Sashe 90
Triplets Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
After some minutes ya fito ya dawo gaban gate ɗin, wani ɗan ƙaramin kwalba da ya ɗauko ya buɗe ya zubawa kwaɗon ruwan dake cikin kwalbar, nan take kwaɗon ta ɓalle gida biyu gate ɗin ta buɗe, daddyn Rimsha ya cika mai sa'a da har Lion ya tsaya tsayin daka a kan case nasa har haka, dan ma dai idan ya ce zai yi abu, to wuya ko akasinta bata sanya shi ya juya baya, muddin ya fara abu, to sai ya kai in da yake buƙata, komai wuya komai daɗi baya sarewa kuma baya gajiyawa, akwai shi da taurin zuciya na bala'i, ga zafa a kan aikinsa da ya sa a gaba, rashin tsoro, tashin tausayi, karfin da kuma zafin zuciya, baya tankwaruwa kamar yadda baya juyuwa, in ya miƙe, ya miƙe kenan har sai in shi ya ga damar zama.
Da kansa ya buɗe gate ɗin sannan ya koma ya shigo da motar ciki, babu ko tsoro a ransa, yana sane sarai akwai masu shigowa gidan, da alama ma ƴan shaye shaye ne, ko kuma wasu criminals, sun mai da gidan gidan maɓoyansu idan suka aikata wani laifi.
A parking space na gidan ya yi parking na motarsa, a nitse ya fito yana bin ko'ina da kallo, tabbas hasashensa gaskiya ce, akwai masu zuwa gidan, dan ga tayan motoci nan alamu sun nuna ma kwana biyu da suka wuce waƴan nan motoci suka shiga, suka kuma fita, da yake akwai taɓo na ruwan sama a jikin tayun ne sai ya bada shati sosai, da hasken screen ɗin wayarsa ya haska yake gani, dan gidan babu wuta, da alama an yanke wutar gidan an cire baki ɗaya.
Ya ɗauki almost 10 mins yana ƴan dube dubensa kafin daga bisani ya dawo cikin motar, da hannu ɗaya ya saɓeta a kafaɗarsa dan yanzu kula da ita zai yi sosai kada wani abin ya sameta, dan ya cinma abin da yake son cin ma wa, trolleynsa ya zaro da ɗayar hannun nasa ya ja zuwa cikin palon, da yake suma kofar palon nasu mai amfani da fingerprint ne, sai ya saki trolleyn nasa ya sanya hannu a aljihunsa ya fito da wata kati, har lokacin tana kwance a saman kafaɗarsa tana zuba barci, ta wahala baiwar Allah tafiyar dare, Lion sai Allah bai tashi yin tafiyar ba sai dare.
Sanya card É—in mai kama da ATM card ya yi a daidai saitin fingerprint na kofar, nan take kofar ta buÉ—e, gyara É—aukarta da ya yi da kyau ya yi sannan ya ja trolleyn zuwa ciki, palon kawai duhu sosai, a haka ya shiga zuwa tsakiyar palon, kafin ya saki trolleyn ya ciro wayarsa ya haska, saman doguwar sofa ya kwantar da ita, sannan ya ja trolleynsa ya haura sama tamkar already ya san gidan, É—akin daddynta kai tsaye ya nufa, komai yana nan yadda suka barshi, da alama masu shigowa gidan basu shiga cikin bedrooms sai iya tsakar gida or palo.
Ƴan dube dube ya yi a ɗakin kafin ya wuce zuwa toilet, wanka ya yi, Allah yasa akwai ruwa sosai, da ruwan sanyi ya yi wankar tasa, ya fito, shiryawa ya yi cikin kayan barci masu kyau da tsada farare tas, ya sanya perfume nasa sannan ya fito zuwa balcony dake tsakanin bedroom ɗin mum da na dad ɗin, kun san irin gine ginenmu a nan, mafiya yawanci balcony ɗaya ake yi wa gida, saɓanin ginin turawa da ko wani bedroom yana da balconynsa, a nan ɗin ma akwai manya gidaje masu irin wannan, sai dai ba sosai bane, to suma dai gidansu Rimsha, balcony babba guda ɗaya suke da shi tsakanin bedroom ɗin mum da dad.
Wajen ya nufa ya tsaya, zafi yake ji sosai shi, shiru ya tsaya yana kallon gidaje guda biyu dake makwabtaka da nasu Rimshar, nazari yake yi a kan waƴan nan gida guda biyun, a tunaninsa dole suna da saka baki a abin da ya faru da family'n Nawazudden, ace suna makwabta duk wannan abin da ya faru kuma basu sani ba? Sannan basu yi jajen ina family'n suka ɓata lokaci guda haka ba? Tabbas akwai sa bakinsu, suna da masaniya a kan komai, koma ace matan gidan basu sani ba, to tabbas mazansu sun san komai, ai Nawazudden ba mutun ne da za'a ce zama da shi babu daɗi ba da har zai ɓata basu shiga damuwa ba.
