Sashe 62
Triplets Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Bayan sun fitar da ita zuwa saman gadonta ne ita ma Jehan É—in ta fito, dama sai da Zinariya ta kira wata wai tattabara tazo ta tayata fitar da A'isha, to suna fitar da ita tattabara ta koma bakin aikinta, ita kuma Zinariya ta tasasu a gaba tamkar wata uwarsu tana basu umarni kamar haka.
"Wlh ko da gigin wasa, idan wata ta kuskura ta sanar da hajiya abin da ya faru da ku, to sai na lahira ya fi ku jin daÉ—i, shekarunku sun yi kaÉ—an da su É—auki azabata, zan iya kashe rayinya wlh".
Cike da confidence babu tsoro ko kaÉ—an a tattare da ita Jehan ta mai da mata da martani kamar haka "Saboda ke ce uwar mu ba, ai dole ki saka mu a gaba kina wani bamu umarni, ke bari ki ji in gaya miki fa, a bariki babu uwa, a bariki babu babba, duk wanda ya taka, kai ma ka taka shi, ko da kuwa shi ya koya maka bariki, kina tunanin bansan komai dan gane da bariki bane? To idan haka kike tunani ki canza, kowa babban kansa ne a bariki, kowa ga shin kansa zai ci, bari ki ji nayi yawo a Media fiye da tunaninki, sannan ke daga ganina baki ga kalar jahila ba, babu wadda ta isa ta zana mini ga abin da zan yi, tun asalina abin da nayi niya nake yi, to kuma a haka zan rayu a cikin gidan nan, da kuma kike maganar zaki kashe mu idan muka faÉ—a, an gaya miki rayukanmu a hannunki yake ne? Babu wanda ya isa ya kashe wani har sai kwanansa ya kare, duk wanda kika ga an kashe, to kwanansa ne ya kare, ko ba'a kashe shi ba zai mutu a wannan lokaci, sai maganar azabtar damu da kike yi, ke baki san mu kafuwar Allah bane? Duk azaban da kuka yi mana, kuka kullemu a cikin toilet babu ci har na tsawon kwana uku da wuni É—aya, kuka buÉ—e mu babu abin da ya same mu, daga nan ya kamata ki sani kafuwar Allah ne ba na É—an adam ba, sannan kina da wuta da aljanna ne? Tun da baki da ko É—aya ai shekenan duk wani azabanki na banza ne, ni ba zan gaji da gaya miki ki ji tsoron Allah ki sani akwai lahira, akwai ranar da zaki biya duk wani abin da kika yi, ranar da babu uban da ya isa ya tare miki, kuÉ—i ba zasu tsinana miki komai ba a wannan rana, kina da sauran lokaci da zaki iya tuba, to kada ki bari dama ya kubce miki, sai magana ta karshe, wlh zaman ki lafiya a gidan nan shi ne ki dai'na nuna mana wani izza kamar ke kika haifemu, idan ba haka ba, na yi miki alkawarin wlh ni zan sanya ki ki fara danasanin zuwanki duniya a rayuwarki, da ni kike magana JEHAN NAWAZUDDEN SALMAN SULTAN, ni kai'na wani lokaci tsoron kai'na nake ji, dan haka zaman ki lafiya ki fita harkata, idan kuma kika ki, wlh na juyo muka sanya kafar wando É—aya, Allah sarki, sunanki sorry". Duk wannan magana da Jehan take yin shi fa, bala'in tsoro ne cike fal a ranta, kamar yadda kuka sani ne, kwarin gwiwar a iya baki ne kawai, ita dai kawai ta yi Imani da cewa duk tsoron mutun da kake ji, idan ka dake ka nuna baka shakkarsa ba kuma ka tsoronsa, to tabbas sai fara shakkarka har ma ya ji tsoron naka, kuma haka ne, rayuwa idan ka nuna kana tsoron abu, to tabbas yafi tsoratar da kai, amma idan ka dake, ka nuna jan wuya, to fa ba makawa zai fara tsoronka, zai yi ta tunanin ko ka taki wani abin ne.
Duk rashin kunya irin ta Zinariya yau dai sai da ta ji tsoron Jehan ya kamata, mamaki take yi tare da tunanin anya ba wani abu Jehan ta taka ba kuwa? Abin ya fara É—aure mata kai, shiru ta yi bata sake ce da su komai ba, wannan shi ne gaba ma da gabanta.
Suna a wannan hali Yar gwal ta shigo ɗakin ɗauke da abinci kala biyu, na Jehan daban, nasu Adiva daban, nan ma ba karamin dirama suka sha ba, dan Jehan ta ce wlh idan sun ga ta ci abinci, to tare da su Adiva zata ci, ba zata ci wannan abincin da suke bata ita kaɗai ɗin ba, domin kuwa tun da suka kafe sai taci shi tun farkon zuwanta, daga nan tasan tabbas akwai wani abu a cikinsa, ba haka kawai ba, to kuma ba zata ci ba, ba yadda basu buga ba, ta kafe ta ce sai dai yunwa ya kasheta, ƴar gwal har ta fara yunkurin ƙoƙarin zata dake ta, Zinariya ta dakatar da ita, ba dan sun so ba, sai dan saboda kada yunwa ya kashe Jehan Hajiyar daɗi ta sanya su biya, haka suka hakura suka fita da abincin Jehan ɗin, suka ce taci nasu Adivar, hakan kuma ya kara tabbatarwa da Jehan tabbas akwai abin da suka zuba a ciki, idan da babu komai ai da zasu juye musu abincin ne su haɗa musu su ce su ci, amma sun koma da shi, to akwai wani abu a kasa. Allah dai ya kyauta.
