane menene matsalarta. "Tashi ki zonan". Shi ne abin da ya faÉ—a.

Ba musu ta tashi ta koma kusa da shi ta zauna.
"Meyasa kike guduna har haka ne A'AFIA?". Kasa ta yi da kanta. "Babu komai yaya Nawid" ta yi maganar cikin sanyin murya.

Hannunta ya riƙo a cikin nasa. "Ni yayanki ne, kada ki mance da Ummi da Aunty Khadijah ƴan uwa ne, dan Allah ki gaya mani menene yake damunki Kin ji? Kada ki damu, kuma kada ki ɓoye mani komai".

ÆŠan satar kallon shi ta yi ta kasan ido. "Da gaske yaya Nawid babu komai". Gefensa ya nuna mata ba tare da ta sake magana ba, ba musu ta karisa hayewa saman gadon, ta kwanta a gefen nasa, shi ma kwanciya ya yi, ya sanya kansa a saman pillow da ta kwantar da nata kan.

"Ba zan ɓoye maki ba, a lokacin da aka bani aurenki, kwata kwata babu sonki ko kaɗan a raina, amma daga daren jiya zuwa yau, Allah ya jarrabeni da sonki, ina fatan kema kin na sona?". Ya yi maganar can kasa kasa maƙoshinsa.

ÆŠan juyowa ta yi kaÉ—an "Ina son ka nima yaya Nawid". "Da gaske?" Ya faÉ—a cikin zolaya, gyaÉ—a mashi kai ta yi alamar e.

"Kada fa dan kinga idona ne yasa kika faÉ—i hakan, fatan Allah yasa babu wani a zuciyarki". Nan ma cikin zolaya ya yi maganar.

"Yaya Nawid ba wai dan ganin idonka bane, wlh da gaske ne ina sonka, kuma ni wlh ban taɓa yin soyayya ba, bani da saurayi ko a school, ni koma a ina bana kula kowa, zaka iya tambaya ma ka ji".

Hannu ya kai ya É—an ja hancinta yana murmushi "To waye zan tambaya É—in?" "Nima ban sani ba, kawai dai ka tambayi koma waye".

Kara juyowa ya yi da kyau ta yadda zai sami damar ganin fuskarta sosai. "Ni ba sai na tambayi kowa ba, domin kuwa, na taɓa kamaki kina soyayya, a kan idona kika sace wa wani sarauyari bawan Allah zuciyarsa da kallo ɗaya".

Zaro ido waje ta yi "Yaya Nawid a ina aka yi hakan? Kuma ni Aafia É—in ce na yi hakan?" Ta kai karshen maganar tana yin narai narai da idanu kamar zata yi kuka. ÆŠaure fuska sosai ya yi "E mana, ke É—in dai, ai a gabana aka yi komai".

Shiru ta ɗan yi tare da nutsa ƙwaƙwalwarta a cikin tunani, ita dai tasan wlh bata taɓa tsayawa da wani saurayi ba, bata taɓa soyayya ba, Rufee ta yi ƙoƙarin koya mata soyayya, ta yi ƙoƙarin haɗata da maza, amma idan baku mance ba, ta ki yarda, bata kula kowa, karatu kawai take yi, bata shiga harkar kowa.

"Yaya Nawid ni wlh ban tuna yaushe aka yi hakan ba, ni ba zan yi musu da maganarka a kan cewa ba haka bane, amma dai abin da zance kila daga É—an nesa ka gani, to kila mai kama da ni ce sai kaga kamar ni ce...."

Katse ta ya yi da cewa "Ba wata mai kama dake, ke É—in ce ba wata ba". Shiru ta yi na É—an lokaci. "Tom shikenan Yaya Nawid na yarda ni É—in ce, amma ka yi hakuri".

Shafa face nata ya yi. "My beautiful wife, jiya ba kin sace zuciyar mijinki da daddare a nan ba, to ai shi ne saurayin da kika sace wa zuciyar, kuma ai kinga a gabana aka yi komai ko?". Bata san lokacin da murmushi ya suɓuce mata ba.

Tsareta da ido ya yi, yana kallon yadda take murmushin gwanin ban sha'awa. Ganin yana kallonta sosai ne yasa ta ɗan sauƙe idanunta kasa. "Kunyata kike ji?" Dawo da kallonta kan face nasa ta yi, ɗaga mata gera ɗaya ya yi yana kashe mata ido ɗaya.

Kara faɗaɗa murmushin kan face nata ta yi, ba ƙaramin daɗi ya ji ba, ganin ta yi murmushi, kuma ta ɗan saki jikinta.

"Gaskiya fa ina kara yi wa Allah godiya, sannan ina kara yi wa Abbina godiya da ya mallaka mani ke, ya zama dole gobe muje mu gaida shi, na ji daÉ—in bani ke da ya yi". Hannu tasa ta rufe fuska tana murmushi.

Hannun nata ya kama tare da zame shi daga kan face É—in nata. "Ki daina hana ni ganin fuskar matata, ko fuskarki ce?" Ya tambaya yana É—aga mata gera É—aya.

Kin yarda ta yi, ta dage sai ta rufe fuskarta, shi kuma ya ce a'a bai yarda ba, haka suka kama kokawar wasa, daga karshe dai ya yi nasarar kame hannayen nata dukka biyu, ya riƙe cikin nashi, tare kuma da mannata da jikinsa yana murmushi, ita ma sai murmushi take yi.

"To dai na fiki karfi sai ki rinƙa bina a hankali, idan ba haka ba, zaki sha wahala". Cikin zolaya tare da so da kauna ya yi maganar.

"Ai daman Yaya Nawid ka fini karfi mana, bama haÉ—i ai". Sake hannayen nata ya yi tare da jawota sosai ya matseta a jikinsa, matso da bakinsa ya yi saitin kunnenta, ya fara zuba mata kalaman masu shegen daÉ—i.

Tuni ya mantar da ita wani bakin ciki, cikin kankanin lokaci ya sanya ta saki jiki da shi, tun tana mai da mashi da martani ɗai'ɗai, har ta fara zuba mashi nata salon kalaman kamar, yadda yake zuba mata shi ma, ba ƙaramin daɗi ya ji ba, wani irin yanayi mai cike da annashuwa ya tsinci kansa a ciki, har cikin ransa yake jin breast ɗin nan nata da suke sokinsa a kirjinsa, dannewa kawai yake yi, ita kuma ta saki jikinta da shi.
Chapter 14 · 0% Book details