Ya nitsa cikin tunanin lamarin sai yaga kamar dirowar mutane cikin gidan, da yake dugune babu haske, ba ka iya gani sosai, dan ma neighbors ɗinsu akwai wuta suna ɗan haske gidan kaɗan, tabbas karti ne har guda uku suka diro cikin gidan, tafiyar sanɗo suka fara yi kamar ɓarayi, da ga gani kasan sun sami labarin an buɗe gidan Nawazudden ne, shi ne suka biyo koma wane ne. Da farko bai yi niyar nufarsu ba, ya yi niyyar ya kyalesu su kawo kansu gare shi ne a balcony su same shi, ya ci ubansu a wajen ya watsasu ƙasa, amma tuna Rimsha tana palo yasa ya yi saurin juyawa ya nufi palon.
Dai'dai zai saka kafarsa a benen ya sauƙa izuwa polon, ya ji takun sahunsu, suna haurowa saman benen daga can kasa, to da yake benen kusan guda biyu ne, ɗaya ya kwanto a kan ɗaya kamar cross, yana kuma da ɗan tsawo benen, sai ya fasa sauƙa ya laɓe a wajen kofar ɗakin mum yana jiran su iso ya yi musu kisan mummuke, sai dai fa zuciyarsa na tuna mishi Rimsha da ya bari kwance a palo tana barci, kada su illatata kafin su hauro, duk da cewa suma sun shigo ne a duhu suna wani sanɗa, da wuya su ganta, kuma shigowa da suka yi a duhu sun yi shi ne dan kada wadda yake cikin gidan ya gansu, suma da alama kisan mummuke suke son yi wa duk wadda suka samu a cikin.
Dai'dai lokacin ita kuma ta buÉ—e kofar dakin mum ta fito sanye da kayan barcinta a jikinta, lokacin da ya haura sama ashe ta farka, da yake wayarta na aljihun wandonta ne, sai ta kunna wutar wayar ta haura sama, ta sha mamakin ganinta a cikin gidansu, sai dai bata wani damu ba, dan tasan duk abin da Lion zai yi to da dalili.
Ta fito ne riƙe da wayarta a hannunta tana faman kunna haske torch light ɗin wayar, bata lura da shi a wajen ba, tana kokarin nufar benen ta sauƙa kasa, cikin sauri ya jawota jikinsa tare da sanya hannunsa ya toshe mata baki, dan yasan zata iya yi mishi ihu, kaɗan ne daga halin mata, da sun ɗan tsorata sai ihu, ɗayar hannunsa yasa ya karɓi wayar nata ya tura cikin aljihun wandon kayan barcinsa, tun lokacin da ya jawota jikinsa ta gane shi ne ta hanyar kamshin perfume nasa, sai dai ba zata iya kwanciya a jikin nasa ba, ba kuma zata iya ce mishi ya sake taba. Ta nutsa cikin tunanin me mafita a gareta, zazzakar sexy voice nasa ya daki dodan kunnenta can kasa kasa gently ya furta "Ki kwanta shiru". Ya yi maganar yana zame hannunsa daga bakin nata, da ɗayar hannunsa kuma yana kwantar mata da kanta a faffaɗar kirjinsa.
A wannan lokacin kuma mutanen suka kariso wajen, cikin dabara ya kara yin baya kaɗan da ita, baya ganinsu saboda duhu, amma da lumshe da kuma takun tafiyarsu yake iya irga su nawa ne a wajen, kai tsaye bedroom na daddy suka nufa, sai da ya bari sun wuce sun shiga, sai ya damki na baya ya toshe mishi baki tare da murɗe mishi wuya ya zube kasa gawa a wajen, kasa kasa ya ce mata ta sake shi ta koma ɗakin mummynta yana zuwa, ai ina kara kankame shi ta yi, da Iya karfinta dukka ta rike shi, da ta mutu a hannun waƴan nan azzalumin, gara shi ya kasheta sai ya fi mata sauƙi, ko ba komai ta mutu a hannun masoyinta.
Dama already yasan za'ayi hakan, yasan ta da bala'in muguwar tsoro, dan bincike da ya yi a kan ƴaƴan Nawazudden, babu wanda ya kaita tsoro, ba yadda bai yi ba, fir taki sakinsa, ta ce sai dai su mutu tare, ba shi da zaɓi dole ya goyata a bayan shi, domin ba zai yarda wani abin ya same ta ba, idan wani abu ya sameta shikenan, ba zai sami damar kama wadda ya zo kamawa ba, idan baku manta ba, lokacin da uncle Shitu ya ce su gudu, ya ce kada su yadda su bari a san suna raye, hakan zai nuna muku cewa mai neman hallakar da jinin Nawazudden a yinwace yake da neman Family'n Nawazudden ɗin, to Lion kuma zai yi amfani da Rimsha ne dan ya kama mutumin, ya san da cewa mutumin idan ya sami labarin ga ɗaya daga cikin familyn Nawazudden nan ta zo Abuja, to dole koma a ina ya ɓuya zai bayyana dan ya kashe Rimsha, a nan ne kuma Lion yake son kama shi cike da hujja, shi ne dalilin zuwansu Abuja, to kunga idan wani abin ya sameta, ko ta ji ciwo, ai ba yadda za'ayi ta fita har a san tana raye, har a ganta a kaiwa mutumin labari ya zo farautarta, yanzu mutanen nan da suka zo, basu san suwaye ne suka zo gidan ba, su dai an ce musu koma wanenen ya shiga gidan Nawazudden su kashe shi, aikinsu kenan, su saka idanu a kan gidan, shi ne da suka sami labarin yau wani ya shigo, suka biyu sahu dan su kashe shi, kunji abin da ya faru, mu koma kan labarinmu.