Sashe 41
Triplets Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Sai bayan Æ´an mintuna da tafiyarsa ne, da ta ji shiru sai ta waro idanun nata waje, ganin wayam babu kowa ne yasa ta ja guntun tsaki tare da komawa ta kwanta a saman gadon ta rungumo pillow, ba jimawa barci ya yi awon gaba da ita, sai faman sauke nauyayyar ajiyar zuciya yake yi cikin barci.
(Akil da Umaisha manya, abin ba sauki🤣)
MU KOMA GIDAN LION DAN JIN YADDA AKE CIKI.
Misalin karfe 2 na dare, sanyi A.C ne fara ratsa dukkannin ilahirin jikinta, har cikkin kashi ɓargo da jijiya take jiyo wannan bala'in sanyin, ta jima a hakan kafin ta waro idanunta a hankali, kai tsaye saman ɗakin ta fara kallo, a hankali take jiyo sautin zazzaƙar muryarsa yana tashi, rera karatun Al Qur'ani mai girma yake yi cikin surarul Mai'da, ba karamin iya rairai kira'a ya yi ba.
A hankali ta juyo da dara daran sleeping eyes ɗin nata izuwa ta in da take jiyo wannan zazzakar murya tasa, tsaye yake saman dadduma yana fuskartar gabas, jikinsa na sanye da jallabiya fara tas, blue light dake ɗakin ba ƙaramin kara bayyanar da kyan fuskarsa ta yi ba, ya ƙulle gashin kan nan nasa, jin abin Rimsha take yi tamkar a mafarkinta da ta saba yi, bata yarda a zahiri bane, dan haka sai ta tsare shi da idanu tana kare mashi kallo.
A haka Areef ya fito daga cikin toilet ya isko ta, shima Alwala ya É—auro, da alama ya yi wanka, dan ya cire kayan barcin jikinsa, ya zura farar kalla ash color.
Bai lura da idanunta a buɗe ba, wucewa ya yi, gefen ɗan uwan nasa yazo ya tsaya tare da ta da hiƙama ya tada kabbara, da yake daddumar irin manyan nan ne masu faɗi ga bala'in laushi, sai ta ishe su suka tsaya a tare.
Ganin Areef yasa ta yarda ba mafarki take yi ba, a hankali ta miƙe zaune, har wani jiri take ji, sanyin Ac ne ya farfaɗo da ita. Sai da ta bari Lion ya yi sujjada ta miƙe da sauri ta nufi waje, sai tangal tangal take yi kamar zata faɗi kasa sabida yunwa, bata ci abincin dare ba, haka ta jure ta kame jikinta ta nufi waje.
Kai tsaye bedroom nata ta wuce, Akila nata sharara barci kamar bata duniyar mutane, sai wani sauƙe numfashi take yi a hankali hankali, gefenta ta je ta haye ta kwanta, ta so ta yi nafila koda raka'a huɗu ne, amma ina barci ya ci karfinta, sai kawai ta hakura ta kwanta, ranta cike da mamakin hali irin na Saif, duk wani abu da cikakken musulmi mai imani ya kamata ya yi, Saif yana yin shi, sai shegen bakar zuciya kamar kafuran farko, bashi da Imani da tausayi a cewarta.
Ranta cike da tunanin zazzakar sexy voice nasa har barci ya yi awon gana da ita.
Washegari gari da misalin karfe 8: 30. A hankali ya waro ash eyes nasa a kan fuskar É—an uwan nasa, zuba mishi idanu ya yi yana kare mishi kallo, hannu ya kai cike da tsokana zai ja hancin É—an uwan nasa, kamar daga sama ya damki hannun nasa yana girgiza mishi kai alamar kada ya kuskura.
"Good morning my Lion". Ya yi maganar cikin zolaya, har lokacin bai buÉ—e idanunsa ba, dan yau barci sosai yake ji.
Sake kai hannu ya yi zai taɓa shi, can kasa kasa da murya irin na mai barci ya ce "Wai meyasa nikam kake takura mini ne Areef?" Matsowa kusa da kunnensa ya yi, kamar mai raɗa ya furta "So mana, son ka yasa nake takura maka". Shammatarsa Lion ɗin ya yi idanu a rufe ya damƙo gashin kan ɗan uwan nasa.
Ƴar kara ya yi yana faɗin "Kai kai kai wlh yau ba zan kyakeka ba, amma dai please ɗan sake mini gashin, ko dan saboda kai wlh dole na yanke gashi nan ya huta, muguntarka a kan gashin nan ta fara isata". Lion bashi da wajen kamawa a jikin ƴan uwan nasa sai wannan gashin nasu, da shi yake morarsu.
