← Book details Triplets Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 121

Sashe 16

Triplets Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tana ƙoƙarin yin magana ta ji Nawid yana ƙoƙarin fitowa daga toilet, cikin sauri ta sallami Umaishar a kan za su yi waya wani lokaci kawai.

Katse kiran ta yi, ta koma ta kwanta tana tunanin mafita, har cikin ranta ta tausayawa Ommun tasu.

Gaban mirror ya tsaya, ya gama shafa mai da perfume nasa, sannan ya juyo ya kalleta, cike da zolaya ya ce "Amarya azo a sanyawa ango kaya". Miƙewa zaune ta yi tana sunkuyar da kanta kasa, da kallo ɗaya ya yi mata ya fahimci akwai abin da ya ɓata mata rai, dan haka sai ya ajiye zancen wasa, cikin natsuwa ya kariso gareta.

A saman bedside drawer ya zauna, cike da kulawa ya riƙo hannunta. "Menene kuma kanwata? Waye ya taɓa ki?" Ƙaƙalo murmushi dole ta yi. "Babu komai yaya Nawid" ta bashi amsa.

"Are you sure?" Ya yi maganar yana ɗan leƙo face nata, ɗagowa ta yi suka haɗa ido, cool murmushi ta sakar masa domin ta tabbatar mashi da babu komai.

"Zaki iya bawa yaya Nawid É—in ki sumbata a kumatu?" Ya faÉ—a cikin sigar soyayya. GyaÉ—a mashi kai ta yi alamar e, sannan ta É—aura da cewa in dai zai sanya shi farinciki zata yi mashi.

Sosai ya ji daÉ—i tare da É—an juya mata kumatun nashi yana murmushi, kirginta sai bugawa yake yi, amma haka ta daure, ta matso da bakinta, cikin natsuwa ta bashi hot sumbata a kumatun nasa.

Kusan a tare suka sauƙe nauyayyar ajiyar zuciya, hannayenta ya riƙo "I really love my wife" "I love too yaya Nawid". Miƙewa ya yi ya koma gaban mirror yana faɗin "To za'a zo a sanya mani kayan ne ko ya ya?". Komawa ta yi ta kwanta "Yaya Nawid ni ai ban iya ba". Girgiza kai kawai ya yi tare da wucewa wajen drawer kayansa.

Kayan da yake buƙata ya ɗauka ya wuce toilet, ita kuma ta gyara kwanciyarta tare da kashe wayarta gabaɗaya, a cikin zuciyarta kuwa, ji take yi kamar ta kira Irfan ta gaya mashi abin da Ommu ke buƙata shi ya bata kuɗin, sai dai kuma ta san mawuyacin abu ne Irfan ya bada kuɗin, domin kuwa ya fi Abbi ma yin fushi da Ommu ɗin, ko ganinta baya son yi, kawai dai dan ba yadda zai yi ne, ta zo a matsayin mahaifiyarsa, sai dai hakuri kawai, amma fa tabbas ba zai bata wannan kuɗin ba, shiyasa ma bata tinkare shi ba.

A haka Nawid ya fito ya sameta, ya shirya cikin kananan kaya, kusa da ita ya zo ya kwanta tare da fara janta da hira, tun tana biye mashi kaÉ—an da kaÉ—an, har ta ware suka fara zuba hira tare da zubawa juna kalman so da kuma kauna.

To a ɓangaren gidan Lion kuwa.

Rana ta ɗage ta yi sanyi, yamma ta yi, misalin karfe 4 zuwa 5 haka, barcinsa yake yi cikin kwanciyar hankali, daga yanayin kwanciyar da ya yi, zaka fahimci a cikin kwanciyar hankali yake, a hankali hankali yake sauƙe numfashinsa, jikinsa na sanye da pajama launin fari tas, kyakkywar dark black curly hair sa, ya zuba mashi har fuskarsa, bai ɗaure ta bane, hakan yasa ta zubo mashi har kan face nasa, ta rufe mashi fuska sosai, sai sheki gashin nan yake yi, abin mamaki kuma gashin nasa, kusan iri ɗaya dana Rimsha, sai dai nasa bata kai na Rimsha nannaɗuwa kamar indomie ba, ita Rimsha nata ya naɗu sosai.

