← Book details Triplets Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 101 OF 121

Sashe 101

Triplets Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ko sannu bai ce ba, sai ma kara ɗauko wani salan lemu da ya yi ya kai bakinsa, dan shi bashi da lokacin biyewa daddyn nasa a cewarsa, sai hana shi daddy yake yi, amma saboda an nuna ba'a so, sai ya ce ai tun da yake shan fruits ma bai taɓa shan mai daɗin wannan ba, dan haka ta karo mishi, tamkar daddy zai yi hauka ya katse kiran dan ya kira Michael wato Aseef, sai dai fa duk da haka ko kaɗan daddy bai yi nadamar irin horon renon da ya basu ba, shi ya koya musu hakan, yanzu da suke yi Mishi, yana mugun jin ba daɗi, amma bai taɓa yin danasanin irin tarbiyar da ya yi musu ba, da yake ɗabi'arsu ce yin hakan,......LALLAI DADDY DA SAURANKA, IN DAI BAKA YI NADAMA BA, TO DA SAURANKA, KA KOYAWA YARA KADA SU YARDA WANI YA ƊAGA MUSU MURYA A DUNIYA, ANYA KA NEMI ZAMAN LAFIYA KUWA? ALHADULILLAH, ALLAH MUN GODEMA DA KA BAMU IYAYE MASU TSAWATAR MANA A KAN DAI'DAI DA BA DAI'DAI BA, ALLAH KA KARA MUSU LAFIYA, KA JIKAN WAƳAN DA SUKA RIGAMU GIDAN GASKIYA, KA BAMU IKON CIGABA DA YI MUSU BIYAYYA MUNA FARANTA MUSU.

Misalin karfe 8 na dare bayan sun ci abincin dare sun yi sallah, ita indomie da kwai ta girka ta ci, shi kuma fruits ya sha sai Maltina guda É—aya, ya ce ta shirya zasu je wani waje na musamman, okey ta amsa mishi da shi sai murna take yi zasu fita, wanka ta tsara, har da zama a gaban mirror ta tsantsara make up ba karya, bata sanya janbaki ba, lips balm kawai ya sanya, ta yi kyau over na wuce misali, kamar dai kullum wandon jeans baki mai bala'in kyau ta É—auko tare da riga maroon color mai doguwar hannu, high neck ce rigar, ta sanya a jikinta, kayan sun kamata sosai, da yake shima rigar kamar roba haka take, bayan ta sanya sai ta ciro wani dankareren turban cap nata baki kalar wandon ta sanya a kan nata bayan ta É—aure dark black curly hair ta kenan, hular kamar É—aurin gwaggwaro aka yi shi, ba karya ta fito kamar ka saceta ka gudu da ita, sauri sauri ta sanya perfume a jikinta ta fito zuwa bedroom É—in daddyn nata, har ta fita sai kuma ta dawo ta É—auki Booth É—in Jehan ta sanya a kafarta, launin maroon color ce kalar rigarta kenan.

Tsaye a gaban mirror ta isko shi ya kammala shiryawa cikin wando jeans shi ma, da kuma T-shirt, ba karya shi ma ya fita over, ya É—aure gashin kan nan nasa, fuskarsa sanye da black face mask tare da p-cap, yana kallon fusataccen fuskarsa a jikin mirror, sai tashin fitinannen daddaÉ—ar kamshin perfume nasa yake yi, har wani curly sosai soft skin nasa yake yi, idanun nan nasa sun kara wani kyau ba kaÉ—an ba, lips nasa har wani sheki suke yi kamar wadda ya sanya lips balm.

Sallama ta yi mishi, kamar lullum kasa kasa ya amsa ba tare da ya juyo ba kuma bai kalli in da take ba, sai da ya kammala kallon face É—in nasa kafin ya wuce ya nufi waje ba tare da ya kalli in da take ba, da sauri ta bi bayansa, mota suka je suka shiga, ita ta buÉ—e musu gate sai da ya fitar da motar sannan ta rufe ta zo ta shiga suka wuce.

Cikin natsuwa yake tuki, bai yi gudu ba ko da sunan wasa, da alama akwai dalilin yin hakan, yana tuki yana duba diamond watch nasa dake É—aure a hannunsa, alamar yana duba time, hakan yana nufin akwai lokacin da yake son isa wajen da zasu je É—in, wayar tane ya fara kara, a É—an tsorace ta É—auki kiran, tana tsoron kada ya yi mata tsawa, ya ce akan me zata É—auki kira?, Anaya ce take kiranta, Allah sarki taga yau bata zo school ba, shi ne ta kira ta ji dalili.

Kara wayar a kunnanta ta yi can kasa kasa ta ce "Hello Anaya". Daga ɗayan ɓangaren Anaya ta amsa da "Rimsha ina wuni?" "Lafiya lou Alhadulillah yasu Zaira?" Da lafiya ta amsa mata kafin ta ɗaura da tambayarta ya bata zo school ba yau, ɗan satar kallonsa ta yi kafin ta ce "Babu komai zan zo jibi In Sha Allah". "Rimsha kina ganin fa mun gama test Exam zamu fara on Monday, amma sai wasa da zuwa school kike yi ko? Kina son ki zo last ko?" "A'a Anaya, In Sha Allah ba zanzo Last ba, ki rinƙa taya ni da addu'a".

