← Book details Triplets Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 67 OF 121

Sashe 67

Triplets Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan ya mayar da kayan kyakkyawar mazaunin da ya yi musu, toilet ya wuce dan ya yi wanka, ruwa mai sanyi ya sakarwa kansa dan ya samu zuciyarsa ta yi sanyi, yana shiga toilet Areef ya É—auko laptop nasa ya fara bincike a cikinta dan ya gane menene ainahin matsalar É—an uwan nasa, shi kuma Aseef abinci ya wuce ya je ya É—auko musu dan su ci.

After some minutes, bayan ya kammala shiri cikin kayan barcinsa masu shegen kyau da tsada, sai tashin kamshi yake zubawa kamar me, wajen abincin ya nufa, suna zaune suna jiransa, Aseef shi ya yi serving nasu a plate guda, a nutse suka fara cin abincin, ba wanda ya ce da ɗan uwansa ko uppan, har suka kammala cin abincin suka miƙe, Lion ne ya fara tashi ya haye bed nasa, Aseef ya kwashe kayan abincin ya fitar, ya dawo ya gyara wajen.

Dukkansu gadon Lion É—in suka haye dan su sanya shi nishaÉ—i, sun san yana cikin damuwa, sun ko yi nasara, sai da suka saka shi nishaÉ—i, suka sanya ya mance duk wani abin da yake damunsa, Allah sarki Æ´an uwa rabin jiki, sai dai kuma har gobe yaki ya yi koda murmushi ne su gani, abin yana damun Aseef sosai, shi kam Areef normal ne, ko a jikinsa, ba dai ya tabbatar da É—an uwan nasa ya yi murna ba? Hankalinsa ya kwanta, to ba sai ya yi murmushi ba.

Da kyar suka rabu da ɗan uwan nasu suka koma ɗakin Areef, Aseef ya ce ba zai kwana shi kaɗai ba, tare suka kwana da Areef, suna kwanciya ba jimawa Areef ya yi barci, shi kuma ya hau aikin waya da Heartbeat nasa, sai zuba mata shagwaɓa yake yi, tana zuba mishi nata ita ma, kamar dai yadda suka saba, haka suka raba dare, sai misalin karfe 3 na dare suka yi sallama ya yi mata sai da safe, kwata kwata bai so su rabu ba, dare ne ya yi sosai yasa ya hakura, yana ajiye wayar ya yi addu'ar barci, ba jimawa barcin ta yi awon gaba da shi. ASUBA TA GARI.

Washegari da safe, misalin karfe 8, ta tsara wankanta cikin pakistan na Indiyawa, ta yi kyau sosai, wandon farine tas mai É—an faÉ—in, riga kuma launin blue, mayafin ma blue ne kalar rigar, ta yi kyau sosai ba kaÉ—an ba, sai tashin kamshi take yi abinta.

Palo ta fito, babu kowa, kai tsaye ta nufi garden dan tasan da wuya idan bata same su a can ba, da sallama É—auke a bakinta ta shiga wajen, suna zaune su biyun, kowannensu yana latsa wayarsa, sun yi shiga iri É—aya, ga shi dukkansu sun sanya black glass a face nasu, no respect, idan har ba irin Rimsha da ta yi musu farin sani ba, to da wuya mutun ya iya banbantasu, wandunan jean ne blue color a jikkunansu, sai kuma riguna polo t-shirt farare tas, ga gashin kan nasu ma iri É—aya, dukka brown hair ne, sai dai na Aseef ya fi shiga brown sosai, na Areef ya É—an yi haske, amma sai ka lura zaka gane hakan.

Ganinta yasa suka saki cool murmushi a tare, ita ma cool murmushi ta sakar musu tare da karisawa ciki, kamar abin haÉ—in baki suka wani matsa mata tsakiyarsu akan tazo ta zauna, zata wuce zuwa É—ayar kujerar Areef ya jawota ta zauna a tsakanin nasu.

"Good morning my lovely brothers". Cikin sanyin murya ta yi maganar, Areef ne ya iya amsa mata, shi kuwa Aseef yana can duniyar sahibar tasa, baya tare da su, "Muje sayan abinci ko?". Cewar Areef "Yaya Areef zaka ci abincin ne?" Gyaɗa mata kai ya yi alamar e zai ci. "Yaya Areef da gaske kana son abincin mu?" Ta yi maganar cikin zumuɗi, fuska ɗauke da mamaki. "Sosai our Queen, wlh abincinku is so sweet, jiya baki ga naci ba? Amma matsalar ni bana son abincin restaurant ne, idan zaki rinƙa girka mana, to zan rinƙa ci sosai, bamu taɓa cin abincin restaurant ba sai jiya, duk wuya duk daɗi a gida muke cin abinci, idan tafiya ta kamamu, muna tafiya da mai yi mana girki, duk in da muka je, shi zai yi mana girki". "Yaya Areef to ai wannan Mark ɗin ya hanani yin girki, ranar da nayi ya zubar" "Akan me zai zubar miki?!" Ya faɗa a ɗan zafafe, "Nima ban sani ba".

Shiru ya ɗan yi kafin ya ce "Okey yanzu dai zamu je mu sayo abincin, amma in the afternoon ke zaki girka mana, nima kuma zan taya ki yin girkin, jeki wajen Lion ki ce nace ya baki kuɗi zamu je sayan abu, daga nan sai mu je wajen gyaran gashi ko?". Cike da mamaki ta ce "Yaya Areef waye ya ce maka ina son a gyara mini gashi na?" Kashe mata ido ɗaya ya yi yana faɗin "Ai duk abin da yake da mahimmanci a wajenka, to ya zama maka dole ne ka rinƙa gane abin da yake buƙata, ke dai jeki ki karɓo mana kuɗi kizo, zan baki mamaki yau, zan saya miki abubuwan da kike buƙata wadda baki san kina da buƙata ba".