É—an motsawa ya fara yi tamkar mai mafarki, a hankali ya cigaba da juyawa tamkar wani ke juya shi, ya É—an É—auki tsawon minti biyu a haka kafin ya waro dara daran blue eyes nasa waje, wadda kuma farin cikin idanun suka yi ja sosai, da alama barcin bata ishe shi ba.

Slowly ta sauƙe idanun nasa a saman ɗakin nasa, kafin daga bisani ya dawo da idanun nasa saman gadon nasa. Shiru ya yi na tsawon mintoci kafin nan ya mai da idanun nasa ya lumshe su, a hankali ya motsa kyawawan lips nasa ya furta "Why mummy, why are you always coming in my dream with useless thinks? Why are you disturbing my life?! Do you want me to do something for you, so that you should forget about me? Oh what?". Shiru ya sake yi na tsawon mintoci da a kallah za su iya kai minti 30.

A hankali ya miƙe kuma tare da zama a gefen gadon yana mai tsananta tunani akan cikin daddynsu da mummynsu waye ne mai gaskiya? Me yasa shi kaɗai ne mai yawan mafarkin mum ɗin tasu? Meyasa kuma kullun yake yawan mafarkai marasa kyau ne a kanta? Meyasa take zuwa mashi a siffar da ko wani ɗan adam ba zai so ganin wani nashi a ciki ba? Meyasa take yawan yi mashi ikirarin zata kashe shi a mafarkin? Amma kuma a zahiri tana nuna mutuwar sonsu, tabbas da ya ɗauka shirmen mafarki ne kawai, amma yanzu tsawon shekara 15 yana wannan mafarki bai dai'na ba, babu rana ɗaya da zai kwanta ba tare da ya yi ba, dole wannan Mafarki ta sanya shi cikin ruɗani, menene ainahin makasudin ciwon Michael? Sannan daddy yaki gaya mashi gaskiyar a ina ne gidan magicians (matsafa) da ta kai su, yaki gaya masu in da gidan yake bare su binciki gaskiyar lamarin, ya ce masu ya mance a in da gidan yake, amma abin mamaki shi ne ƴaƴanka har guda uku za'a kai su irin wannan gida dan a salwantar da rayuwarsu, amma har ka iya mancewa da wannan gidan? Abin da mamaki gaskiya, daddy bai yi tsufar da zai yi irin haka ba, dan ma shan wine (giya) ne da ya yi a baya ce ta taɓa mashi lafiyar jikinsa, ba dan haka ba, lafiyayyene sosai, dole dai akwai abin da daddy da mummy suƙe ɓoyewa, wadda ba su son ƴaƴan nasu su sani, Lion bai cika son yana shiga hurumin iyayen nasa ba, kai shi ba iyayensa ba, koma waye baya shiga huruminsa, sai idan abu ya zame mashi dole, amma yanzu a ƴan kwana biyun nan yana ji a jikinsa tabbas dole ya binciko gaskiyar da aka binne tsawon shekaru, bai so hakan ba, domin daga daddyn har mummyn nasu ba wanda yake so a cikinsu, hakan kuma yasa bai shiga wannan faɗa ta su ba, ɗan garama Josephine ɗin ya fi sonta ita a kan daddyn nasu.