Waro dara daran blue eyes nasa masu ɗauke da barci ya yi, kai tsaye fuskar ɗan uwan nasa ya sauƙe su. "Wai kai Areef me ma ya dawo da kai ɗakin nan ne?". Sai ciza laɓɓansa yake yi saboda zafi. "Ni da ɗakina ka ce me ya dawo dani, ai ni na dawo nan kenan". "Baka isa ba, yau zaka bar ɗakin nan saboda kana takura mini".
Yana riƙe mishi da gashinsa yana ja amma bakinsa yake mutuwa. "Wlh Lion babu in da zanje, sai dai kai ka canza ɗaki, ni nan ɗakin ne ya yi mini". Kara jan gashim nasa da karfi Lion ɗin ya yi.
Da sauri ya ce "Wash daddyna, haba mana É—an kyakkyawan mu, beautytin TRIPLETS, kai fa babynmu ne, to sake ni".
Zubawa face ɗin Areef ɗin idanu ya yi, mamaki yake yi na irin gasken da shi kuma ya kara, shi Lion ya ɗan yi duhu saboda zafi, shi kuma Areef ya kara haske, hakan zai tabbatar maka kowa da yanayin jikinsa, kowa da abin da ta fi karɓar jikinsa, sai kaga wani ya sha magani ta yi mishi, kai kuma idan ka sha, ba zata yi maka ba, saboda yanayin jikin daban daban.
"Haba mana Lion ka sake ni mana, kai ne fa farincikin mu, shi ne ni kuma kake saka ni kuka, ba komai mai rama mini na nan zuwa". Shiru dai Lion bai tanka shi ba, kuma bai sake shi ba, dama sai su yi magana wajen sau uku ba ya tankawa.
"Wlh Lion ka jira ka gani duk wannan abin da kake yi mini mai rana mini na nan zuwa, shiyasa fa kaga nake kula da i......." Sai kuma ya yi shiru, dan yasan idan ya karisar da wannan magana ba zasu wanye lafiya a É—akin nan ba, kuma ya ja ma Rimsha sabuwar wahala da bala'i, dai in ba'a sa'a bama Lion sai ya koreta daga gidan nan ko kuma ya haÉ—ata da aikin azaba, tuna hakan yasa ya yanke maganar.
Tsab Lion ya san karkashin harshensa, yasan abin da yake son faÉ—e, sai dai bai san a kan waye Areef É—in yake magana ba, mace ce ko naiji, oho bai san mishi ba, abin da yasa bai damu ba ma kenan, kuma shi yana ganin ai inaaa, ba wadda ya isa ya É—aga mishi murya a duniyar nan.
"Lion wai ba zaka sake ni ba?". "Areef Allah kana kure ni, idan ka bari wata rana na yi maka wata capka ba zaka ga da kyau ba". Ya kai karshen maganar yana sakin gashin.
Areef zai yi magana Imran ya shigo É—akin bakinsa É—auke da sallama, a tare suka amsa sallamar.
Saman gadon nasu shima ya haye, kallo É—aya Areef ya yi mishi ya kwashe da dariya.
Da mamaki Imran yake kallon yadda Areef É—in ke dariya kamar ba lafiya ba, shi kuwa Lion da yake yasan me Areef yake yi wa dariya sai ya kawar da kansa gefe guda, dan da Areef da Imran sai dai shiriyar Allah za'a neman musu, da kallo É—aya shi ma Lion ya yi wa Imran É—in ya fahimci matsalar, amma bai bi ta kansu ba, sai ya kawar da kansa gefe guda.
"Areef ban san iskanci fa, me kake yi wa dariya kuma?". Bai tanka ba har sai da ya yi dariyarsa mai isarsa, ya tsagaita na Æ´an mintoci kafin ya ce "Wai Prof ni kam ba kana da mata ba?" GyaÉ—a mishi kai ya yi alamar e.
"To me yasa ba zaka É—auko kayarka ba, kake wahalar da kanka, kasan illar yin hakan kuwa? Tana da illar sosai ga lafiya wlh, tun muna school na gaya maka kada ka daka ta Lion da Aseef basu san daÉ—in duniya ba, idan ka biye musu zaka mutu a bushe kamar itace". Wani damka Lion ya kai mishi a gashi kai again, Areef ya yi mugun sako shi a gaba kwana biyun nan, dan iskanci ko wani misali ya tashi yi sai ya kwatanta da shi, yanzu shi da Aseef ne basu san daÉ—in duniya ba kenan? To me daÉ—in duniyar?.
Shi kuwa faÉ—awa jikin É—an uwan nasa ya yi yana dariya. "Allah Lion baka son gaskiya, yanzu ba gaskiya na faÉ—a bane? Duk wanda ya biye muku kai da Aseef to zai mutu kamar bushasshiyar kifi or itace, idan kuma ka ce ba haka ba to me yasa......." Kasa karisa maganar ya yi saboda wani dalili nashi na kansa.
"Ni kam Areef ni sa'an ka ne? Ni abokin wasan kane?" Ya faÉ—a yana É—aure fuska alamar ba wasa.