Shiru ta É—an yi tana tunanin ta yadda zata shiga É—akin Lion ta ce ya bata kuÉ—i, É—an dafa ta ya yi yana faÉ—in "Ki je babu abin da zai faru". Mamaki ne ya kara kamata, wai shi yaya Areef É—in nan waye yake gaya mishi abin da yake zuciyar tane? Bata san da babban jam'i hukumar sirri take tare ba.

Jiki ba kwari ta miƙe ta nufi bedroom ɗin na Lion, da sallama ɗauke a bakinta ta shiga, babu kowa a ɗakin, ɗan leke leke ta yi mishi, shiru babu kowa, juyawa ta yi zata fita kenan wayarsa dake saman bed nasa ya fara kara alamar shegowar kira,

Babu ko tsoro ta juyo ta dawo wajen wayar nasa, video call ne, ake kira, My dad shi ne sunan da ya bayyana a kan screen ɗin wayar, ba tsoro bare tunanin me zai je ya zo, kwata kwata ta manta wayar waye zata ɗauka, zuciya ya ɗebeta, shaiɗan ya zugata, ɗaukar wayar tayi, taɓe taɓe ta fara yi har ta yi picking call ɗin, a matukar razane ta saki wayar ya faɗa a kan gadon, hakan ya faru ne kuma sakamakon yin ido huɗu da blue eyes na daddy da ta yi, sai dai kuma bata kawar da kanta daga kallon shi da take yi ba, yana zaune a saman bed nasa, ya yi kewar ɗan nasa ne yasa ya kira, ganin ta yasa ya yi muguwar ɗaure fuska da bai taɓa yin irin shi ba, wani uban tsawa ya daka mata akan ina mai wayar? Me kuma ya haɗa ta da wayar? Cikin tsoro ta fara tattaɓa screen ɗin wayar dan ta katse kiran, hannunta sai kerma yake yi, kirjinta na dukan uku uku, sai yanzu da aikin gama ya rigada ya gama ta tuna da wayar waye ma ta taɓa, hankali a matukar tashe take ta faman katse kiran, sai magana daddy yake yi mata bata amsa ba, da kyar ta samu ta katse kiran tare da kwasawa da gudu ta nufi waje.

Bata zame ko'ina ba sai garden, yadda ta barsu haka ta dawo ta same su, a bakin garden ɗin ta tsaya ta daidai ta natsuwarta kafin ta shiga, bata bari su Areef sun gane abin da ta yi ba, a nutse ta ce mishi Lion baya ɗakin, taɓa Aseef ya yi tare da ce mishi ya je ya ɗauko musu kuɗin su tafi kawai.

Okey ya amsa da shi tare da miƙewa ya nufi cikin gida, shi kuma ya miƙe ya riƙo hannunta suka nufi wajen mota, da shigarsu bai fi 2 mins ba, sai ga Aseef ɗin ya dawo hannunsa riƙe da key ɗin motar da kuma kuɗin, mazaunin driver ya shiga tare da kunna motar, tun kafin su iso gateman ya wangale musu gate ɗin, da gudu ya kutsa hancin motar waje, sai dukan uku uku kirjinta yake yi, addu'a take yi Allah yasa kada Lion ya gane ta ɗauki wayar............ TO SAI DAI MU CE AMIN, AMMA DA KAMAR WUYA DAI.❤️❤️TRIPLETS❤️❤️

E27-28

"Ina muka nufa Areef?" Cewar Aseef, kallon Rimsha dake ta faman kallon titi ya yi, "Sister ina zamu fara zuwa? Super market ko kuma restaurant?". Jin voice ɗinsa sai da ya sanya gabanta ya yi wani mummunar faɗuwa. "Restaurant" ta bashi amsa tana kallon hanya. "On Monday zaki fara zuwa school ko?" Gyaɗa mishi kai ta yi alamar eh, dogon hancinta ya yana faɗin "To kin dai shirya ko?" E ta bashi amsa, shi kam Aseef sai tuki yake yi yana latsa waya, ga shi sai zabga uban gudu yake yi kamar babu gobe, ɗan uwan nasa kuma bai wani damu da ya hana shi taɓa waya yana tuki ba, ya mance cewa nan fa ba Washington DC bane, a Washington DC ne idan aka ga motocin gidansu sun hau hanya, abubuwan hawa ke kaucewa su basu hanya, shiyasa suke yin duk irin tukin gangancin da suke so a kan hanya, dan babu wani abin hawa da zai keta da gabansu, a nan Nigeria kuwa, basu san gidan jajayen wuya suka zo ba, yo ko doka ce a ka kafa ƴan Nigeria irin haka, ai sai sunci uwar dokar sun kora da ruwan mai sanyi daga fridge, koma uban waye yazo wucewa a kan titi ƴan Naija babu ruwansu wucewa zasu yi, idan ya ga dama ya wuce ko ya tsaya matsalar sa ce, su dai sun rigada sun wuce.

Restaurant da suka je jiya, shi yauma suka je, yau dai a nan suka ci abincin, sai kallonsu jama'a suke yi, sun ga masu jajayen kunnuwa, fararen tattabaru, kyawawan gaske, kamar dai ko yaushe sai aikin latsa waya yake yi, yana makale da Heartbeat nasa suna hira, ya hanata ko motsawa, Rimsha da Areef sai zuba hira suma suke yi, cikin natsuwa suka ci abinci, sai dai Aseef bai ci ba, ya ce ba zai iya ba, Areef ne kaÉ—ai ya tayata ci.
Chapter 67 · 0% Book details