Shiru ya yi ƙwaƙwalwarsa na tariyo mashi abubuwa da dama dan gane da iyayen nasu, tabbas yana ji a jikinsa mummynsu na sonsu da gaskiya, kuma tamkar ta fi daddy gaskiya, sannan wannan ciwo da Michael ya yi na tsawon shekaru 30, to tabbas daddy yana da sa hannu, domin kuwa yana yawan ganin Musharraf yana magana da Aseef ɗin a kan ciwo, tabbas ba ciwo ce ta tsakani da Allah ba, akwai wata a kasa, to amma babbar abin tambayar a nan shi ne, meyasa ita kuma Josephine ɗin take zuwa mashi a mafarki tsawon shekaru 15, kullun maganarta a cikin mafarki zata kashe su, ba zata taɓa bari su rayu ba, wani lokaci ta yi ƙoƙarin caka mashi wuƙa har sai an riƙe ta, ba mafarki ce da za'a yasar da ita ba, ba mafarki ce da za'a ce shirme ba ce, tsawon shekaru 15 tabbas akwai wata aya da take son isa masu a cikin wannan mafarkin, to menene? Kuma shi ne kaɗai mai yin wannan mafarki.

Can wata zuciya ta ce mashi to ko dai kai ba ɗan su bane, da sauri ɗayar ɓangaren na zuciyar ta amsa mashi da no ba zai yi wu ba, dole kai ɗansu ne mana, dole kai ne cikon TRIPLETS na MICHAEL and JAMES, idan kai ba ɗansu bane ta ya za'ayi kuyi irin wannan muguwar kamanni haka? Ai zancen kai ba ɗansu bane ma bai ta so ba, ta ko'ina ku ɗauko iyayen naku, daga Josephine ɗin har William ɗin, ta kowani ɓangare kun ɗauko su, so dole sune iyayenku, sai dai kawai ku nemo wata hanya kuma ta daban da zaku nemowa kanku mafita.

Har lokacin shi dai yana ji tamkar ba daddy bane mahaifinsa, domin ko kaɗan baya jin son daddyn nasa, kuma ba shi kaɗai ba dukkansu, duk da wannan uban kammanin dake a kan fuskarsu, amma yana jin tamkar dai shi ubansa daban. TO UBANSA DA BAN KUMA?🤔 A'A KU ƘIRA MANA JOSEPHINE TA ZO TA YI MANA BAYANI, TAYA YA YA ZAMA SHI UBANSA DABAN, KUMA SUKE A TRIPLETS? KO DAI BA TRIPLETS NA GASKE BANE? BABBAR MAGANA WANNAN CAKWAKIYA DA YAWA TAKE.

A ɓangaren ita kuma Rimsha, zaune take a palon kasa, har lokacin shigar ɗazun ce a jikinta, abinci take ci cikin natsu, yaya Imran ya saho mata abinci, Mark mugu ya hanata yin girki, wai abincin kasarsu na da wari, ɗan banza ya zo ya zauna mana a kasarmu amma dan iskanci wai abincin mu na da wari.

Cikin kwanciyar hankali take taunar abincinta. Sanye cikin fararen kaya masu shegen kyau Malika ta bayyana a gefenta, wani irin haɗaɗɗen murmushi ta saki. "Malika ina kika shiga kwana biyu?" Dogon numfashi ta ja tare da sauƙewa a hankali.

"Rimsha ke dai bari, ba zaki gane bane, ina can ana ta faman faɗa a kasarmu, kinsan sarkinmu kwanaki bashi da lafiya, to Allah ya yi mashi rasuwa, shi ne fa ake ta faɗa akan waye zai hau mulki, shiyasa kwana biyu na ɓuya, yanzu ma na ɗan leƙo mu gaisa ne kawai, ba jimawa zan yi ba, zan koma saboda har yanzu bamu samu zaman lafiya ba, duk da cewa Yarima Haruna ya karɓi Mulkin, to amma ƴan uwansa sunki yarda, wannna ya ce shi ne zai riƙi mulki, wannan ma ya ce shi ne, aikin kenan, har yanzu hayaniyar da ake yi kenan.

Ita dai Rimsha almara take É—aukar abin, ji wai harda wani sarkinsu ya mutu ana yaki, to ko a gidan uwar wa suke yakin Oho? Ko dai a saman iska suke yakin ne? Sai tambayar kanta take yi, saboda yarinta irin tata.

Ganin haka yasa Malika ta kawar mata da wannan tunani "Ina angonmu Rimsha?."
Chapter 16 · 0% Book details