Nisawa ta yi kafin ta amsa da "To zan rinƙa tayaki, amma dai kema ki dage sosai". "Okey my Anaya ina godiya yanzu muna hanya ne idan mun koma gida zan kira ki". Tana ƙoƙarin katse kiran ta katseta da cewa "Rimsha ina wannan Baturen? Allah jiya nayi mafarkinsa, gaskiya yana da kyau sosai wlh, ga shi shiru shiru kamar yaya Feroz, dan Allah ina yake, ki turomin hotonsa idan kina da shi". Juyawa ta yi gabaɗaya ta zubawa Lion idanu tana faɗin "Tom zan ɗauka miki shi hoto idan bai sani ba na turomiki". "To dan Allah Rimsha yau ba sai gobe ba". Zata yi magana ta ga Lion ya yi parking na motar a parking space na wani wajen da bata san ko ina bane, cikin sauri ta katse kiran tare da zubawa wajen idanu tana kare mishi kallo, ga dukkan alamu clubs ne, ga ƴan mata da samari birjib a ko'ina na harabar wajen, mafiya yawan matan suna shaye shaye, ga sigari a hannunsu suna busawa, dressing ɗin jikunansu na banza, wasu ma da su da tsirara duk ɗaya ne, sai dai fa clubs ɗin a sihirtaccen waje yake, da alama clubs ne na manyan mutane ƴan sharholiya, dan gabaɗaya dankara dankaran tsadaddun motoci masu numfashi ne cike a parking space na wajen, sannan gabaɗaya ƴaƴan da suke wajen komai na jikinsu masu zafi ne, masu tsadar gaske, haka zalika wayoyin hannunsu masu zafi ne.

A sukawane ta dawo da kallonta kansa, sai latsa waya yake yi bai bi ta kanta ba, jim kaÉ—an ya fito da bakar glass ya sanya a face nasa bayan kuma ga face mask, da alama baya son a gane shi ne, domin kuwa ya sanya hands gloves, kafarsa kuma tana cikin Booth, da alama shiri ne duk abin da ya yin nan.

Bayan ya sanya glass É—in ne ya ce da ita suje, bai tsaya sauraronta ba ya fice daga cikin motar, ya É—an yi gaba ya barta a baya, tana fitowa samari suka fara kewayeta suka tare mata gaba, ga shi tayi irin dressing na karuwan ita ma, daga mai cewa jimana Æ´an mata, sai mai cewa nariga, sun sha gabanta sun hanata bin shi, sai kakkauce musu take yi tana son wucewa sun hanata, da alama kuma dayawa daga cikinsu a buge suke, sun sha sun bugu sosai, sai wani layin maye suke yi mata, baki duk warin giya.

Ta ruɗe ta rasa ya zata yi, bata ankara ba sai ji ta yi an jawo hannunta ta faɗa saman kirjin mutu, tun daga yanayin faffaɗar kirjinsa ta fahimci shi ne, nufa cikin ainahin wajen ya yi da ita, tana manne a jirjinsa, dan ya lura idan ba rungumeta ya yi ba, ba zasu daina tare ta suna taɓa ta tare da shafe mata jiki ba, shi kuma baya son a gane shi, shiyasa bai yi yunkurin ɗagawa kowa murya ba, kawai ya rungumeta a kirjinsa dan su yi saurin kammala abin da ya kawo su.

Sosai ta kankame shi tana shakar numfashinsa, ɗan sauko da kansa kasa ya yi yana kallonta, sarkin tsoro duk ta bi ta tsorata, abin da bata saba gani ba, sai ya yi mata wani banbara kwai. Bayan sun shiga waje, sai kuma ya ji ba zai iya sanyata wannan aikin ba, ba zai iya sanyata zuwa ga mutumin dan ta fito mishi da shi ya kama shi ba, baya son shiga ya kamashi saboda wani dalili nashi na kansa, amfani da ita yake son yi wajen kama shi, yasan idan ya kalleta dole zai biyota, dan a haukace yake da neman sauran family'n Nawazudden da suka rage, ɗan raba jikinsu ya yi yana kallonta, yadda ta yi shigar tata marabanta da waƴan da suke wajen kaɗan ne, shi ba ma shigar kayanta ne a gabansa ba, idan ya raba jikinta da nashi kafin ta isa ga mutumin samari da dama zasu tare ta, zasu yi ta rungumarta suna shafata, ita kuma sarkin tsoro tsab zata ɓata musu shiri, dan zata iya waje baki ta yi ta ihu a cikin jama'a har komai ya lalace.

Shiru ya yi yana tunanin me mafita kenan? Dan tun da ya sako kafarsa a cikin nan ya ji gaskiya ba zai iya tura ta ba, ya zuba mata idanu, amma a zahiri ba ita yake kallo ba, tunani yake yi, da yake dai a cikin glass idanun nasa suke, sai ka yi, zaton ita yake kallo.

Wasu samari ne ke nufo in da suke, sun sha sun bugu suna ta tangal tangal suna layi tamkar zasu faÉ—i kasa, sun zo dai'dai kusa da su, cikin sauri ya mai data jikinsa ya rungumeta dan kada su bangajeta ta faÉ—i kasa ta fara yi mishi ihu a nan, wannan mai da ita da ya yi sai da ya ji shock ba kaÉ—an ba, dan da karfi ya jawota jikin nasa har sai da ta buge shi sosai a kirjinsa, waje ya juya da ita, cikin mota ya mayar da ita kafin ya fito ya rufe motar da key dan kada wasu ma su nufeta ta yi mishi hauka, takure jikinta waje guda ta yi tana kallon yadda Æ´an mata da samari ke shagawagi a wajen ga uban kiÉ—a da yake tashi kamar zai É—auke garin.
Chapter 101 · 0% Book details