Suna fita su Adiva suka fara cin abincin hannu baka hannu kwarya, bayin Allah sun wahala, ita ma Jehan É—in hannu baka hannu kyarta ta fara cin abincin, jolof rice ce, ta ji kayan haÉ—i ba karya, ko wanka basu tsaya yi ba, sai da suka kusan cin ye abincin, Jehan ta É—auki tray É—in ta dawo kusa da A'isha dake kwance tamkar babu rai a tattare da ita, dan ta bata abincin a baki.
Zama ta yi a gefenta tare da fara ambatar sunanta a nutse, "A'isha, A'isha". Shiru bata amsa ba, taɓata ta fara yi tana mai cigaba da ambatar sunanta, nan ma shiru bata amsa ba, a razane ta fara jinjigata da karfi tana kiran sunanta, da sauri suma su Adiva suka yi kanta dan su ga menene ya same ta, ina shiru bata ko motsi, da gudu Jehan ta diro kasa daga saman gadon ta nufi waje.
Bata zame ko'ina ba sai office É—in Zinariya, zaune ta iskota saman kujera tana shan lemun kwalba mai sanyi, a ruÉ—e ta gaya mata abin da yake faruwa da A'isha, babu ko tsoron Allah a cikin zuciyarta bare tausayi ta ce "To ina ruwana dan bata motsi? Ta mutu mana idan ta ga dama". Hankalinta kwance ta yi wannan magana.
Tsabar bakin cikin Jehan bata san lokaci da ta yi wani irin mahaukacin kukan kura ta damko wuyar rigarta ba, idanunta sun rufe, rashin imanin gidan nan ya wuci tunanin mai tunani, zuciyarta tafasa yake yi tamkar zai fasa kirjinta ya fito waje, ga idanunta dama sun kara girma sabida rama, yanzu kuma sun yi jawur kamar wuta, zarosu waje ta yi sosai tare da shaƙe wuyar Zinariyar da iya karfinta na karshe, cikin tsawa ta ce "Tabbas idan A'isha ta mutu wlh ba zan barki ba, baku da imani, baku da tausayi, me A'isha bata yi muku ba a gidannan?, jikinta fa kuka sayar kuka sami kuɗi, yau an wani gari tana kwance rai a hannun Allah ne zaku ce babu ruwanku da ita? Wlh kukam ko kun tuba Allah ba zai barku ba, domin nasan akwai yara da dama da suka mutu a dalilinku, to ku sani Allah baya yafe hakkin wani, iya laifin tsakaninku da shi kawai yake yafewa, to taya zaku nemo yafiyar waƴan da suka mutu? Wlh ku bakaƙen azzalumai ne, macuta, makirai, kuma kafurai, sheiɗanu kai komai da komai ma, da izinin Allah sai Allah ya kawo karshenku tsinannu, baku babu ganin Annabi, wlh mutuwar walakanci zaku yi, ko kare sai ya fiku mutuwa mai daraja, Allah ya tsine muku albarka, ya kwashewa iyayen da suka aifeku albarka, da haihuwar irinku gara ɓarinku, shegu mugayen iri kawai". Tana magana tana hawaye wani nabin wani, ji take yi wani mahaukacin jiri na ɗibarta, saboda tsantsar ɓacin rai, da alama kuma ta fita a hayyacinta, dan wannan surutai da take yi bata san tana yinsu ba, abin ya yi mata muguwar ciwo, dama kun san halinta, zata iya ɗaukar komai banda cin zalin wani bawa, bata ganin za'ayi rashin adalci ta bari, kuma hakan ne yazama sanadiyar shigarta kaddarori da dama, saboda taimakon Hanan ta yi wa FAROOQ karyar ta yi recorded nasa, daga nan ya turo a kasheta, hakan ya yi sanadiyar zuwanta wannan gida, ta shiga bala'i kala kala a kan taimakon wasu, kun san da hakan!.
Da Iya karfinta na ƙarshe Zinariya ta sa hannu zata kwaci wuyarta, amma ina ta kasa, sabon jini da tsohon jini ba ɗaya ba, duk ta ragwargwaɓe maneji take yi dama, Jehan tazo tana ƙokarin karisa ta.
suna cikin wannan hali sai ga Æ´ar gwal, ganin abin da yake faruwa yasa ta kariso ciki da gudu ta yi kansu, tana zuwa ta kwashe kafafun Jehan ta zube kasa Zinariya ta bita ta faÉ—a kanta, dan kuwa taki sakin wuyar tata, Jehan akwai taurin rai da taurin kai ga taurin zuciya over.